shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Monday, 20 July 2015

WACE CE*******ITA? 62

computerimages1.jpg

WACE CE ITA..?? 62
Na ABBA-GANA
Mama tace Waike iffaatu bakida kunya ko, miye
na jifanshi da kwallon mangoro? umma tace
rabudamin da ya, wallahi shiya tsokaneta ina
kallonsa ya taketa, Dan ya taketa sai ta jefe shi,
karki sa mata baki Dan Allah ke iffaat tashi ki
shiga ciki.
Bayan ta wuce umma tace kin ganiko,? Haka
suke kamar tom & Jerry, hajiya kulu tace ai aure
daban yake alkhairin sa zamu nema kawai,...
*
Hajiya kulu na komawa gida ta sami mijinta
mahaifin Suhaila tamai xancen ai tuni ya amince
abbah ma da umma ta masa magana ya amince
100% mama ma haka tayi shawara da su Yaya
Ameen akan wannan auren kowa ya aminta
yanxu ya rage aji ta bakin gogayen...
Abba da umma suka kira farhaan aka fara masa
maganar Dan tsananin rudu da tsoro saida ya
manta yana gaban iyayensa, atafau farhaan yace
aah miye dalilinsa yace kawai matsayin farahnax
ya dauketa, shi bazai iya auren taba tun ana
lallashi har Abba ya yanke dole ya aureta ko
bayaso, kana tunanin zamu aura maka macen da
zakayi kuka da ita? Duk cikin mu ka fimu sanin
WACE CE ITA! cox ka zauna da ita tun tana Yar
mitsiyayarta,
Farhaan dai kawai yajisune amma Sam bai amin
taba,
Itama madam iffaat an mata maganar farko
dariya ta saka musu irin ga zancen nan Mara
kan gado.
Da taga dai da gaske akeyi kawai saita saka
musu kuka! Aka buga Sama da qasa tace bazata
auri mijin yayartaba...
Abba Suhaila ne yace sun Riga sun yanke
magana ba chanji ba mijin yayartaba ko waye
shi zata aura..
Nikam abba gana abin mamaki ya bani yanda iffaat
tayi jinyar son farhaan tun batada wayo amma
yanxu ga dama ta samu tace batasosa! Uhum
kuma ga dukan alamu da gaske takeyi, ta daga
ba nasara taci gaba da kuka ta wuce dakinta,
Yaya Ameen ne yabi Yar qanwarsa yana lallashi,
Haba iffaat miye aibin farhaan? Kina gani wallahi
guy ne gashinatsatse ga kamala, wallahi yanzu
dagyar ki sami namijin na kirki kamarsa baya
shaye shaye baya Neman mata. ta dago kai da
sauri ta kalleshi amma sai ta kasa fadar cewa
yana Neman mata, kowa ya shedeshi ke kanki
shedace akan haka! Sabida kinyi rayuwa dashi,
iffaat dai batace komai ba har Yy Ameen ya qare
rarrashinta ya tashi ya fito!
Ta miqe wallahi da na auri farhaan gara na shiga
duniya....
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive