Ladabin shiga bandaki (1).
Ladubban Shiga Bandaki (Fitsari Ko Bayangida):
Akwai tsari na ladubba da musulunci yake dasu a
lokacin da mutum yake niyyar kewayawa.
Wannan zai nuna maka cewa addinin musulunci
ya karade komai:
(1) Anbaton Allah:
Ana bukatar kafin kashiga ka ambaci Allah domin
ba'a anbaton Allah a makewayi, kuma kanemi
Allah ya tsareka daga sharrin aljanu, domin irin
wadannan wurare matattarace tasu.
Sai ya karanta wannan addu'a yace:
ﺑِﺴْﻢِ ﺍَﻟﻠﻪِ، ﺍَﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺇِﻧِّﻲ ﺃَﻋُﻮﺫُ ﺑِﻚَ ﻣِﻦَ ﺍَﻟْﺨُﺒُﺚِ ﻭَﺍﻟْﺨَﺒَﺎﺋِﺚِ
Ma'ana
Da sunan Allah, Ya Allah lalle ni ina neman
tsarinka (Daka tsareni) daga aljanu maza da
kuma aljanu mata.
Idan kuma zaka fito sai kace:
ﻏُﻔْﺮَﺍﻧَﻚَ، ﺍَﻟْﺤَﻤْﺪُ ﻟﻠﻪِ ﺍَﻟَّﺬِﻱ ﺃَﺫْﻫَﺐَ ﻋَﻨِّﻲ ﺍَﻷَﺫَﻯ ﻭَﻋَﺎﻓَﺎﻧِﻲ
Ma'ana:
Ina neman) gafararka Allah, Dukkan godiya ta
tabbata gareka, wanda ya rabani da wannan
kazantar kuma ya bani lafiya.
Kusani ba'a shiga bayi da dukkan wani abu da
yake dauke da sunan Allah, kamar zobe, ko carbi.
Hakanan kuma ba'a katse bayangida da dukkan
wani abu da yake da sunan Allah.
(2) Fara Gabatar Da Kafar Hagu A Lokacin Shiga.
kafar dama kuma lokacin fitowa.
(3) Ayi A Tsugunne:
kada mutum yayi fitsari ko bayan gida a tsaye,
sai dai idan wurin kangone ko yana tsoron fitsarin
ya fallatso masa, sannan ba wanda zai ganshi.
Darasi mai zuwa zanci gaba daga yadda muka
tsaya.
Insha Allah.
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.