shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Tuesday 21 July 2015

***KULA DA JIKIN UWAR GIDA*****(maza kawai)

img-20141222-wa0000.jpg

KULAWA DA JIKIN UWAR GIDA.


by muhd abba


DOMIN KE DA MIJINKI.
««fitowa na 5»»
ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ
ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﻭﺳﻠﻢ
Maigida munfa dawo kanka yauwa.
Meyasa ka buqaci aure ???
Kanada wata manufa ne ko kuwa kawai kaga
magabatanka da tsararrakinka ne sunyi kaima
kaga yadace ace kanada mace a qarqashinka
kamar yadda kowa yake da ita ???
To kafin kafara neman aure, kamata yayi kasami
natsuwa kanemi yarinyar kirki, ko a cikin
'yammata nagari ka nesanci guda 3 sune kamar
haka:
(1). Tagari ce amma bata sonka.
(2). Uwarta bata da tarbiyar muslunci ko kadan.
(3)Uwar itama tagari ce amma tana nuna maka
matsananciyar adawa.
Sannan idan katashi neman aure kasani cewa:
Ko motar da take qarfe wace zaka riqa hawa ta
kaika duk inda kakeso a lokacin da kake so dole
sai kasamo lafiyayyiya sannan ka koyi yadda ake
sarrafa ta, da yadda zaka lalla6a ta harta jima
maka sosai.
Dole kariqa kula da ita wajen kwalliyarta da
gyaran injinta lokaci zuwa lokaci, gwargwadon
yadda wanda yayita ya tsara, kana wanketa kana
bata irin man da take sha wanda zai gyara
injinta.
Kuma in katashi yin tafiya baka qure maleji ba
bare ta makaka cikin daji ko tasaka kayi hatsari
da sauransu.
To haka mace take, idan ka aura kaima dole
kamiqe da yin wasu hidimomi matuqar kanada
buqatar ganin lafiyarta da kwanciyar hankalinka,
da zama mai dorewa.
Mace zata riqa yimaka hidima, amma kaima
maigida na qwarai akwai naka.
Shin ka auro wace take sonka ?
Domin idan tana sonka komai kakeso zaka samu.
Sannan kaza6o mai tarbiyya mai sanin addini da
kama kai, mai kunya, bayan haka sai kafara
dorata akan hanyar da kai kake buqata, ta tafi a
kanta.
Amma ka fahimci abu guda Daya.
Mace har kullum tana hukunci da zuciyarta ne,
tana da tausayi da soyayya da daukan abu mai
hatsari a matsayin qaramin abu.
Duk lokacin da zuciyarta ta6aci zata iya yin
komai batare da tunanin abin da zaikai ya
komoba.
Saboda dogaron da tayi akan zuciyarta, shiyasa
komai ilimin mace idan ranta ya6aci ko kuma
akayi mata auren dole da ita da watanta duk
sammakal.
kenan idan ka auri wace bata sonka, don Allah
kayi mata uzuri.
Kayi qoqari qaunarka tashiga zuciyarta tukunna
sannan kanemi haqqoqinka daga baya kamar dai
sauran mata.
Maigida na qwarai munayi maka zaton aiki da
qwaqwalwa samada zuciyarka, kana da qarancin
nuna soyayya, da tausayi, ba kamar matarka ba,
to amma qwaqwalwarka takan nuna maka me
yadace kayi ???
Annabi yayi rayuwar aure shekara 38 yazauna da
Khadija shekara 25 ita kadai ce matarsa, dan
sauran 13 ne yazauna da mata 9 lokaci guda, har
Khadija takoma ga Allah soyayyarta tana bin
qawayenta.
Miji na qwarai kenan,wanda yasan darajar mace,
yake bata haqoqinta, idan mace tayi aiki da
zuciyarta to lallai shi kuma sai yayi aiki da
qwaqwalwarsa.
Amma ya dauki mace kamar abin hawa kullum
saidai yahau ya more ya sauka ba wani kulawa
da ita gaskiya akwai matsala.
Yanzu ya za'a yi kazama maigida na qwarai baka
kulawa da jikin matarka ???
Binciken dazamu fara kenan idan Allah ya yarda.
Amma kanemi taimakon Allah, sannan kasami
mace ta qwarai, kanemi mai sauqin kai wace zata
tafi daidai da buqatarka, sannan kanemi WACE
TAKE SON KA, kaza6o mai addini mai son
muslunci, ka auro 'yar namiji ba 'yar mace ba.
Sauran kuma kabarwa Allah ikonsa.
Bayannan ka shirya cewa zaka riqa ganin
abubuwan da bakaso, amma haka Allah yayita
dole sai kayi haquri, karka ta6a saukowa daidai
da matsayinta, sai gidanka ya lalace, kullum
kariqa cewa ita mace ce kai kuwa namijine to sai
a zauna lafiya.
Zamuci gaba daga yadda muka tsaya a darasi
mai zuwa.
Insha Allah.

www.abbagana.pun.bz
Share:

2 comments:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive