shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Friday 27 May 2016

WAYE SANADI??? 21---24

waye-sanadi.jpg

WAYE SANADI?

21


MUH'D*ABBA*GANA
09039016969

www.abbagana.pun.bz


ihun data ji na saki ne ya sata katshe maganar "dole ne sai na gode masa wallahi in dai sai nayi masa ne kar ya ban ni kawai ki mai dani dangin babana,tunda ke bakya kaunata ina maganar ina hada kayana "ki mai dani dangin babana, ita ce kalmar da take yawan yi mata ciwo a cikin kunnenta ganin zan fita daga dakin yasa tayi saurin rike hannuwana "nana yanzu ban isa nayi miki fada ba to tunda haka ne nayi miki alkawarin duk abinda zaki bazan kara yi miki fada ba kiyi hakuri ki zauna tana fadan haka ta fita, washe gari karfe tara da rabi na shirya cikin farar doguwar riga me adon duwatsu tayi min kyau sosai takalmina milk colour high hills na jawo durowa na dau glass dina fari siriri na dora nace yau dai bara na dau wayata. na fita dakin umma na fada cewa zan tafi makaranta gashi inji daddy ya shigo kina barci dubu biyu ta mikon na juya na fita kai tsaye wayen motata na nufa sai daukar ido takeyi me kyau 2007 fara sol maryam na hanga tana jiran direba na shiga na bata wuta na tafi nayiwa maryam bye bye wata uwar harara ta zabgan nayi mata murmushi na fita jina nake cikin nishadi mara misaltuwa in da muka saba daukar sadiya nan na tsaya na san tana hanyar fitowa. waya tace naji tayi kara alamun shigowar message ne suka shigo har guda uku, nana me yasamu wayar taki tsawon kwanaki a kashe dayan kuma akace: nana duk inda kika shiga cikin duniyar nan ba zaki guje min ba mutum baya gujewa kaddararsa muna tare har abada wani kuma yace; ni nasan muna tare gara ki tsaya ki fahimce ni duk inda kika shiga imran mai nemo kine. ganin sadiya a sanyaye na bude na fito zuciyata cike da tunani baki ta saki tana kallona har na karasa "meye haka kin wani saki baki sai kuda ya fada miki sufy kice yau ke kike jan motar to ko ban dace ba no wallahi ban taba ganin macen da take jan mota tayi mata kyau ba sai ke gaskiya kin dade fitowa fa darajarmu a B.U.K kinga kinzo mu tafi lokaci yana tafiya muna shiga kira ya shigo wayata sufy kina jin calling "sady lamarin wannan me kiran nawa yana bani tsoro ban gane ba "wrong number yayi ta kirana nafa gaya masa wrong ya kira amma kullum sai ya kira har kiran sunana yake abinda matukar mamaki kuma yana tsoratani".


Abbagana hausa novels @ facebook.
WAYE SANADI?

22


MUH'D*ABBA*GANA
09039016969

www.abbagana.pun.bz


kin ga message din shi bayan ta gama dubawa ta dago tana girgiza kai gaskiya shawarata kawai karki kara gayawa mutumin nan magana inkina son kanki da arziki dai anyo ko mutum ne kibi a hankali dan ya rabu dake duk lokacin daya kiraki ki daga kuma kar kice zaki masa rashin kunya "sadiya wallahi har tsoron wayar nake ni kawai yarda ita zanyi na huta ke waya gaya miki in kin yar kin huta a yani duk inda kika shiga kuna tare kawai kawai ki dau shawarar dana baki shikenan sadiya na gode tunda muka shiga makaranta ake kallonmu duk inda muka shiga nuna mu ake har mukayi parking muka fito sufy kallo ya dawo kanmu duba ki ga mutumin naki na juya ina kallon ina ta nunan saifu na hange shi zaune da abokinsa duk suna kallonmu muna hada ido ya sakarmin murmushi ya dagan hannu fuska na hade hannuna biyu nayi masa umbola naja hannunta muka tafi muna shiga class sakon m.yusuf ne ya same mu na same shi a office sadiya zaki raka ni gaskiya kawata bbu inda zani kawai kije ki dawo bani wayarki nayi game ban koyi sallama ba na shiga in da kai tsaye nace "gani" nana safiyyya mukhtar ki zauna mana ina da abinyi to nana ina maganar mu ta kwana ban dau maganarka a bakin komai ba tunda ba ita ce a gabana ba ina na riga haba ka amsa bana sonka dan ba soyayya nazo yi ba nana saffiya nima bance muyi soyayya ba aure nake so muyi sannan ina sonki please ki taimaka ki karbi soyayyata kanan......... kan ya karasa nayi ficewata sadiya na tarar akan mota na har kin fito? to kwana zanyi wallahi sadiya zan rufe idona na zabgawa malamin nan rashin mutunci,ki dai bi a sannu tun dazu nake kiran number taki shiga sai yanzu......"Assalamu alaikum sunana sadiya dawa nake magana ke baki san dawa kike magana ba gaskiya ban sani ba a a towa kike nema? ina neman wanda yake kiran kawata nana safiyya inji meye nufin shi a kanta sannan imran salis,ni dan nigeria ne karatu ne ya kaini america zan kira momyna kira wrong number bazan boye miki ba ina son kawarki taki tsayawa muyi magana ta fahimta kullum sai fada sai zagi ki taimaka ki shawo kanta".gaskiya ka dau babban aiki dan kuwa bauddaden hali gareta musamman akan maza amma ya akayi kasan sunanta??


Abbagana hausa novels @ facebook.

WAYE SANADI?

23


MUH'D*ABBA*GANA
09039016969

www.abbagana.pun.bz

ran da muke waya da ita kanta kashe naji wata ta ambaci sunanta shine naji nana safiyya bata da kawa ni daya ce kawarta nace maka wani irin hali gareta? ita fa yanzu.ta daukeka a matsayin aljani kafa bata tsoro sosai" yauwa sadiya naji dadin wannan labarin kuma zan so ace kin boye mata cewa baki sanni ba karki nuna mata kin yi waya dani kuma dan Allah kici gaba da tsoratar da ita kanni aljanine sannan ina so ki dinga gayan wani abu daya faru akanta wanda kike ganin zata kara tabbatarwa ni aljanine shikenan imran zan yi maka kokarin okey na gode sadiya nafi wata uku ban ji wayar aljani nan ba wanda a wannan lokacin shekara ta biyu a makaranta yau muna zaune da sadiya da kuma sabuwar kawarmu mai suna rukayya wanda nake kira da momy waya ta tayi kara nasa hannu na dauka na shiga uku sadiya aljani ya dawo waye kuma aljani? inji rukayya to kinga ki nutsu ki daga to sadiya ya zance kiyi masa sallama hannu na yana rawa na daga cikin shakewar murya nace salamu alaikum kamar na fashe da kuka ya amsa wa alaikissalamu wata zazzakar muryace ta amsa nana saffiya ya gida ya karatu nasan yanxu kina makaranta ko? sufy kinyi shiru kimin magana Dan Allah ka gayan waye kai kana tayar min da hankali "sunana imran kuma gaskiya ni aljanine kar kuma kice zaki ji tsorona zan dinga kiranki karki tunanin kubuta daga tarkona yana fadan haka ya katse, sadiya naga ta kaina kuna jin maganar da yake fadan wai kr meye haka kiyi abinda nace miki dan ku rabu lafiya ko class ban koma ba nayo gida lafiyar ki nana? umma kaina ke ciwo Allah ya sauwake to kije ki kwanta na shigo miki da abincinki ina shiga na kwanta ina ta tunani naji wayata tana kara cikin dauri na daga nayi sallama. ke baki iya gaisuwa ba ya fada cikin wata katuwar murya kayi hakuri yanzu zan gaisheka daman ke bakya gaida kowa koh hantar cikina ta kada waye ya gaya maka? kina tunanin waye ya gayan ko? karki manta ni fa aljanine karkiyi mamakin ganina zabura nayi na mike ina kallon dakina dan Allah yanzu kana ganina?


Abbagana hausa novels @ facebook.

WAYE SANADI?

24


MUH'D*ABBA*GANA
09039016969

www.abbagana.pun.bz


au kin dauka wasa bara na tabbatar kiga shaida da gudu na kara bakin kofa dan Allah kayi hakuri barrister ki nutsu to na nutsu in kina so mu shirya duk safiya ki dinga gaida ummanki da mijinta da kuma abokiyar zamanta kin ji, naji wallahi zan dinga gaishesu to ki tashi kiyi sallah,nima yanzu zan tafi makka zanyi sallah ban san lokacin da bakina ya furta a hirgi zaka? wane jirgi minti biyar zan isa in kuma zaki mu tafi,zubewa nayi ina bashi hakuri dan Allah kayi hakuri yanzu zanyi sallata to da kin idar kije kiyiwa umma aiki ina kallonki kan nayi magana ya katse wayar da sauri na mike nayi toilet ina idar da sallah na mike na fito umma in kina da aiki ki kawo nayi miki cikin mamaki ta dago kai tana kallona umma kinyi shiru zuba min ido tayi"nana ban da aiki ke da kanki yake ciwo na gama komai kije ki kwanta ki huta kamar na saka kuka na juyo na dawo dakina nasan yanzu yana kallona kuma gashi naje tace bata da aiki haka na yini ranan daidai da wanka ma kasa shiga nayi ina tsoron karya ganni ni gashi fitsari ya cikan mara tunda na dawo nake son na kasa tsungunawa nayi, wata zuciyar tace naje toilet din umma nayi imran kinje yana ganinki haka hawaye ya shiga bin fuskata wayata na dauka na kira sadiya sufy ya gida? sadiya ki taimaka min duk motsin da zan aljanin nan yana gani na me kuma ya faru? fitsari ya cika min mara na kasa zuwa yace yana ganina kan tayi magana kudina ya kare wayar na cilla kan gado tana fadawa aka kira da sani na dauka ina tunanin sadiya ce number shi na gani nan da nan jikina ya hau rawa hannu na yana rawa na dauka sufy kije kiyi abinda zakiyi a bandaki zan rufe idona ba zan ganki ba kuma ina ganin bugawa da kikawa sadiya sannan karki kara kirana da aljani ki kirani da imrana sunan da mahaifina yayi min hudu ba dashi dakyar na iya cewa to karki kashe wayar jeki da ita da gudu na mike nayi toilet dan Allah ka rufe idonka zan tsunguna"bara naje london na kai sako kan kiyi amma karki katse min waya minti uku zan dawo cikim murna nace to na gode. washe gari muna zuwa school na fada jikin sadiya hannuna ta kama muka fito cikin motata muka koma har da momina "sufy wai lafiyarki kuwa???


Abbagana hausa novels @ facebook.
Share:

WAYE SANADI?? 17---20

waye-sanadi.jpg

WAYE SANADI?

17


MUH'D*ABBA*GANA
09039016969

www.abbagana.pun.bz

taso muje ki rakani gurin ummanki oh mama ita ma yanxu ta tahi daga nan zo muje dakin daddy kinga shima saiku gaisa ta mike ta jawo hannuna muka nufi wani barin daban shima waje ne mai kyau yana zaune kan kapet ummansu tana hada masa tea yana ganina ya hau murmushi safiyya har kin yi shirin makaranta banyi magana ba har muka karasa gabansa nace antashi lafiya lafiya klau ya kan naji sauki yanzu dakyar na danne zuciyata nace mata sannu da aiki sannan ta dago fuskarta a daure ta dago kai ke za'a yiwa sannu ta mai da kanta taci gaba da juya shayi yadda fuskar maryam da na daddynta sun nuna basu ji dadi ba, a zuciya ta nace kar ma ki damu ni da kaina zan yi maganinki duk abinda ta taka nima shina taka na mike zan tafi makaranta. to safiyya ungo ki hau mota nasa a nemo miki direban da zai dinga kai ki da dauko ki tunda muka zauna zanyi break maryam dasu abba suke ta jana da hira ban basu wani cikakkiyar amsa ba daga E sai a'a na mike zan tafi abba ya mike nana bara na karbo key na kaiki ba dan naso ba na amsa masa da toh tunda muka tafi yake ta jana da hira ina kokarin kauce amsa dan dukansu haushinsu nake ji "nana safiyya tunanin me kikeyi? ina ta magana kinyi shiru,bbu tunanin da nake kawai dai maganar ce bana sonyi kamar ance juya naga sadiya a tsaye a titi ka sauke ni anan ga kawata can sai kawai mu karasa haba ya za a yi na bar kanwata a nan bari ita ma na dauke ta sai na kaiku tana ganin mota ta tsaya a gabanta ta dauke kai daga wajen ganin an bude yasa ta fara tafiya ina kuma zaki? jin murya ta yasa ta juyowa lalala safy kece daman kinga lokacin yana tafiya kizo mu karasa school ta shiga baya,sannu ina kwana lafiya klau ya karatu? har muka karasa bbu wanda ya kara magana yayi parking sadiya ta fita har na yunkura zan fita naji maganar abba sufy sunan ya min dadi sosai gashi kya yi break ka barshi daddynku ya ban nasan ya isheni kan yayi magana na fice banko tsaya ba rufe masa murfin ba na karasa wajen sadiya. sufy daman shine darling din amma gaskiya kun dace ya sunansa? Allah ke wani lokaci dariya kike ban kawai daga kinga mutum sai wani surutu kike nifa duka yau na fara ganinsa kuma wallahi haushinsa nake ji kamar na kashe shi dama daurewa kikai kenen 'daina yi min tadin shi"


Abbagana hausa novels @ facebook.
WAYE SANADI?

18


MUH'D*ABBA*GANA
09039016969

www.abbagana.pun.bz


gaskiya sufy baki da mutunci to me yasa kika shiga motarsa har ma kuma ya akai ya sanki,kinga bara nayi miki a takaice wannan aban dan mijin ummatane,dan ni bana kaunar maganarsa nakeba,kai suffy Allah ya gyara miki na zaro waya ta kira na gani har guda uku sai kuma message daya zuciyata ta kasa samun nutsuwa hankalina ya kasa tattatuwa waje daya har sai da naji muryar yarinya kin tashi lafiya? kiransa ne ya shigo ban karasa karantawa ba nayi saurin dagawa cikin hargagi nace wai kai baka da hankali kana kiran matar aure banza.na kashe waya uhum wallahi nana kibi a hankali ba ayi wa namiji haka"na juyo ina hararanta ke kin cika abin haushi goya mazan zanyi bara kiji ni a tsarina dana kula namiji gara na zauna ban magana da kowa ba saboda me? kai tsaye na bata amsa saboda bana kaunarsu meye dalilinki? sadiya ni kaina ba zan iya kawo miki dalili ba illa dai kullum zuciyata tana gayan namiji bai da wani buri na gari akan mata shi dai burinsa daya ya cuceki ya gudu ya barki tsanata ta dada karfi akan namiji tuna na karanta wani littafi "yaya sunansa littafi kuwa waye yayi shi? sabon marubucine, sunan littafin NA DAINA SO wallahi sadiya naji na tsani duk wani na miji na tsane shi to an ce miki duka mazan halinsu dayane duk abin da zaki ji a littafi karya ne kawai dan a fadakar ni kam ban yarda da abinda na ke gani a littafi ba.wai wayene yayi? ina jin sunansa muhd abba"to kinga ni duk cikin marubuta bbu wanda nake jin dadin littafinta irin "hauwa jabo" labarinta yana burgeni jiya sai dana karanta sabon littafinta mai suna"hasken idaniya" yayi dadi sosai kuma dana koma zan sa a nemo min wannan din ya sunansa"NA DAINA SO. muna shiga class na dauko wayata zan kashe naga wani message nana jiki na yana gayan baki da aure ki daure muyi magana ta nutsuwa imran S. gabanane yayi mummunar bugawa waye wannan yasan sunana na shiga tambayar kaina na shiga uku kaddai ace aljani ne. lafiyarki kuwa kina ganin malami ya shigo nayi saurin kashe wayar na jefa cikin jaka tun dana koma gidan alhaji nasir naji rayuwata ta sauya kamar lokacin na fara rayuwa nayi kyau sosai lokacin na san ina da kyau gaskiya sai yanzu na san ina rayuwa me kyau kayya kam har bana iya irgawa ni da ummata duk abinda muka bukata alhaji nasir yana yi mana daidai da rana daya bai taba nuna gazawarsa ba,



Abbagana hausa novels @ facebook.
WAYE SANADI?

19


MUH'D*ABBA*GANA
09039016969

www.abbagana.pun.bz

tsakani na da matarsa da yarsa bbu mai shiga harkar wani tunda muka yi fada da maryam shikenan babarta ta kafan kagon zuka nima bana rangawanta mata umma bata taba cemin na bari ba shima maganarsa daya nayi hakuri. yau ban shiga school ba misalin karfe sha biyu na tashi na shiga dakin alhaji nasir yana jin bbc maryam tana zaune a kusa dashi ban koh yi sallama ba na shiga na zauna a kan kujera kusa dashi na juya ina kallon fuskar maryam harara ta zabga min nayi mata murmushi na juya ina kallonsa sannu da aiki abinda bai taba jin nayi masa ba cikin mamaki ya amsan yana tambayata ko da wata matsalar ce maka zanyi ina son zan shiga islamiyya shine nake so ka yankan form kuma yanzu naiya mota da kaina ina so ka sai min mota mai kyau ta zamani. safiyya duka kwananki nawa kina koyar motar? wannan ba damuwarka bace ni dai nace ina bukatar mota shikenan safiyya zan siya miki sannan maganar islamiyyar kin taba yin wata koko a nan xaki fara? tun muna fanshekara har muka koma dorayi ko lokacin da na daina zuwa izina arba'in. shikenan safiyya in yamma tayi zan je sai na yanka miki form din. haba daddy yanzu har agola tafi mu daraja tazo maka da bukata bbu ladabi sai magan ganu kai tsaye ta zo ta zauna kusa da kai abinda ko momy ba tayi maka haka amma ita sabida ba ta da tarbiyya ta zo ta zauna kusa da kai, sannan dady nafi shekara ina cewa ka sai min mota amma baka sai min ba ko su yaya da abba ma baka sai musu ba sai tsohuwar taka ka basu amma ita tana tambaya har ka amsa mata wallahi ba zaki hau motar ba tunda ba uban.........kan ta karasa ya sakar mata mari daman baki da kunya safiya ba gaba dake take ba tashi ki bar min daki mara kunyar banza fita tayi tana rusa ihu juyowa yayi yana kallona safiyya kiyi hakuri insha Allahu gobe zan shigo miki da motarki wai ina wayarki ne ban taba ganinki da ita ba tana nan kawai dai na ajeta saboda karatu okey na mike ina zuwa daidai kofar fita naji an zabgamin mari ina dagowa banyi wata wata ba na zabge mata mari har sau biyu kururuwa ta saka da sauri ummata fito tana tambayarta lafiya zakice lafiya mana munafuka bada daurin gindinki take komai ba to wallahi bazan yarda ba agola ta dagar hannu ta mare ni har sau biyu ta juyo kan ummana nayi saurin shan gabanta ni nayi miki ba ita ba dan haka karki kuskura ki taban umma in ki kace zaki taban umma kina ganin zan rabu dake to gata nan ki taba ta batun yau nake ganin ta kun ku ke da yarki wallahi in din gudace banza jaka me kishi akan namiji.


Abbagana hausa novels @ facebook.
WAYE SANADI?

20


MUH'D*ABBA*GANA
09039016969

www.abbagana.pun.bz

naja hannun ummata mukayi daki wallahi alhaji kayi kadan ka wulakantani a gabanka yar matarka ta maren har sau biyu baka yi magana ba kuma a kanta ka mari yarka to wallahi bazan zauna ba gara na tafi in kina ganin tafiyar ta fiye miki alkairi to sai kin dawo in kuma zaki iya tsayawa ki sauraran to, yana fadar haka ya juya yayi daki tunda muka shiga daki nida umma zaune take tayi tagumi umma tun dazun na tambayeki kinyi shiru ko dan nayi fada da kishiyarki kike jin haushina' nana ba haushinki nake jiba jikina kaka nake tunani tun shekaranjiya take kwance ya kamata kije ki dubata nana tunda kika dawo gidan nan kusan wata tara kenan baki taba zuwa kun gaisa ba ya kamata ki jeki ga ya jikin nata yake. wallahi umma bbu inda zani kawai kina so kice na bar gidan mijinki saboda yana da kudi bakya so na zauna naci arziki kuma yau zan bar.gidan "na mike na shiga dakina bata koce min kala ba na shiga hada kayana har na gama na dau jakata na ganshi a tsaye, safiyya mayar da kayanki kiyi hakuri kuma gobe in zaki makaranta ki biya ki gaida baba karki min gardama Allah yayi miki albarka ya juya ya fita kawai naji yau yaban tausayi dan haka na juya na mayar da kayana bayan kwana uku ina zaune a falon umma ina kallo ya shigo ko kallonsa banyi ba umma ta fito tana yi masa sannu da zuwa,na mike zan shiga daki naji muryarsa safiyya ga alkawarinki da nayi miki na juya ina kallonsa wane alkawari na fada ina hararansa, motarki an kawo ga key din kuma naje islamiyya na yanka miki form har an cike gobe zaki fara zuwa. hannu nasa na karba nayi cikin daki umma ta juya tana kallonsa an gode Allah ya kara arziki. amin rukayya na gode da addu'arki na kuma ina adduar Allah ya barmu tare har karshen rayuwarmu keh har gidan aljanna. murmushi tayi ta sunkuyar da kai ya mike ki mikon abincina.
ni kam tunda na shiga daki nake tikar rawa yau nice nake da mota sabuwar rayuwa tazo yaya sadiya zatayi in ta ganni da mota Allah Allah nake gari ya waye na tafi school. umma ce ta turo kofar ta shiga tana hararata sannu mara kunya 'umma me kuma nayi? ban sani ba wallahi nana in baki canja wannan mugun halin naki ba bazaki taba jin dadin rayuwarki ba ace mijin mamanki ya zama makiyinki mutumin nan burinsa ya kyautata miki amma dai dai da rana daya baki taba masa godiya ba, tsakaninki da shi sai harara kamar sa'anki."


Abbagana hausa novels @ facebook.
Share:

AMINAN***JUNA 271---280 (END)

aminan-juna.jpg

AMINNAN JUNA

END



EXTREME HAUSA WRITERS


Na Xarah~B~B


271-275


Sosai maganganun Farouk sun d'aurewa Amrah kai, itakam Zarah batayi mamaki ba sai dai ya bata tausayi sosai ta yanda taga ya dage yana kuka sosai kamar 'karamin yaro, wannan dalilin ne yasa itama ta kama kukan. Amrah kuwa sai ta ringa tuno irin wula'kanci da cin fuska da tayiwa Zarah, a ranta tana tunanin "shin da wane ido zan kalli Zarah yanzu? Zata amince dani muci gaba da AMINTAKA kamar yanda muke da?", kanta ta gyad'a a zahiri tace "nooo! Bazata amince ba, kuma koni ce hakan zanyi".
Da 'karfi ta fasa kuka tace "ka cuce ni Farouk! Kaci amanar AMINNAN JUNA, ka raba mu'amala ta data AMINIYATA wadda nafi so a rayuwata".

Farouk ya dafe kai yama rasa abnda zaice, Zarah ce tace "Farouk indai da gaske ka shiryu tou na yafe maka, Allah ma muna masa laifi mu ro'ke shi gafara kuma ya yafe mana barin tana ni baiwa wacce ba kowan kowa ba, ina maka fatan shiryuwa ta har abada, masu irin halinka ma Allah ya shirye su". Tayi shiru saboda kuka da yake shirin cin 'karfin ta.

Goge hawaye yayi yace "nagode Zarah da kika yafe man, yanxu kam nawan ko mutuwa nayi banda ha'k'kin ki", ya juya ga Amrah yace "ki taimake ni Amrah, nasan ni mai laifi ne, amma ina so ki sani wallahi nayi nadama, dan Allah ki yafe mani muci gaba da rayuwar mu kamar da".

Saurin d'ago kanta tayi tace "its too late Farouk, na yafe maka duk abnda ka mn, kuma kaima ina so ka taya ni ro'kon AMINIYATA data yafe mn, amma bazamu ta'ba zama kamar da ni da kaiba domin kuwa yanzu haka akwai baikon wani a kaina, kuma Idan kaji ko waye baza kayi marmarin zuwa ko bikin mu ba". Da sauri Zarah tace "Amrah ashe kema auren zakiyi?",
Murmushin ya'ke tayi tace "aure zanyi Zarah yau saura sati biyu ma, kuma ba kowa zan aura ba face MUSTAPHA UMAR wanda kuka fi sani da MUSTY".
Ido mud'e Farouk yace "Musty?".........Urs Zarah~B~B

276-280

"MUSTY dai wanda ka sani, babban abokin ka" Amrah ta bashi ansa cikin halin ko in kula, Zarah tace "ashe rana d'aya za'ayi nau da naki",
Amrah tace "ehh haka naji wurin Momy wai zaki auri Yaa Affan".

Farouk yace "Allah sarki! Rayuwa kenan, (a novel by Amrah and Nafee Ankah) dama Musty yace mn har ya gama Msc d'inshi har zayyi aure, ashe kece zai aura",
"Ehh nice" ta bashi ansa a ta'kaice. (Farouk bai wani damu ba saboda dama baya son Amrah, yafi damuwa da jin zarah za tayi aure, amma itama d'in da yasan baida yanda zayyi dole ya cire damuwar a ranshi). Da murmushi yace "tou Allah ya nuna mana, insha Allahu zan hallara kuwa za'ayi komai dani", nam ya hau ro'kon Zarah akan ta yafewa Amrah, cikin 'kan'kanin lokaci suka daidaita kansu, suka koma tamkar yanda suke da.
A ranar kowa yasan AMINNAN JUNA sun shirya har mutanen Katsina.

Bayan kwana goma.
Shirye shiryen biki ne ya kankama a duka gidajen. Amrah da zarah kuwa had'e zaman su sukayi a gidan wata Aunt d'in Amrah da gidan ta yake a kusa da unguwarsu. Futha ma tazo tare suke ta shiri, Mom ita ce ke shirya yaranta biyu da nagartattun kayan mata. Musty da Farouk ma dai tare suke shirinsu. Amrah ta ro'kawa Farouk Dad d'inta ya bashi manager na wani company'nshi dake cikin garin Sokoto, ya shiryu sosai ya zama nitsattsen mutum.
Yau ta kama Thursday (kamu day), amare na hango sun sha kyau sanye da lace iri d'aya kamar tagwaye, a bayan su Futha ce da wata friend d'in Amrah suka kama masu bayan rigunan su (flower girls).
Ranar Friday aka d'aura aure. 'Daurin auren daya tara manyan mutane sosai. A ranar akayi dinner 'kayatatta, duka iyaye sun hallara, amare sunsha wedding gown fara, angwaye kuwa suits suka saka black and white, babu wanda basu burge ba. Washe gari aka d'auki amare aka kaisu gidajen su, Amrah anan cikin Sokoto aka ajeta, Zarah kuwa har Katsina aka kaita.
Tuni soyayya mai 'karfi ta shiga tsakanin Farouk da Futha, sai mu masu fatan alkhairi tare da zuri'a mai albarka.

TAMMAT BI HAMDULILLAH

Duka duka anan na kawo 'karshen wannan dogon labarin nawa, kurakuren dake ciki Allah ya yafe mn, fatan alkhairi ga masoyana baki d'aya.

Note:
Wannan labarin ya koyar damu abubuwa da dama, cikin su akwai;
1) Soyayya ba dan Allah ba, ana so mutun yaso mutun dan Allah, kar kaso mutun saboda abn hannunshi, duk wanda yayi haka tou daga 'karshe akwai dana sani.
2) yanke hukunci cikin fushi. Anfi so mutun ya tabbatar da laifin wani kafin ya zartar da hukunci, daga 'karshe akwai dana sani.
3) muhimmancin Amintaka, ana so duk wanda yake da amini ko aminiya tou ya kasnace akwai yarda a tsakaninsu, kar su bari wani yana shiga tsakaninsu. Da sauran su.



Sadaukarwa ga:Na sadaukar da wannan book ga IYAYENA da kuma MASOYANA a duk inda suke,,,, Allah ka gafar tawa mahaifina ya mashi rahama, yasa aljanna ce makumar sa da shi da duk musulmai "Ameen ya rabbi"




Jinjina ga:Gareki my princess Amrah, u mean alot 2 me my dear, i dnt knw hw to even tnx u my Luvly and caring Frnd, lyf wld be no fun wizout u, luv u so much .


Godiya ga:Godiya ta musammam gareku

'YAN Group d'ina


XARAH~B~BFANS.


SMART LADIES
SADIYA ND ZARAH~B~B NOVELS.
AMRAH ND RABI'AT NOVELS
AMRAH'S KITCHEN
KHADIJAH CANDY NOVELS
HOUSE OF NOVEL na kdeey
WORLD OF HAUSA NOVELS.
Dama Sauran wad'anda ban ambata ba ina mek'a gaisuwa ta gare ku.

GAISUWAR KU TA DABAN CE

EXTREME HAUSA WRITERS
WISDOM HAUSA WRITERS
Nagode kwarai da kulawar ku agareni Allah ya bar zaman tare



Kunfi kuwa son wannan book, nagode kwarai da kulawar ku


〰Sadiya~Jegal
〰Miss Moriki{Qawata}
〰Deejah Luv
〰Aisha~'Dayyabu



Taku gaisuwar ta musammance

My Khadijah Candy
My Rabi'at sk msh
My Beelert Zango
My Raehan{Reporter}
My Basmah{Habeebaty}
My Kdeey
My Futha
My Sadeeya Afka
My Kausar Luv
Zarah{my besty}
Meesha lolo
Fidodo
My Munay
Halima Haima
My Sisi Aisha Ya'u Kurah
Sisinah Hauwa Jabo
My Asea B Aleeyu
Zee Xuciya
Teemerh lolo
My Afrah
Hafsat Usman Gusau
Ummu Ammar

Dama wad'anda ban Fad'a ba duk ina gaida ku


LUV U ALL MY CWT CWT FANS



ZARAH~B~B KE MAKU FATAN ALKHAIRI.
Share:

AMINAN***JUNA 251---270

aminan-juna.jpg

AMINNAN JUNA



EXTREME HAUSA WRITERS


Na Xarah~B~B




251-255



Kwance yake sai juyi yake yi ya rasa abunda ke mashi dad'i sai tunani yake, yasak'a wannan ya kwance wancan, rurin wayar shi ne yasa shi dawowa daga tunanin daya keyi, ganin mai kiranshi ne yasa shi d'aga wa "Hello abokina ya kake?", a d'ayan b'angaren bansan me aka fad'a ba naji dai yace "da gaske musty? kai amma naji dad'i Allah ya sanya alkhairi", musty ya ansa da"amin" "wacece amaryar tamu?" Farouk ya fad'a", "zaka santa amma ba yanxu ba", a haka dai har sukayi sallama tare da katse wayar".


Kwance tashi ba wuya agurin Allah, dan kuwa ya Affan da Zarah har ammasu baiko, ita kuwa Amrah taba musty daman ya turo iyayen shi, Alhamdulillah abubuwa na tafiya yadda ya kamata, matsalar su d'aya ce shine rashin Shirin su da junan su saboda yanxu Amrah ta fara saukowa.


Zaune yake yayi tagumi, a ranshi kuwa ya gama yanke shawarar zuwa har gidan su Amrah domin fad'a mata gaskia abunda ya faru kuma ya neme gafarar su baki d'ayan su koya samu kwanciyar hankali a rayuwar shi, saboda tin ranar da abun ya faru bai qara samun natsuwa a tare da shi ba, sai yanxu magagganun da musty ke fad'a mashi suke dawo mashi, tabbas yayi Babban kuskure a rayuwar shi daya biyewa son zuciyar shi, gashi yanxu ya tashi tutar babu, domin kuwa ba Amrah ba Zarah uwa uba gashi ya rasa karatun shi.

Lallai hausawa sunyi gaskia da suka ce duk abunda mutum ya shuka shi zai girba......... Urs Zarah~B~B.





-256-260




Zaune suke a parlour ita da Mum suna firar su abun gwanin ban sha'awa, shigowar baba maigadi ce ta katse masu firar bayan yayi sallama anbashi izinin shigowa suka gaisa sa'annan yace "Hajia anayi wa Amratu sallama" ido ta zare "wake man sallama baba mai gadi?" "idan kika je ai zaki ga koma waye" Mum ta fad'a tare da cewa baba maigadi yace tana zuwa, "uhm uhm gaskia ni Mum bazan jeba dan bansan ko waye ba" "to idan kika je ai zaki sani, garama ki tashi kije ki ga", da kyar Mum da lallaba ta sa'annan ta saka hijib dinta ta fita


Tsaye yake a bakin gate, tin kafin ta k'araso taji gaban ta na fad'uwa, shikuwa Farouk aranshi sai tunanin ta inda zai fara yake, a haka har ta k'araso dai2 inda yake tsaye, sallama tayi ya ansa d'ago idnuwan ta dazatayi suka had'a ido da Farouk "wana ke gani a kofar gdn nan?" murya na rawa da kyar ya iya furta "Am... rah......." kuma sai yayi shiru.

Shiru ne ya biyo baya kowannan su da abunda yake tunani a ranshi, Amrah ce tayi k'arfin halin katse shirun da cewa " me kuma kazo yi? ko kuma kazo ka k'arasa abunda baka k'arasa ba a shekarun da suka wuce?tou ka koma wurin Zarah badai wurina ba, Farouk na tsane ka na tsani rayuwarka, bana son ganinka, domin kuwa ganin ka yana 'kara tayar min da wani tabo da nasha wahala kafin ya goge, Farouk idan ba kana so in wulakanta ka bane tou kayi gaggawar barin gidan nan", da kyar ya iya furta "a'a Amrah dan Allah ki saurare ni", "au sai yanxu kasan Allah koh Farouk? Lokacin da ka ruguzaman rayuwa ka rabani da farin cikina duk kana me? shin wai meyasa ka dawo cikin rayuwa ta Farouk?" duk wannan maganar da take cikin kuka take yinta


"Dan Allah Amrah ki saurare ni nasan nayi kuskure Dan Allah ki yafeman, kin san dama d'an adam ajizi ne, ki taimaka min ki saurare ni, wlh da kinsan irin halin dana shiga da kin tausaya man, yanxu zan warware miki duk abun daya faru, amma ina so ki taimaka ki biyo ni muje gidan su Zarah dan nafi so ayi komai a gabanta".
Amrah tace "what? Allah ya kyauta min inje gidan su Zarah. Ai ni da Zarah har abada. Babu ni babu ita, saboda haka tun wuri ma ka tafiyarka dan baka da wani abu da zaka fad'a min".
Da 'kyar ya shawo kan Amrah ta yarda zasuje gidan su Zarah amma da sharad'in bazata shiga gidan ba sai dai ta tsaya a 'kofar gida........ Urs Zarah~B~B




kuci gaba da biyo ni danjin k'arshen wannan labarin, ya kusa 'karewa insha Allah.


Taku har kullun




EXTREME HAUSA WRITERS.



Fatima~Bello~Bala.

AMINNAN JUNA




EXTREME HAUSA WRITERS.




Na Xarah~B~B





261-265




Ba yadda ya iya haka ya yadda da sharad'in ta, bata kuma cikin gd ba, kawai tace ma baba maigadi zataje ta dawo sa'annan suka wuce gdn su Zarah.


Bakin ' kofar gdn suka tsaya, nan Farouk ya samu yaro ya aike shi ya kiramai Zarah, ummah ce ita kad'ai zaune a parlour tana kallon wa'azin Dr. Mansur Ibrahim Sokoto a tashar WISAL HAUSA TV, sallamar yaron ne ya katse mata kallon nata, bayan ya gaida ta sa'annan ya fad'a mata cewa anama Zarah sallama a waje, "wake mata sallama?" Ummah ta fad'a, "nima ban san shi ba" "ok kace tana zuwa" tare da mi'kewa tayi hanyar room din zarah.


Kwance take tana waya daganin yadda take wayar basai ma anfad'ama kodawa take waya ba, shigowar ummah yasata tsinke wayar tare da fad'in "ina zuwa yayana, ummah ina wuni?", lfy qlw Zahra'u, kije waje ana maki sallama", ummah ta fad'a fauskar ta d'auke da murmushi, "wake mani sallama a wannan lokacin ummah?" "bansani ba yaro aka aiko amma inkin je ai sai kiga koma waye fatana dai Allah yasa lfy" zarah ta ansa da "amin" tare da zira hijab d'inta, tare suka fito parlour ita da ummah, anan suka rabu Zarah ta fita waje ummah ta cigaba da kallon wa'azin ta.



A 'kofar gida ta tarar dasu tsaye suna jiran ta, da sallama ta isa gurin ganin Farouk yasa ta kasa idar ta sallamar ta ta, murya na rawa ta fara fad'in "Farouk me kazo yi anan? bayan ka rabani da Aminiya ta? katarwatsa duk wata ala'kata da ita, kayi man tabon da har in mutu bazai ta6a gogewa ba?Farouk kayi gaggawar bar mana 'kofar gida tun kafin na nemo wanda zasu tafi da kai cikin sau'ki" Haka taciga da fad'in abinda ke ranta hawaye na tsilala a fuskar ta...... Urs Zarah~B~B.





266-270



"Zarah ki tsaya ki saurare ni kiji abinda ya kawo ni plz", Farouk ya fad'a cikin mirya ban tausayi, "kai malam kai nake jira kafad'i abinda zaka fad'i dan nagaji da tsayuwa" Amrah ta fad'a cikin tsiwa, baki sake Zarah ke kallon ta dan ita sam bata lura da ita ba sai yanxu da tayi magana.


Kusan 5mnt ba wanda yace da kowa komai, Farouk ne yayi k'arfin halin fara mgn yana cewa "da farko dai ni mai laifi ne a idanuwanku amma dan Allah ina mai rok'on gafarar ko saboda sai yanxu na tabba ta nayi babban kuskure a rayuwata dana biyewa son zuciya ta gashi bata haifa man komai ba sai danasani, Amrah tun lokacin dana fara ganin ku nake bibiyar ku duk wani details naku sai da na samu, ganin ke d'iyar mai kud'i ce yasa ni cewa ina sonki amma mgnr gaskia ni Zarah nake ma SON GASKIA, nayi zaton irin mutanan nan ce wad'anda basu damu da damuwar kowa ba sai tasu, na zata idan na biyo ta baya nace ina sonta zata amince amma sam yadda nayi tuna ni ba hakan bane, domin kuwa sam ban samu amincewar Zarah ba hasali ma idan nakira ta bata d'agawa shine dalilin dayasa kikaga idan na kiraki nake cewa kiba Zarah, Amrah wallahi Zarah bata yaudareki ba laifina ne saboda a wannan Zamani da wahala kisamu aminiya kamar Zarah, na za6i zuwa in fad'a maku gaskia ne badan komai ba sai dan abubuwan da suka faru dani nasan tabbas hakk'in ku bazai barni ba, dan Allah dan darajar Annabi Muhammad (S.A.W)Ku yafe man wallahi nayi nadamar abinda nayi maku, nayi danasanin shiga tsakanin ko dan Allah ku yafeman kuna samu natsuwa a tare dani, ku sani wallahi matu'kar baku yafe man ba tou ina cikin matsala, domin kuwa nasan haka zanci gaba da rayuwa cikin 'kas'kanci da tagayyarar rayuwa", har 'kasa Farouk ya du'ka kuka sosai yakeyi yana ro'konsu gafara.....Urs Zarah~B~B.





Happy birthday 2 u "ASEA~B~ALEEYU" Wish u long life nd prosperity,,,,,, sorie for d late wishing.





LUV U ALL MY CWT CWT FANS




EXTREME HAUSA WRITERS.



Fatima~Bello~Bala
Share:

AMINAN***JUNA 221---250

aminan-juna.jpg

[7:39PM, 5/20/2016] my mtn: AMINNAN JUNA



EXTREME HAUSA WRITERS



Na Xarah~B~B




241-245



5 MONTH LTR

Abubuwa da dama sun faru daga cikin su har exams d'in second semister da su Amrah sukayi kuma "Alhamdulillah" result d'in su yayi kyau duk da basu cikin walwala hakan baisa sukayi wasa da karatun su ba.


B'angaren Farouk kuwa damuwa da tunani sun hana mashi maida hankali ga karatun shi hakan yasa da result d'insu ya fito point d'in shi yayi LOW sosai, dalilin haka kuwa aka kori FAROUK daga Skul duk da magiyar da yayi tayi amma basu saurare shi ba, hakan ba k'aramin tada hankalin Farouk yayi ba ya k'ara shiga damuwa fiye da ta da. Bayan ya koma gida tun yana 6oyewa iyayen shi har dai ya yanke shawarar fad'a masu, fad'a sosai yasha dalilin haka kuwa hawan jinin mahaifiyar shi ta tashi, tsine mashi kad'ai ne Abban shi baiyi ba.


Kwance take tana waya da Futha cikin kwanciyar hankali domin kuwa ba k'aramar kulawa Futha da ya Affan ke ba Zarah ba, shiyasa yanzu damuwar ta d'aya ce shine Aminiyar ta tasan bata yaudare ta ba.


"ya kamata kinatsu kicire duk wata damuwa a ranki, haba Amrah sai ka ce Farouk shine autan maza dubi fa yadda kika koma sai kace wadda tayi shekaru tana jinya" Mum ta fad'a, "wlh Mum na kasa manta abunda Zarah tamani ne, kuma gashi idan nakira Farouk wayar shi bata zuwa" "to kiyi hak'uri mana ki koya ma kanki cire son shi a ranki, kiba wasu dama su zo mana" Mum ta fad'a tare da janyo hannuwan y'ar ta ta a ranta kuwa tana mai tausaya mata..... Urs Zarah~B~B.






246-250



Haka rayuwa ta kasan cewa Farouk dan kuwa yanxu komai ya had'e mashi, ga rashin karatu gashi bayada wata sana'ar yi, mahaifiyar shi ba lfy Abban shi kuwa har yanzu fushi yake da shi duk abun duniya ya dame shi.




BAYAN SHEKARA UKU.



Wani saurayi da budurwa na hango zaune a balcony wanda daka gansu kasan masoyane dan kuwa firar su sukeyi cikin jin dad'i da farin ciki, a hankali na fara takuwa dan ganin suwaye wad'annan masoya dan kuwa sunyi matuk'ar birgeni, kafin na k'araso naji murya na fad'in " haba dai MY DEAR kaima kasan bazan iya rayuwa ba kai ba" idona na k'ara murzawa dan k'ara tabbatar da abunda idona ya ganan man, wazan gani ? AMRAH ce da MUSTY sai soyayyar so sukeyi abun gwanin ban sha'awa.


Zaune suke a parlour ita da umman ta suna fira, ummah tace " Zarah wai yaushe ne Affan yace zai turo dan nama kawon ki mgn da wuri?" "Eh ummah daman cewa yayi da munk'are Skul zai turo ayi mgn amma bai fad'a mani ko yaushe ne ba" "ok Allah ya taimaka yasa adace ya kuma yi maku albarka" ummah ta fad'a, zarah ta ansa da "amin" wayar Zarah ta d'au ruri ganin ya Affan ne ke kiranta yasata mik'ewa tana murmushi tare da fad'in ummah ina zuwa ta wuce d'akinta

Da shigar ta ta fad'a kan gado, waya sukeyi mai cike da kulawa had'e da so da k'auna, anan ta shaida mashi yanda sukayi da Ummah yace "ai dama ni ke kawai nake jira, a shirye nake ko gobe ma, amma dai zan fad'awa Ammi, sai in kira ki idan mun yi maganar". "Ok sai na jika"a haka har sukayi sallama tare da tsinke wayar.......Urs
Zarah~B~B.




EXTREME HAUSA WRITERS.



Fatima~Bello~Bala.
[7:39PM, 5/20/2016] my mtn: AMINNAN JUNA



EXTREME HAUSA WRITERS



Na Xarah~B~B




221-225



Yau ta kama SUNDAY ranar dasu Ya Affan zasu koma Katsina, bayan sun shirya ne Futha tace "dan Allah akai ta gidan su Zarah suyi bankwana", Ammi tace "bayan wanda kukayi jiya?" Futha a shagwa'bance tace "wayyo Ammi", "bari Affan ya kai ki amma kar ki dad'e tunda kinga tafiya zakuyi" inji mumy, "yauwa Mumy na tanx alot" Futha ta fada tana mai jin dadi.

Ya Affan yaji dad'i sosai dan ko bakomai yana son ya 'kara ganin Zarah, cikin 'kagara yace " kisame ni a mota" ya fita waje, bayan shi tabi suka wuce gidan su Zarah.


Zaune suke a parlour ita da umman ta, ba laifi yanzu Zarah ta rage damuwa da yawa duk da rashin shirin su da aminiyar ta ba 'karamin ta'bata yakeyi ba amma a haka ta fawwalawa Allah komai har lokacin da Allah zaisa Amrah ta gane bata yaudare ta ba.

"Assalamu Alaikum" "wa'alaikun salam" Zarah ta fad'a tare da mi'kewa, "Laah my Futha ashe bakuwuce ba?" "Eh cewa nayi sai na'kara zuwa na ganki kafin mu wace", "Allah sarki my Futha tnx alot 4 ur caring" "bakomai my Zarah you deserve more". Bayan sun gaisa da ummah Futha taja Zarah sukaje waje gurin ya Affan sun jima suna fira abun gwanin ban sha'awa kamar kada su rabu sukeji, wayar Futha ce ta d'au ruri ganin number da ke kiran ta yasa ta saurin d'aga wa "Hello Ammi", banji abinda aka fad'a ba a d'ayan 'ban garan sai naji tace "ammi gamunan kan hanya mun kusa 'karasowa" sa'annan ta katse wayar. Cikin rashin son tafiyar tace "Ya Affan muje Ammi ta kirani tana fad'a wai mun zo munyi zaman mu", Ya Affan yace "ok mu tafi". Kud'i masu yawa Ya Affan yaba Zarah duk da da'kyar ta kar'ba har saida Futha tasa baki, sukayi sallama tare da shaida mata "daya samu lokaci zai zo kuma dan Allah ki 'kara rage damuwar nan", "insha Allah yaya nagode sosai" Zarah ta fad'a, haka suka rabu suna kewar junan su........Urs Zarah~B~B.





226-230



Suna isa basu 'bata lokaci ba suka wuce da yake daman sun shirya komai nasu, Amrah kam kin fitowa ma tayi suyi bankwana sai da Ammi ta same ta a Room d'in ta tamata nasiha sosai akan ta fawwalawa Allah al'amarin ta tayi ha'kuri ta rage wannan damuwar aranta "to" kawai ta iya cewa Ammi, sa'annan Ammi ta fito suka wuce, itakam Futha batama shigaba dan tasan ko ta shiga bazata saurare ta ba.


Har gate Mum da Dad suka raka su tare damasu Allah ya kiyaye hanya suka kama hanyar katsina.


Farouk ne zaune 'kar'kashin wata bishiya yayi tagumi sai hawayen dake ambaliya a fuskar shi, duk wanda ya ga Farouk yasan ya sauya sosai dan ni da farko dana ganshi ban gane shi ba saida na'kara dubawa da kyau sa'annan na gane ashe Farouk ne, Musty ne naga ya doso inda Farouk yake zaune, bayan ya zauna ya kalli abokin nashi yace "a ganina kanada hanyar magance wannan matsalar taka, saboda har yanzu kanada chance kaje ka fad'a masu gaskiya tare da ro'kon gafarar su, ko ka samu sau'kin abunda kakeji aranka, saboda wallahi alhaki bazai ta'ba barin ka ba",, "uhm Musty kenan, me zan fada' masu ni yanzu? burina d'aya naga sundawo Skul saboda rashin ganin Zarah ba 'karamin cutarwa ce a gareni ba. {Jama'a kuji Farouk fa, shi baisan idan da abinda Zarah ta tsana ba to shine amma shi wai har son ganin ta yake yi, hmmmm duniya ina zaki damu?, Allah kasa muda ce ya kuma yi mana karshen kwarai Ameen Ameen }. Ganin Farouk yayi nisa baya jin kira yasa musty yanke shawarar 'kyaleshi tunda bayajin shawara ko ya bashi...... Urs Zarah~B~B.





231-235



TWO DAYS LTR


Su Amrah ankoma makaranta sai dai yanzu ba tare suke zuwa da Zarah ba, ita Zarah keke napep take shiga ta kaita bus stop, tashiga bus ta 'karasa cikin Skul idan ma ta gama lectures haka take biyo Skul bus, kud'in da ya Affan ya bata da sune take maneji sai kuma abunda ba'a rasaba dayake Ummah na y'ar sana'arta kuma Alhamdulillah.


Haka dai rayuwar su ke tafiya ko wanen su baya cikin walwala sosai bama kamar Amrah da idan ta kira wayar Farouk bata samu sai idan ta kira Musty yakan kwantar mata da hankali sosai.

Duk wata hanya da Farouk yabi dan yaga Zarah amma abin ya faskara dan kuwa Zarah na hango shi zata canza hanya.


Yau takama Friday kuma ranar result d'in su Amrah ya fito, wajen duba result d'in ne Zarah da Amrah suka had'u, fuskar Zarah da'uke da annuri take kallon Amrah da alaman tana son yi mata magana, sai dai me? wata harara Amrah ta bankama Zarah had'e da tsaki, abunda Zarah tafi tsana a rayuwar ta kenan tsaki. Tuni hawaye suka wanke mata fuska a ranta kuwa tana tunanin irin zaman da sukayi da Aminiyar ta mai cike da so da kauna amma gashi lokaci d'aya FAROUK ya ruguza masu rayuwa, wata tsanar Farouk taji ta 'kara shiga a ranta...... Urs Zarah~B~B.





236-240



Koda ta dawo daga duniyar tunanin da ta lula Amrah har ta duba ta wuce abinta, cikin rashin kuzari ta isa inda ake duba result d'in, ganin sakamakon tane yasa ta washe baki tare da fad'in "Alhamdulillah!" cikin hanzari ta maida kallon ta gana Amrah, ganin duk sunci, result d'in yayi kyau sosai yasa ta 'kara fad'in "ALHAMDULILLAH".

Da fara'ar ta tashiga cikin gida kan cinyar Ummah ta fad'a,,, "aaaaaaaaa karki karyani, lafiya Kuwa Zarah?" ummah ta fad'a, "lafiya 'kalau ummah, albishirinki" "goro fari tass" inji ummah, Zarah tace" ummah result d'in mu ya fito kuma mun samu point d'in da ake so nida Amrah" " MASHA ALLAH kai naji dad'i sosai Allah ya taimaka" Zarah ta ansa da "amin ummah na". Ummah tace " tou kin had'u da Amrah?" " Eh mun had'u amma sai bayan tawuce na duba nata da yake kinsan idan mutum yasan ADM NUMBER d"inka zai iya dubawa", " tou Allah ya taimaka yasa adace "amin ummah" "tashi kije kici abinci" "a'a ummah sai nayi wanka zan ci", Zarah ta fad'a tare da yin room d'inta....... Urs Zarah~B~B
EXTREME HAUSA WRITERS
Share:

AMINAN***JUNA 201---220

aminan-juna.jpg

[7:39PM, 5/20/2016] my mtn: AMINNAN JUNA



WISDOM HAUSA WRITERS.




Na Xarah~B~B



211-215



"Dan Allah kiyi hkr ki rage wannan damuwar zarah dube yadda kika koma fa, duk kin saka ummah a cikin damuwa", "hmmmmm! futha kenan dole ne na damu dufa ba kiga tun muna yara muke tare da amrah babu wanda ya taba jin tsakanin mu har muka girma, lokaci daya ta tsane ni akan abinda bansan nayi ba" sai kuma ta fashe da kuka, ahaka dai futha tayi ta rarrashinta har sai da taga tasamu natsuwa, sa'annan ta rinqa yimata fira bai ban dariya har dai ta saki ranta

Alhamdulillah yau abun na zarah da sauki dan kuwa har abinci taci sosai, ummah taji dadi sosai ganin yadda futha take kula da zarah, a cikin hirar ne futha tace " zarah dan Allah ki tashi ki shirya anjima idan ya Affan yazo daukana sai mu dan fita ki nuna mana garin naku", murmushi kawai tayi tace "Allah ya kaimu", aranta kuwa taji dadi sosai saboda itakan ta tasan tayi kewar ya Affan ba kadan ba.

Amrah ce kwance kan gado sai juyi take ta rasa meke mata dadi a duniya gashi tana kiran wayar Farouk amma layin a kashe yake idan takira musty kuma sai yace basa tare duk abun duniya ya isheta kullun sai qara jin tsanar zarah takeyi dan ita aganin ta duk itace silar wannan abun, kullun Mum da Dad suna qoqari gurin ganin sun fahimtar da amrah amma abun yaci tira, suna tausayawa 'yar tasu duk tawani koma wani iri da ita.

Ringing biyu ta daga "hello ya Affan ina wuni?" a dayan bangaren aka ansa da "lfy qlw kun shirya?" " eh, kai kawai muke jira" "ok ganin na kusa qarasowa sai ku fito", " ok sai ka iso" A ranshi kuwa baya ma iya misilta irin farin cikin da yake ciki shidai harga Allah yana jin zarah a ranshi........Urs Zarah~B~B.






216-220



A daki suka samu ummah bayan sun gaida ta futha tace "ummah ya Affan yazo zan wuce", "Allah sarki ashe har tafiya kenan, Allah ya saka miki da alkhairi yabar zumnci" ummah ta fada "ameen ummah ai yiwa kaine" sa'annan tace "ummah dan Allah inason zarah ta rakani naga gari", "tou bakomai sai kun dawo Allah ya kiyaye hanya" duka suka ansa da"amin" sukayi sallama da ummah suka fita

Jingine da motar shi suka same shi yana latsar wayar shi, dago kanshi yayi sukayi ido hudu da zarah wani murmushin jin dadi yasaki wanda ke qara fitar mashi da kyanshi itama mayar mashi tayi, sa'annan ya bude mata gaba tashiga futha ta shiga baya sa'annan suka wuce, a mota sai kallun2 sukeyi, futha kuwa dariya kawai take masu tana farin cikin taga yayan ta cikin farin ciki, a haka har suka isa a "A G G MALL" sayayya mai yawa ya Affan yayiwa zarah tundaga kayan sawa, kayan make up dadai sauran su hakama yayiwa futha saidai na zarah sunfi yawa, daganan suka wuce shan ice cream, ranar sunyi yawo domin kuwa zarah har ta manta da wata damuwa hakan ba qaramin dadi yayiwa ya Affan ba.

A bakin kofar gdn su zarah yayi parking, kallon ta yayi yace plz zarah ki bude wayar ki rashin jin muryar ki ba qaramin illah bace a gareni, ok yaya insha zan bude yauwa qanwata tnx alot, daga nan sukayi sallama ta wuce cikin gd......Urs Zarah~B~B.





WISDOM HAUSA WRITERS.



Fatima~Bello~Bala.
[7:39PM, 5/20/2016] my mtn: AMINNAN JUNA

WISDOM HAUSA WRITERS


Na Xarah~B~B






201-205





A parlour suka samu ummah zaune ta lula duniyar tunani dan halin da 'yar ta ke ciki abin tausayi ne,, zarah kuwa cikin yan kwanan kin nan duk ta canxa ta rame tayi baqi ba ci ba sha sai aikin kuka da zaman daki.


Sallamar su ce ta dawo da umma daga duniyar data lula, cikin karfin halin ta tashi da yaqe ia fuskar ta wanda yafi kuka ciwo, iya fuska kawai ya tsaya, "sannun ku da zuwa hajia" suka ansa da "yauwa ya muka same ku?" " lfy qlw wlh hajia", anan ta kawo masu ruwa suka sha, shiru ne ya biyo baya, ummah kuwa a zuciyar ta tana tunanin to me yakawo su mumyn Amrah a gdn dan da datagansu tayi tunanin cin mutunci suka zo suyi mata sai taga akasin haka, ammi ce takatse shirun da cewa"ummah nasan bazaki rasa sanin dalilin mu na zuwa nan gdn ba, da farko dai muna son mu tamby ko zarah nan tazo da ta baro katsina? dan bada sanin muba ta zo" jin bayanin ammi yasa ummah ta tabbata cewa itace Ammin da su zarah sukaje gurinta a katsina, ajiyar zuciya tayi kana tace "eh ammi nan tazo kuma ta fadaman duk abinda ya faru har dalilin ta na dawo wa batare da sanin ku ba" Alhamdulillah ammi ta fada kana tace ina zarar take ne? tana ciki inji ummah, anan dai sukayi mgn akan matsalar tare da ba ummah hakuri, futha shiga ciki ki kira zarah inji mumyn Amrah, "tou ta fada hade da mikewa tayi hanyar dakin...........Urs Zarah~B~B






206-210



Kwance ta same ta kan gado tafi 5mnt tana kalln yadda zarah ta sauya haka sai kace wanda tayi jinyar 1yr, a sanyaye ta iso daidai gurin da zarah take kwance wanda ita zarah har tym din batasan da wanxuwar Futha a dakin ba, jin antabata yasata firgigit ta tashi daga kwancen da take, ganin futha a gabanta yayi matuqar bata mamaki sake da baki take kallon ta, daqar bakin ta ya iya fadin futha sai kuma ta fashe da kuka mai ban tausayi, kwallar da ke maqale a idon Futha suka fara zuvuwa zama tayi kusa da zarah tare da riqo duka hannun ta biyu ta fara bata baki harsaida taga ta dan samu natsuwa kana tace tashi muje parlour su ammi na kiranki hijab kawai tasa suka wuce parlour akasa suka zauna, mumyn amrah da taga yadda zarah ta canxa ta tausaya mata sosai duk da wanigafen zuciyar ta naso ya yarda da abinda 'yarta ta fada amma ganin halin da zarah ke ciki yasata qaryata abinda zuciyar ta ke raya mata, zarah bakida lfy ne? Ammi ta fada, shiru tayi sai sasshekar kukan da takeyi akeji ganin bata niyyar yin mgn yasa ammi cewa "zarah kiyi hkr ki rage wannan damuwar kada kijawa kanki wata matsalar daban",
Mum tace "ba ke ba, ba Amrah ba, kowacenku babu natsuwa a tare da ita",
Ammi kam cewa tayi "duk kansu sunbi sun rame har futha, Allah dai ya kyauta ya kawo maku qarshen komai",
Duka suka ansa da "amin".

Sallamah Yaa Affan yayi cikin natsuwa, ummah ta ansa sallamar fuskarta dauke da dan guntun murmushin rashin sani, ammi tace "shigo daga ciki mana", takowa yayi ya zauna yana qarewa Zarah kallo ko gaishe da ummah bayyi ba, ammi tace "wai kai baka ji ana maka magana ne?, yayi saurin zabura yana sosa qeya yace "ina yini ummah"
"Lafiya lau" ta bashi ansa, duk kansu sun fahimci irin kallon da yakewa Zarah, Ammi ce ta fara miqewa tace "alhamdulillah! Tunda tana gida ai komai yayi kyau, ku tashi mu tafi an bar Amrah gida ita kadai",
Mom ma ta miqe amma sam futha tace ita ba yanxu zata tafi ba, da Ammi ta hana amma ganin Zarah na kuka yasa tace "ki zauna anjima sai Affan yaxo ya dauke ki",
Dadi taji sosai shima Affan din haka, dan yasan ya samu damar da zai sha love da Zarah wanda yayi kwanaki basuyi ba.



Yanxu meye amfanin abinda kayi?ka tashi totar babu ba zarah ba amrah suma kuma ka tarwatsa masu farin ciki, wlh idan baka gaggauta sanin abunyi ba to ina gujemaka haduwar ka da ubangijinka musty ya fada, shikuma Farouk dake kwance sai famar hawaye yake a zuciyar shi kuwa wani irin zafi yakeji kamar ya hadiye rai ya mutu dan bakin ciki......Urs Zarah~B~B.




WISDOM HAUSA WRITERS



Fatima~Bello~bala.
Share:

AMINAN***JUNA 181---200

aminan-juna.jpg

[7:39PM, 5/20/2016] my mtn: AMINNAN JUNA



WISDOM HAUSA WRITERS




Na Xarah~B~B



191-195



Washe gari tun safe suka hau hada kayan zuwa Sokoto banda Amrah da tayi jugum duk ta fita hayyacinta, Futha kam ta fita batunta dan ba kadan take tsananin jin haushin Amrah ba.
Jin shiru har sun fito parlour amma babu amrah yasa ammi ta shiga dakinsu, ta sameta kamar mahaukaciya sai sabbatu take ita daya tana fadin "ni Zarah! Ni kikaiwa kwacen saurayi? Hubby na wanda nake burin aure, yake kiranki da swty, kin cuce ni, bazan taba yafe miki ba a cikin babin soyayya".
Ammi taita magana amma shiru bata ma san tanayi ba, saida ta tafa hannu da qarfi sannan ta zabura hawaye nabi mata kumatu tace "na'am ammi, ina kwana?".
"Ba wannan ba, me kike da har yanxu baki shirya ba? Kuma kin san ke muke jira",
Cikin kalar tausayi tace "ammi ai ban ma san har garin ya waye ba, tunda nayi sallah nake anan, barin hada kayan yanxu dama komai a shirye yake", Ammi tace "tou barin turo futha sai ta tayaki harhadawa", "noo ki barshi ammi ai daman duk a hade suke, gyrane kawai zanyi nasan yanxu zan gama" tayi saurin fadi.

Cikin qanqanin lokaci amrah ta hada komai nata, da qyar take jan trolly dinta ta fito dashi parlour, ta samu Ammi, futha da yaa affan zaune kowa yayi tagumi, kowan su da abnda yake tunani a ranshi, miqewa ammi tayi lokacinda Amrah ta fito tace "Affan karbi akwatinta ka kai a mota", cikin rashin kuzari ya karba ba tare da yace mata uffan ba, bin bayanshi sukayi ya bude masu motar futha a gaba sai Ammi da amrah a baya..........Urs Zarah~B~B




196-200




Tafiya suke cikin natsuwa babu gudu dan ammi bata son ana gudu da ita a mota, qarfe 1:40 suka isa babban birnin Sokoto. Basu zarce ko ina ba sai gidansu Amrah.


"Ahh lale marhaban da mutanen katsina, tafiya haka babu sanarwa, sannunku sannku", momy ce ke fadin haka fuskarta sake tare da faraa.
Ammi tace "wlh kuwa maman Amrah, yauwa yauwa, mun sameku lafiya?"
"Lafiya lau ya hanya?"
"Alhamdulillah" Ammi ta fada.


Bayan sun samu natsuwa sunci abinci sunci, Amrah ta koma daki taci gaba da jimami. Futha kuwa qaramin parlour ta koma ta kunna kallo. Yaa Affan ya tafi masallaci sallar jumu'ah dan a ranar jumu'ah ne.
Ya rage saura Ammi da momy kawai a dakin. Ammi tace "nasan zakiyi mamakin ganin mu kwatsam ba tare da kun san da zuwan mu ba"
Momy tace "gaskiya ne, wannan xuwan bazatar ya daure min kai",
Ammi ta nisa tukuna tace "wata 'yar matsala ce ke tafe damu, inda kin kula zakiga yanda Amrah ta canza duk babu walwala a tare da ita",
"Ehh na kula da haka kam, me yake faruwa ne?"
Nan Ammi ta kwashe duk abnda ta sani tun farko har qarshe ta fadwa momy, harda tafiyarda Zarah tayi ma ta fada mata.
"INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN" kawai momy ke fadi, "tou ai ammi bamuga ta zamaba, dole a bincika Zarah idan gida ta dawo, Allah dai ya rufa mana asiri yasa tana gida",
Ammi tace "amin".

Sallamar yaa affan ce ta katse masu zancen da suke, momy tace Affan ko kai zaka kaimu gidansu Zarah? Sai na ringa gwada maka hanya tunda babu nisa ma daga nan, wlh drivern mu yayi tafiya ne, dady kuma yana office bai dawo ba".

Dad'I sosai Affan yaji dan an ambaci Zarah, rabonshi da samun natsuwa yau kwana uku kenan tun barin Zarah katsina.
"Muje momy a shirye nake", ya fada tare da fita daga dakin. Caraf futha ta fito tace "dan allah aje dani ammi", Ammi tace "ya za'ayi a tafi dake bayan kuma ga yar uwarki? Ki zauna ki jira mu bazamu dade ba, kedai kiyi mana fatan samun nasarah kawai".
Momy tace "aahh baza'ayi haka ba, jeki sako hijabinki mu tafi, itma Amrah ai ba wani ya hanata ba",
Kaman daga sama sukaji Amrah tace "Allah ma ya kyauta min inje gidansu maciyya amana, ni wlh ko sunanta ma bana son jin an ambata".

Ammi tace "rufewa mutane baki daallah can", a fusace ta fita tabi bayan yaa affan dake tsaye bakin mota yana jiransu.........Urs Zarah~B~B




WISDOM HAUSA WRITERS
[7:39PM, 5/20/2016] my mtn: AMINNAN JUNA



WISDOM HAUSA WRITERS.



Na Xarah~B~B




181-185


Futha tace "amin yaya, amma kam gaskiya Amrah na cikin rudin soyayya kuma......", bata qarasa maganar ba taji Amrah na fadin "sannu magulmaciya, wato gulmata kika kawo gurin yaa Affan ko? Tou wlh koma me zaku fada sai dai ku fada, nace babu ni babu Zarah, na yanke duk wata alaqa dake tsakanin mu, kuma ma da kike fad'in haka, shin wai ni na kori Zarah ne? A gabanki fa akayi komai, ban koreta ba ita ta kori kanta", Futha ranta bace tace "amma ko baki furta kora ba ai kin furta me kama da haka, kin mata gori Amrah, wanda ya kamata ace kinfi qarfin nan, an daina yayin gori fa, an barwa qananan yara, ke kuma yanzu kin wuce minzalin qananan yara", cikin masifa Amrah tace "well! Ki fadi duk abnda kike so Futha, nasan a gidanku nake dole na dauki duk wata baqar maganar...", saukar marin da taji ne ya hana ta qaraaasa maganar da take, yaa affan ne ya mareta ta dafe kumcinta, bata ankara ba ta qara jin saukar wani marin, ba shiri ta fadi qasa tana kuka kamar ranta zai fita........Urs Zarah~B~B


186-190



Da sauri ammi ta fito jin sautin kuka na tashi, cin burki tayi a lokacin da taga amrah kwance a qasa shame shame tana kuka, da hanzari ta isa inda Amrah take, ta dafata tace "daughter! Me ya sameki kike kuka?", Amrah ido rufe ko kallon ammi batayi ba, ganin bata da niyyar bata ansa ne yasa tace "kai Affan me kayiwa Amrah? Futha meke faruwa ne? Answer me mana, am asking youh, tell me what happened with my daughter?", kasa bata ansa sukayi su duka, sun dauki kamar munti 15 a haka, ganin ammi na kuka hawayen ta na ta fita yasa Affan gurfanawa a gabanta, ya dafa kafadarta yace "ammi kuka kike? Me ya saka ki kuka? Rabo na da ganin kukanki tun rasuwar abbah, pls kiyi haquri", sai a lokacin ammi tace "ba dole nayi kuka ba Affan, nayi nayi daku kunqi fada mun abnda yake faruwa, ga yarinya nata faman kuka kuma nasan kun san komai", cikin rashin son fada mata yace "Ammi lafi na ne, nine na mareta" nan ya kwashe komai daya faru ya fada ma ammi, yasha fada sosai shida futha, da qyar ta samu ta rarrashi Amrah tayi shiru amma da sharadi, wai dole sai ta koma Sokoto gobe, ammi tace babu komai tare ma zasu tafi daga nan har su bincika labarin Zarah, ranar haka suka kwana kowa cikin takaici, ita Amrah babban haushinta ma idan ta kira Farouk baya dauka, daga qarshe ma sai yayi off na layinshi.............Urs Zarah~B~B


WISDOM HAUSA WRITERS.



Fatima~Bello~Bala.
Share:

AMINAN***JUNA 161---180

aminan-juna.jpg

[7:39PM, 5/20/2016] my mtn: AMINNAN JUNA


WISDOM HAUSA WRITERS.




Na Xarah~B~B.


161-165




Faduwar wayar da sukaji ne ya maida hankalin su gare ta, da sauri zarah ta nufI gurin da amrah take jikin ta sai rawa yake yi, ganin zarah zata taba ta yasa da k'ar ta iya cewa "kada ki tabani macuciya, azzaluma maci amana" sai kuma ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi, tsaye zarah tayi ganin halin da aminiyar ta ke ciki fuskar ta cike da damuwa, a ranta kuwa tana tunanin wace irin mgn ce FAROUK ya fada tunda shi a tunanin shi itace ta daga wayar, muryar amrah ce ta katse mata tunanin da takeyi tana fadin "kin cuceni kin ci amanata zarah, sakayyar da zaki min kenan? daman hausawa sunce tsintatciyar mage bata mage duk abunda namaki a rayuwa da wannan zaki sakaman?," zarah da tunda amrah ta fara mgn hawaye ke ambaliya a fuskar ta tare da girgiza mata kai amma sam amrah taqi ta saurare zarah" futha ce tayi karfin halin cewa "wai meke faruwa ne Amrah? kun barmu a duhu fa" cikin dasasshiyar muryar ta tace "futha yanxu zarah ta rasa wanda zata cuta sai ni, meyasa tun farko bata fadaman SON SHI take ba? meyasa zarah zata man haka? meyasa take son ta tarwasaman rayuwa? meyasa.............. "futha ce ta katse ta da fadin "wa'annan tmbayoyin naki banida ansar su, me tamaki ne? sa'annan wanene take so?" janjayen idanuwan ta tadago tana kallon ta tace "yanxu ta rasa da wanda zatayi soyayya sai hubby na, Farouk wanda nake burin in aura, ashe daman dalilin da yasa ya chanza man kenan a lokaci daya", "wat?" Inji futha..... Urs Zarah~B~B.




166-170




"A'a amrah impossible, hakan bazata taba faruwa ba, kada kiyi saurin yanke mata hukunci batare da kinyi bincike ba nd duk da kinki fadaman me FAROUK yace a waya nasan ba laifin zarah aciki, kada soyayya ta rufe maki ido ki aikata abunda zakiyi nadama a gaba, kada ki manta zarah nada wanda take su kuma take muradin aure nd......" hannun da ta daga matane yahana ta karasawa "dalla malama ki man shiru bana buqatar jin komai, ke kuma" tare da nuna zarah "daga yau bani ba ke, kar ki kuma nuna kin sanni tunda ke matsiyaciya ce, hmmm.....banga laifinki ba Zarah, laifina ne ai da tun farko na nuna miki soyayya fiye da kaina" Ta inda amrah ke shiga batanan take fita ba duk yadda zarah taso ta saurare ta kin yadda tayi kuka sosai zarah keyi[ni kaina saida na tausaya mata ]


Ranar yadda zarah taga rana haka taga dare sam bacci kin zuwa yayi hakan yasa taje toilet ta dauro alwala ta fara nafila wanda ita kanta batasan adadin ku raka nawa tayi ba, bayan tayi sallar asuba ne ta fara hada kayan ta, cikin sa'a kuwa koda ta fito parlour kofar abude take kasancewar ya affan ya je masallaci, haka ta samu ta fita daga gdn ba wanda ya ganta, tafiya takeyi ba dan tasan inda ta nufa ba haka har gari ya waye keke napep ta samu tace ya kaita tasha.....Urs Zarah~B~B.





WISDOM HAUSA WRITERS.



Fatima~Bello~Bala.
[7:39PM, 5/20/2016] my mtn: AMINNAN JUNA



WISDOM HAUSA WRITERS



Na Xarah~B~B.





171-175




Koda suka isa tasha ba mutane dayawa kasancewar da safe ne, sai zuwa 8 aka fara lodi, tana tunanin kudin motar da zai kaita sokoto, can ta tuna da kudin da ummanta ta bata lokacin da zasu tafi katsina, bayan anqare lodi ne suka kama hanyar sokoto, kallo daya kama zarah kasan tana cikin damuwa.


A bangaren su amrah kuwa, bayan sun tashi basu ganta ba ita amrah ko ajikin ta kasancewar wata tsanar zarah takeji, futha ce ta shiga duba ta har toilet amma wayam ba kowa, a parlour ta tarar da ammi a rikice ta fada jikin ammi, ganin yanayin futha ne yasa ammi cewa " futha lfy naganki haka? , "ammi wlh bamuga zarah ba koda muka tashi ammi kuma duk na duba batanan harda kayanta bangani ba", "innalillah wa'inna'ilaihir raji'un" ammi ta fada "to me aka mata ne wanda zaisa tabar gdn ba tare da bankwana ba?", futha tace " ammi daman jiyane suka samu missunderstanding da amrah", nan dai futha ta fadama ammi duk abinda ya faru, fada sosai ammi tawa Amrah, hakama ya Affan kamar tabbabbe ya zama da yaji zarah bata gdn, ya Affan yayita kiran wayar zarah amma switch off, hankalin shi yayi matuqar tashi har gdn aunty beelert yaje amma Zarah bata can, haka ya dawo jiki ba sukuni, a ranshi yana tunanin ko sokoto taje, da wannan tunanin har baccin wahala yayi gaba shi........Urs Zarah~B~B.





176-180




"Assalamu Alaikum" "wa'alaikun salam..., aaaaaaa mutanan katsina sannun ku da zuwa maraba daku, ya hanya?" " lfy qlw umma" zarah ta ansa a taikaice ummah sake da baki tace " lafiya kuwa naganki haka ina amrah ne? "umma............ "Sai kuma ta fashe da kuka mai ban tausayi, "wai me akayi ne kike kuka? wani abunne yasami Amrah?" kai kawai ta gyadamata alamar a'a "to meya faru?" tare da janta zuwa daki, bayan ta rarrasheta ne tace ta tashi taje tayi wanka taci abinci sa'annan suyi mgn, "tou" kawai zarah ta iya fada tare ta mikewa, bataji ma ba ta fito bayan ta shirya, a parlour ta same ummah bayan taci abinci ne cikin natsuwa ummah ke mata mgn "zarah kinatsu ki fadaman meya faru? meyasa baku dawo tare da amrah ba"? cikin dasasshiyar muryarta ta fadama ummah komai da yadda ta baro gdn har ma soyayyar su da ya Affan bata 6oyemata ba kasancewar zarah yarinyace ba mai boyema mahaifiyar ta abu bace, ummah ta tausayawa yartata, haka ummah tayi ta ba zarah mgn tare dayi mata nasiha har taji ta natsu


Ya Affan ne zaune a tsakar dakinsa yayi uban tagumi duk ya rame yayi baqi ya lula duniyar tunani, Futha ce takatse masa tunanin shi ta hanyar dafashi da tayi "ya Affan plz kadaina wannan damuwar ka dubi fa yadda ka koma cikin qanqanan lokaci" cikin rashin son maganar yace " sister kenan dole indamu mana zarah ta kashe wayar ta, kuma banida tabbacin sokoto ta tafi fa, gaskia ni sister gobe zanje sokoto can inda Mum din amrah infadamata abinda ke faruwa dan nasan amrah bata fadamata ba, daganan anuna man gdn su zarah, ko ya kika gani?" " ehh bruhh, kuma wannan ma dabarah ce, Allah yasa adace, amma ka shawarci ammi kaji tata shawarar", "ok haka za'ayi insha Allah, amma ni ina mamakin amrah wlh saboda koni da bamu wani jima da zarah ba akwai abunda bazan taba yarda zatayi shi ba, ina gujema amrah ranarda zata gane gaskia saboda yanxu soyayya tariga ta rufemata ido", cikin qosawa Affan yace "uhm Allah yasa ta gane gaskiya, amma kam Amrah tayi butulci, ta ha'inci zaman tare, sai kice dai ba AMINNAN JUNA ba? A yanda naji labarinsu fa tun suna yara suke tare, aikuwa yaci ace sun fahimci junansu, su gane abnda ko wacensu zata iya yi.........Urs Zarah~B~B.






WISDOM HAUSA WRITERS.




Fatima~Bello~Bala
Share:

AMINAN***JUNA 151---160

aminan-juna.jpg

,AMINNAN JUNA


WISDOM HAUSA WRITERS,.




Na Xarah~B~B




151-155





"BAYAN KWANA BIYU"

Abubuwa da dama sun faru daga ciki harda amincewar soyayyar ya Affan da zarah tayi, tun daga tym din soyayya mai qarfi da shaquwa suka shiga tsakanin ZARAH DA YA AFFAN, ammi kuwa tafi kowa jin dadin faruwar hakan sbd ta yaba da hankali da natsuwar ZARAH

Su Amrah na hango sun shirya tsaf kowanan su yayi kyau bama kamar zarah ba, wayar zarah ce ta dau ruri ganin ya Affan ne yasa ta yin murmushin da ke qara fitar da kyan ta "Assalamu Alaikum", naji ta fada, adayan bangaran aka ansa da "wa'alaikun salam y kk tauraruwata?" ta ansa da "lafiya qlw nd u?" "D same" yabata ansa a taikaice", " idan kun shirya ku fito muje ina parking area" "ok gamunan fitowa "tou sai kun fito" tare da tsinke wayar"

"My futha ya Affan yace fa mukadai yake jira" zarah ta fada, dariya sukayi sa'annan sukace "tou matar yaya" tare da fita daga dakin, a palour suka same ammi tana kallo a TV, "ammi zamu tafi fa" inji Futha, "au kuce har kun shirya ma" "eh ammi mun shirya", "ok Allah ya kiyaye hanya ku gaida NABEELERT din" "zataji Amii" tare da yimata sallama suka wuce, a parking space suka tarar da ya affan bayan sun gaida shi suka shiga mota zarah zata shiga baya ya affan ya harare ta "ohhhhh kuce na zama driver dinku kenan", "uhm aa" ta fada "tou oya shiga gaba mu wuce" "ok" sa'annan ta shiga su Futha kuwa ba abunda sukeyi inba dariya bt basu bari ta fito ba.

Haka suka dau hanya sai GRA unguwar su aunty BEELERT kenan, anan ya barsu tare da shaida masu da cewa anjima zai zo ya dauke su, daganan ya wuce.....Urs
Zarah~B~B.





156-160




A parlour suka same ta kwance kan 3 seater tana kallo mbc bollywood da fara arta ta tarbesu bayan sun zauna ne take cewa "ni nayi fushi kwanan ku nawa a garin nan sai yanxu zaku zo?,, "aunty beelert plz we are sorry wlh muna son zuwa kin san komai sai Allah yasa" Amrah ta fada, " ai yanxu gashi munzo ko?" inji Futha "ni yiman shiru daman nasan kece kika hana su zuwa dan daman kema ba son zumuncin ne Dake ba", "aa fa aunty nifa ba ruwana" tana wata dariya can kasa2, " Amrah wacece wannan bangane ta ba" futha tai carab tace "zarah ce qawar amrah tare suka zo kuma........ " kallonda zarah ta mata ne yasa takasa qarasawa, "kuma me?" inji aunty beelert, "no aunty zan fadamiki bt ba yanxu ba" ta qarashe mgnr cikin zolaya, sun jima suna fira kiran sallar azahar ne ya tada su, bayan sun qare sallah ne wayar zarah ta dau ruri tana dubawa taga dai wannan sababbiyar number ce da ake damunta da shi saidai yanxu ta san mai number ba kuwa bane illah FAROUK har ta tsinke bata daga ba qara kira akayi ganin batada niyar dagawa yasa amrah daga wayar "ajiyar zuciya ya farayi kana yace "haba my zarah meyasa bakya son daga wayana? Kiyarda dani plz wlh zarah INA SONKI son da ban tabayiwa wata ya'mace ba, duk wata soyayya da nakewa Amrah wlh duk shirme ce, kece madubin dubawa na", jin batayi mgn ba yasa shi cewa "talk plz zarah" Amrah da tun da taji muryar hubbin ta ne tayi mutuwar zaune tuni hawaye suka wanke mata fuska ta kasa fadin komai sai rawar jiki da takeyi.........Urs Zarah~B~B

LUV U ALL MY SWEET SWEET FANS.

Note: pls kuyi haquri na rashin jina kwana biyu, hakan ya faru ne kasantuwar biki da mukayi,,,,,,,,,, kuci gaba da kasancewa da Zarah domin jin ci gaban labarin AMINAN JUNA.....


WISDOM HAUSA WRITERS AND WORLD WRITERS ASSOCIATION




Fatima~Bello~Bala.
Share:

AMINAN***JUNA 101----150

aminan-juna.jpg

[7:39PM, 5/20/2016] my mtn: AMINNAN JUNA


WHW



Na Xarah~B~B




111-115


koda suka farka daga bacci har ankusa shiga garin katsina da shigar su Katsina baba ilyasu bai tsaya da su ko ina ba sai Lay out, unguwar su Ammi kenan" horn yayi mai gadi ya bude masu gate, parking yayi sa'annan suka fito,

Jin tsayawar mota yasa Futha fitowa da sauri tunanin ko su Amrah ne, kofar shiga parlour suka ci karo "oyoyo mutanan sokoto sannun ku da zuwa" futha ta fada tana mai farin cikin ganin yar uwar ta.

Anan parlour suka tarar da Ammi itama sannu da zuwa ta hau yimasu, bayan sun huta aka wuce dinning suka ci abinci, anan ne Ammi ke tambayar Amrah mutanan sokoto ta ansa mata da "suna lfy ".

Zaune suke su uku adakin Futha suna ta fira, Futha tace " Amrah shin wannan qawar taki bata mgn ne?"murmushi Zarah tayi wanda ya qara fito da zahirin kyanta, Amrah ce ta bata ansa da " Aa tanayi mana me kika gani?" sai a lokacin zarah tace "meyasa kika ce haka Futha?" "Uhm uhm bakomai kawai dai naga bakice komai ba ne tun zuwanku", dariya sukayi sa'annan suka ci gaba da firar su cikin jin dadi da walwala, wayar Futha ce ta dau ruri ganin aunty NABEELERT ce ke kiranta yasa ta dauka cike da farin ciki tace "hello auntyna" banji me akace ba a dayan 6angaren sai naji tace "Allah sun iso tin dazu ma bara na baki amrar ku gaisa kafin mu zo", bayan sun gaisa da Amrah sukayi sallama tare da tsinke wayar.....Urs Zarah~B~B.





116-120


"Haba Farouk meyasa baka jin shawara ne?, yakamata kafi qarfin zuciyar kada ka biye mata ta kai ka gayin nadama a tym din da batada amfani", ajiyar zuciya yayi sa'annan yace "musty kasan fa shi SO baruwan shi da wannan yana zuwa ne a ko ina koda babu son muntun, so baruwanshi da wanda ya dace ko wanda bai dace ayi dashi ba", Musty yace "to naji , amma waya fadama ita ZARAH tana sonka? dahar ka daura wa kanka soyayyar ta haka, haba Farouk ina mai qara baka shawara da kayi hakuri kada kayi sanadin rabuwar way'annan masoya ka tuna fa" AMINNAN JUNA ne" sa'annan........ " Hannun da Farouk ya daga mai yahana shi qarasa mgnr, yace " kaga malam dan Allah ka kyaleni naji da abu daya idan ma zarar bata sona me naka aciki" musty sake da baki yake kallon shi aranshi kuwa ya tausayawa AMRAH dan yasan irin son da takewa Farouk. Baida yanda zayyi da farouk dole ya haqurah ya barshi.


Washegari!!!

Amrah ce zaune akan gado tana tunanin "meyasa Farouk bai kirata ba tun xuwan su katsina?" tin tana hakuri abun har ya fara damunta nd idan ta kirashi wayar bata zuwa, zarah ce ta katse mata tunanin da takeyi tace "my Amrah lfy Kuwa nagan ki haka? Ina kule dake fa duk kin canza tun kafin mu baro sokoto,miye damuwarki haka da har zaki 6oye min ita?"ajiyar zuciya tayi tace "Hmmmm!!! Wlh abun na damuna my zarah tinfa zuwan mu hubby bai kirani ba nd idan na kira bata zuwa, kusan ma ince miki tun kafin mu baro sokoto nake ganin canji a wurinshi, na rasa yanda zanyi dashi, ni damuwa na ma d'aya ne Allah yasa yana lafiya" Zarah tace " amma kuma bana ji kina waya da musty ba jiya?"Amrah tace "ehh wai shima be sani ba ko yana lafiya, munyi dashi zaije ya dubashi a Hostel kin san ya koma can, so kuma shima d'in ina ta nemanshi yaqi picking call d'ina, shi yasa kikaga na damu da yawa" cikin tausayi da jinqan qawarta Zarah tace "kiyi hkr my Amrah may be matsalar network ce, kibari zuwa anjima sai ki qara trying number" haka dai tayi ta bata mgn har ta samu natsuwa.

Shakuwa ce tashiga tsakanin Futha da Zarah kamar sun dade da sanin junan su, ita dai Futha tana jin son zarah aranta nd tana jin dadin zama da ita haka itama zarah take jin son Futha.

"Ammi wai yaushe ne ya AFFAN zai dawo?" ta qarashe maganar cikin shagwa6a, Ammi tace "yakusa dawo insha Allah munyu waya yace baifi kwana biyu ko uku ba ya dawo " Amrah tace "ok Allah ya maidoshi lfy, Ammi kun san fa na dad'e rabona dashi, dan ko a hanya na ganshi ba lallai bane in gane shi nasan shima d'in haka" Ammi tace "injiwa ya fad'a miki? Sai dai idan kexe bazaki ganeshi ba amma shikam dole ya gane ki", ta'be baki Amrah tayi tare da cewa "tou Allah ya dawo dashi lafiya" duka suka amsa da "amin"....... UrsZarah~B~B.



WWA


Fatima~Bello~Bala.
[21/03 10:17 PM] Zara Bb: AMINNAN JUNA



WHW



Na Xarah~B~B




121-125



BAYAN KWANA BIYU!!!

Yaune ranar da ya affan zai dawo daga uk ya kammala karatun shi na likita.

Shirye2 ne suke tayi a gdn na tarban ya affan basu da kammalawa ba sai 12:00pm kasancewar sai 2 jirgin su zai iso,

Sun shirya tsaf kowanan su yayi kyau sosai sai kace wasu yan uku, ammi ce keta zolayar su suna dariya, anan dai suka wace sai airport, da isar su basu jima ba sai ga jirgin ya iso,

Wani kyakkyawan saurayi ne naga ya fito daga jirgin, fari ne tass shekarun shi baxa su wuce 29 ba, ahankali naga ya nufi gurin da su Futha suke tsaye, da gudu Futha taje ta rungume shi "oyoyo ya affan" fuskar shi dauke da murmushi wanda ke qara fito mashi da kyan shi ya ansa mata da "yauwa lil sis".

Rike da hannun ta har suka iso gurin da su ammi suke cike da girmamawa ya gaida mahaifiyar shi, kamar daga sama yaji su Amrah na fadin "sannu da zuwa ya affan" wanda sai a tym din ya gansu ya ansa da "lfy qlw", ahaka suka kama hanyar zuwa gd......Urs Zarah~B~B.





125-130



"Da isar su gd ya affan ya wuce room din shi,bathroom naga ya shiga bai wani jima ba ya fito riqe da towel a hannun shi yana goge ruwan jikin shi, bai wani bata tym ba ya shirya tsaf cikin riga da wando 3Q ya feshe jikin shi da turare yayi kyau sosai, sa'annan ya fito.

A parlour ya same su,"oya tashi muje dinning daman kai kaidai akejira" inji ammi ba musu ya miqe suka wuce dinning, futha ce tayi serving dinsu sa'annan suka fara cin abinci da ka gansu kasan suna cikin jin dadi da walwala "happy family kenan".

Bayan sun kammala parlour suka koma anan fira ta 6arke, shi kuma ya affan sai satar kallon zarah yake yi, kiran sallar la'asar ne ya tada su,dakin su suka wuce don gabatar da sallah, shigar su keda wuya wayar zarah ta dau ruri tana dubawa taga dai wannan sababbiyar number ce da ake damun ta da shi tsaki tayi kana da aje wayar "meyasa bazaki daga ba?" inji futha, nima dai narasa dalilin ta naqin picking din call din nan inji Amrah, kallon ta zarah tayi tace "bakomai kawai dai ban san number bane", Amra tace " bt yakamata ki daga kuda sau daya ne kiji kuma waye ai" Zarah tace "ok naji zan dauka".

Bayan sun kammala sallar ne ya affan ya kira Futha, a dakin shi ta same shi yace "wai lil sis wacece ta tare da Amrah?naga kaman ban santa ba" zarah ce qawar amrah tare suka zo ta bashi ansa, ya akayi ne ya affan?" "no bakomai i just ask kya iya tafiya" tare da bata kayan tsarabar ta harda su amrah sa'annan ta wuce zuwa room dinta.....Urs Zarah~B~B.


NOTE: Plz am very sorry kwana biyu kunji ni shiru bana jin dadin jikina ne shiyasa. Tnx alot. Luv u all my Fans

WHW


Fatima~Bello~Bala.
[7:39PM, 5/20/2016] my mtn: AMINNAN JUNA



Na Xarah~B~B



101-105

" Ummah mun kusa tafiyar "cewar Zarah, Ummah tace "Au daman da gama exam ko hutawa bazakuyi ba sai tafiya?" "Uhm Ummah wane hutu kuma idan muka je ai mayi acan kinsan hutun bawani yawa ne da shiba fa", ummah tace "ehh hakane, yaushe zaku je ne?" " nan da 2 days insha Allah" Zarah ta bata ansa, " ok Allah ya kaimu" cewar Ummah, Zarah ta ansa da "amin Ummah na".

Amrah ce kwance tana waya da Futha sun dade suna waya sa'annan sukayi sallama tare da shaida mata cewa sun kusa zuwa. Ba qaramin farin ciki Futha tayi ba, saboda yanda take tsananun son ganin Amrah, nan suka kashe wayar kowa na mararin d'an uwanshi.

Washegari!!
Ta kama Friday Amrah ce dasu Mum zaune a parlour, Amra tace " Dad jibi ne muke son tafiyar nan xuwa katsina fa" , Dad yace "Au kice har tym yayi kenan ?", "eh Dad yayi" "ok sai ku fara shirye2 kenan, ko dawa wani abune wanda kuke buqata?", Amtah tace " Eh dad ina so zan masu tsaraba ne" Dad yace "ok kamar nawa kike buqata?", sai da tadanyi tunani kafin tace " dad koma nawa ka bayar zasuyi" ,kudi masu yawa Dad ya zaro a aljihu yabata.

Shirye2 sukeyi ba kama hannun yaro sai kace masu Shirin bari kasar baki daya koni Zarah saida suka bani dariya tafiyar da ba wata mai dadewa ba amma sai wannan shiri ake, shiru nayi da bakina na masu fatan sauka lafiya.

Zaune take suna fira da umman ta cikin jin dadi, qarar wayar ta taji tayi saurin dubawa, sunan da tagani yasata daqawa cikin hanzari, "Hello My Amrah ykk?" cewar Zarah dayan bangaran aka ansa da "lfy qlw My Zarah ya umma na?" ta ansa da "lfy qlw take", ok ki gaida ta cewar Amrah" " zataji" "yauwa Zarah na daman inaso ne muje mu ida siyayyar da bamuyi ba saboda time ja qurewa", Zarah tace 'kai my Amrah duk wannan siyayyar da mukayi har sai munyi wata?" "Eh sai anyi ta" qarishe mgnr kamar zatayi kuka, "haba am srry my besty na daina" cewar Zarah "ok to ki shirya gani nan zuwa muje" "sai kin zo amma fa kiyi sauri kafin likacin islamiya yayi", sallama sukayi tare da katse wayar....Urs Zarah~B~B




106-110



Zarah bata 6ata tym ba ta shirya tsaf cikin riga da zane yellow nd wyt atamfa , hijab ma wyt tayi kyau sosai, Amrah na zuwa suka wuce, siyayya sukayi mai yawa sa'annan suka koma gd.

Yau ta kama SUNDAY ranar da su Amrah zasu yi tafiya, Amrah ta shirya tsaf cikin riga da skirt blue nd wyt in colour sun mata kyau sosai ta jawo trollyln ta zuwa parlour, "Au har kin shirya tun da wuri haka?" cewar Mum "eh" Mum, "tou kije kiyi breakfast tunda da sauran lokaci" Amrah tace " uhm mum ni na qoshi", kamar ya kin qoshi me kika ci ne? "bakomai cewar Amrah "oya wuce kiyi breakfast" haka dai tayi breakfast din ba don taso ba,

Har gate Mum da Dad sukayi mata rakiya. "To ilyasu dan Allah ku lallaba Allah ya tsare hanya nasanka baka gudu da mota, tou pls kaci gaba da hakan, sannu bata hana zuwa, saidai a dade ba'ajeba inji hausawa, kabi mota a hankali harku isa, Allah ya kaiku lapia" cewar Dad duka suka ansa da "amin" bayan sunyi sallama, Amrah ta shiga mota suka wuce gdn su Zarah.

Ringing biyu ta daga "dafatar kin shirya?" Cewar Amrah, cikin hanzari Zarah tace "eh na shirya ke kadai nake jira" bata rufe baki ba taga Amrah a gabanta tana mata murmushi, Zarah tace " Au kinma iso shine kika kirani, dariya sukayi gaba dayan su sa'annan Amrah taja trollyln Zarah suka fita,

A parlour suka tarar da ummah, nasiha ta masu sosai tare da masu Allah ya kiyaye hanya sukayi sallama har mota ummah ta masu rakiya sa'annan suka wuce wayar Zarah tahau ruri, koda ta duba taga wannan sababbiyar numbern ne dai da ake damunta, barin wayar tayi har ta tsinke bata dauka ba, Amrah tace "Zarah ki dauka mana ana kiranki kina ji", Zarah tace "rabu dani pls! Wlh an dameni da kira ne da number'n nan, ni bana son disturbing wlh", ta buga uban tsaki, Amrah sake da baki tace "Allah ya baki haquri aunty masifan bani na kashe zomon ba rataya aka bani", Zarah tace "naji dai ki qyale ni..." bata gama fadi ba aka kuma kiranta, switch off dib wayar tayi baki daya tana jin haushin wannan anacen dake kiranta kullun duk da ba dauka take ba, a haka har bacci ya daukesu, saboda tafiya daga Sokoto zuwa katsina ba abune me sauqi ba.........Urs Zarah~B~B.
la
[7:39PM, 5/20/2016] my mtn: AMINNAN JUNA



WISDOM HAUSA WRITERS.




Na Xarah~B~B






131-135



Akwana atashi ba wuya agurin Allah yau su Amrah satin su daya a katsina shakuwa me qarfi ta fara shiga tsakanin zarah da ya AFFAN saboda ta dan fara sakin jikin ta da shi sai dai ba sosai ba, duk da har yanxu bai furta mata yana son ta ba amma su Futha har zolayar ta suke suna cemata matar yaya, tun tana nuna bata so har ta kyale su.

Amrah ce kwance tana ta tunanin abn qaubarta, wayarta ta dau ruri ta sauri ta dauka jin special ring tone data saka mishi, "Haba hubby sai yanxu zaka kirani tun zuwan mu garin nan? Kuma kona kira wayar ka bata shiga", ajiyar zuciya Farouk ya sauke tare da cewa "no my luv bahaka bane wlh", "to yane?" ta fada cikin kunar rai, "banida lfy fa kuma wayana faduwa tayi saida nayi welcome back" ya fada cikin muryar tausayi, "hmmmm!! to meyasa baka kirani koda da wayar musty ce ba? ku bakada number na a kanka ne?" rasa ansar da zai bata yasa yace mata "yanxu dai ba wannan ba plz nd plz am very sorry my luv ki yafe mai kinji" ya fada kamar zaiyi kuka, ajiyar zuciya tayi kana tace "bakomai ya wuce", aranta kuwa wani irin dadi taji daya kirata ga wata soyayyarshi da kullun yake qara mamaye zuciyarta. {Allah sarki soyayya kenan, Allah ya hada mu da masoyan gaskia ba irin su FAROUK ba, ameen ya rabbi},waya suka cigaba dayi kamar batayi fushi da shi ba, ahaka har sukayi sallama tare da tsinke wayar.


Ya AFFAN ne kwance a dakin sa sai juyi yake yi shidai har ga Allah yana son zarah kuma son gaskia yake mata amma ya rasa da yadda zai sanar da ita, ahaka dai har ya yanke shawarar fadawa lil sis dinshi ko zata iya taimaka mashi gurin isar da saqon zuciyar shi,da wannan tunanin har bacci ya dauke shi.

Washegari!!!
Ya affan ne ya kira futha zaune suke suna kallon junan su, ya nisa yace
"lil sis inaso muyi wata mgn dake kinji" Futha tace "ok ina jinka big bro", Affan yace "daman..."sai kuma yayi shiru, dariya Futha tayi don ta gane me yake son fadi tace "daman me ya affan ka fadi mana", "uhm sis kenan Allah ina son zarah amma na rasa ta ina zan fara tun karar ta ne", dariya tayi kana tace " ya affan kenan ai kuwa gara ka fadamata saboda kaga sun kusa tafiya may be ma jibi zasu kuma wlh zarah bata da matsala ina tunanin zata amince dakai".....Urs Zarah~B~B.





136-140



" Ido ya zare da gaske kike lil sis"? Tace "Allah da gaske nake ya affan gara ma ka fadamata", Affan yace "to yanxu ya kike ganin za'ayi?" Sai data murmusa sannan tace " Kawai kabari na turo ma ita yanxu dana shiga ciki, amma dan Allah karka kopsa big bruhh" yace "ok sis tnx alot, bazan kopsa miki ba".

Da shigar ta dakin da fara arta ta kalle zarah tace "my cwt Zarah ya affan na kiran ki yana parlour" ido ta xare tace " ni? Ya Affan?" "eh ke fa" Futha ta fada tare da neman wurin zama ta zauna.
A parlourn kuwa ta same shi yana zaune kan kujera a kasa ta zauna "ya affan ina wuni" ta fada cikin girmamawa ya amsa da "lfy qlw ya baqunta?" " Lafiya qlw" tace atakaice, yauwa zarah daman ina... sai kuma yayi shiru ganin shirun yayi yawa yasa yace "yaushe zaku wuce ne?"
Jibi insha Allah ta bashi ansa ok Allah ya kaimu ta ansa da "amin" zaki iya wuce wa, "ok"

Bayan ta wuce kuma duk yaji haushin abunda yayi why why nakasa fadamata,

Zarah ce kwance tana waya da umman ta sun jima suna waya kana sukayi sallama.Alamar shiguwar text taji ganin number ya affan ne yasa ta budewa da sauri ta fara karantawa kamar haka:

"I want to treat you lyk a queen simply bcos you rule my world. I am at ur Service, ur majesty". I really really love u, i hope u luv me too.

Ajiyar zuciya tayi kana ta aza wayar kan kirjin ta, koh dama shine ya affan ke son fadaman ranar da ya kirani? haka ta cigaba da tmbyr kanta, shigowar su Amrah ne yasa ta natsu bt still ta juya mgnr "i really really love u, i hope u luv me too" mgnr Futha ta dawo da ita, wai mekike tunani ne haka inji Amrah, uhm bakomai ta bata ansa..... Urs Zarah~B~B




WWA





WISDOM HAUSA WRITERS

Fatima~Bello~Bala.
[23/03 11:40 PM] Zarah B B: AMINAN JUNA

WISDOM HAUSA WRITERS.


Na Xarah B B

141-145

A daren ranar haka Zarah ta kwana da tunanin Affan, amma kuma ta kasa mishi reply da ta amince, a bangarenshi shima tunanin shi bai wuce qila Zarah bata karbi soyayyarshi ba, haka ya kwana kamar wani zautacce dan son da yakewa Zarah bai misaltuwa, dis is his first time daya fara soyayya, shi yasa yake jinta a jinin jikinshi.

Washe gari tunda safe Zarah ta tashi kamar yanda ya saba ta shiga kitchen, bata tsaya jiran su Futa da Amrah ba ta hau hada masu breakfast n haka Zarah take bata da ganda ko kadan, komai yawan aiki ita baya bata haushi.

Bayan ta gama ta jera komai akan dining table ta shiga ta kira kowa kamar yanda ta saba amma sai ta samu kanta da kasa kira Affan, har sun zauna mum tace "wai ina Affan ne? Hala nawar tashi ce daya saba? Dan na tavvatarda Zarah ta fada mashi tunda kullun saita fada mashi", Zarah sai qwalo ido take sai ji tayi ance "kamar kin sani kuwa mum, ta riga fada min akan kowa, na tsaya yin wanka ne", kyakkywar ajiyar zuciya Zarah ta sauke tare da sinne kanta qasa, koda suka hada ido ya qifta mata qwara daya har cikin ranta taji, taga kuma zahirin soyayyarta a idon Affan, da wannan tunanin suka kammala kalaci itakam kadan taci bada yawa ba.




146-150



Bayan sun gama komai na gida Futha tace "yau muke resuming a skul fa kuma ya kamata inje, kunga saiku takani muje tare daga nan har kuga yanda skul din mu take", Amrah tace "aikam haka ya dace, sai mu dora girki da wuri yanda zamu gama da wuri", Futha tace "ai da yake ma yau baba Rabi zata dawo, nasan da wuri zata zo", Amrah tace "hakane kuma, wai qawa yau ya akayine kikayi shiru?" Budar bakin futha cikin sauri tace "she is in love fa" suka dauki shewa harda tafawa, zarah dai batace masu komai ba dan tasan gaskiya suka fad'a, sai can kuma tace "ai qawa da yake kin samu baki dole kimun iskancin da kikeso, dan kin samu Farouk ya kiraki ne fa", wayar Amrah ta dauki ruri da farin ciki tace "kinga dan halak, bawan Allah ana cikin gulmarshi sai gashi ya kira, wama yasan ko jikinshi ne ya bashi", daukan kiran tayi tace "hubby how fa?" Bai bata ansa ba sai yace "dear pls idan kina kusa da Zarah ki bata, ina son gaisawa da ita", cikin kishi Amrah tace "shine kuma bazaka karva gaisuwata ba ko", haquri ya bata nan da nan ta haqura saboda bata sin laifinshi, ta miqawa Zarah wayar, Zarah tace "lapia?" Amrah ta mayar mata da "I dont know, just take d phone kedai zaku gaisa ne I thinks", kar'bar wayar tayi tace "na Amrah ya kake?" Sai daya sauke ajiyar xuciya alaman missing d'inta tukuna yace "lafiya kalao, wai me yasa baki damu dani bane Zarah? Me yasa bazaki dauke ni kamar yanda Amrah ta daukeni ba?" Mamaki sosai maganarshi ta bata tace "ban gane ba", saurin kawar da maganar yayi yace "barshi kawai dear, xan kiraki anjima amma pls karki daga kiran a gaban Amrah", "tou" kawai tace tare da miqawa Amrah wayarya, koda ta kara a kunne taji har ya kashe, abn ya bata haushi sosai amma sai ta kawar dan bata so qawarta ta fahimci tana kishinta ne.

WISDOM HAUSA WRITERS.

Fatima Bello Bala
Share:

AMINAN***JUNA 61---100

aminan-juna.jpg

[7:39PM, 5/20/2016] my mtn: AMINNAN JUNA


Na Xarah~B~B


71-75


Zaune suke suna fira cikin jin dadi da farin ciki abin gwanin sha'awa "Dad kaga mun kusa fara exam, Plz dad idan mun qare inson inje katsina nida Zarah gurin Ammi muyi hutun mu acan plz Dad, ta qarashe maganar cikin shagwa6a" Dad yana murmushi yace Amratu kinsan bana son kiyi nesa damu fa, Amrah cikin shagwa6a tace plz dad nafa dade banje ba plz, yace ok Allah ya kaimu tym din, cewar dady suka ansa da "amin" Mum da tunda suka fara mgn kallon su kawai take tana murmushin su na manya, Mum bakice komai ba fa, cewar Amrah, Allah ya kaimu lokacin cewar Mum, Amrah ta ansa da "amin"

Anan Amrah ta bar iyayen nata bayan ta masu saida safe ta wuce room dinta, ta shigarta kuwa Shirin bacci tayi, bayan ta kwanta ne taji qarar wayar ta alamar ana kiran ta, Hubbyn ta, ta gani ya fito kan screen 6aro 6aro, bayan da daga wayar suka gaisa anan kuma suka cigaba da soyewar su, can kuma naji a dayan 6angaren yana fadin "My luv" daman kuma sai yayi shiru, daman me? Cewar Amrah, Plz hubby feel free nd say what ever u want to say plz, daman ina buqatar kudi ne, ajiyar zuciya Amrah tayi sa'annan tace daman wannan ne ka kasa fadaman, ok bakomai kamar nawa kake buqaka?ganin baya da niyar magana yasa tace 20k zasu ishe ka? Cikin rawar murya yace "eh zasu ishe ni my luv" Tnx alot Allah ya saka maki da alkhairi, Amrah ta 6ata rai kamar yana ganin ta tace "No need" kafi karfi komai a wurina hubby insha Allah gobe zan shigo ma dasu......Urs Zarah~B~B


75-80


Am srry na daina cewar Farouk, ok tnx gud nyt Farouk ya ansa da ok swt drm bye bye ta katse wayar.

Har bacci ya suma daukar ta sai taji alamar text ya shigo wayar ta kamar bazata duba ba kuma sai ta duba taga number Hubbyn tace tayi murmushi ta fara karanta wa kamar haka

"Words alone will never be able to express the depth of my luv 4 you".

Gud nyt my luv" Swt drm " Tnx alot once again bye.

Ajiyar zuciya tayi tare da fitar da wani iska huuuuuuuuuuuu sa'annan ta aza wayar akirjinta ta lumshe idonta tare da fadin" I really love u Farouk" ahaka har sarkin barayin ya sace ta.

Bangaren Farouk kuwa murna kawai yakeyi bt acikin zuciyar shi yana tunanin ta ina zai 6ulluwa lamarin don shi har ga Allah bason Amrah yakeyi ba hasalima Aminiyar ta yake so{Ni ku Xarah nace me hankalin ka daya kuwa Farouk? Me kake Shirin yi ne? Ganin banida mai ansa man tambayoyina yasa naja baki na}

Musty ne ya shigo ganin abokin shi bai masan da shigowarshi ba yasa shi dafa kafadar shi, cikin tsoro Farouk ya juya don ganin waye, ganin musty atsaye yasa shi yin ajiyar xuciya, lafiya kuwa kake Farouk? Cewar musty, yace abokina bazan 6uye maka ba a gaskia ina cikin wata damuwa, musty yace meke damun ka?

Farouk yace musty a gaskia ni bason Amrah nake ba hasalima Aminiyar ta nake so, musty yace wat kasan mekake fada kuwa Farouk?.....Urs Zarah~B~B



Fatima~Bello~Bala
[7:39PM, 5/20/2016] my mtn: AMINNAN JUNA


Na
Xarah~B~B


61-65

Ya kalle Musty yace bakomai abokina, are u sure? cewar musty, Farouk ya gyada masa kai alamar"Yes" yace ok Allah yasa muda ce duka suka ansa da "amin".

Washegari!!
Ta kama Monday Amrah ce ta shirya tsaf cikin doguwar riga black, tayi rolling da qaramin gyale mai rabaja red in colour,ta fito ta wuce dinning area acan ta sa me su Dady bayan ta gaishe su, suka fara yin breakfast, soyayyen dankali ne da kawai, da soyayyar doya sai ferfeson kayan ciki, da ruwan tea a flask,

Breakfast sukeyi cikin walwala da ka gansu kasan suna cikin farin ciki, ahaka har suka qare tamasu sallama ta wuce gdn su Zarah.

Ringing biyu ta daga "gani a qofar gd na iso" cewar Amrah, Zarah da sauri2 tama ummah sallama kasancewar yau sun danyi late suka wuce sai UDUS.

Kuda suka isa lecturer har ya shiga da sauri suka nufi hall din suka zauna, bashi da fita ba sai 10 sa'annan wani ya shigo haka suka rinqa yin lectures yau har 4:00pm sa'annan suka kammala.

A kan hanyar kuma warsu ne Amrah ke cewa "My ZARAH" ta juyu da kallon ta ga Amrah tace Na'am ya akayi ne? Amrah tace kinga munkusa fara exam, da munqare inason muje katsina inda qanwar Dadyna, muyi hutun mu acan, inason ki fadawa ummah plz nd nima zan fada mata, Zarah tace Allah ya kaimu nd insha Allah zan fada mata, haka suka ci gaba da firar su har suka isa gd,sukama juna sallama, Zarah bata shiga cikin gd ba sai da taga Amrah ta wuce sa'annan ta shiga.

A parlour ta same Mum tana kallon TV, direct gun Mum ta wuce ta zauna kusa da ita bayan sun gaisa mum tace ya skul din? Amrah ta ansa da lafiya qalau Mum, mun ma kusa fara exam,ok Allah ya taimaka cewar Mum, Amrah ta ansa da "amin" dinning Mum ta nuna mata, tace taje taci abinci, No mum sai nayi wanka tukunna"ok"cewar Mum, daganan ta wuce sai dakinta.... Urs Zarah~B~B



65-70


Da shigar ta, ta nufi bathroom bata jima sosai ba ta fito, bayan ta shirya tsaf cikin qannan kaya riga da skirt ne sun mata kyau sosai sai dan qaramin mayafi da ta dura akanta ta wuce sai dinning area, bayan ta qare ne zata wuce room dinta isuwar dady ne ya hana mata qarasawa "oyoyo dady sannu da zuwa" yauwa Amrah kina lfy? lfy qlw dadyna ya aiki? "Alhamdulillah" cewar Dady, sai a tym din suka gaisa da Mum, tana murmushi tace tahanaka ka huta ta dameka da surutu Amrah ta turo baki Dad yayi dariya yace kyaleta Amratu ta, tayi murmushi sa'annan ta wuce dakinta tabar Mum da Dad nan a parlour,

Tana shiga tayi gun wayar ta, 5 missed call tagani tana dubawa taga 2 missed call na zarar ta ne, sauran kuwa na Farouk ne, ido ta xare sa'annan ta zauna kan gado ta sa kiran Farouk har ta katse ba'a dauka ba ta kara sa kira har ta kusa katsewa sa'annan aka dauka ajiyar zuciya ta fara sauke wa sa'annan tace"Hello hubby shine kaki daukar wayar? Aa bana kusa ne tace ok, nima na bar wayar a dakine ina parlour nida su Mum shiyasa ban daga ba, a dayan banqaren naji yace bakomai my luv, murmushi tayi tare da rungumar pillow" haka suka cigaba da firar su suna zuba soyayyar su,har sukawa juna sallama badun sun gaji da wayar ba.

Sai tym din tasa kiran Zarah bayan sun gaisa, suka ta6a fira kasancewar anfara kiran sallar magreeb yasa basu jima suna wayar ba sukayi sallama.

Toilet ta nufa don dauro alwala bayan ta idar da sallah ta dauko Alqur'an ta fara karanta wa ba ita da tashi ba sai da tayi sallar isha'ee sa'annan ta ninke sallaya da hijab din ta ajiye, Ta wuce parlour anan ta tarar da Mum da Dad da alama dawowar shi kenan daga masallaci....Urs Zarah~B~B
[7:39PM, 5/20/2016] my mtn: AMINNAN JUNA


Na Xarah~B~B


91-95


Futha! Futha!! Futha!!! Wai kina ina ne haka inata kiranki, Na'am Ammi gani nan zuwa, a parlour tasame Ammi na kallo a TV ta zauna akasa kusa da ita tace Ammi gani, ina kika shige ne inata kwala maki kira bt baki jiba, Wlh Ammi bana kusa ne cewar Futha, ok daman Amrah ce tace takira wayar ki bata shiga, tace na maki albishir nan da 2 days zasu zo itada qawar ta,

Futha ta dago kanta da sauri cikin farin ciki, Ammi yaushe ta kiraki? yanxun nan tace ma anan zasu yi hutun su, sai ki fara shirye2 tarbar su, ok Ammi ta fada tare da tashi zuwa room dinta.

Amrah da Futha yan sa'ane shekarun su zasu zo daya, Futha itace diyar Ammi Watau qanwar dadyn Amrah ita ke bimashi su biyu ne kacal ga iyayen su,

Transfer da akayiwa Abban su Futha ne a wurin aikin su, ya maida su zama a katsina, duk da tym din da zasu dawo Ammi bata ji dadi ba, ba don kome ba sai don nesan da zatayi ne da dan uwanta, saida dady yayi ta bata baki tare da yimata alqawari duk lokacin da yasamu chance zai rinqa zuwa.

Ya'yan su uku ita da mijin ta Namiji daya macce biyu, Usman wanda sukafi kira da "Affan" sai Nabeelert itama tayi aure sai autar su Futha, kasancewar batayi karatu mai tsawo ba tayi aure nd kuma ta riga dadyn Amrah yin aure saboda krtn da yayi mai tsawo kuma Allah bai basu haihuwa da wuri ba shida Mum din Amrah...... Urs Zarah~B~B.




95-100


Alhamdulillah yaune su Zarah da Amrah suka kammala exams dinsu cikin jin dadi da farin ciki, can na hango su suna sallama da course mate dinsu kasancewar yau zasu tafi hutu, bayan sun qare ne naga sun nufi motar su.

Da shigarsu Amrah tasa kiran Farouk bayan ya daga wayar naji tace kana inane yanxu? Ina hostel cewar Farouk, ok ka fito gamu nan zuwa, yace ok sai kun iso,

Hanyar hostel naga sun dusa, a qarqashin wata bishiya tayi parking sa'annan ta sheda ma Farouk cewa sun iso, kafin yazo ne Zarah ta kuma seat din baya ta zauna, saiga Farouk ya iso, da isowar shi ya shiga mota ya zauna "ya exams my luv? exams Alhmdllh, hubby ya taku exams din? da godiya cewar Farouk,to Allah ya taimaka yabamu sa'a da rabu baki dayan mu, duka suka ansa da"amin" da yake su Farouk basu ida tasu ba.

Anan dai sukayi mgnr da zasuyi har take fada mashi cewa nan da 2 days zasu je katsina, Haba my luv yanxu tafiya zakiyi ki barni? No hubby bahaka bane gun qanwar dady zanje fa nd na jima banje ba shiyasa bt ba dadewa zamuyi ba ta qarasa mgnr cikin shagwa6a tare da langa6ar da kanta, ok bakomai Allah ya kiyaye hanya cewar Farouk, ta ansa da "amin"

Anan ta ciro 20k ta bashi tace yayi hkr da wannan, ba musu ya kar6a tare dayi mata godiya, ganin ta 6ata rai ne yasa yace "ohhhhh am sorry na daina" suka sakarwa junan su murmushin dake qara fitar masu da kyan su,

Anan sukayi sallama ya wuce, zarah ta dawo seat din mai zaman banxa suka wuce sai gd..... Urs Zarah~B~B.



Fatima~Bello~Bala.
[7:39PM, 5/20/2016] my mtn: AMINNAN JUNA


Na Xarah~B~B


81-85


Haba Farouk kaji tsoron Allah wlh kada kaxama sanadin rabuwar way'annan masoya ka tuna fa AMINNAN JUNA ne idan har kuwa kayi qoqarin rabasu to wlh hakkin su bazai barka ba, ka tuna irin son da AMRAH ke maka, kasan bason ta kake ba meyasa zaka yaudare ta?

Farouk ya tashi a fusace yace kaga malam ni ba wa'azi na ne meka ba idan wa'azi kake son kayi kasan inda yadace kaje kayi shi don haka baruwan ka da rayuwata daman dalilin da yasa kaga na fada ma shine don ka fadaman ta yadda zan 6ulluwa lamarin, ba don kaman wa'azi ba yayi tsaki ya fice daga dakin,

Musty kasa aiwatar da komai yayi kallon shi kawai yake yi saki da baki har yabar dakin, yana tunanin irin hali na abokin shi, a fili yake fadin Allah ya shirye mu baki daya"Ni Xarah na ansa da amin"

Washegari!!
Amrah ce tare da Aminiyar ta na hango da alama sun fito daga lectures ne, motar Amrah naga sun nufa suka jingina akan motar, kira naga Amrah tasa har saida ta kusa katsewa sa'annan ya dauka "Hello hubby kai muke jira fa" a dayan bangaren banji me yace ba kawai naji tace ok kayi sauri plz,

Ta juya kallon ta ga Zarah wai yana zuwa, Zarah tace ok bakomai sai yazu...... Urs Zarah~B~B.



85-90


Ba'a dau wani tym ba sai gashi ya isu bayan sun gaisa ne sai Zarah tace "My Amrah ina zuwa plz" ina zaki je ne? Cewar Amrah, ba nisa zanyi ba yanxu zan dawo, Amrah tace ok karfa ki jima, tace insha Allah yanxu zan dawo,

Murmushi kawai Amrah tayi don tasan halin qawar ta sarai bawani gurin zata je ba tayi hakane kawai don ta basu guri ita da hubbyn ta, Shiku Farouk yaji haushin dagawar da tayi bt dole ya danne,

Mota suka shiga Amrah a seat din driver Farouk ana mai zaman banxa bayan sun qare firar su ne ta bashi kudin sa'annan sukayi sallama ya wuce.


BAYAN KWANA BIYU!!
Su Amrah sun fara exams karatu takeyi serious, shiyasa ma yanxu sukan iya 2 days basu hadu da hubbyn ta ba, some tyms saida daddare suke waya mai tsawo,

Zarah ma haka karatu take yi serious, yau ma kamar kullun zarah na room dinta tana karatu qarar wayar ta taji ganin baqowar number yasa taki dagawa, haka akaci gaba da kira bt Zarah ku ajikin ta, taqi daga wayar daga karshe silent ta sakata bcos tana damun ta....Urs Zarah~B~B.


Fatima~Bello~Bala
Share:

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).