shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Tuesday, 19 April 2016

BANA KAUNARKA!!! 50 [KARSHE]

bana-kaunarkajpg.jpg

BANA KAUNAR KA

50

MUHD-ABBA~GANA Da Amrah

A hankali Shahid ke taku har ya iso Inda nake, hanky din hannun shi ya fara goge min hawaye dashi, sosai naji kunya amma sai na samu kaina da kasa hana shi. Sai daya ga babu sauran hawaye tukuna ya daina gogewa, yace "Wahida ina so kiyi haquri ki dauki kaddara, ki cire duk wata damuwa dake ranki, duk abnda kike gani ya faru tou dama can rubutacce ne. Zainab da kike gani wlh bazata taba yin kishi dake ba, ki dauke ta tamkar kanwarki ta jini, Wahida ina sonki, son da bazan taba iya yiwa wata mace ba".

Zainab tayi saurin zuwa inda nake tace "qwarai kuwa Wahida, tunda nake a rayuwa ta ban taba ganin soyayyar gaskiya irin wadda shahid yake miki ba, so da yawa yana yi mn maganarki, sai dai naita mashi adduah akan Allah ya karkato da hankalinki ki so shi, sai gashi yau ke da kanki kin furta kina son Shahid, nafi kowa jin dadin hakan. Dan Allah ki riqe ni tamkar yar uwarki ba kishiya ba". Tsam ta rungume ni tana mayar da numfashi, hawaye na na sauka a kafad'arta. Babu wanda baiji dadi ba musamman Mahida da harda sajdatul-shukr tayi, mom ma har da hawayen murna tayi tana shi mana albarka.

Bayan shekara hudu.

Wasu yara muka hango su uku kusan duk girman su daya, sai dai daya tafi biyun girma. Biyun siffar su daya baka ita banbance su, sanye suke da kaya pink iri daya. Tun daga nesa mukaji suna fadin "Momy! Momy where you dey?", "I dey here my bebes, ba dai kuna nufin har kun dawo ba?", wadda tafi girman ce tace "Momy Afrah ce ta fara kuka wai Ita sai an dawo gida, shine momy Mahida tasa driver ya dawo damu". Wadda aka kira da Afrah tace "Momy fa Farhat ce tace wai tunda gobe Monday muyi saurI mu dawo yunda bamuyi Home work na Friday ba", Farhat tace "Laa Momy fa babu ruwa na, dan Allah Aunty Meenat ba Afrah ce tace mu dawo ba?". Tun daga cikin gida mukaji muryar Zainab tana fad'in "kai yaran nan akwai ku da rigima, ku dai dole sai kowa yasan kun dawo". Da gudu Farhat ta rungume Zainab tace "My dear wlh babu ruwa na Afrah ce", nan suka hau rigima kowa na fadin babu ruwanta.

Zainab itace ta fara haihuwa bayan tarewar Wahida, ta haifu kyakkyawar yarinya aka saka mata Aminatu (Meenat). Bayan shekara daya kuma Wahida ta haifi twins duka mata aka saka masu Afrah da Farhat. Yanzu haka Wahida na dauke da juna biyu haihuwa ko yau ko gobe. Zaune suke cikin farin ciki da qaunar juna, idan ba an fadawa mutun ba bazaka taba gane kishiyoyi bane. THEY LIVES HAPPILY.

TAMMAT BI HAMDULILLAH. ANAN WANNAN LITTAFIN MAI SUNA "BANA KAUNAR KA" YAZO QARSHE. KURAKUREN DAKE CIKIN SHI MUNA ROQON ALLAH YA GAFARTA MANA.

MUNA FATAN AN FADAKARTU KUMA AN NISHADANTU A CIKIN WANNAN LABARIN.

SHAWARA GA 'YAN MATA:

mu daina cewa lallai mu sai mun gama karatun boko tukuna muyi aure. Aure baya hana karatu, haka kuma karatu baya hana aure. Sannan kuma mu daina tsananta tsanar namiji, saboda wannan muguwar tsanar otace take zama soyayya, wadda daha qarshe mu koma dana sani. Allah yasa mu amfana da abnda muka karanta.

KALAMAN GODIYA: Duk kan yabo da godiya sun tabbata ga Allah madaukakin sarki, tsira da aminci ka qara su ga shugaban mu annabi Muhammad (SAW) tare da alayensa. Muna godiya ga duk kan masoyan mu maza da mata aduk Inda kuke, Allah ya qara dankon zumunci Ameen.

SADAUKARWA: na sadaukar da wannan littafi ga kannena da yan uwana da iyayena da masoyana Allah ya bar zumunci.

JINJINA GA: Aunty sadiya, sister amina, sis amrah ina yabamiki Allah ya karabasira tare da bilkisu muhd.

GAISUWA GA: Raheem jega,Auwal yusuf bauchi, sis billy gero, sadiya bala muhd, teemah luf,kairat,Baby zahra da sauransu.

YA ZA'AYI IN MANTA DAKU?

iyayena abin alfaharina a kullum addu'ata Allah yaja kwananku ga baku tsawon rai mai amfani.Allah yasa aljanna ce makomarku ameen.

DUBUN GAISUWA ZUWA GA MEMBERS NA

ONLINE HAUSA WRITERS✍

DUNIYAN MARUBUTA

HAUSA NOVELS

HAUSA NOVELLAS

PRESDENTIAL VILLA

HOME OF HAUSA NOVEL

BAN MANTA DA KUBA MEMBERS NA GROUP NA

HOUSE OF NOVELS (1-4)

DA WAYANDA BAN SAMU LISSAFOWA BA.

SAI MUN SAKE HADUWA A WANI SABON LITTAFIN NA GABA MAI SUNA.."WAYE SANADI?

ABBA GANA 09039016969

DA

AMRAH 07037603276

KE MAKU FATAN ALKHAIRI.

Share:

28 comments:

 1. muna godiya

  ReplyDelete
 2. Allah kara basira

  ReplyDelete
 3. wow tnx muna jiran sabo

  ReplyDelete
 4. abba karashin shamsiyya pls

  ReplyDelete
 5. abba karashin insiya pls

  ReplyDelete
 6. abba karashin dan alhaji insiya da sireenah muna jira dan Allah

  ReplyDelete
 7. muna godiya Allah kara basira

  ReplyDelete
 8. muna jiran sabo

  ReplyDelete
 9. Allah kara basira

  ReplyDelete
 10. muna godiya da yawa

  ReplyDelete
 11. tnxs mallam abba

  ReplyDelete
 12. tnxs dan uwa

  ReplyDelete
 13. aseeya abduhameed22 April 2016 at 13:53

  mun gode muna jiran karashi

  ReplyDelete
 14. aysheeya kareem22 April 2016 at 14:02

  oh! more el 2 ur elbow

  ReplyDelete
 15. Allah kara basira

  ReplyDelete
 16. Allah ya kara basira ameen

  ReplyDelete
 17. mallam abba muna godiya

  ReplyDelete
 18. tnxs dan uwa

  ReplyDelete
 19. amrat abdullahi26 April 2016 at 12:11

  muna godiya yashe za a fara mana sabo

  ReplyDelete
 20. Asma'ul husner26 May 2016 at 16:07

  dakyau.gdy make sosai

  ReplyDelete
 21. Nafsat alkaleri14 June 2016 at 22:51

  Mungode allah yakara basira

  ReplyDelete
 22. Agsky yayi dadi mungode

  ReplyDelete

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).