WACE CE ITA? 36
.: WACE CE ITA..?? 36 Na ABBA GANA ************ Iffaah ta isa qauyensu cike da tunanin rabuwa da da iyayen farhaaan.. Goggo tayi mamakin yanda ihhatu ta chanza tayi kyau duk wani Abu da ake buqata a gurin mace ihhatunta tana dashi saidai tunda iffaat taje bata zuwa ko ina daga gida sai gida, ta natsu matuqar natsuwa, ga yawan shiru shiru da takeyi. Ranar goggo ke tambayarta bata sami miji a birniba, goggo ni har yanxu ba Wanda yakesona,! Ta dafe qirji kardai birnin ma kin musu halinsu kin kashe kasuwarki, zancen goggo ya bata dariya, goggo Allah ne bai kawoba, hakane kuma Dan yanxu naga kin tsama yan mata, wallahi sai mai mota zaki aura kikaini makka ko? Ta amsa da sosai kuwa ta fada tana miqewa tashige daki, zan iya CE muku tunda iffaah ta dawo qauye kullum sai tayi kuka, wani Abu takeji ya tsaya mata a zuci ya tokareta ya hanata sakat, bata iya aikin komai Idan wannan abin ya motsa mata.. abinka da yarinta Sam bata gane cewa soyayyah bace, bata gane kanta Sam. sau tari takanje bayan gari ta sami bishiya ta zauna taci kukanta har ta godewa Allah, sannan ta dawo gida ba abinda yafi damunta illa rashin gane takamammen abinda yake damunta. Wayartace tayi qara, ta dauka farahnax ce. Hello Ta amsa tanajin dadi Farahnax chikin dariya take maganar bayan sun qare qaisawa, kee iffaat Yaya ya dawo dazu sai tambayar ki yakeyi, qirjintane yayi bala'en bugawa sai ta tsinci kanta da zubar da hawaye, na rashin dalili ta yi shiru. Hello hello iffo kinajina? Tanata magana amma iffaah ta kasa bata amsa, qarshe ta tsinke wayar, iffaat ta shige dan dakinta ta zauna ta rasa mi yake damunta yan watannanin Miyasa duk lokacinda take tunanin yaya farhan take shiga wani hali?? Miyasa duk taji sunanshi sai taji faduwar gaba?? Miyasa taji tanason ta Ganinshi yanxu ?? Miyasa duk ta zauna labarin sa take sonyi?? Kai tambayoyinta sunyi yawa, batada amsar ko daya. Tayi wani tsaki Ba abinda yake daga mata hankali irin son ganin farhaan da takesonyi, Wanda ji take kamar tayi fiffike taje ta Ganshi, Amma ba halin yin haka, Su iffaat an fada tarkon soyayyah amma batada labari har yanxu ba tasan miye soba..
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.