shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday 22 July 2015

WACE CE*******ITA? 72

computerimages1.jpg

WACE CE ITA..?? 72
Na ABBA~GANA
Tana ganin yabar gurin dama driver yana gurin
tamai waya tace yayi sauri ya dawo da mota
gida yayi gudu sosai farhaan kam traffic ya tsare
shi a hanya ga uban go slow ya biyo ta PZ shi
kuwa driver ta by pass yabi kamin farhaan ya
kawo tudun wada tuni an dawo da motar gida
yana shigowa gida yaga motar, yana huci Kamar
kasa tana zaune a Palo ta saka fura gaba
tanasha yana xuwa yasa qafa yayi ball da furar
gaba daya ya finciko gashin kanta ya wurgata
saman kujera, yazo Dai dai da ita zai kasheta da
mari ta wani riqe hannunsa da qarfi, tayi tsaye
saman kujerar wallahi idan ka mareni ba mijina
bane ko waye kai sai na rama...
A fusace yace ke Dan ubanki ubanwa kike yiwa
kwalliya kina kina fita?
Ta watsa mai harara tace ubanda ya
chanchanchi na yiwa kwalliya shi nake yiwa.! Ya
daki iska ya juya yana huci iffaat ni kike yiwa
rashin kunya?? mi kike zuwayi a Zaria hotel? Mi
kikiye achan?? tsaki ta masa ta diro daga
kujerar ta kama hanyar dakinta ya biyo ta
kinsan Allah wallahi idan bakiyi magana zan iya
kashe ki iffaat wallahi xan sallantar da
ruwuyarki..!!
tashin hankali lallai farhaan yafi iffaat kishi
hadda zancen kisa ta bala'en jin tsoro ta juyo ta
kalleshi taga yanda yayi wani iri dashi, tayi sauri
tabi gefensa ta fita bata tsaya ko inaba sai
Gidan su farhaan tana zuwa ta fada jikin umma
tana kuka... Akayita tambaya amma ba amsa
umma ta kira farhaan tace maxa yaxo tana
Neman sa ya kuwa zo, umma ta fara tambayar
sa mi ya mata haka duk ta firgice shiru yayi ya
kasa magana umma ta dakamai tsawa ya mata
bayanin komai tsaki tayi, rudadden banxa wai kai
mi yake damunka ne? Ko kunya bakajiba Dan
Allah kace ka ga mota amma baka gantaba
kuma ka dawo ka tarar da ita gida, haba wane
irin shirme ne wannan umma wallahi har
kwalliya fa takeyi.! Umma tace to mace a Gidan
mijinta batayi kwalliya idan batayi kwalliya ba mi
kake son tayi kaji shiriritar banxa, kai waya gaya
maka haka ake kishi da hauka, ka bari sai ka
tabbatar sannan ka yanke hukuncin waima kai
uban me kakeyi a Zaria hotel? Da har kaje kayita
ganinta? Ya Sosa kai iffaat data narke jikin
umma ta dago ido ta saci kallonsa ya duqar
dakai, yace umma baqi nake saukewa a gurin.
Tayi tsaki wallahi ka shiga taitayinka. kada ka
qara daga mata hankali da haukarka kaji na
gaya maka sannan duk abinda kakeyi ka bari sai
ka tabbatar sannan ka yanke hukunci farhaan
kam ya rasa bakin magana umma ba fahimtar sa
zatayiba tonon asiri ne ma zai yiwa kansa idan
yace zaiyi ma umma bayani har ta gamsu,!!
akace ta tashi ta bishi ta sa kuka ita bazatajeba
dole umma tace ya tafi gobe ya dawo ya tafi da
ita,
Na gaya muku iffaat fa taji tsoro matuqa taji zai
kaita lakhira...
Dole ta chanxa wata hanya...
Muje zuwa muji hanyar da zata komawa.

by
muhd abba gana
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive