.: WACE CE ITA..?? 39
Na ABBA-GANA
Umma ta nunfasa tace idan wannan ne
damuwarki karki damu xamu nemo miki mamarki
duk inda take, ta danyi shiru amma jifa jifa
takan zubarda hawaye, bayan kwana biyu, muna
zaune palo nidai kamar hoto ko nace gunki
kawai cika wuri nakeyi. Suhaila ce ta shigo ina
ganinta naji qirjina ya wani buga, da Leda a
hannu, tana murmushi ta gaida umma tace nazo
dubiyar mara lafiyane suka saka dariya ai ga
tanan taji sauqi, ta zauna tamin ya jiki, na amsa
mata inata kallonta har tadan tsargu, suhaila
tace iffaat wallahi kinyi kama da qanwar
babanmu sosai saidai tafiki haske amma hatta
gashinki irin natane ke ko murmushinku iri daya
tafiyarku ma iridayace ke hatta maganarku iri
dayane ke komai naku iri daya, duk aka saka
dariya har iffaat din ganin yanda Suhaila ta
jajirce da bayani, sai kun sami lokaci kixo muje
gidan mu ki ganta a gurinta nake zaune, iffat ta
amsa da insha Allah....
***
Iffaat dai bata gane karatu yanxu, gashi an mata
nisa sosai abubuwan da bata yisuba a lesson
take samu a namatasu, karatun ma haushi yake
bata yanxu, zaman gidan ya gundureta, idan har
aka zauna Idan ba hirar farhaan akeyiba bata
taba samun sukuni a rayuwarta, wutar sonsa
kullum Dada ruruwa take a zuciyarta amma har
yanzu bata gane cewa she is fall in love ba...
Yar baqa qawarta tayi tambayarta har ta gaji sai
tace ba komai, to batasan mi yake damunta ba
bare ta fada,
Zaman birni ya gagare iffaat, kusan kullum saita
xubar da hawaye wace irin rayuwace wannan?!
ta matsa musu akan ita sai ta koma gurin
iyayenta ta gaji da zama anan, aka buga sama
da qasa amma taqi amincewa har suka gayawa
abba,
Ranar yasa aka kirata ya tambayeta ko ana
mata wani abinne tace ba abinda ake mata,
iffaat bamu daukeki a matsayin Yar aikiba a
matsayin Yar cikinmu muka daukeki wannan
dalilin yasa har muka damuwa da damuwarki,
muka sakaki makaranta Dan kema ki sami gata
da yanci irin Wanda ko wacce yarinya take samu
a gidan mahaifinta, iffaat kamar jiran abba take
ta fara kuka kamar ranta zai fita, Abba nagode
da dawainiyar da kukayi dani Allah ya saka da
alkhairi, abba wallahi ni kaina bansan abinda
yake damunaba rayuwata bata min dadi ba
abinda yake burgeni a duniya komai haushi yake
bani, banason naci gaba da wannan hali na
damuwa kuma na sakaku akan shakkun kanku,
wallahi kun min komai a rayuwa kuma na gode,
wata qila Idan na koma qauyenmu tunda nasan
yayyena suna zuwa nemana wataqil Idan nagan
su in sami sassauci.
Amma Dan Allah Abba Ku mayar dani gida taci
gaba da kukanta......
Tofa muje zuwa muji anya zata iya rayuwar
qauye? Yama za'ayi ta gane cewa soyayyah ce
take damunta...??!
WACE CE ITA? 39
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.