shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Sunday 27 March 2016

SIRRIN ZAMA DA MIJI 3

sirrin-zama-da-miji.jpg

SIRRIN ZAMA DA MIJI

{KASHINA 3}

(AMSA KIRAN MIJI)

BY

MUHD*ABBA*GANA 09039016969

yazo a cikin hadisin manzon Allah (SAW) cewa idan miji yayi kiran matarsa to ya zama dole ta je koda tana akan deruna don haka wannan hadisi wani ban garene dayake nuna wajab ci akan mace ta je kiran mijinta ako wane hali take,kuma yana nuna cewa wajibine ta amsa kiran mijinta domin biyan bukatarsa koma wace iri ce, dan haka ya kamata mata su kiyaye domin jin dadin mazajensu. kuma har yanzu dai shi wannan hadisi yana nuna watsar da yanga ko kuma jan aji a gurin ma aurata, don haka babu zancen jan aji agurin ya mace indai a cikin sha'anin aure kuma in ya zama umurnin bai sabawa koyarwar addininmu ba. Allah bamu ikon gyarawa

Share:

SIRRIN ZAMA DA MIJI 2

sirrin-zama-da-miji.jpg

SIRRIN ZAMA DA MIJI

(TSARIN MU'AMALA TSAKANIN ANGO DA AMARYA)

BY

MUHD*ABBA*GANA 09039016969

Akwai abubuwa da suka zama wajibi a gurin ma aurata domin koruwar zamanci da soyayyar a tsakanin su, kamar na musulunci to da farko dai Allah madaukakin sarki ya fada a cikin alqur'ani mai girma cewa yana daga cikin ayoyinsa cewa ya sanya mana mataye daga garemu domin mu samu nutsuwa dasu. to a nan yakamata a ce a duk lokacin da ango da amarya suke tare a matsayin ma auratan juna ana son bukatarsu da zaman lafiya da kwanciyar hankali atsakaninsu. dan haka ashe a duk lokacin da amarya tatare a gidan mijinta ana bukatar tazama wacce take kwantar da hankalin mijinta ta kuma samar masa da nutsuwa ba waccce zata sa mijinta a cikin tashin hankali da damuwa ba. yana da kyau amarya takiyaye wasu abubuwa da kyau domin sune zasu taimaka mata izuwa samun dorewar zaman lafiya da kuma soyayya atsakanin ta da mijinta ga abubuwan kamar haka:

A KYAUTATA MU'AMALAR MIJI

wajibine a gurin mace ta kyautata mua mala atsakaninta da mijinta a lokacin da suke tare a gida ta zamai mai kiyaye duk wani abinda zai bata masa rai, karta zama mai cutar dashi da har shenta ko kuma da ai kinta koda kuwa zayi yarane don haka yana da kyau mace tayiwa har shen ta cin zami daga barin fadar abunda zai janho fushin mai gidan ta. insha Allah gobe zan daura daga inda na tashi

Share:

BANA KAUNARKA 41 & 42

bana-kaunarkajpg.jpg

BANA KAUNAR KA!!!

41-42

MUHD*ABBA*GANA 09039016969 -------------------------------------------- baba rabi'u shi ya biyu musu sadaki kowannan su dubu hamsin hamsin (50,000) haidae kuma small boy shi ya hada musu lefe akwati shida shida manya masu tsanin kyau sai sabuwar mota kasaitacciya kirar zamani kai gaskiya koni na yaba haidar domin yayi bajinta sannan na jinjinawa ya al'amin domin shi ya zubawa kannansa kayatattun kayan kicin na azo a gani,ya faruq kuma yayo musu kayan daki ita kuma mai taji da gyaran jiki yaranta takanas ta tura sokoto aka samo me gyaran jiki sannan akwai wata makociyansu yar maiduguri ita tayi rawar gani wajen fito da yaran mom din ina zaune mom ta shigo na kalle ta fuskanta dauke da damuwa,nace nifa mom ban gane ba ni ba amarya ba amma komai sai a dinga yii min irin na amare,anya mom ba wani abu kuka boye min ba? mom ta gyara zamanta tace auta kenan,ai abin da yasa kika ga ana muku haka don anga ku yan biyu ne ya zama dole kome akai miki ayiwa yar uwarki domin tare aka haife ku na kalle ta au shi yasa naga komai ana mana iri daya nifa abin ya daure min kai shi yasa lokacin da yan katsina suka zo naji sunce min amarya,amaryar shahid ni fa ina jin haushin in aka hada ni da shahid to ai ko shima haka abokan wasanku zasu ce masa domin sunga ku yan biyu ne ni dai gwanda a hada ni da wani sam bana so ana hada ni da shahid.......na fafa miki abokan wasa sai hakuri in fa kika nuna musu ba kya so sun dinga ce miki kenan gwanda ma ki saki ranki ki dauki komai ba komaiba nai murmishi farin ciki nace ni kuwa har gabana ya soma faduwa,amma yanzu naji dadi sosai domin na fiso ku barni inyi karatuna mom ta rungume ni tace zakiyi alfahari damu auta.yau saura kwana biyu daurin aure yaune kuma muka shirya zuwa gambu gurin su mom kasancewae mu rubuta komai mun amfani da direban gidanmu domin shima dan gyanmbun ne sai dai wani abu da baku sani ba,ko da wasa bamu sanar dasu mom ba bbu wanda ya san da tafiyar sai nida mahida,ya amin ya faruq sam bamu sha wahala ba wajen gani gidan kasancewar mahaifin mom fitace ne sannan gidansu bac wani boyayyan gida bane in kace gidan tsamiya koda titi ne to za akai ka gidan,munyi sallama dan ma dai dakin gidan mai yar katanga wadda duk rabin gidan ya rushe sai dai an gyara shi ta hanyar jera wasu karare,kallo daya zakai wa gidan kasan mutanen gidan suna cikin kunci talauci munyi sallama turus mukai fakin a zaure domin wata tsohuwa muka gani tanawa wani tsoho fifita zaune suke a soron suna shan iska sai dai da alama wannan tsoho bashi da lafiya domin gaba daya ya koma kalar tausayi,tsohuwa tace sannunku da zuwa yan samari ciki ta koma ta dauko mana taburmar kaba ta shimfida mana muka zauna ta kawo mana ruwa mai sanyi muka sha sannan muka gaishe ta muka gaida wannan tsohon ya amsa da kyar da alamu yana jin jiki mu kai masa sannu matar ta zuba min ido kafin daga bisani tace yan mata yan samari daga ina kuke don Allah ina kuke?

Abbagana hausa novels @ facebook.

www.abbagana.pun.bz

bana-kaunarkajpg.jpgbana-kaunarkajpg.jpg

Share:

BANA KAUNARKA!!! 40

bana-kaunarkajpg.jpg

BANA KAUNAR KA!!!

40

MUHD*ABBA*GANA 09039016969

--------------------------------------------

tsiwa da masifa ni ka fita min daga mota ko yanzunnan in kurma maka ihu,ya kalld ni cikin kwantar da murya yanzu wahida niki kewa wannan tsawar kar fa k manta nine al'amin naki yi hakuri kinji wahida yanzzu ina za ki nace ni katsina zani shi kenan bari in raka ki kinga sai in taho da motar inna kai ki kona ce eh to dawo nan in yaso sai ka tuka mu ji mu kayi ana mana hon ashe tuni wannan cunkoson ya baje a guje ya amin yaja motar na dinga ihu kamar wanda ya sato ni muma zuwa ya tisani gaba har cikin gida,ai kuwa a falo na dinga birgima ina kuka bbu wanda ya kula ni har nai mai tsata na bar gun ina daki a kwance ina jin san da abba ya dawo yace ina nake? aka ce masa nayi bacci yace wanne irin bacci da magariba maza ataso ni inyi alwala inyi sallah. wahegari gaba daya gidan bbu wanda na gaida asali ma ko fita ban yiba ina zaune mahida ta shigo wahida good morning nai mata banza ta kare surutunta ta fita tana fita ya al'amin ya shigo wahida ya karaso tare da dafa kafadata,wahida ina kwana nayi shiru oh wahida fushi kike dani im sorry my sister please na mike na bar masa falon haka ya faruq ya shigo yau sister tamu lafiya muka ji gidan shiru kai har mom hatta yan aikinmu sun rude autar mom ta zama kurma haduwa sukai suka dinga bani hakuri har na sauko na dawo normall. mamy muga littafinnan ta miko min "INSIYA" na kalle ta yana da dadi? gaskiya yayi min sai dai gaskiya tana shan wahala na tausaya wa yarinyar na daya dana biyu ne ko har na uku? na daya na siyo amma ina tunanin har na biyu zaiyi sai dai na dau alwashin duk matar data karkace ta shirya karya ya wuce 1-2 na daya dana biyu in tayi na uku ba zan ko kalli litrafin ba, me yasa kikace karya ne? kina nufin duk littafin da ake rubutawa karya ne? tabbas shida tatsuniya duk kusan daya na dauke su to me yasa kike bata lokacinki kina karantawa? ai a iya sanina tatsuniya bata da wani amfani ai kawai tunda kina ganin karya banza ce to kawai ki bar katantawa tunda bbu wani abu dayake amfana miki.(bari na yanke zance kuji masu tsigalun mu) BA KE KADAI BAMA MAMY NA SHA JIN IRIN WANNAN WAI ACE LITTAFI KARYANE SHIN IN KARYANE MUKE ZAMA MUNA GUNDIRA MUKU MAI ZAI HANA KOWACCE MACE KOH NA MIJI YA/TA DAUKI BIRO DA LITTAFI ITAMATA SOMA RUBUTA TATSUNIYAR TABBAS BA KARAMIN KUSKURE BANE MASU CEWA LITTAFI KARYANE ABIN DA MUKE SO KU FAHIMTA SHI RUBUTU BAIWA CE DAGA ALLAH BA DUKA MUTANE KOWA YAKE DA WANNAN BAIWAR BA BATUN MASU GANIN LITTAFI KUMA KARYANE GASKIYA SHI YA MUNAFUNCI ZUCIYARSA TUNDA HAR YASAN KARYANE YAKE BATA LOKACINSA AKANSA YAKE KARANTAWA TABBAS IN MARUBUTA SUKA JI BA SASUJI DADI BA KASANCEWAR SU SUMA SUNA KOKARIN ZAKULO MUKU ABINDA ZAI KADAR DAKU ZAI NISHADARTAR DAKU,SANNAN ZAI FARANTA MUKU ZAI FADAKAR DA KU ZAI NISAR DAKI ZAI KARKATO DA HANKULANKU TO MENE KARYAR ANAN ANAN SABODA ALLAH? MECECE KARYAR ANAN DUK ABIN DAKIKA JI KAJI ANCE A LITTAFI ANYI TO WALLAHI IN KA KIN DUBA WANNAN ABUN YANA KARUWA KUMA ABIN DA NAKESO MAKARANTA KU FAHIMTA CE MU MUNA RUBUTUNE DOMIN KU ILIMINTARWA TARE DA NISHADANTARWA DA FADAKARWA,KOH SHIN KUNA TUNANIN MU MASU RUBUTUN BAMU DA WATA AIKI SAI RUBUTA MUKU LITTAFI NE ALHMDULLAHI NI INA DA AIKINA KUMA ALFAHARI DA SHI BAYAN HAKA INA KARATANA A JAMI'A HAKA ZALIKA SAURAN MARUBUTA MAZA KAI HAR DA MATAN MA SUNA DA AIKIN IRIN SU: ANTY HAUWA JABO, ANTY BENA,MAMAN SHAKUR,ANTY FIRDAUSI,ANTY MIMI,KHALEESA, SIS SADEEYA BALA, SIS BILLY GERO,HUMAIRA, SU ROKEEY BABY ZAHRA DASU KAUSAR LUV BAWAI SUMA ANCE MATA NE BASU DA AIKI BA WALLAHI SUNA DASHI WASUN SU KUSOSI NE BANGARE AIKI ,WASUN SU MA SUNA DA AURE HMMM ZAMA DA MIJI MA BABBAN AIKINE,WASUN KUMA DE SUNA GIRKI DA SAURAN AIKI A GIDAN IYAYENSU,MU HADA KANMU MU ZAMA TSINTSIYA MADAURINTA DAYA IN BAKU BAMU HAKA IN BAMU BA KU A GUJI FADAR MAGANA DOMIN MANZON ALLAH (S.A.W) YA CE KU FADI ALKAIRI KO KUMA KUYI SHIRU NA GODE KWARAI DA GASKE DA KA/KI DAURE KA KARANTA NAKU HAR KULLUM JIKIN MARUBUTA MUHD ABBA GANA .

Abbagana hausa novels @ facebook.

www.abbagana.pun.bz

Share:

Wednesday 23 March 2016

TAMBAYA DA AMSA

bana3.jpg

Assalamu Alaikum Malam gidanmu yana kusa da masallaci, muna jiwo kiran sallah da ikama ta lasifika, koya halatta in bi sallar jam’i daga laspika ??? (Daga Husna Ahmad). AMSA: ----- DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI. To ‘yar’uwa wannan mas’alar takasu kashi biyu: 1- Idan ya zamana dakinki yana like da masallacin, to tabbas wannan ya halatta, saboda Nana A’isha (R.A) tabi sallar kisfewar rana daga ‘dakinta, a zamanin Annabi (s.a.w) kamar yadda Bukhari ya rawaito hakan a hadisi mai lamba ta: 184, sannan Abdur Razzaq ya rawaito cewa: Ta kanbi ragowar salloli daga dakinta” kamar yadda yazo a littafinsa na (al-Musannaf, hadisi mai lamba ta: 4883). Saboda ‘dakinta ajikin masallacin Annabi (s.a.w) yake. 2. Idan ya zama ‘dakin baya kusa da masallacin, to zance mafi inganci shine: Bai halatta kibi ba, saboda a zamanin Annabi (s.a.w) sahabbai suna haduwa a wuri ‘daya ne idan zasuyi sallar jam’i, basa rarrabuwa. Wannan sai yake nuna cewa, hakan shine siffar sallar jama’i, sannan jera sawu a sallah, wani yana bin wani dole ne a sallar jam’i. Allah Shine Masani.

Share:

BANA KAUNARKA!!! 39

bana-kaunarkajpg.jpg

BANA KAUNAR KA!!!

39

MUHD-ABBA~GANA

09039016969 --------------------------------------------

nace bomboy n tsane shi na tsani halayansa ya amin ya kamo hannuna ya zaunar dani yace please my sister bani labari saboda Allah me ya hada ku ban fiya boyewa ya al'amin sirrina ba domin mun fi shakuwa fiye da kowa a gidan,don hakan bbu abin dana boye masa sai dai na lura na batawa yayan nawa rai mikewa yayi yana safa da marwa inalillahi wainna ilaihi rajiun kawai yake maimaitawa ya kalle ni ransa a bace,wahida kowanne hali shahid ya shiga kece sila,domin wallahi tallahi ni shaida ne shahid bai taba shan wani kayan maye ba,shahid ba dan iska bane,shahid ba manemin mata bane,shahid mutum ne shahid mutumin kirki ne wanda samun irinsa sai antona kin ban kunya wahida,a da ina ganin kin fi mahida hankali amma wallahi mahida ta fiki sanin ya kamata ta fiki iya magana,ya faruq ya shigo shi da mahida saukar mari naji ya cire belt dinsa ya shiga dukana da kyar ya amin ya kwace ni ya faruq yace naji komai kuma kamar a kunennen abba ya amin ya dafa shi yace bai dace ba wannan sirri ne tsakin shahid da wahida,nima donna matsanta mata ne naji na mike nace wato shi shahid bakuga laifinsa ba baku yi kishin yar uwaarku ba sai shi ba kuji zafin abin da yayimin ba sai ni kuka ji zafin maganganun dana fada masa cool down na gode wa Allah daya tserar dani,ya kuma tsallakar dani daga mummunar manufar shahid ta son rabani da mutuncina ya goga min bakin fantin da har abada bbu mai iya goge min shi sanin kanku ns tun farko ban munafurci shahid ba na fito face to face na fada ba gaskiya bani da lokacin soyayya amma kun kafe kun goyi bayansa kuna shirin yi min auran dole toku tsaya kuji tunda nace bana sonsa bana sonsa soyayyar ba nayi toko zaku haka rami ku binne ni ba zan amince da shahid ba,domin ba sona yake ba sha'awata yake in kun kuskura kun bada goyon baya amin auran dole wallahi baku ba har wadda suka hada auran zan baku mamaki tai ficewarta .ina shiga dakinmu na hada kayana ina kuka ina fitowa na gansu a falo ina cikin jan akwatina ya amin ya fito lafiya ina kuma zaki? bar muku gidan zanyi tunda bakwa sona, din Allah madadin ku dawo da shahid tunda shi kuke so shi kun fi son farin cikinsa gwanda in bar gidan tun kan ku kashe ni,na shiga jan akwatina mom ta fito tace me ya hada ku? mom sun gaji dani ne basa sona farin cikina,burinsu su muzguna min,burinsu su bakantamin gwanda in bar musu gidan .mahida ta rike akwatin ina ja tana ja koda naga sun dauki abin wasa sai na sakar mata akwatin basu ankara ba sai tashin mota suka ji da gudu suka fito suma suka shiga motarsu suka bita da gudu mahida kuka ta kama. matsala gosilo shi ya taka mata birki duk da kutsa motar take yi amma ina hanyar ta tushe kasancewar motar su al'amin tana bayan to wahida,al'amin ne yai hanzarinn fitowa ya sh iga motar wahida ta mudubi ta hango shi tace cikin fushi,

Abba gana hausa novels @ facebook.

www.abbagana.pun.bz

Share:

Gyaran gashi

clean-flower.jpg

{1}. Danyen ganyen lalle ko na magarya. {2}.Garin hulba ko tsaba. {3}. Zaitun laun, wato (man dinya). {4}. Zaitu sim sim, wato (man ridi) {5}. Man danyen zaitun. {6}. Man habbatus sauda. {7}. Man kwakwa, wato (coconut oil). YADDA AKE HADAWA Da farko zaki hada garin hulba da danyen ganyen lalle kona magarya kisa a tukunya kizuba kofin ruwa ko pure water uku kisa a wuta ya tafasa ki sauke lokacin da zaki dora lallen nan da hulba zaki hada sauran mayukan naki sai kiyi oiling kanki kisa a leda ki daure zaki barshi a kanki kamar mintuna 15 ki dinga diban ruwan dafaffen lallen nan kina wanke kanki dashi. Idan kingama saiki barshi yabushe, kikara oiling kije ayi maki kitso. NOTE: Zaki iyayi sau 2 a wata. ALLAH YA BAYAR DA SA'A.

www.abbagana.pun.bz

Share:

Tuesday 22 March 2016

SIRRIN ZAMA DA MIJI

clean.jpg SIRRIN ZAMA DA MIJI (KASHINA 1) WRITTING BY MUHD*ABBA*GANA ASSALAMU ALAIKUM, YAN UWA MUSULMAI MAZA DA MATA INSHA ALLAH MAKONAN ZAMU TATTAU AKAN ABINDA YA SHAFI MA,AURA ZAMU FARA NE DA SIRRIN ZAMA DA MIJI ABUBUWAN SUN KUNSHI KAMAR HAKA: *AURE *TSARIM MU'AMALA TSAKANIN ANGO DA AMARYA *A KYAUTATA MU'AMALAR MIJI *AMSA KIRAN MIJI *TSAFTA *KAUNAR MIJI *KIYAYE GANINSA *KIYAYE DUKIYARSA *KIYAYE SIRRIN MAI-GIDA *IYA MAGANA ZAMUYI BAYA DAYA BAYAN DAYA INSHA ALLAHU AURE aure wata daraja ce wacce mutum yake samun daukaka da daraja a lokaci da yayi shi, bayan ladar da ma'aurata suke samu a gurin ubangiji haka kuma wani rufin asirine a tsakanin ma aurata guda biyu domin dukkan matan dabata da aure ba zata zama a cikin matayen da suka da kuma ko kwarjini a gurin jama'a ba hasalima ba a daukarta amatsayin cikkai yar mai hankali to amma a duk lokacin da mace take sance mai aure to zaka ga dukkan jama'a suna jin tsoronta kuma sai girmanta yaci gaba da karuwa a cikin zakatan jama'a kuma tafita daga zargin jama'a kuma zakaga ko afagen kwanciyar hankali da sannin ya kamata matar aure tafi dayan a cikin muta yan uwanta domin baza ka sameta tana yin irin shashancin da sauran mata yan da basu da aure suke ba. dan haka shi aure wata daraja ce wacce Allah ne kawai yasan irin ni'imimin da suke a ciki tare da hikimomindashi aure ya kunsa aure yana da matukar muhimmanci arayuwar dan adam, hasalima sabo da muhimmancinsa ne, ambatonsa yazo a cikin alqurani mai tsarki a cikin gurare daban daban inda Allah madau kakin sarki yake nuna muhinmar cin aure a musulunci. a cikin suratul nisa'i Allah (SWI) yafi to da maganar aure karara inda yake nuna cewa idan mutum yana da hali to zai iya aurent mace biyu ko uku harma hudu to amma idan bbu hali to sai ya auri mace daya wato idanba zai iya yin adalci a tsakaninsu ba don haka ire iren wadannan hadisan suna nan da yawa wa yanda suka nuna mafificiyar rayuwa itace mutum ya zama mai aure yazo a cikin hadisin ma aiki (SAW) inda yake nuna cewa bbu yan kewa daga aure wai domin mutum yaje yai ta iba da wanan kuwa yana faruwa sosai da sosai a cikin wannan zamanin domin sautari zakaji wai wani ko wata tana cewa ni wallahi ba zanyi aure ba domin da nayi aure gwara na zauna ina uba da sallah ko azumi, tofa wannan maganar kuskurene kuma ba haka ko yar war manzo SAW ta ko yar ba domin shi yace yanason ya zama a'ummarsa itace mafi yawan sauran al'umman da suka gabata don haka dolene muso abinda annabinmu yake so.
Share:

Monday 21 March 2016

BANA KAUNARKA!!! 38

bana-kaunarkajpg.jpg BANA KAUNAR KA!!! 38 MUHD-ABBA~GANA 09039016969 -------------------------------------------- na fadi haka ne don in tura masa haushin ni dai yaya ka bani key din motar in tafi kwa taho,anty mahida zo mu tafi,no ni sai ya amin zai tafi shikenan ni ku bani in tafi in yaso ku direba yazo ya dauke ku ya amin ya mike mukai sallama musu sallama har kuzo kuga zugar yan rakiya sai kace shugaban kasa zasu raka an raka mu bakin mota amir yai saurin bude min mota na shiga to anti mahida sai naxo mahida ta kalle su da fatan zaku zo bikinmu?ina gayyatar kowa da kowa insha Allahu zamu zo goode bye,suna daga mana hannu ya amin yaja mota.tun kan yayi fakin na hango abba zaune yana kallonmu toh abba ya dawo muka fito gunsa muka nufa abba sannu da zuwa kuya kamata inyi wa sannu ku da kuka iso yanzu daga ina kuke mahida tace abba daga gidan baba rabi'u muke na ce la! wallahi abba karya take abokin yaya muka je muka taya murnar bikinsu kaga abba inba ma zuwa muma bbu me zuwa namu yauwa wahida gwanda da kika fada min gaskiya,ya amin yace abba kayi hakuri abba murmushi yayi yace kunci arzikin auta amma da duk sai na muku bulala, mahida tace abba tsaya kaji.....ni ba ruwana dame karya wai tace tawa mahida tace ni kuma ta mom da ya faruq yace ai shikenan ku wuce muka shige mahida tace me yasa kika fadawa abba gaskiya? ya amin yace gwanda data fadi gaskiya ai gaskiya dokin karfe ce in kin kula sam wahida bata iya karya ba. abba zaune yace abinda yasa na tara ku shine ina son hada aure tsakanin wahidda da shahid amma ba tare da sanin wahida ba har sai ranar da shahid din ya dawo dakin yayi tsit ba wanda yace kala abba yace alamin kayi shiru gaskiya abba ina gudun rikincin wahida shi yasa nake so a fara sanar in ta amince shi kenan ya faruq yace haba alamin wai me yasa kake nuna kana tsoron wahida ne mune sama da ita ko itace sama da mu? ni shawarata anan itace in an tashi bikinsu mahida kawai a hada a daura musu aure in yaso a bar wahida a gida har sai bom boy ya dawo yanxu a sanar da smallboy shi zai yi komai,mahida tace haka shine daidai sannan ko bayan daurin auran abba kar ka hanata zuwa makaranta mun riga mun san halin wahida zata kare mutuncinta sauran dabara kuma ta mom ce sai a san yadda akai mata wayo aka boye mata. al'amin ya kastse ta wai me ku ka dauki wahidar? kuna nufin bata da hankali ko karamar yarinya ce? ni dai wallahi bbu ruwana, abba shawara ka samu wahida ka sanar nata inta amince na amince, in kuma bata amince ba ina bayan yar uwata yana kai aya ya bar dakin.zaune nake ina kallo ko da filim din ya kare sai na kashe na nufi dakin ya amin domin in samu wani kaset din nai sallama yana zaune ya hada kai da gwiwa ya dago nace ya amin lafiya yace lafiya amma ba lau ba na zauna kusa dashi meke damunka big brother yai murmushi yace ba komai bane illa ina tunanin big brother wafa bomboy tuni na tuna irin cin fuskar da bomboy yai min bbu wani namiji daya taba yi min makamancinyarta ban san sanda naja tsaki ba. Abbagana hausa novels @ facebook. www.abbagana.pun.bz
Share:

Friday 18 March 2016

BANA KAUNARKA!!! 37

bana-kaunarkajpg.jpg BANA KAUNAR KA!!! 37 MUHD-ABBA~GANA 09039016969 -------------------------------------------- kamar yadda nake yi a makaranta sam bana kula samari kai hadda dattawan na kance ammin mji,amma an kusa bikina in naga zaka takura min in ma fata-fata.salamu alaikum,sai dana dan firgita domin ban san zuwan sa ba amin wa'alaikas salam,ya tsungunno sannu bebi ni sunana umran s sulainman tunda kuka shigo gurinnnan na kasa samun sukuni ina son inyi miki wata magana sai dai ki min kwarjini maganar gaskiya naji na kamu da sonki nai murmushi nace ah maganar gaskiya sai dai kayi hakuri domin tuntuni am mana miji ya wani zabura kin san koni waye? nai masa kallon sama da kasa ba shi da wani kyau na tabe baki yace waye shi wanda aka zaba mikin kin san Allah zan iya gogawa dashi nai murmushi na rasa wa zan ce masa sai dabara ta fado min nace ka san shahid yaro dan kwalisa,wai bomboy kike nufi nace ashe ma kasan shi gani nai ya sara min yace na barki lafiya nai murmushi,ina nan zaune sai ga wani guy yace sannu hajiya nace yauwa alhaji to ni sai sunana small ismail na jima ina ganinki sannan na dade ina fama da sonki domin na fuskanci ke yarinya ce nitsattsiya nayi bincike akan gidanku mahaifinku mutumin kirkine,da fatan zaki amsa tayina to mallam small na gode ainun batun so kuwa nima ina sonka da wannan damar kuma nake baka hakuri domin maganar gaskiya am min miji na gode da kika fada min gaskiya don Allah ya sunanki "wahida sulainman muhd,to wahida na gode. wani guy yazo yana zuwa bbu wata sallama ya tsunguna gabana sannu bebi ban kalle shi ba nace bomboy ya kamata mu tafi gida what me kika ce? nace sorry na dauka shahid ne what ina kika san bomboy? nace ban gane ba ai yau saura wata biyu bikinmu kina nufin ke bomboy zai aura,ko ba mu dace da juna bane? no ba haka bane ina mamaki to ko za kai takara dashi ne? no ni da bomboy bama haka na hakura.wani guy ne ya nufo ni hadda masu take masa baya tun kan ya karaso kamshin turaransa ya cika gurin yana zuwa ya tsunguna ya kamo hannuna wata wawuyar sumba ya kai min na kuwa tofa masa yawu tare da fizge hannuna a fusace,nace kai wanne irin dabba ne a fusace shima ya mike yana shirin sharara min mari aka rike shi ta baya,yana kar ka taba musu bebi ka barni in duke ta in yaso inga uban da ya tsaya mata,ita kuwa take da mai tsaya mata kasan ko waccece kar ka yadda ka tafka abin kunya,domin wannan yarinyar kanwa ce ga abokinku bomboy,sannan ta wani bangaran mata domin an kusa bikinsu.....ido ya zuba min da alamu kunya ce ta kama shi na mike da sauri na bar gun,gun motar mu na koma abin haushi har gun motar aka dinga bina raina ya baci na kudirce a zuciyata ni da zuwa fati sai de a aljanna.yaya ni dai gaskiya zan tafi amir yace haba anti wahida ko dan kinga bomboy baya gurin nai murmushi nace ai yanzu muka gama magana ta waya da shi sai sa ma ban damu ba, Abbagana hausa novels @ facebook. www.abbagana.pun.bz
Share:

Thursday 17 March 2016

BANA KAUNARKA!!! 35

bana-kaunarkajpg.jpg BANA KAUNAR KA!!! 35 MUHD-ABBA~GANA 09039016969 -------------------------------------------- mahida ta mike ni na gaji da jin wannan labarin ya amin yace don Allah zauna mahida mu gama ji ma na muji karshen toni yaya haushin jauro nake ji nai dariya nace ai kuwa babankine tunda mijin babarkine Allah ya sauwake talakan sai,ya faruq ya harzuka tuni muka yi shiru mom taci gaba. koda na kulle mata na kuma kashe kunamar na shafa mata ruwan sai taji dadi har tace in kwantar da hankalina zata kubutar dani nace na gode,amma don Allah ta bari a yankani domin in na fita ban san inda zani ba,ta girgiza kai tace ba zan bari ba yanzu shekarunki nawa? nace sha uku domin shadaya akai min aure gashi ina da shekara biyu ta sani a hanya har titi sai sai sam bana cikin hayyacina,saboda haka wata mota na zuwa tai gaba dani daga nan ban san me ya faru ba illa na farka na ganni a wani kayataccen guri ina bisa gado me dan karan laushi,sanyin AC da kamshin wani irin turare....wata farar mace sanye da farar kaya ta shigo tace min sannu,nace yauwa ta min aune aune sannan tace me yake damunki yanzu na nuna cikina tace wannan sai a hankali saboda barin da ki kayi cikin jikinki ya zube,ku tashi kuyi sallaha ina yaso sai in karasa muku,wayar mahida tai kara ta dauka haba kinga na kalle ta haka aka iya soyayya Allah ya shirya ku,ku ko gajiya bakwa yi,to ina ruwanki ni bana son shiga sharu ba shanu la!! ya amin ka ji tace min shanuwa ko,yi hakuri ke mahida kar ki kara ce mata shanuwa,don Allah ya faruq kaji nace mata shanuwa? ke ni kar ki dame ni ku kenan fada kamar kaji. ina kwance jikin mom suka soma shigowa mom taci gaba,matar na tambaya don Allah a ina nake tace min a kano tace wanda ya kawo ki anjima zai zo nace to.da yamma ina zaune yayi sallama saurayine kyakkyawa in kunga al'amin kun ganshi hannunsa ya zuba cikin aljihu yana kallona na sunkuyar da kai tare da gaishe shi ya amsa yana me tambayata jiki nace da sauki,yace baki sani ba ko na daga kai ya ce nine wanda na bige ki a kaduna sai dai ina sauri ban tsaya a asibitin can ba,na kawo ki nan ni sunana sulainman muhd radda,mahida tace iye iye abban mu ne fa ya faruq ne ya doketa.koda ya bukaci jin labarina ba abin dana boye masa ya tausaya min haka ya dinga ziyarata wataran yakanzo shi da kanwarsa khadija wataran kuma shi da babarsu koda aka sallame ni ma gidansu na koma kanwarsa khadija na soma sani kuma tana hidima dani haka mahaifiyarsu sam bata nuna min kyama na basu labarina ta tausaya min sannan tai min alkawarin rike ni fisabillilahi sai dai me koda yayansa ya dawo ya samu labarina akai masa bayani ai sai ya dinga bala'i muddin yana numfashi sai na bar gidan hakan kuwa akayi sai da yaya yasan yadda yayi ya fitar dani,na rasa inda zani gani dai naje titi amma sam na kasa tsallakawa,sai kalle_kalle kawai nake,oh ni Allah kai min magana wata mota ce irin ta sulainman tai fakin kusa dani mai motar ne ya fito ya jima yana kallona da alama yana mamaki ganin ya juyar da kaina bani da niyyar yi masa magana sai ya karaso, Abbagana hausa novels@ facebook. www.abbagana.pun.bz
Share:

BANA KAUNARKA!!! 36

bana-kaunarkajpg.jpg BANA KAUNAR KA!!! 36 MUHD-ABBA~GANA 09039016969 -------------------------------------------- maryam zo mu tafi gida nayi shiru yace wai ma me ya fito dake? bbu abin da na boye masa zo mu tafi yace,ni fa bbu inda zani da kyar ya shawo kaina na bishi mahaifiyarsu taiwa yayansu fada sosai sai dai bbu wata sakewa da nake a gidan domin ya kasa ya tsare kullum cikin zagina yake sam ban damu ba tare amai bikinmu da kanwarsa khadiya,Allah yayi mata rahama ameen. ba zan taba mantawa da karamcin da wadannan bayin Allah sukai min ba shekara biyu khadiya ta haihu tsiranmu kwana goma na haife ku shekara takwas tsakaninku dasu wahida wannan shine labarina.Al'amin yace mom yaushe zaki koma? mom ta girgiza kai tace agaskiya nayi missing din iyayena amma ina tunanin yanzu bbu su,na mike nace gaskiya mom ni sai naje garinku koda kuwa su baffa sun mutu mahida tace tabbas nima sai naje ya amin ma yace shima za shi ya faruq yace nima zani kai nima sai na bisu amma sai na kulle baffa dariya sukai,sallamar abbanmu muka ji a falo da gudu muka fita,abba sannu da zuwa yauwa ya miko min wata leda gashi nan ke da antinki,yabawa ya faruq shi da ya amin ya wuce dakinsa.washe gari misalin karfe 5:10pm ina zaune ina kwalliya ya amin ya shigo wahida gama kira kani unguwa nace to na shirya cikin wani arnan materials mai tsananin kyau daman ranar sallah bom boy ya dinka mana mu uku ni da mahida da mamy,material ne me kyau da tsada yasha aiki kamar ba a san ciwon zare ba,hatta fashion din da nai amfani dasu bom boy ne ya sai min kasancewar baya siyan abin banza akwai tsada akwai kyau ina fesa turare mahida ta shigo tace ke wahida ki dinga jin tausayin turaran mana,na harare ta ya amin ya shigo shima yayi kyau ya kalle ni kin yi kyau nai murmushi ya kalli mahida ba zaki ba ta tabe baki ta ce ba inda zani yace duk wannan kwalliyar? tace ya haidar nace Allah ya kyauta haka dai ku ka iya har mun fita sai gata da gudu wai zata.wahida zo kiji don Allah ki ban farin mayafinki ban ga nawa ba nace yana cikin kayana fararan mayafi takalmi da jakarmu duk farare mu kai amfani dasu mom ta kalle mu tace har kun shirya? muka ce eh,tace Allah ya kiyaye.yaya wai ina zamu? ina wannan aminin nawa wanda suka zo kwanakin baya shida amir? eh to bikinsa akeyi karku so kuga irin naci da yai min in zo da ku wani kayataccen hotel akai fatin muna yin fakin muka fito sam bana son kallo tuni na dabarbarce ganin yadda akayo kanmu da ido da kyar na saita kwakwalwata muka soma tafiya a nutse ango da amarya muka ga sun fito mu gaskiya an karrama mu kasancewar bana son hayaniya saina mike na canza guri ina zaune ni kadai kan kujera naji dadin zama a gun domin tsalle_tsalle ake ganin mutane ai kuwa samari suka yo min ca sai dai koh kallo basu isheniba, Abbagana hausa novels @ faceebook. www.abbagana.pun.bz
Share:

Wednesday 9 March 2016

BANA KAUNARKA!!! 34

bana-kaunarkajpg.jpg BANA KAUNAR KA!!! 34 MUHD-ABBA~GANA 09039016969 -------------------------------------------- amarya ta tare iyayan jauro masu kirki sai dai suma basu da hali domin duk rashinmu mun fi su hali domin su tun safe za a dama kunun nono shine abincinsu sai kuma wata safiyar sam ba a ruwo sai ranar sallah sai dai madarar shanu in kana so ka tatso shi kuwa jauro tun safe inya fita sai can dare a waje yake siyan abincinsa mai rai da motsi a haka na soma laulayin ciki kasancewar cikin na bani wuya ga yunwa duk sai nabi ba tsotse gashi mahaifiyar jauro sam bata tausaya min tunda ta fuskanci ina da ciki sai ta shiga muzanta min komai ni zanyi gashi yanzu jauro in ya fita ya kan yi sati,sati biyu baya gida wata dawowa da jauro yayi tun kan ya huta inna tai kiransa bi ban san abin da ta sanar masa ba ya dai kama ni da duka sannan yace inje gida tun kan naje ya hau mashin yaje ya shirya min karya gun babana ban san abin da ya fada ba a kofar gida na tadda bbana na tsunguna ina gaidashi yace haba yarinya ai mijinki ya fada min komai ashe in baya nan yawon banza kike kinje kin samo ciki kin zo kin manna masa ko to kin wa kanki amshi takarddarki yace ya sake ki anshi nace,hannu nasa na amsa ina kuka ki kama hanya ki san inda dare yayi miki don ba za ki haife min shege a gida ba,na tsunguna ina kuka ina bashi hakuri amma faruq yace sai na bar masa gidansa ganin dare yayi nace don Allah ya barni in kwana gobe na nemi hanya nan yayi ta zagina yana tsine min ganin yana tara min jama a sai na tafi ina kuka ga duhu ban san sanda naje titi ba wani mai mota ya faka kusa dani yace baiwar Allah shigo in rage miki hanya nace to ko da na shiga ban kuma sanin inda nake ba sai farkawa nai na ganni a wani katon gida girman gidan ya wuce hankali.na kalli wasu mata dake ta kuka nace bayin Allah me ya kawo ni gidannan matan suka ce suma basu sani ba domin wani mutum ne ya kawo su gabana ya fadi nan nai ta addu a cikin zuciyata wani katon mutum shirgege yazo inda muke ya ce zan shiga dakinnan daya bayan daya ku dinga shigowa yana shiga aka dinga shigar da mu ashirin ne ni ce ta karshe ina shiga sai naga dukanninsu an musu aski nima zura kaina akayi cikin inji sai ma fafur inji yaki tashi sai dai wata kara ya dinga yi ka ka ka ka mutumin ya fusata ganin ina bata masa lokaci sai ya dinga dukana amma a banza mikewa yai ya fita bai jima ba ya shigo shi da wata mata suka nuna ni suna magana da turanci ni dai ban san abin da suke cewa ba na dai ga taja hannuna matanan ina jin ihunsu wasu na addua ni kuma zama nai nayi ta kuka ina zaune tace in yanka mata albasa ita kuma tana yankan alayahu sai kunama ta harbe ta tai ihu da sauri na kulle mata kafar da dankwalina sannan na kashe kunamar.mahida ta dinga dariya tace mom ci gaba muji ko sun yanka ki nace bbu yanka fa bada sun yankata ma ganta wai ba zaku yiwa mutane shiru ba munyi shiru mom ci gaba mahida don Allah kiyi shiru ki barta zata laftu inta ji saukar socket. Abbagana hausa novel@ facebook. www.abbagana.pun.bz
Share:

Sunday 6 March 2016

BANA KAUNARKA!!! 33

bana-kaunarkajpg.jpg BANA KAUNAR KA!!! 33 muhd abba gana 09039016969 -------------------------------------------- ya amin yace mata meya hada ku ta ce zagi wahida fito na fito nace ya zanyi ta dinga raina min hankali wai acikinku waccece babba? da sauri wani abokin yaya saifu yaya amin yace ke wahida bata hakuri yaya itace fa ta fara tsokanata ni dai nace ki bata hakuri kiyi hakuri mun juya zamu tafi yace kuzo nan baku iya gaisuwa ba ko ba kuga baki nai ba na kalleshi kunya ta kama ni da gudu na fita dakin mom na shiga na kwanta jikinta mahida ta shigo nace mahida don Allah kama min kaina ai kuwa sai dai ki mutu.....please anty wahida, ina kwance ina yiwa mom hira har bacci ya soma daukata,mahida ce tace daga ganin yadda wahida take lumshe ido bacci zatayi mom tace ai gwanda tai bacci muma mu huta da rigima,mahida tace mom in tambaye ki ina jin ki kar fa kiji haushi mom tai dariya wanne irin haushi wai mom ina iyayenki? ban taba ganinsu ba ko sun mutu in sun mutu ina ne garinku sannan ina yan uwanki? hawaye mom suka digo min a kumatu,zumbur na mike ke mahida dan me zakiyi wa mom irin wanan tambayar me daga hankali,wai ma ina ruwanki gashi nan ai gashi kin sata kuka ya amin ne ya shigo ganin mom tana hawaye duk sai ya rude ya tsunguna gabanta yana fadin lafiya nace ba mahida bace ta saka ta kuka meye tayi mata? wai cewa tayi mom ina iyayanki ban taba ganinsu ba ko sun mutu in sun mutu ina yan uwanki,ina ne garinku kuma kina da yan uwa koke kadai ce? ya amin yace kiyi hakuri kin ji mominmu ke kuma mahida kar ki kara yi mata irin wannan tambayar mai tada hankali mom tace ba komai ku kira faruq sai in baku labarina ya amin ya kira faruq suka nutsu kamar masu cin dan wake don jin labarin mom. Da farko dai ni sunana maryam mahaifina mallam abdulkadir haifaffen gyambu ne auran zumunci akai musu shi da mahaifiyata fulani ne sosai mahaifiyata ta kasance tana tallan nono kasancewar mahaifina ba shi da hali koda ta haife ni sai ya kasance muna tallan nonon tare ko dana girma sai nace inna ta zauna ni zan ci gaba da yin tallan,mahida tace Allah ya kiyaye in yi tallan nono yaya yasa kafa ya doke ta mikewa tayi ni bazan ji labarin mom din ba nina dauka iyayen mom masu kudine kamar abbanmu,ya faruq yace in baki zauna ba sai na duke ki da sauri tace na zauna yi hakuri yaya nace sannu yar masu kudi waya sani ma koda abban dako yake yi sai lokacin ya amin yai magana yace ku tashi ku fita yaya yi hakuri ni dai ba zan kuma magana ba mom cigaba. a wanan lokacin na hadu da wani saurayi wai shi jauro ya nuna yana sona domin kullum naje kasuwa sai ya goyo ni a mashin dinsa ya kawo ni gida abu kamar wasa har aka sa ranar bikinmu da jauro,amma har lokacin ina tallan nono mahida tai tsaki domin bbu abinda ta tsana irin tallah bbu wanda ya kulata koda lokacin biki ya zagayo akayi biki irin na al'adarmu an daura aure anzo an min jere iya bakin kokarin iyayena sunyi kokari. Abbagana hausa novels@ faceebook. www.abbagana.pun.bz
Share:

Friday 4 March 2016

BANA KAUNARKA!! 32

bana-kaunarkajpg.jpg BANA KAUNAR KA!!! 32 MUHD-ABBA~GANA 09039016969 -------------------------------------------- haidar ya tabbatar masa zai dinga ziyartatsa akai akai lokaci daya suka shige mota ni dama daga nan nima na tari mai adaidaita sahu domin ga kaini gidansu wahida,domin ba zan iya bin bom boy ba saboda ina tsoron sojoji ainun.ina zaune ina tunanin abin da ya hada mu da bom boy tabbas ina son munafintar kaina maganar gaskiya ina son bomboy sai dai yanzu haishinsa nafi son nasa rinjaye bomboy mashayi ne inalillahi bom boy.........ya amin ne yai sallama ya zauna kusa dani yace yar uwata me yake damunki na ga duk kin canza na lumshe ido nace nothing,ya kuka yi da mutumin? wafa? amir mana na taba baki ni ban ce masa komai ba asali ma ko wayarsa bana dagawa ya kalle ni cike da mamaki kin tabbata bbu wata magata ta batanci da kika fada masa? wacce irin magana sai dai in bom boy don shi na bawa wayar...........haba shi yasa ni na san da walakin,ina zaune amir yayo min waya wai ya fasa auranki ya janye maganar neman auranki nina rasa dalili duk yadda akayi wani abun bom boy ya fadawa amir amma bari inje gidan bomboy din ya mike na bishi da kallo har ya fice.mahida tace"Allah ya haidar ina tunanin sabani suka samu tsakanin bom boy da wahida,wallahi duk tunaninta na gidannan ta kwashe tasa su kasan filo.haidar yace ni ai nasan sunyi fada domin har nina daukota daga get din gidanmu na kawo ta gida kuma daga alama ta batawa bomboy rai domin cewa yayi ba zai dawo ba sai fa mata mahida tai murmushi tace lalle ran maza ya baci ni kaina duk na cina ta fada min abin da ya hada su taki gashi koda yaushe tana cikin damuwa wani lokacin kuma sai tai ta kuka gaskiya abin yana damuna dan ba yadda zanyi domin wahida tana da zurfin ciki dani ce dai da tuni na fada mata ko dan ta bani shawara.ina kwance jikin mom tace wahida wai me ya hada ku da shahid? mom bbu komai illa na fito face to face na fada masa i don't like you in da sabo wannan kalma bomboy ya saba jinta amma tsabar naci ya mannen sannan nace in har ya cika shahid alitu muhd kar ya dawo daga legas sai da mace ma'ana yayi aure ba abin daya shafen,ke auta haka kikace masa so what a kan me zai takura min in ban da naci nace bana sonsa bana kaunarsa dan me zai takura min?mahida tace nina san ruwa baya tsami banza don ubanki maga wanda zaki samu me sonki da gaskiya shima shahid dinne ya manne miki amma kamar shahid wanda yanmata suke rububinsa har zaki wulakanta Allah yasa in zai dawo ya taho da matar muga karyar wulakanci,wahida kin mare shi akan yace yana kaunarki kin zage shi akan yana sonki kin tofa masa yawu.......to wai ina ruwanki banza uwar shishigi yar ficika sunan data tsana da gudu ta biyo ni nai dakin yaya ina mata gwalo.abin kunya abokansa sun cika dakin na riga na shiga don haka nai bed dinsa bayan sif dinsa ina boye ta shigo tana wallahi sai na dokeki, Abbagana hausa novels@ faceebook. www.abbagana.pun.bz
Share:

Tuesday 1 March 2016

BANA KAUNARKA!!! 31

bana-kaunarkajpg.jpg BANA KAUNAR KA!!! 31 MUHD-ABBA~GANA------------------------------------------- bbu shiri ban san sanda ya raba ni da kayan jikina ba gaba daya ya gama kidimewa ganin irin baiwar da Allah yai min gaba daya ya gama hautsinani ya gama fita daga hayyacinsa kuka nake tuburan bom boy na gaf da cimma mugun burinsa sai naga yaja da baya tare da sakin oh na manta ina fashin sallah kwalbar nan ya jawo hakori yasa ya balle murfin ya kafa ban ankara ba sai kwalbal na gani ya dire,innalillahi wa inna ilaihi rajiun,tuni na zube gun ina gunjin kuka oh my god,nai sairin saka kayana don kar ya soma haukan yayo kaina gashi kallona kawai yake ina kuka ina karawa ganin ya kwalalo min ido na kara tsurewa ko hijabi ban sa ba nai saurin ina shirin barin dakin yai kirana wahida zo wahida kar ki gujeni zo wahida ba halina bane ya mike yana tangadi ganin ya biyo ni na zura a guje.zubewa yai a gurin ya saki wani marayan kuka wanda tunda ya mallaki hankalinsa bai taba tin makamancinsa ba,wahida me yasa ba kya sona? me nake dashi wanda bai miki ba to ke aikina ne ba kya so an sa min billahillazi la'ila ha illa huwa in har ba kya so a yau sai na cire kaki wahida sonki sai ya dafe kirjinsa haka nan ya dinga kwara wani irin amai a cikin zuciyar ya dinga kiran sunan Allah ya yaye ma son wahida in har ba alkairi bane ubangiji Alllah ya yaye masa in kuma alkairi ne Allah ya kwantar da son wahida ya karkato da hankalinta gare shi ta so shi fiye da yadda zata so kanta amai ya dinga yi har ta hanci cikin ikon Allah sai ya samu nutsuwa yana jin matsanancin sonta amma da sauki. wanka yai ya shirya kayansa aka ra min kil ya fito cikin kananan kaya ya kare falon kallo shi kenan na koma legas gida sai na dawo amma na dau alwashin ba zan taba dawowa ba sai da mata,zan ba wa wahida mamaki,waya sa tashin ga ringin gani nan kawai ya ce ya kuma kashe waya manyan hotunan wahidar ya diba ya fita yana rungume fa su bomboy kenan son wahida kaunarta sun hadu sun gama yi masa illa Allah yayi mana tsari damu ya dauka ya matsa kusa da dakinsa ya rubuta da manyan haruffa DAKIN WAHIDA,sannan cikin hanzari na fita.wahida na fitowa taci karo da haidar kanin shahid bai tambaye ta dalilin kukanta ba ya bude mota kawai ta shiga yaja gida ya kaita yana dawowa daga kaita sukai kacibis da bomboy shi yana shirin shigowa bomboy na shirin fita gaba daya suka fita suka rungume juna haidar na dariya ya dago yace bomboy yai tsaki yace ka kula da gida small boy duba dana sonka ba na san wasa ban da tara shashan abokai zaka dinga jina anytime ka dinga bude gidana kana gyara min insha Allahu ba zan dawo ba sai da mata small boy ya zaro ido dariya da tausayin dan uwansa ya rungume bom boy yana hawaye bomboy dago dan uwana please big brother na san irn son da kake yi jaruntaka in kana kuka mahida zata raina ka please na san kan na dawo amarya ta tare zan aiko ma komai na lefe da sadaki tukuncina in dawo in tadda beby me sunan antinmu sukai dariya tare da yin musabaha, Abbagana hausa novel @ faceebook. www.abbgana.pun.bz
Share:

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).