shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday 22 July 2015

WACE CE*******ITA? 65

computerimages1.jpg

WACE CE ITA..?? 65
by
muhd Abba Gana
hankalinsa ne ya tashi! Ya rude yama rasa
mizaice mata, itama haka wato wani tashin
hankalin sai mutum yama rasa mi zaiyi, ta
kalleshi tayi murmushin qarfin hali tace sannu Yy
farhaan.!! Kamin ya bata amsa hawaye ne suka
zubo mata batasan dalilin zuwansuba, gaskiya
hawayennan sun kwafsa mata taso tayi chin
mutunci cikin ruwan sanyi amma ina kuka ya
kwafsa mata, bazai yiwuba chin mutunci ana
kuka baiyiba, da sauri ta bar gurin tana juya
kenan sai ga yy amin yaxo nemanta, lafiya kike
kuka? Tace
Ta hadu da wata qawartace shine take bati
labarin mutuwar mijinta .........
Eyyah Allah yajiqanshi ina take? Tace sun wuce,
farhaan yana jinsu kuma yaji abinda tace, yayi
tunanin zata tona masa asiri amma ina bata
fadaba,
Suka kama hanya idon iffaat Sam bata gani
gabanta hawayene suke rally a fuskarta.! ta kasa
jurewa sai wani Abu takeji yana taso mata,ta
rasa gane kanta, Yy amin yana gefenta yanata
bata labari amma taqi bari su hada fuska kuma
taqi cemar komai, har suka isa suka zauna!!
Waike har yanxu kukan kikeyi?
Ta dago kai ta kalleshi, wallahi Yaya ta bani
tausayine tana matuqar son mijinta amma
mutuwa ta rabasu, sai na tuna da yy Suhaila...
yace Eyyah sai haquri Allah yajiqanta ya Dan
qara lallashinta har tayi shiru amma zuciyanta
cike da tunani.! Har suka dawo gida tunani
takeyi.
Shiko farhaan yana ganin sun bulle ya kori
ramcy tana tambayar lafiya ya daka mata tsawa
akan ta bace mai da gani, ta tattara yan kayanta
ta wuce, ya fada kogin tunani,!
Baisan miyasa wannan yarinya takeda bala'en
tasiri rayuwarsaba, duk abinda yake a boye yake
yinsa, amma kuma bawai yana damuwane da
kada a Ganshi ba amma yana jin haushi idan
iffaat ta Ganshi..! Gashi tun tana qarama
tasanshi da wannan hali,amma har yanxu
baidainaba, yasan yana fama da sonta kuma tun
tana qarama yakejin haka yaqi qasqanta hakan
ne, ya yakamata fa ya daina. Kai wannan
mitsitsiyar yarinyar tama isa ta hanashi abinda
yakeso!? Amma miyasa take yawan kamashi?
Yaja tsaki ya juya ya miqe tsaye yana zagaye
dakin. Chan ya daki iska yace auren ta kawai
zan aminta dashi shine zaiyi maganinta, shima
ya huta da azabar rashinta.
haka dai ya qare yan tunane tunanensa cike da
damuwa.
Iffaat kuwa ana isa gida ta fada daki ta kulle ta
fara sana'ar tata yanda take kishin farhaan
tasan wata rana kisan kai zatayi, gara kawai ta
nemawa kanta zama lafiya ta aureshi, ba wata
hanya da takeda da ta wuce ta amince masa
kamin baqin cikin sa ya kasheta ko banxa zata
rage azabar rashin ganinsa da take fama da ita,
haka har bacci ya dauketa, Yy amin ne ya tayar
da ita daga bacci, ya kawo mata pizza tayi
murmushi Yy amin ne kawai yake rarrashinta
idan tana fushi mama kam ko kallo bata
ishetaba itama haka....muhd Abba Gana
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive