shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Sunday 26 July 2015

WACE CE********ITA? 81 & 82

computerimages1.jpg

WACE CE ITA??

81


*******by***********


muhd-Abba~Gana
(sharifin_zamani)

Anyi suna lafiya ansha shagali taga yanda ake
soyayyah gurin farahnax ranarda mijinta yaxo
tana wani mai shagaba tana narkewa abin dariya
yake bata, kuma gaban kowa zata mai haka
saidai a bata guri badai ita ta basu guriba
abinsu yana burgeta, farahnax takance niko
sister iffo zanso naga ranarda zaki daina halin
ki, takanyi murmushi baatace mata komai. duk
abinda sukeyi tana recoding a kanta kuma shima
yana shiga cikin list dinta zata ma farhaan dinta
fiye da wannan idan ya dawo...
Duk kudinda abba yake xuba mata da wayanda
farhaan yabar mata taje ta siyo arnar nyte dasu
ta siyo English wr masu zafi ita kanta tasan dole
ya girgixa idan ya gansu gashi yana sonta dole
kuwa yayi sha'awarta..
Nidai sai kallo nake wai iffaat ce take tanadin
kayan da za'a sakawa miji, batada matsala gurin
kwalliya ta iya kayanta tana biye da group chat
duk abinda akace yana saka ni'ima saitaci tasha,
duk wannan tanadin na PURHUUN dinta ne,
Ranar tana zaune a Palo ta qare gyara gunba
yatsunta sunyi kyau abinta, tayi zaune tsakayar
daki saman center carpet tana kallo taji
tsayuwar mota ta dauka maman Nargees ce Dan
taje siyyah kasuwa kuma kayan sunada yawa da
zata siyo, ko motsi batayiba taci gaba da
kallonta daga bayan ta taji mutum ya Dora
wuyansa akan kafadarta ta wani zabura da qarfi
amma qamshinsa ya bayyana mata wayeshi!
farhaan ne batasan lokacin da maqalqaleshiba
tana dariya yayi surprised dinta ba kadanba
mutumin da akace zaiyi wata biyu koma fiye
amma yau kwana 48 ya dawo, farhaan kam
murna yakeyi yauga iffaat dinsa a jikinsa kuma
da ra'ayin kanta, ta sakeshi ta riqe kunkumi tana
dariya tace, wai Kaine naka gani ko kuwa
mafarki nakeji, yace sosai nine farhaan na dawo
na gaji da rashinki kusa dani koda kuwa kasheni
zakiyi gara ina ganinki tayi dariya na Isa na
kashe yayan farahnax, yayi dariya dhima ya
janyota jikinsa uhum su farhaan an sami yanda
akeso....
.: WACE CE ITA..??82




********by**********
muhd-Abba~Gana


Ya jata kujera Suka zauna tace Bantaba tunanin
zaka dawo yanxuba shine ko waya kaqi gaya
min ai da sai ko girkine a maka, mamakine ya
cikashi shikam gara da yayi tafiyar nan tayi
missing dinsa, hadda su girki,! ana wani mai
murmushi shida idan yaga dariyar ta to tabbas
tamai mugunta ne take dariya....!! .
mai gadi ya fara shigowa da kaya niqi niqi yana
ijiye wa gefen qofa, ya rungumota sosai jikinsa,
Abu daya ta manta bata tambaya ba idan miji ya
dawo sai yasha ruwa sannan zaiyi wanka yaci
abin ci ko kuma sai yayi wanka sannan yaci
abinci, ta rasa yanda zatayi kamar taje kitchen
ta ma maman Nargees waya ta tambayeta sai
tace bari kawai ta masa yanda ta iya, ruwa ta
kawo masa da drink ta zuba masa yace
hannunsa ya gaji saidai ta bashi a baki, dariya
tayi ni ban Iya baiwa ko yara abinciba bare
manya, yace ai nima yarone a gurin ki ko
bakyaso,? murmushi tayi aranta tace shima yaxo
da nasa kwandon iskanci, tace inaso mana,!
Yace to ki baiwa babyn ki ruwa ta kuwa taso ta
tsuguna gabansa ta bashi ya kwankwade yace a
qaro ta qara mai ya kwankwade yace a qaro
tace aah ya Isa,yayi murmushi idan dai ke zaki
bani xan tasha har sai na shanye duka,murmushi
kawai tayi batace komaiba, tace muje kayi
wanka, yace iyeeeee duk ni kadai gaskiya dole
duk sati na riqa yin tafiya tunda idan na dawo
gata ake min, ta waigo ta Dan qaramai harara
ta murguda baki, saida ya tuna da ita a yanda
take da tamai gata gwanar murguda baki,tuni
yayi tsitt kamar ruwa ya cishi, suka shiga bayin
zata fito yace kixo muyi wankan tare mana tace
ni nayi daxu kai kayi yace to kixo ki wankemin
bayana hannuna baya kaiwa, kallon sa kawai
tayi ta wuce abinta duk shekarunda kayi kana
wanka wa yake wanke maka bayanka!
Shikam murna da dadi ya ma rasa abinda zaiyi
dan murna, iffaat ta rasa mi zatayi girki zata
masa ko kwalliya zata tsaya tayi, sai kawai ta
Yanke shawarar girki, ta shiga ta duba duk wani
abinci idan tace tayi shi zata bata lokaci sai
kawai tayi sauri ta hadamai danbunb cos cos
da busashen kifi yaji ganye, duk Wanda
Yaji qamshin girkin to zaisan cewa abincin ma
zaiyi dadi dambun cos cos dan taga yafi sauri
dama farhaan idan ya shiga wanka sai mutum
ya manta da cewa ya shiga, taxo gaban madubi
ta Dan goga powder ta gyara fuskar batayi
kwalliya ba kada ya rainata da xuwa yaga ta
fara shafe shafe, taje ta Dora mai abincin akan
table ta dauko mai wasu kaya da taga idan yana
gida yake sakawa.....by abba gana
Muje zuwa muji shin kulawar iffaat zata sa
farhaan ya chanxa ko kuwa halinsa dai!!
Idan bai chanxaba wane mataki anti iffaat zata
daika,?
Ya soyayyah zata guda tsakaninsu!? KU BIYO
DAN MUTAN MUHD ABBA GANA KUSHA LABARI..muhd-Abba~Gana

www.abbagana.pun.bz
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive