shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Sunday, 19 July 2015

WACE CE****ITA? 45

computerimages1.jpg

WACE CE ITA..?? 45
Na ABBA-GANA****-*******
Ya riqeta ya dagota yana jijjigata yana kiran
sunan ta, amma iffatu ko motsi haka ya dauketa
chak dama ba wani aukine da itaba, yakaita
dakinsa yaci gaba da jijjigata yana fadin sunan
ta, farahnax yaji tana kiran iffaat iffaat kina
ina??
Ya xuba mata ruwa shiru,Yayi sauri ya tura qofa
yayiwa mama waya bata daukaba tana chan
suna gaisawa da suruki, ya dakko ruwa a fridge
ya qara zuba mata yarinya still ko motsi yaga
kamin yaje ya kira mama zata iya mutuwa, tuni
ya fara hawaye yana kiran sunanta yana jijjigata,
Muryar mama yaji, Aminu naga ka kirani lafiya?
Nidai kuje Ku gaisa fa yaron chan mai Neman
qanwarku Suhaila, mama kizo iffaat ba lafiya,
Subhanallahi.!! Miya sameta ta shigo da takalmi
a qafa taga yarta kwance kamar gawa ta fara
jijjigata, taqara watsa mata duka ruwann dake
cikin robar swan din, iffaat tayi wani gwauro
numfashi ta bude Ido kadan ta kalli yayanta ta
kalli mamanta ta fashe da kuka, mama ta
rungumeta tana rarrashinta, wai ya akayi haka
aminu miya sameta?? Wallahi mama kawai naga
ta tsaya jikin window tana kallon su farhaaah da
sukazo shine na tambayeta miya
faru,..................
Yayi bayanin komai umma ta kalleta taga ta rufe
ido lallai xatonta ya zama gaskiya, tayi jeeem
amma ba halin magana wannan tashin hankali
har ina.!?
Suna zaune jugun jugun dasu saiga Suhaila ta
shigo, iffaat wai ina kika shiga tun dazu sunata
nemanki Yy farhaan kuwa ya kawo miki....... Ai
bata qarasa zancen ma taga su mama an xuba
uban tagumi ta kallesu mama miya sami sister
na?? Hankalinta ya tashi, mama batace komai.
iffaat kuwa sai ma qara runtse ido tayi wasu
hawayen suka ci gaba da sauko mata, tsanar ta
takeji a ranta Yaya Ameen zai fara mata bayani
mama ta katseshi. Kije ki sallami baqinki ki dawo
mama wallahi ba zan iya komaiba sister na
acikin wannan halin mama miya faru da ita,?
bakomai bane kune kullum cikin saka takalmi
masu tsini garin rawar kai ta fadi kanta yadan
daki jikin qofa shine kawaifa,
Ta dafe qirji Allah sarki sister sannu kinji bara na
kirawosu anan suxo su dubaki ta miqe tana
sauri
Iffat da qarfin hali tace kada ki kirasu banason
ganinsu bana so, mama tayi sauri ta toshe
matabaki, Batasan lokacinda ta fada hakan ba
lallai iffaat soyayya tana wujijjigata, suhaila ta
waigo mi tace mama??
Cewa tayi kada ki kirasu,
Nima ina ganin ki barsu kada hankalinsu ya
tashi,...
Share:

9 comments:

  1. Aishat alkasim19 July 2015 at 01:46

    9ce job Abba

    ReplyDelete
  2. wai matar kace take hana ka karasar mana?

    ReplyDelete
  3. Muhd Abba Gana19 July 2015 at 01:47

    waya sani

    ReplyDelete
  4. weldon, its very interestin

    ReplyDelete
  5. Awww...keep up with d good work Gana

    ReplyDelete
  6. gak ngerti sob heheee

    ReplyDelete
  7. mutum da tuzuru a tuzurai wa zai basa mata har ta hana shi aiki

    ReplyDelete
  8. abba a kara sar mana da lbr

    ReplyDelete

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive