shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday 9 March 2016

BANA KAUNARKA!!! 34

bana-kaunarkajpg.jpg BANA KAUNAR KA!!! 34 MUHD-ABBA~GANA 09039016969 -------------------------------------------- amarya ta tare iyayan jauro masu kirki sai dai suma basu da hali domin duk rashinmu mun fi su hali domin su tun safe za a dama kunun nono shine abincinsu sai kuma wata safiyar sam ba a ruwo sai ranar sallah sai dai madarar shanu in kana so ka tatso shi kuwa jauro tun safe inya fita sai can dare a waje yake siyan abincinsa mai rai da motsi a haka na soma laulayin ciki kasancewar cikin na bani wuya ga yunwa duk sai nabi ba tsotse gashi mahaifiyar jauro sam bata tausaya min tunda ta fuskanci ina da ciki sai ta shiga muzanta min komai ni zanyi gashi yanzu jauro in ya fita ya kan yi sati,sati biyu baya gida wata dawowa da jauro yayi tun kan ya huta inna tai kiransa bi ban san abin da ta sanar masa ba ya dai kama ni da duka sannan yace inje gida tun kan naje ya hau mashin yaje ya shirya min karya gun babana ban san abin da ya fada ba a kofar gida na tadda bbana na tsunguna ina gaidashi yace haba yarinya ai mijinki ya fada min komai ashe in baya nan yawon banza kike kinje kin samo ciki kin zo kin manna masa ko to kin wa kanki amshi takarddarki yace ya sake ki anshi nace,hannu nasa na amsa ina kuka ki kama hanya ki san inda dare yayi miki don ba za ki haife min shege a gida ba,na tsunguna ina kuka ina bashi hakuri amma faruq yace sai na bar masa gidansa ganin dare yayi nace don Allah ya barni in kwana gobe na nemi hanya nan yayi ta zagina yana tsine min ganin yana tara min jama a sai na tafi ina kuka ga duhu ban san sanda naje titi ba wani mai mota ya faka kusa dani yace baiwar Allah shigo in rage miki hanya nace to ko da na shiga ban kuma sanin inda nake ba sai farkawa nai na ganni a wani katon gida girman gidan ya wuce hankali.na kalli wasu mata dake ta kuka nace bayin Allah me ya kawo ni gidannan matan suka ce suma basu sani ba domin wani mutum ne ya kawo su gabana ya fadi nan nai ta addu a cikin zuciyata wani katon mutum shirgege yazo inda muke ya ce zan shiga dakinnan daya bayan daya ku dinga shigowa yana shiga aka dinga shigar da mu ashirin ne ni ce ta karshe ina shiga sai naga dukanninsu an musu aski nima zura kaina akayi cikin inji sai ma fafur inji yaki tashi sai dai wata kara ya dinga yi ka ka ka ka mutumin ya fusata ganin ina bata masa lokaci sai ya dinga dukana amma a banza mikewa yai ya fita bai jima ba ya shigo shi da wata mata suka nuna ni suna magana da turanci ni dai ban san abin da suke cewa ba na dai ga taja hannuna matanan ina jin ihunsu wasu na addua ni kuma zama nai nayi ta kuka ina zaune tace in yanka mata albasa ita kuma tana yankan alayahu sai kunama ta harbe ta tai ihu da sauri na kulle mata kafar da dankwalina sannan na kashe kunamar.mahida ta dinga dariya tace mom ci gaba muji ko sun yanka ki nace bbu yanka fa bada sun yankata ma ganta wai ba zaku yiwa mutane shiru ba munyi shiru mom ci gaba mahida don Allah kiyi shiru ki barta zata laftu inta ji saukar socket. Abbagana hausa novel@ facebook. www.abbagana.pun.bz
Share:

3 comments:

 1. Slm, se jira nake a cigaba wlh. An ja mana rai a wannan lbrn dayawa wlh. Gud work

  ReplyDelete
 2. dan allah ka dan dinga turo muna in time plz

  ReplyDelete
 3. IBNKATHEER ZULQARNAIN AHMAD16 March 2016 at 09:45

  What is happing 4 dis days no post bros???

  ReplyDelete

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).