shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday 11 January 2017

Ashe kishiyatace


baby afreen: 👒👒👒👒👒👒 ~*Ashe kishiyatace*~ بسم الله الر حمن الر حيم *A short story* _in dedication to_ 💖 *Abba gana*💖 *01* "Sadeeq karka yarda raina ya baci akan batunan".. "kiyi hkr mama" mama na kaiwa nan tayi tsaki ta shige daki abunta..busar da isaka sadeeq yayi ya miqe yana shafa gashin kansa harya fice... *Sadiq Ajmad shine asalin sunansa..sadiq likitane kwararre ..mahaifinsa bashida wani kudi sosai sedai ace masha Allah...Asalinsu 'yan garin katsina ne kuma sunazama acikinta..sadeeq saurayine kyakyawa..* Tin tasowar sadeeq mama take adduar taga danta ya samu mace kyakyawa ya aura acewarta ya da nta yake kyakyawa hk ma matarsa zata zama kuma yar gidan masudashi ba talaka ba... 👒👒 Zaunevsadeeq yake a office dinsa sanye da labcourt yanata juyi akan kujerarsa da ka gansa kasan ya zurfafa a tunanin da yakeyi..ahankali abokinsa hydar ya turo kofar da sallama amma shiru ba a ansa ba...shigowa yayi yana kallonvabokinnasa ya girgiza kai ahankali ya nufi inda yake ya masa tafi a fuskaa afurgice sadeeq ya miqe.. "mstwvhaba hydar meye hk" "yi hkr naga kayi nisane meke faruwa" "kaidai bari kawai yaushe ka shigo?" murmushoi hydar yayi "banjima ba ynxu na shigo...me yasameka ne?" "wlhi kaima kasan xancen baze wuce mama ba..ita dole dole sena aure 'yar kawarta" "🙊Kardai kace min akan xancen Husna ne?" "mtsw kaidai kabari kawai" "toh inbanda kai inna laifin husna?" "mtsw nifa kasanbasanta nake ba bata min babe kai" "Dallahni kaisheni da tsakikamar wanitsaka" tsaki sadeeq ya kumayi hydar ma hakan yayi... "Allah ya shiryeka....kawai ka yarda kaaure husna wlhi ni kan naga yarinyar nada hankali" "Hm ai sekuma kayi kanka akehji" janyo takardun gabansa yayi ya cigaba da dubasu.. 3days later👒 "sadeeq kaje kun gana da husnar kuwa?" "a'a mana dama innason innaje nadawo sena je ndw" shiru mama tayi kamar bazatace komai ba "shknan bkmnaji Allah ya dawo dakai lafiya" "ameen insha Allah gobe zanwuce ndw jibi" "toh Allahya bada sa'a..." amsawa yayi da ameen ya miqe ya fice ya nufi dakinsa** *washe gari* ~Dutsin-ma~ *Kauyen bahuna* Tafe sadeeq yake cikin motarsa da kauyen daqyar motarsa ke wuce wani gun sbd hanyar ba kyau saukinsama lkcin rani ne da da damina ne baze iya wucewa ba .. yana shiga ya soma tmbyr gidan me anguwa akamuna masa...yana zuwa ya tarar da mutane a kofar gidan zaume..sallama ya musu tare da miqamusu hannu suka gaisa... "sedai ban shaidaka ba" cewar me anguwa murmushisadeeq yayi tare da fadin "nine likitan daaka turo sunana sadeeq" "oh masha Allah naganeka sannuda zuwa" kara gaisawa sukayi da su daidai nan wasu "yan mata guda uku sukazo wucewa suna hira 'Kai ku kalli wani saurayi can kyakyawa" acewar alawiyya dasauri shatu da dije suka jiya suna kallon gutin "kaiii amma gsky yana da kyau" turo baki shatu tayi tare da fadin.kanku akeji alawiyyace ta soma fadin "dan xakiyi aure shine inkinga abu yamiki baza kice yayiba?" "toh akan mezance yayi?"aure nafa saura satibiyu" hira sukacigaba dayi har suka wuce sadeeq kuwa me anguwa yasa aka rakasa masaukinsa.. *Night* tsaye shatu take da saurayinta iro suna hira "shatu ykmt in akwai abinda kike buqata kifadamin dawuri kinsanlkci na ta tafiya" "toh shknan innaje gida zanduba insha Allah gobe zanfadama in akwai" nanfasukai hirarsu kafin daga bisani sukayi sallama tashige gida.. dikabinda suke sadeeq na tsaye yana kallonsu yana murmushi shikadai..shikamarayuwarsa rayuwar kauye ns birgesa sosai shiyasa baya gajiya da zuwa gurate irin wa'anan saboda suna sashi nishadi.... bama kamar yadda saurayi dabudurwa ke hira abin nabasa shawa'a...yana cikin wannan tinanin husna ta fado masa arai tsali yayi ya koma inda yasauka ransa dik ba dadi.... 👒👒 Da safe safeeq ya tashi yayi wanka ya shirya abinsa fitowa yayi ya dan zagaye gari yana tafe yana murmushinsa me qayatarwa .. harda pics ya dinga dauka dik abinda yaga ya birgesa... Misalin karfe 12pm sadeeq ya musu sallama akan nanda sati biyu ze dawo zrje yabadavreport din abun da yaxo yi.. godiya sukamasa mutane suka dinga kallonsa kyauta ya musu sosai kafin ya tafi sunata masa godiya.. *katsina* yana isa gida ya tadda mamazaune a palo tana waya saurarawa yayi yaji me take fada... "eh gaggo suwaiba auren nmranarjuma:ah mezuwa insha Allah" bejime goggo suwaiba taceba mama ta amsa da "shknanzeji Allah ya kawoku lfy" katse wayartayi tana murmushi daidai nan sadeeq ya shigo da sallamarsa cike da fara:a mana ta ansa "ahhh sadeequ yaushe kadawo" "ynxu nashigo mama inna ummi?" "ummi taje rabon katin biki wa'andaza agayyata" "mama bikin wa za ayi ne?" "kajika da shirme naka ne mana ykmt ka huta kaje ku gana daita kaji abindatake buqata" kamar amafarki yaji zancen kansa na sarawa ya miqe zefita zeji dakinsa mama ta kuma fadin "sadeequ bakaji me nace bane?" "naji mamazanje insha Allah" "kokaifa jeka Allah yama albarka" amsawa yayi da ameen yafice yanufi dakinsa kansa kwai yakeji yana sarawa.. 👒 [12/26/2016, 9:53 PM] baby afreen: 👒👒👒👒👒👒 ~*Ashe kishiyatace*~ *A short story* _In dedication to_ 💖 *Abba gana💖* *02* Washe gari da safe sadeeq yashirya ya ma mama sallama ya nufi gurin aiki...direct office dinsa yawuce yana shiga hydar yabi bayansa... "yan tafiya shine andawo bako dan kira?" murmushi sadeeq yayi tare da fadin "Kabari kawai jiya nadawo a gajiye ne shiyasa" "ok, tohya kaga kauyen?" "Zancen kauye kabari zan baka lbr...kajiwani batu inna dawowa wai aurena da husna saura sati daya" Xaro ido hydar yayi cike da mamaki... "kaiii haba wasa kake ko?" "wlhiinna dawowa naji mama na waya dasu goggo suwaiba ni banmasan yazanyi ba" "cab di..hkr zakayi kayi biyayya kawai kaje ku sasanta kanku" "mtsw wlhi basanxuwa nake ba dandai mama ne kawai zanje mumushi hydar yayi tare da janyo file din dake gaban sadeeq... lumshe idanu safeeq yayi ya jingina jikin kujera yana murmushi tabosa hydar yayi 'ya akayi ne? cewar sadeeq wanda har ynxu idanunsa na lumshe "murmushin me kakeyi ne?" "kawai kauyenan nake tinawa wlhi dadin xama" "hhh lallai sekakoma can ka tare" dariya sukayi dikkansu cike da nishadi suka cigaba da hira... _7:25pm_ Tsaye hydar yake jikin motar sadeeq daidai nan sadeeq dinma ya bude motar ya fitoh... yana fitowa husna ma ta fitoh cikin shigar atamfa ta yafa gyalenta... cike da fara'a ta karaso inda suke tayi sallama suka amsa hade da gaiduwa... "ya sadeeq sannunku da zuwa" "yauwa" ya amsa ataqaice murmushi hydar yayi "bari nadan baku wuri inkungamanadawo" murmushi husna tayi tare dafadin toh ...shilo sadeeq bako alamar murmushi afuskarsa...juyawa hydar yayi ya basu wuri... shiru ne ya ziyarcesu nadanlkci sadeeq ne ya katse shirun da fafin "dame damevkike buqata?" "eh toh inna buqatar kudi sbdvevents din da za ayi" "event din har nawa xakiyi?" "ko guda hudu hk dun isa" murmushin mugunta sadeeq yayi😏 "dama can kin shirya wa bikin ko? zaro ido tayi cike da mamaki "haba ya sadeeq wani irin xance ne wanan inxaka bani kudi ka bani " :"nawa kike buqata?" "dubu dar*****? "cabdi karma ki qarasa danbazan kashe kudi na a auren da banaso ba" "toh wlhi ni se ka bani " zaro ido yayi yana kallonta aransa yana fadin " Lallai yarinyarnan bata da kunya shi zata dinga fadawa hk tinkan ayi auren ma" afili kuwa tsaki yayi tare da fadin "bazan bayarba wa anda suka samiki rai su baki ni kinga tafiyata ba" jiyawa yayi ya shige mota da niyar inya soma tafiya yakira hydar yaji inda yake..itako husna tsaki tayi tashige tana yan maganganunta... bintavyayi da kallo daga bisani yavgirgiza kai yana fadin "Yau naga takaina mama ta hadani da wannan yarinya *jangwan*😝" Shigewa yayi motar yadau wayarsa xe kira hydar jin anna buga dayan glass din gefen seat din murmushi yayi yasa hannu ya bude masa yashiga.. "ya harkun gamane?" "mtsw kyaleta kudi takeso kuma ni bazankashe kudi na a auren da banaso ba" murmushi hydar yayi tarevda fadin "Wai kai meyasabaxaka hkra ba kawai ka bata tayi abinda ya kmt" "toh kai inka matsu ka bata mana zaka wani takurani" shiru sukayi dikkansu har yakai hydar gida ya saukesa shima ya nufi gida... Dasalama ya shiga palo ummi da mama ya tarar zaune ... "Inna wuni mama" "lafiya lau sadeeq harka dawo?"? "tih masha Allah" "ya sadeeq sannu da zuwa" "yauwa ummi ya gidan" "lafiya lau yaya" "hk akeso barivna shiga ciki" "sadeeq kaje kungana da asama'u kuwa" "eh mama daga can ma nake" washare baki mama tayi tare da fadin masha Allah kaje babanku na nemanka... amsawa yayi da toh ya nufi dakinsa aransa yana fadin "narasa me mana tagani agun husna hm Allah dai ya sa hkn shine mafi alheri" ansawa yayi da ameen ya cire kayansa..watsa ruwa yaje yayi ya sauya kaya kafin ya nufi dakin baba... dasallamarsa yashiga baba yaamsa masa..zaune yasamu baba yana jin radio.. "ahh abubakari harka dawo"? "eh bababandade dashigowa ba" "toh madallah dama sonake naji inji dai kagama gidan naka ko?" "eh baba nagama painti ne ya rage shima gobe insha Allah zansa ayi* "toh maddallah Allah yama albarka" amsawa yayi da ameen sunsha hira sosai sewajan karfe 8:45pm kafin sadeeq yabar dakin baba ya nufi nasa... 👒 *Husna* Can kuwa husna nashiga gida umma dake zaune tana kallo hanan na gefenta... raibace ta samu guri ta zauna "husna ya akayi ne?" "umma wai kawai se ace hk xa ayi bikinan ba ko event" "inji ubanwa?" "ya sadeeq mana wai baze bani kudi ba" "be isaba dan ubansa uwar tasa zankira bannidasu" "wlhi anty husna wannan yaya sadeeq din ya fiye girmankai" acewar hanan tsaki husna tayi tare da fadinbanni dashi zan rage masa shi... tana kaiwanan suka jiyo sallamar yaya haneef... dasallamarsayashigo suka gaishesa ya ansa shima ya gaida umma xama yayi alamun ya gaji...yana fuzar da iska "husna dan Allah dan dafamin gwaten doya shinake marmarinci" acewar ya haneef turo baki husna tayi tana maida hankalinta ga tv "ke husna bakiji me nace bane" miqewa tayi tana buga qafa tanufi hanyar daki tana qunwunai... "gsky ni ban iya girki ba...baga inna me girki can ba kaje tana" fusace hannef ya miqe ze bita umma ta tsayar dashi tare da fadin "xonankarka takuramin 'ya kaje ga inna canakitchen kace tadafa ma" "haba umma ya zaayi ace yaranan su zauna basu iya komai ba sedai a musu ahaka husnanzatayi aure? "Inna ruwanka innace bakai zata aura ba?toh wuce kaban wuri yarana yanhutu ne" afusace haneef ya fice ya bar palon umma tading masif tana fadin "yarana yanhutu kuma husnar dakake fada dame aikinta zata tafi yauwa" ahk tayita masifa hartayi shiru dankanta... 👒 [12/28/2016, 2:17 PM] baby afreen: 👒👒👒👒👒👒 ~*Ashe kishiyatace*~ _In dedication to_ *💖Abba gana💖* *03* Zaune mama take wayarta tasoma ruri dasauri ta daga ganin sunan umman husna daya bayyana akan screen din "Assa** "Maman ummi kinajina ko? "Eh innaji amma kya tsaya mugaisa ko?" "bana buqatar hkn dama inna infada miki ne ki jawa sadeeq kunne yazo ya bama husna kudin dazatayi abubuwan daya kamata ahk za ayi bikin?" hkr mama tashiga bawa umma kafin tasaukosuka gaisa cike da fara a daga bisani sukai sallama. Zaune mama take tsakar gida tana jiran fitiwar sadeeq...ummi ce ta fitoh dashirinta na mkrnt "umma na tafi " "toh sekindawo Allah ya miki albarka " amsawa tayi da ameen ta fice abinta...ba afi minti biyar ba sadeeq ya fitoh shima cikin shirinsa... tsugunnawa yayi kusa da mama "Inna kwana mama" "daban kwana ba zaka ganni?" "mama laifin me nayi kuma?" "me ya hanaka ba husna abinda take buqata kaje ka bata tinkan raina ya baci" "mama ba kudi a hannu na ne ga aiki gida annayi ga kuma lefen da ake hadawa abubuwan sun minyawa" nunfashi mama taja tare da fadin "Sadeequ" "ya amsa mata da ameen" "kayi hkr kaji kaje ko nawane ka lallabaka bata kaji?" gyada kaiyayialamun eh yamiqe yanafadin nizan tafi albarka mama ta samasa kafin ya tafi... 👒 Misalin karfe 8 sadeeq ya gama shirinsa ze tafi gida ransa bace ya shiga mota beko tsaya ko inna ba se qofar gidansu husna yanaxuwa kuwa yayi sa a hanan ta fitoh ya turata ta kira masa husna ba musu ta koma tanata wani karairaya murmushin takaici yayi yarinya qarama da ita... ya kusan minti goma tsaye agurin bata fitoh ba ransa dikinda yake battace ne...juyawa yayiya bude marfinmotarsa yajiyo muryarta tana anbatan sunansa...juyawa yayi ya shaqo wuyatan ta ya hada da jikin motarsa "ke nikika rainawa wayau zaki shanyani a waje?" daqyar ta somamgn samasama "toh bakasangidan akwai mutane bane?kasakeni akwai zafi" "bazan sakeki ba tin ynxu kinakai qarata gun mahaifiyata ko kinaso ki hadani da ita ko?" "nifa ba*** bata qarasaba yasa dayan hanunsa ya bige bakinta daga bisani yasaketa motarsa yabude ya cito bandir din yandari biyar ya bata karba tayitana murmushi... wani irin sansane takeji yana shiganta arayuwarta tana mutuwar san sadeeq kallonsa tayi tana murmush "kekuma meye hk?" murmushi ta kumayi "kawai inna sanka sosai bazan iyajure kamin kishiya ba" tana kaiwa nan ta shige gida da gudu shiko binta yayida kallon mamaki "lallai yarinyarnan ta rainani" dagabisani kumaseya soma dariya shi kadai ahaka yashige motarsa yana driving yana tinazancen husna 👒👒 Abu kamar wasa akwana atashi ba wuya snyi prgms amma ba ko daya wanda sadeeq yaje ranar juma'ah bayan anyi sallar juma'ah aka dauraauren *Abubakar sadeeq* da amaryarsa *Asma'u husna* skan sadakinera dubu dari...masha Allah bikin yayi jama'ah sabd sadeeq ya kasance meson mutane dan hk bikinsa ma sai masha Allah.... Bayan anyi sallahr magrib akazo daukan amarya nasiha aka mata sosai hydar shine kangaba sbd shine abolin ango... gidan iyayen sadeeq aka fara kaita can suka tarar da sadeeq aka hada hardashi aka musu nasiha sosai amma abun manakitindaaka taho da amarya ba allamun kuka ko hawaye sema in anna hira a mota tayi dariya.. goggi suwaibace ta kasa hkr tasoma fadin "Wai ita wannan amarya bata kuka ne se dariya" gabadaya sukasa dariya harda ita husnar kawarta ce hafsa dake gefe tasoma fadin "goggo karki damuqawar tamu jaruma ce ai" tabe baki goggotayi ta tsayatana kallon ikon Allah amarya ta yaye gyale anna hira... kusan rabin hour ya daukesu kafin suka isa gidan...lullube mata fuska sukayi aka fita da ita dik da gidan na cike da mutane hkn be hana husna ganin gidan nata ba gidan yayi kyau sedai masha Allah murmushi kawai husna keyi har aka shiga da ita.... bayan ankaita da mintina aka rako ango fuskarnan tasa babu alamun fara'a atattare da ita...hk yazauna kawayen amarya da abokansa suka gama surutu suka fita bin bayansu yayi dan yimusu rakiya...nanfa suka dinga zaulayarsa har sukasa sa dariya sosai... husna kuwasuna barin dakin ta niqe dasaurijakar dake gefenta ta dauka ta ciro turaruka da wata night gown ta nufi toilet cikin sauri.. Sauya kayanta tayi kafin ta tafitoh sadeeq ya shigo ganin bata dakin yasa ya juya ze nufi dakinsa domin watsa ruwa... daidai ya murda handle din qofar ta fitoh "ya sadeeq" shine abinda tafada dasauri ya juyo yana kallonta cike da mamakin ganin shigar dake jikinta bakodan kwali akanta se famanfari takeda ido zancen xuci yasoma yi yana fadin "Ance amare nada kunya amma banda tasa itakan bata da ko alamar kunya" girgiza kaiyayi ya juya yana murmushin takaici dasauri ta nufi inda yake har tana tuntube da jikin gado ta riqo hanunsa "Husna lafiyarki kuwa?" "toh ya sadeeq yinwa nakeji" "baga kitchen can bakije kidafa abindakikeso" zaro ido tayitana kallonsa "Cabdijan" "meyafaru kuma?" "nifa kasanba girki na iya ba kuma innace cewa akai kaza ake kawowa amarya" zaro ido yayi yanakallonta lallai yaqara yarda husna bata da kunya har ynxu yarinta na damunta... "husna in bakiiya girki ba waxe dafamin abinci" "ohhh karka damu bayan mungama cin amarcin mu umma tace zata samomin me aiki" "toh a kwananki waze dinga girki?" "Dagacan gidanmu inna zata girka hannan zata kawo" dariya ta basa be iya cewa komai ba yafizge hanunsa daga riqon da tamasa ya fita abinsa.. tanaganin hk tayi tsakitm tasamu gefen gado tazauna... 👒👒 [12/30/2016, 10:24 AM] baby afreen: 👒👒👒👒👒👒 ~*Ashe kishiyatace*~ *A short story* _in dedication to_ *💖Abba gana💖* *04* Yana shiga dali toilet ya fada ya watsa ruwa yana fitowa ya shirya cikin kayan barcin sa kwanciya yayi akan gado zancen husnane ya soma dawo masa *"nifa kasanba girki na iya ba kumainnace cewa akai jaza ake kawowa amarya"* wanga zance na husna na husna na basa dariya sosai nanfa wani tinani ya fado masa "Kardai ace dgsk ne husna bataiya girki ba..🤔.lallai kywa da anga shirme🙊" kamar wanda aka mintsila ya miqe ledar dake saman dressing mirror ya dauka yayi hanyar qofa fita yayi be tsaya ko inna ba se qofar dakin husna ahankali ya murdahandle din ya shiga xaune bakingado ya sameta tana faman chatting harya dhiga bama tasani ba kusa da ita yaje ya zauna ya girgiza kai ganin ita kadai se dariya takeyi.. Fizge wayar hanunta yayi dasauri tadago da niyar yin masifa ganinshi yasa ta miqe da sauri "meya dawo dakai dakina?" Xaro ido yayi yana kallonta da mamaki "innace innada ikon shiga ko inna a gidana?" "eh naji ynxu dai ya sadeeq wlhi yinwa nakeji sosai" bece komai ba ya mika mata ledar karba tayi tare da masa murmushi ta juya tana tafiya kamar wacce kwai ya fashewa aciki... dariya yayi ya kwanta abunsa ya dauwayarsa harya kunna data sekuma ya kashe ya soma game din zuma abinsa Itako uwa gayya zama tayi taci me isarta ta fadi alhamdulillah kafin ta kwanta... kwanciya tazoyi taga sadeeq a kwance bata raivtayi tasoma mgn "ya sadeeq ka tashi kafita barci nakeji" "ni annan zan kwana gwara ma ki kwanta abinki" miqewa yayi ya nufi toilet tabisa da kallo...har yayi alwala ya fitoh tana tsaye a inda ya barta... "husna kije kiyi alwala kizo muyi sallah" ba musu ta nufi hanyar toilet dinbata wani jima ba ta fitoh... hijab tadauka cikin wani qaramin akwati dake gefe tasa ...darduma suka shinfida ya musu jagora... Suna idarwa ya musu addu'a , shi ya fara miqewa ya nufi kan gado...cike da masifa ta nufi inda ya kwanta... "gsky ya sadeeq kazo kaje dakinka" "toh ni akusa da matata xan kwanta" juyawa tayi zata bar wurin dasauri sadeeq ya yanyota ta fada jikinsa... "Nikasaleni wallahi" "inna zakije inna sakeki?" turo baki tayi tana fadin palo qara riqeta gam sadeeq yayi nanfa salo ya canja... *na tsaya kwaso labari 💖Abba gana💖 ya janyo ni...wai is not my hurimi...kumafa hakane🤔😝* ~washe gari~ Tindasafe sadeeq ya tashi ya makara yin sallah ganin husna nata sharar barcinta ya miqe ya nufi dakinsa....yana zuwa cikin sauri yayi wanka yai alwala yana fitowa yayi sallah abinsa... Miqewa yayi ya nufi dakin husna da zumar tashinta yana shiga daidai nan ta toh daga wanka ....hararsa tayi ta wuce dressing mirror taja kujerarta tazauna... Murmushi yayi yamatso kusa da ita kusa da kunenta ya tsugunna yana fadin "Morning husna" batace komai ba illa dagowar datayi ta kallesa... rungumota yazoyi dasauri ta kauce "nikam banaso" Dariya sosai ya mata itako idanunta dik sun ciko da kwalla "shknan naji...ynxu ya za ayi da bedsheet din?" "kai zaka wanke mana kasan ni bawanki nake ba dan banma iya ba" sadeeq da tinda tafara zancenta ya sake baki yana kallonta ya furta "cabdijan" bekuma cewa komai ba yaje ya yaye zanin gadon ya nufi toilet yana shiga tayi tsaki "Sekace ance baiwa aka kawo ma" tana gama fadan hk ta miqe ta bude wannan akwatin ...riga da skt english wears tasa ta yafa gyalenta wayarta ta dauka ta bude akwatinta ta dauko wani india film na season *king of hearts* Zama tayi tasoma kallon film din tana chatting...kara door bell taji tada pausa tamiqe ta bude...ummi ce dauke flaks na abinci..... "Inna kwana anty husna" ummi ta fada cike da fara'a... tabebaki husna tayi "lafiya" "anty dan Allah kama min da guda daya" Tsaki husna tayi ta juya abinta "dakika taho dasu waya kama miki? kuma wallahkika zubarmin sekin kwashe kin gyaran palona" tana kaiwa nanta zauna tasa play tacigaba da kallonta.....ummi kuwa tafiya tasomayi ahankali ahankakai..hartakai wajan dinning din gurin saukewa ta kasa.. "Anty husna dan Allah xolki dan saukemin" tsaki husnata kumayi "kikira wacce ta dora miki ta sauke miki" wangazancena husna ya batawa ummi rai batace komai ba tasoma qoqarin saukewa dadai nansadeeq ya fitoh riqe da zanin gado a hanunsa alamun yagamawankewa dasauri ya nufi gurin ummi yasoma saukmata kulolin gaishesa tayi cike da fara'a ya amsa soma tayiya tayi ta nufi qofa ya mara mata baya kan su fita husna ta kwashe da dariya tanactafi "kaiiiisyyr sederth da roshni na burgeni wollah" tsakiummi tayi suka ficea tare 👒 [1/1, 9:08 AM] baby afreen: 👒👒👒👒👒👒 ~*Ashe kishiyatace*~ _In dedication to_ *💖Abba gana💖* _Special thanks to yuh *abba gana* Allah ya kara basira...king of writters kukeji😘😀_ *05* Suna ficewa husnah itama tayi tsaki "wallahi badin inna san yayanki ba dakin gane kurenki" murmushin mugunta tayi ta cigaba da kallonta...tana cikin kallo wayarta tasoma ringing dasauri ta daga sunan kawarta *deeja* daya bayyana a screen din yasa tayi murmushi ta daga kiran cilin sauri "hello amarsu ko harynxu anna barcin ne?" "wace ni?kinga ni kallo ma nakeyi" "shegiya yar banzar gari inna angon naki yake" "yana tsakar gida nakega...yaushe zaki zo ne?" "se jibi zanxo insha Allah..toh ya ban labari insha" dariya suka kwashe dashi dikkansu... "hm ai abunba a mgn aini angama daga jiyan nan" "meyafaru yargari?" Nan husnah ta kwashe dik abinda yafaru a darenjiya ta bawa deeja labari..Nikam abba gana ya hanani ji🙈ballena kwaso muku.. ( *wannan nadaya dagacikin kuskurenda mu mata bama ganewabe kmt ace dan ki nada kawa ba kawai ki kwashe sirrin mijinki ki fadamata ba.bakisan ainna ze tsaya ba..ykmt mu gyara halayenmu nasan masu karatu da dan bayanin da nay kungane inda nadosa... se mu kiyaye harshen mu*) Dariya deeja tasomayi sosai bude baki husnah tayi zatayi magana kawai seji tayi afizge wayar atsorace tamike ganin sadeeq atsaye yasa ta kuma dibrrbicewa dan azatonta yaji me take fada awayar... Murmushi shikam yayi ya kashe wayar ya ajiye mata agun dinning ya nufa ya zauna yasoma bude flask zesa abinci..husnah kuwa ajiyar zuciya tayi tare dasa hanunta aqirjinta kasancewar yadda kirjinta kedukan uku2...Sauke ajiyar xuciya tayi ta zauna kan kujera tare da lumshe ido tana maida nunfashi.... "bazakizo kici abinci bane?" Dasauri tamiqe tare da qaqalo murmushi tasoma tafiya harta isa inda sadeeq yake kujerar dake gefensa taja kujera ta zauna tana murmushi... 👒👒 _2days later_ "Husnah ynxu hk zaki zauna ba kya gyaran gidan ba shara ba komai?girkin ma sedai ayi akawo miki kici ko wanke kwanuka bakya yi?" "gsky ni kam yaya kana takurani nafadama agidan mu banayi...inkuma baka yarda ba kaje ka tmby umma mana"😏 "Lallai husnah 👉 ke ynxu agidanan sedai kici kiyi kallo ko?" "toh me kakeso nayi yaya kaga ni fa anata wuceni a film dinan senayi backward ma" "shknan bakomai zan kwashe kayan kallon kaf nayi kauta dasu" "cabdi wallah fade kakeyi" tsaki ya sadeeq yayi yasoma danna wayarsa..ringing biyu aka dauka... "hello ya sadeeq" "naam ummi dan Allah kina gida ne?" "eh yaya meya faru?" "Dan Allah kixo gidana zan dan saki abune" bejira cewarta ba ya kashe wayar ya nufi hanyar daki..husnah dake zaune ta qara gyara kwanciyarta tana kallonta abinta... Ummi kuwa can tana ajiye waya ta soma qunqunai mama dake gefe ta kalleta tana fadin "Kedawa?ya akayi ne" "Mama ya sadeeq ne wai senaje gidansa kuma matarnan tasa batada mutunci wallahi" tsaki mama tayi tasoma ma ummi fada danme zatace husnah batada mutunci...ba shiri ummi tazari gyalle ta fita ranan natainyayi dubu bace yace.... Sadeeq nashiga daki yayi wanka ya fitoh ya shirya tsaf cikin kanan kaya dasuka fit dinsa sosai ... Fitowa yayi har ynxu inda yabar husna agunta ke se qara gyaran kwanciya data keyi tana dariya tsabar dadinda film dinyake nata.... dinningya nufada zumar jan kujeravya zauna qarar door bell yaji ya nufi qofa yana budewa cikin sa'a yaga ummi se turo baki takeyi Matsa mata yayi tashigo dan yariga yasan matsalarta.... "Kiyi hkr ummi dan Allah gyaran gidanan zakiyi kifara daga dakina plxxx". . Zaro ido tayi ta nuna masa husnah da yatsa wacce keta kallonta tana dariya👉 😳 daga hannu yayi ya hadesu 🙏 ..alamu yamatada ido akan ta je tayi kawai..daga kafada tayi tare da tabe baki ta nufi hanyar dakin sadeeq ... "Toh nixan fita sena dawo" yafada tarecda warasawa inda husnah take.... "Toh seka dawo asiyo min abarba" tafada tana murmushi bece komai ba ya fice abunsa .... *kubiyonidan jin yazata qare tskaninta da ummi* 👒👒 [1/1, 9:08 AM] baby afreen: 👒👒👒👒👒👒 ~*Ashe kishiyatace*~ *A short story* _In dedication to_ *💖Abba gana💖* *06* Ummi kuwa tana shiga dakin tayi tsaki ganin dakin ba agyare ba...dage labulayen dakin tayi tasoma gyara kayandakin ta fitar da kayansa masu datti ta share dakin tas ta canja bedsheet ta wanke toilet din ta gyara ko inna tsaf... fitowa tayi pallo nanma ta gyara ta share ta kwashe kwanukan dake kan dining takai kitchen tadawo ta share palon tsaf ...hanyar kitchen ta nufa danyin wanke2 Husnah dake zaune tasoma fadin "Ummi kishiga dakina ki gyaramin " Sake baki ummi tayi tana kallonta... "ynxu anty husna dakin naki ma se an gyara miki" "mtsw kinga bannemi wani dogon bayani agunki ba kije kiyi abinda nasaki". "toh gsky ko zanyi sena gamavsbinda nakeyi tukunna" dasauri husnah ta miqe ta danna pause a film din datake kallo tare da fadin "ke harkinisa nasaki abu kiqi yi?" "nifabaqinyi nayi ba cewa nayi sena gama abinda nake tukun dasauri husnah ta miqe ta nufo inda ummi take cike da gadara itako ummi tsayawatayi ganin ikon Allah Husnah na qarasowa tadaga hannu da zumar marin ummi dasauri ummi ta riqe hanunta... "baki kai matsayin da zaki maren ba...kuma dakinki abu daya zesa na gyara dan ya sadeeq yace nagyara gidan shiyasa badan hk ba wallahi bazan gyara ba.." "ke ni tsararki ce?" "kanki akeji...banda lokacinki" ummi na kai wananta sake hanun husnah ta shige kitchen abinta tabar husna agun sake da baki... tsaki husnah tayi cike da takaici "wallahi zanyi maganinkitinda taqamarkirashin kunya" tana kaiwanan ta koma maxauninta ta cigaba da kallo abinta.... Ummikuwa tana shiga tayi wanke wanke ta gyara kitchen din ta fitoh tayi mopping kafin tabi ko inna da turaren wuta gana fesawa.gidan yadau kamshi...kafin ta nufi dakin husnah ma ta gyara mata tasa mata turare.... lkcin sallar la'asar nayi tayi alwallatayi sallah....husnah ma hk dik sakacinta bata sakacin sallah lkcin sallah nayi zata tashi tayi abinda ke burge sadeeq da ita kenan... 👒👒 Sadeeq kuwa tinda ya fita aaibiti ya nufa yana gama duba patient ya nufi office din hydar... hira suka somayi sosai cike da nishadi.. "Ykmt ace nazo naga amaryarmu fa" hydar ya fada yana dariya "amaryar ku ko shirme.." cewar sadeeq dake dannar wayarsa "kamanya shirne?" "toh ba abindavtakeyi fa se kallo ..bata iya komai ba..girki.gyaran gida kai komaivda komai husnah batayi acewarta bata iya ba agida batayi... Dariya hydar ya kwashe dashi tare da fadin "Ango ango kasha kamshi kaikuwavtana cin amarci xakacwani ce tayi aikin gida ni nine cewa zan ban iya ba" "Mtsw kaifa banzane acire xancen wasa agefe" "inkuwa hakanec knada aiki agabanka seka zage damtse kasomavaikin gida kan kafitoh off"? "cabdi jan wlhi abinda bazanyi ba kenan" . "ynxu knacnufin hk zakuyita zama cikin datti da yinwa?"? "hmm a'a ynxu hk ma nabar ummi tana gyaran gidan aninci kuma ko dagacwajan mama ko mahaifiyar ake kawo wa" "cabdijan wallah zan zige ummi tadena hk kurin bata bata ba zata gyara" dariya sadeeq yayi tare da fadin "kaifa mugune hydar" "ai gsky ce na fada Nanfa suka cigaba da hirarsu cike da nishadi.. "hydar kasan kuwa nxt week xankoma dutsinma wannan kauyen danaje kwanaki" "ok nagane mezakajeyi kuma,?"? "Abu zanje nayi kwana daya kawai xanyi nadawo "ok toh Allah yakaimu ya bada sa'a" ansawa sukayi da amin dikkansu.... 💖👒💖 Xaune Sadeeq yake yana aiki a laptop dinsa husnah ta turo qofar dalin nasa ahankali tare dayin sallama...amsawa yayi batare da ya kalli inda take ba... karasawa tayi ta haye kan gadon ta zauna kusa dashi...kusan minti biyar ba wanda yacewa wani qala acikinsu ..Sadeeq ne ya yanke shirun tare da fadin "Ranar thursday insha Allah zanje cikin dutsinma na kwana washe gari nadawo" gyada kai tayi tare da fadin "ok Allah yakaimu..dama innaso nama magana ne" "Ok dama innaso nama mgn" "inna jinki". . ya fadavtarecda rufe system dinsa "dama zan ma umma magana ne se asamomin me aiki" Shiru yayi yana kallonta daga bisani yasoma fadin "Kibari naje nadawo daga tafiya tukunna" ba musu kamar wata mutuniyar kirki ta ansa da toh...rungumota yayi jikinsa yasoma mata wani salo nadaban ganin yana neman wuce gona da iri yasa ta miqe a dari tabar dakin..... _Thursday_ Shiryawa sadeeq yayi ysaf ya fitoh dauke da dan qaramin jaka dayasa kayansa kala daya aciki ....zaune ya tadda husnah a palo tana kallo... "Toh ni zan wuce" miqewa tayi ta nufo inda yake ga mamakinsa sevganin hawaye yayi nabin fuskarta... 👒👒 [1/1, 9:08 AM] baby afreen: 👒👒👒👒👒👒 ~*Ashe kishiyatace*~ _In dedication to_ ~swt~ *💖Abba gana💖* *07* "Husnah meyafaru ne?" "bayan zaka tafi kabarni.kuma ni tsoro nakeji wlhi "ai ba dadewa zanyi ba ki kira anan ta tayaki zama " gyada kai tayi tare da sharevhawayen fuskarta tavkarbi jakarsa har mota ta rakasa sanda taga ya motarsa ya ficevta soma wani sabon kukan hkvta koma cikin palon kallon ma gaggararta yayi daga bisani ta soma kira hanan awayactana gama kiranta takira deeja... Shikuwavsadeeq be tsaya ko inna ba kuma yana driving da sauri hkn yasavyavisa vikin garin dawuri...yana isa gun me anguwa ya fara sauka... Anna ta masa sannu da hanya...daga masu kawo masa fura se masu kawo ruwansha masu kawo tuwo dadai sauransu... Shikam sadeeq murmushi kawai yakeyi dan hkn na burgesa... "Abunakar ya hanya?" acewar mevanguwa "lafiy ahmadulilah" sadeeq ya amsa cike da fara....hiravsukayi sosai yaci abinci yaqoshi....kafin ya soma gudanarda abubuwan daya kawosa qauyen kasan cewar washa gari yakeson ya koma gida... Tafe yake yanata kalle kalle yadda aketa gyara gyare se guda akeyi wani yaro ya gani yaje tambayarsa "kai yau me akeyi ne?" "bikin yarinyar meanguwa za'ayigobe shiyasa" gyada kai yayi tare da tabe baki ya wuce abunsa.... Gidan me anguwa kuwa ba abinda ake se kidan kwarya anna rawa anna guda .....amarya kuwa can daki anna gyarata...tasha jan baki ga dugonan da sukeyi a fuska irin hk • • • • da • • • dik ta shasu a goshinta anfitoh da ita se guda ake qawaye sunata rawa su alawiyya nagani sun shokare se dancewa sukeyi.... *Husnah* "Ke kin wani bi kin ishemu da wani xancen mijinki" "fada mata dai anty deeja tabar mu muyi ta garara se faman surutu tajeyi" "barni da ita hanan sekace wanivya hanata bin mijin nata" Miqewa tayi fuuuuu ta shige dakinsa hade da banko qofa tavfada kan gadonsa tana rera kuka..... sudeeja da hanan kuwa dariya suka dinga mata *Washe gari* Yau take juma'ah babbar rana sadeeq ya gama shirinsa misalin karfe daya da zumar anna fitowa daga sallahr juma xe kama hanyar gida... Fitowa yayi ya nufi wajan me anguwa ya zauna anata hira anan yakejin sunan amaryar *Aisha*(Shatu) se angonta kuma *musa*(danlami) Sunan zaune suna hira aka soma kiraye kirayen sallah miqewa sukai kowa ya nufi yin alwala... Suna gamawa aka soma hallara a masallacin lokacin sallah nayi suka gabatar nanfa aka fara zumar daurin aure... Kamar daga sama aka soma hayaniya taciki iyayen angosuna fadin "Mu munfasa aure dama sanda nacewa musa ya bari se ya samu aikinyi kuma karatu zashir a binni" nanfa hayaniya ya kaure me anguwa ya fitoh babu abinda yake se fifita yana ta sallati yana sanarwa ubangiji.... yanan tsaye wakilan ango sula fitoh suka wuce se surutai suke .... Nikamganin hk na koma gefe nazauna domin hutawa kamar amafarki najiyo anna fadin "Andaura auren *Abubakar sadeeq* da *Aisha*(shatu) 😳 _10min later_ Zaune sadeeq yake a motarsa shi kadai yafada duniyar tunani *Flash Back* me anguwanecleta fifita se huci yake yana kaida kawowa....sadeq ne ya nufo inda yake.. "ne anguwa meya faru ne?" "Kaidai bari danan....abaini jama'ahsukacwulaqantani bayan angana komaivsuzo suce sunfara auren?" shiru sadeeq yayi aransa yana fadin "Yazanyi in cetoh shi dagacshiga kunya?mutum ne me karamci da kautatawa mutane" sharaf sadeeq ya furta "Zan aureta ga sadaki " Dasauri mevanguwa ya juyo yana girgiza amasa kai baza ayi hk ba "gyada kai yayi akan yanasocze aureta" Sosaixme garivyayi murna suka koma ciki liman ya wakilce shi me anguwa kuma yarsa aka daura auren *Back to current scn* Share gumi sadeeq yayi yasomactinanin "ynxu inna zashi da ita? inyavkaita gidansa matsala...ya kaita gidan iyayensa matsala dan karshe mama tasashi ya saketa....ynxu inna ze kaita?" yana cilon wanga tunani yajiyovguda juyawa bayan da zeyi yaga mutane dayawa ga wata datashia llubi dagani itace anaryarcsun dosa wajan motarsa da ita...nanfa hankalin sadeeq ya qara tashi 👒👒 [1/7, 12:00 AM] baby afreen: 👒👒👒👒👒👒 ~*Ashe kishiyatace*~ _Na_ *Faty Afreen* _In dedication to_ *💖Abba gana💖* _Congratulations sis *Humaira melody* for d sucessful completion of yuhr swt novel *NAMIJIN KENAN* Allah ya qara basir a_ fatyafreen.blogspot.com or http://fatyafreen.blogspot.com/2017/01/ashe-kishiyatace.html *08* kasa fitowa yayi.. yayi lamo acikin motar sukuwa sun tsaya jiranshi awaje se faman gudaakewa amarya wasu kuwa cewa suke "cab aike shatu kin more innice wanne kuka zanyi..kinsamu miji me kudi" alawiyace tayi dariya tare da fadin "wallahi kuwa kinsamu hutu kinhuta da wahalar qauye.ai dani za aganin gidan amarya" Nanfa sukadinga hira kowa daabinda yake fada sunayi suna guda annatafi ga shewa.. Me anguwane da wani dattijo suka nufo indasuke "ahh yanaga kun tsaya anan se hayaniya kuke? yamma zata masa ahanya fa" bejira jin mexasuce ba ya nufi inda sadeeq yake qwanqwasa glass din motar yayi dasauri sadeeq ya bude murfin motar yafitoh... "auh kanaciki shine kabarsu sunata batama lkci?" daga bisani me anguwa ya jasa gefe ya masa nasiha...kuma yacedashi za'a tafi da qawarta alawiya taga in suke.. sadeeq kuwa najin hk ya kuma gigicewa me anguwa daya lura ya soma tmbyrs "sadeeq lafiyarka kuwa?" inda inda yasomayi tare da fadin "ahhh bkm inna qarayin latti agurin aiki ne" murmushi me anguwa yayi bece dashi komai ba ya nufi inda amaren suke. "kai ku taho maza da alawiya za atafi" : "Nima dani za aje ..acewar dije... nanfa suka. dunguma su uku suka shiga seat din .baya.. Cikin sanyin jiki ya soma driving sosai shatu ke kuka bama kamar inta tuna cewar bama tasan waye mijin nata ba... *Husna* "ku tashi mana se faman bata min lokaci kukeyi" acewar husna deja ce tayi murmushi tare da fadin "dallah muje kin wani ishemu da surutu" soma tafiya sukayi hanan na bayansu hankalinta nakan wayarta ... fita sukayi tasawa qofar key dmsuna zuwa bakin gate taba ma megadin key kafin suka wuce abinsu... Basu tsaya ko inna ba se gidan umma zaune suka samu umma ...da sallama suka shiga... "waiyyoo ummata nayi kewarki" acewar husna "oyoyo yar gidan umma..ashe kuna hanya". ciki duka shige kowaccansu ta yada zangwanta nanfa aka hau hira.... *Sadeeq* sosai yake gudu amotar yana tinanin yaddaze isa gidansa ya tadda husna tinda nata dasauqi akan na mama... da ka kallesa kasan yana cikin damuwa...ba bata lokaci suka isa...su alawiyya kuwa se yaba kyan gidan suke tindaga wajan... Horn yayi me gadi ya bude nan me gadi ya fada masa cewar ai husna batanan tabar key amma...busar da iska yayi tare da dauke axiyar zuciya... karban key din yayi ya nufi wajan parking ya paka motarsa... Bude musu yayi suka fitoh se zare ido yake kamar tsohon munafiki...bude musu yayi suka shiga.... Kalle kalle suka farayi gidan yayi kyau dik da palon ba'a gyara yake ba xama sukayi shikuwa tsayawa yayi yana kallon palon daga bisani ya bude dakinsa nanma kaca-kaca...ya bude dakin husna nanma ba agyara ba...ya duba kitchen wanke wanke ne lihidi guda sekace gidan family house... tsaki yayi su dije sukayi saurin juyowa suka kallesa ganinsuna kallonsa yasa yaqaqalo murmushi ya nufo inda suke "kuzo muje na kaiku tasha ku koma gida ko?" "tin ynxu...ai na aza gwana zamuyi" Xaro ido yayi atsorace yana fadin "Kwana kuma?" "kwarai kuwa" shine abinda alawiyya ta fada ganin dik ya rikice yasa dije tasoma fadin "jiyadda yawani rikice sekace munce zamu tafi da ita" dariya sukayi shikuwa se waige waige yakeyi jiyake kamar husna zata shigo.... "kinga tashi mutafi mu bar musu gidansu wataran mazo ganinta" kamar jira yake yamiqe yayi gaba sukuwa sallama suka mata suna zaulayarta kafin suka bi bayansa... ***** in high speed yake tuqi dan sauri yake yaje yakaisu tasha yadawo kan husna ta rigasa dawowa......ai kuwa cikin sa'a yana komawa yasami shatu zaune inda yabarta....mumushi yayi ya fuzar da iska ya qarasa inda take ya zauna "sunanki aisha ko?" "eh amma anna cemin shatu" nabasa ansa kanta na qasa.... "Ok shatu dan Allah innaso kimin wata alfarma ne" "tame fa?" "yauwa...kinga ni innada mata sunanta husna" dasauro shatu ta dago takallesa cike da mamaki daga bisani ta sauke kanta qasa "Kiyi hkr nasan bazakiji dadin abinda zan fada ba... matata bata da hkr balle intaji ance naqara aure bazaman lfy....dan Allah so nake kizauna a matsayin me aiki agidanan kafin daga baya sena sama miki gidanki" Dasauri ta dago tana kallonsa dai dainan sukaji qarar door bell.. 👒 [1/7, 11:24 AM] baby afreen: 👒👒👒👒👒👒 ~*Ashe kishiyatace*~ _Na_ *Faty Afreen* _In dedication to_ swt😍 *💖Abba gana💖* fatyafreen.blogspot.com *or* http://fatyafreen.blogspot.com/2017/01/ashe-kishiyatace.html *09* Atsorace sadeeq ya miqe da sauri ya nufi bakin qofar "Waye ne?" "nine oga"!! jinmuryar megadi yasa yasauke ajiyar zuciya shatu dake tsaye a lkcin ta riga tagama fahimtarsa... "meya faru?" "oga daman innaso nadanje masiyo abu na dawo ne karka jini shiru" "toh bkm seka dawo" yana gama fadan hk ya juya yana kallon shatu wacce take zaune tayi saurin sa kanta a qasa tana wasa da yatsunta... "kinyi shuru bakice komai ba...kiyarda danj wlhi zan baki dik wani abunda mata ke buqata agun mijinta zan miki komai da komai..amma dan Allah kiyi hkr ki rufamin asiri kinji?" gyada kai tayi alamun eh tare da fadin bakomai.. murmushi yayi tare da fadin bari naje na samo miki abinda zakici daganan zan daukota daga gida... Gyada kai tayi ya miqe yana share zufar fuskarsa ita ko binsa da kallo tayi har ya fice daga dakin.. Yana fita ya shige motarsa haryakai bakin gate ya tina da me gadin bayanan...tsaki yayi ya fita ya bude gate din ya fitar da motar kafin ya rufe gate din ya koma cikin motarsa.... *Husna* "kunga ni zan tafi saboda yaudinan sadeeq ze dawo" "toh aikuwa ykmt kotashi kitafi tin dazu kinzauna anan" "ynxu xantafi mama toh aban abinci na kai masa" "jeki dau foodflask kibawa inna ta zuba abincin" tafiya tasomayi zuwa kitchen din dake palon tadaki foodflask din kafin ta fitoh ta kaiwa inna...shinkaface da wake da miya taji kifi da nama ga kuma kayan lambu anyanka a sama...tana karba ko godiya bayi ba ta soma fadin "dija xo muje ko se anjima zaki tafi gida?" "a'a ynxu xan tafi nima... sallama sukawa umma suka fice abinsu...dija ce ta riga sauka kafin aka qarasa da husna har qofar gida.... *sadeeq* sadeeq kuwa tinda ya fita ya nufi restaurant ya musu takeaway na abinci harda na husna .... gidan mama ya fara zuwa "ahh sadeequ yaushe agari" mama ta fada fuskarta dauke da murmushi...ummi ceta fitoh tana masa sannu da zuwa... "inna wuni mama" "lafiya lau sadeeq yaushe ka iso ne? " wallahi banwani jima ba" "Allah sarki sannu sannu...ko zakaci abinci ne?" "yaya inna tsarabar qauyen ?" "kaik kekam da surutu kike jeki sanyo mishi tuwo yaci kafin ya tafi.".. murmushi yayi yama umma godiya... miqewa ummi tayi ta nufi kitchen ta fitoh dauke da plate. "tuwon shinkafane biyan gyada...kaci muje kaban tsarabata" "ai bazan baki ynxu ba sekinzo har gida" "lallaikam baxani gidanka ba inje ah-**" kafin ta qarasa maganarta mama ta bige mata baki da gudu ta miqe ta nufi daki tare da qarasa xancenta "inje amin rashin mutunci nida gidan yayana" murmushi sadeeq yayi mama kuwa ta fara fada daqyar sadeeq ya rarrasheta ...ya rasa meyasa mama takeson husna hk... Yana gama ci ya miqe ya na gwada numbern husna amma a kulle... miqewa yayi yama mama sallama ya nufi gidansu husna... da sallamarsa ya shiga ya gaida umma cike da fara'a ta ansa... "yaushe ka dawone?" "umma ynxu ndw dama nazo daukan husna ne" "kash aikuwa kunyi sabani tafi qilama ynxu ta isa..." dasauri ya miqe tsaye dik yabi ya rude "umma bari na tafi se anjima" amsawa kawai tayi ta bisa da kallo aranta tana fadin "toh meya sameshi?" tabe baki umma tayi shikuwa ficewa yayi cikin sauri ya nufi motarsa yasoma driving in high speed "kardai husna ta isa gida" "toh ynxu kar shatu tayi subutan baki tinda basanin husna tayi ba...kuma kar husna tayi wani abun na rashin hankali" shafa gemunsa yayi tare da fuzarda isakan bakinsa cike da tashin hankali... *husna* kwankwasa gate tayi cikin sa'a me gadin ya dawo ya bude mata qofar... "sannu da zuwa hajiya...ai kuwa oga ya fita" "laaa ya dawo ne?" "eh! ok nagode" ciki ta shiga ta murda handle din tajiabude ..shiga tayi tare da cire gyalenta qoqarin jefar da gyalen take akan kujera sukai ido hudu da shatu... sun jima suna kallon junansu ..cike da tashin hankali bama kamar husna tacika tayi famm... ahankali ta ajiye gyalen hankali da kular dake hanunta... "meya kawo ki nan?" husna ta fada fuskar bako alamar murmushi...kame kame shatu ta farayi "ni ni ni matar matar!!!! Dasauri husna ta finciko shatu...tare da zaro ido "ke matar wa? 👒 [1/9, 1:40 PM] baby afreen: 👒👒👒👒👒👒 ~*Ashe kishiyatace*~ _Na_ *Faty Afreen* _In dedication to_ *💖Abba gana💖* fatyafreen.blogspot.com *10* "ke matar wa?" "ni matar matar da aka kawo me aiki wani irin ajiyar zuciya husna tayi tare da fadawa kan kujera ta zauna... daga bisani ta miqe tare da fadin "waye ya kawoki?" cikin sanyin jiki shatu ta soma magana "me megidan ne ya kawoni yaje ya** kan ta karasa maganarta sukaji an banko qofa dasauri suka kalle kofar a tare sadeeq ne ya shigo kamar wanda aka koro sa yana zare ido... "ya sadeeq meya faru a cewar husna tare da qarasowa ta riqesa" sauke numfashinsa yayi tariqe suka zauna shatu dai ta bisu da ido ne kawai... kallonta ta husna tayi daga bisani ta daka mata tsawa tare da fadin "dallah jeki dauka min ruwa na basa kin wani tsiremu da ido" magana husna tayi tana nuna kitchen ...sumi2 shatu ta nufi hanyar kitchen sadeeq ya bita da kallo ganin hk yasa ta juyovda fuskar sadeeq zuwa kallonta... "ya sadeeq wacece wannan?" "ba ba ke kika ce kina son me aiki ba...shine na na kawota " "ok daga inna kake ne hk?" daidai nan shatu tashigo dauke da cup ta karba tare da bama sadeeq ruwan...ganin shatu a tsaye yasa husna ta daka mata tsawa "kiwuce kije kiyi wanke wanken mana koni xan miki?" Dasauri sadeeq ya dago suka hada ido da shatu dasauri ya saukar da kansa kasa tsabar kunya... Dasauri shatu ta nufi kitchen tana sharar haway e "Ita da gidan mijinta ta koma yar aiki" Sadeeq kuwa kallon husna yayi ya riqo fuskarta "Husna meyasa zakina mata ihu xakisa taji tsoranki " Turo baki husna tayi tana fadin "to kawai se ta tsaya tana kallonka?" dariya yayi yaja karamin bakinta ..dik abinda suke shatu na bakin qofa tana kallonsu.share guntun hawayen dake isonta tayi ta shige kitchen din.... Kallon kitchen din tayi ko inna akwai datti nanfa ta goge ta soma wanke kwanu kan ta da gama ta gyara ko inna tsaf ... Tana fitowa husna kadai ta iske palon "Harkin gana ne?" "eh nagama" "tohshiga dakina gashi can ki gyara minshi" cikin sanyin jiki ta shiga dakin ta soma gyara... Husna kuma miqewa tayi ta nufi dakin sadeeq jin yana wanka yasa yasa ta fitoh ..ba awani jima ba shatu ta fitoh... "shiga dakin mijina ki gyaramin kuma kiyi sauri ki gama kafin ya fitoh daga wanka..." toh kawai shatu tace ta nufi dakin sadeeq ahankali ta tura qofar dakin tashiga da sallamarta.. ganin ba kowa yasa ta soma kauda kayan dake kan gadon wasu ajiyewa kawai take inda taga yaa mata dan batasan mazauninsu ba... tafara yaye zanin gadon kenan sadeeq ya fitoh daure da towel tana dagowa suka hada ido... sosa kai tasomayi tare da juya bayanta tana fadin "Dama tace ne na gyara ma dakin" tana fadan hk tasoma tafiya zuwa qofa da sauri ya damqo hanunta "ki tsaya kiji" "a a gsky kabari karta sa**" bata karasa zancenta ba sukaji anturo qofar dakin 👒👒
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).