shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday, 18 July 2015

WACE CE***ITA 43

WACE CE ITA..??43
Na ABBA-GANA
*******
Wata rana Suna hira da mama take bata labarin
tanada ya,
yarinyar yayanta ne lokacinda babanki ya
kwaceki to lokacin aka bani ita, to ina take
mama? Tana Qatar karatu takeyi wannan
shekarar zata kammala data qare sai a mata
aure,! iffaat tayi dariya da shewa Ashe dai
mama mun kusa shan biki, kinsan kuwa inason
biki a rayuwata, lokacinda muna qauye kullum
sai naje biki ko ba'a gayyaceniba kuma ni
bandamu da su bani abinciba kawai mukanje
muyi tsokana, idan za'a kai amarya da dare mu
sami allura muyita tsikarawa matane ko Ku
muyiwa yayansu da suka Goya suyita kuka sai
mu boye, mama Dan tsabar dariya saida ta kai
kwance, tashajin ana cewa iffaat ta gagari Kowa
a qauye amma ba tasan abin yakai hakaba, nidai
jabo araina nace to iffaat kan tayi hatsabibancin
da yafi wannanma!! Yanxu kinga mama biki
namu sai yanda mukayi ko, mama cikin dariya
tace eh, da yake har baiko ma an mata ai.
Habawa? Ashe munada biki duk suka saka
dariya...
iffaat tanatason ta tambayi mama hoton yar tata
amma Sam ta manta har ta kusa dawowa!
*
Ranar da Yar mama zata dawo gidan mu yasha
gyara anyi girke girke kala kala, guraren qarfe
2pm ta sauka Kaduna daga chan aka daukota
aka kawo ta Zaria da yake an barni gida,
isowarsu keda wuya,
wazan gani a matsayin yar uwata?? Suhaila
matar da akayiwa farhaaah baiko da ita, wani
rass taji ni kaina Abba sai da naji bugun zuciyarta
kuma na tabbatarda kuma Masu karatu kunjiyo
kobakujiba????
Suhaila tana ganina tahau dariya tana
tambayata farahnax, cox ita achan tasañi, tace
iffo surprise dina kukayi haka? So happy wallahi
ina farahnax din? Itakam iffaat tsaye tayi tana
mamaki abinda take gani, wato Suhaila itace
yarinyarda aka baiwa mamanta kuma itace
matar farhaaah!
Sai yanxu ta gane kamar da akace sunyi da
Suhaila, Ashe jini dayane, sai yanxu ta gane
dalilin da yasa takejin Suhaila cikin ranta amma
kuma miyasa take tsanar ta?? Suhaila sai
washe baki take tana tambayarta farahnax,
mama tace keewai waya gaya miki tasan
farahnax? Ke dadi miji dadi dangin miji!! Laaa
mama wallahi gidansu fa nake ganinta farko,
itace wacce nace miki akwai wata cousin din
farhaan mai ban dariya kuma kunyi kama kin
tuna mama? Eh na tuna to itace, nifarko ma na
dauka aiki take a gidan sai ranan umman
farhaan tace ba Yar aiki bace yartace,
anan dai na fayyace musu komai mama da
Suhaila suka gane cewa gidan su farhaan goggo
ta kawoni aiki, mama taji dadin yanda umma ta
kula dani har tana cewa suruka ta gari......
Nida Suhaila mun dinke mun zama kamar abokai
dukda ta girmeni nesa ba kusaba cox lokacin ina
16 ita kuma tana 24 ne, duk iyayen farhaan sun
ganeni sunata jin dadi, mama kuwa hadda zuwa
godiya yanda aka kula da yarta har umma tana
cewa a qara bata ita...
**
Bansan miyasa nake tsanar Suhaila ba nakan
kwatanta boyewa araina amma duk ranarda naji
sunyi waya da farhaaah to kuwa duk yanda
zanyi sai nasan yanda zanyi muyi fada da
Suhaila da yake ita ba mai kulawa da qananan
abubuwa bace so bata kulawa dani Sam. Banxa
takeyi dani kamar ba da ita nake yiba, nayita
gabata har na gaji na sauko.
Mama ta kula kamar na tsaneta amma ita kanta
bata gano dilin hakan ba,
Ranar mama ta kirani take tambaya ta miyake
faruwa tsakanina da Yar uwata nafara kame
kame, ba komai, mamadai tayi ta min wayo har
na fara magana wallahi mama nikaina bansan
dalilin da yasa mafiyawan lokuta nake jin na
tsanetaba haka kawai take bani haushi kuma
wallahi mama banajin dadin abubuwan da nake
mata ta fashe da kuka, mama ta rarrasheta, taso
ta gano sirrin amma aranta tace bari saita qara
gwadata.
Tofa MUJE ZUWA MUJI IRIN GWJIN DA MAMA
ZATAMA IFFAAT...
DA KUMA WANE IRIN MATAKI ZATA DAUKA
AKAN HAKA, ZATA IYA ADALCI KO KUWA SON
KAI ZATAYI TSAKSNIN YARTA DA YAR
RIQONTA??
Share:

1 comment:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive