shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Monday 27 July 2015

QARIN*********JINI---10

qarin-jini.jpg

QARIN JINI 10

Ta daga yatsa ta nunashi shima ya daga yatsa
ya nunata lokaci daya duka numfashinsu ya
tsaya anan suka zube sumammu.! Farkawan da
zaiyi yace Wllhy aliy yau na hadu da DREAM
BABY na.!! Wllhy naganta.! Miyasa bakwa yarda
da abinda nake gayamuku ne? miyasa kukeson
ku qaryatani? alhalin naganta da idona!, Wllhy
naganta aliy, bawai namaka gardamabane A.A
kawai kabari har kaji sauqi sai anemomaka ita,
ni na warke.!!! Loakaci daya ya fada hadi da
cewa.. Wllhy azabar da nakeji na rashinta ya
fiyemin zafi da radadi da ciwo akan duk wani
ciwo na duniya ya danne qirjinsa yace aliy kaga
nan? Yana tattare da wani wani dafi da azaba
da radadi da guna wasu zafafan hawaye suka
qanqaromasa, abinda nakeji bazan iya fadarsaba
a bakiba, bawanda zai iya gane mi nake fada sai
mai irin nawa ciwon wllhy aliy ina matuqar shan
azaba wayyo dream baby na...!!! aliy ka
taimakeni pls...!! Ya sake fashewa da kuka
kamar qaramin yaro aliy kuwa sai aykin rarrashi
har yaqaji amma bazancen yin shiru agun A.A,
yay kuka har barci yay awon gaba dashi anan
yay mafarkinta kamar yanda yake mafarkinta
wata tara da suka wuce sai dai yau sabanin
kullum da yake ganinta nesa dashi tana
nemansa, yau yaganta kusa dashi hartana masa
murmushi, tabbas yaji dadin ganin ta yau
yaganta a fili yaganta a zahiri, yafarka yacewa
aliy yau mutumiyar tawa harda murmushi tamun,
shidai aliy yana biyewa A.A ne dan kawai
azauna lafiya, amma yafi kewtata zaton cewa
yayi gamo da aljanane wacce take wahaladdashi
haka. Waya isa ya fada A.A yadaina yimasa
magana...
Wai lafiyanki kuwa tunda kika farfado kika rige
wannan drawing din na yayanki kina kuka kina
wasu magan ganu wayanda sam bana gane mi
kike fada, ki gayamin mana ko nasamu
kwanciyar hankali, benaxeer nagayamiki ba
komai kawai missing din gidane yake damuna
dan Allah kimin bayanin miyake damunki qarshe
tashige blanket dinta tabar bena tana zare ido
kamar wata mayya..
Hmmmm,
Tashiga duniyar mafarki taqanshi yana mata
murmushi karo na farko kenan da ta fara ganin
murmushinsa har wushiryarsa ta bayyana, yau
shekara uku da wata tara tana fama da azabar
sonsa, yay mata illarda duk wani ciwon so
yakewa masoyinsa,yay mata illarda koda
taganshi azahiri bazata taba amincewa dashiba,
tana balaenn son Wannan dream guy dinta
hartanajin cewa ta matsa kusa dashi amma ta
kasa, haka dai mafarkinta na yau ya gudana
wanda yasha bamban da kowane irin mafarki
nata tatashi cikeda farin ciki da jin dadi, abin ya
daurewa bena kai sosai yarinyar da ta kwanta
tana kuka kuma tatashi tana farin ciki anya kuwa
khair batada komai a cikin kanta? anya aljanu
basu shafetaba?
Nafi kewtata zaton jinnine bena takira
oumulkhair tagayamata abinda take tunani
gameda ita, khair tay dariya sosai harda kwalla
aranta tace (dama kinsan cewa ga abinda yake
damuna da kinfi gane cewa lallai aljanu sun
shafeni gida har ruqiya sukay min) khair
tagayamata cewa missing din gidane yake
damunta kuma tay mafarkin gida yanzu data
kwanta shiyasa tatashi da walwala..
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive