shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Thursday, 14 April 2016

BANA KAUNARKA!!! 47

bana-kaunarkajpg.jpg

BANA KAUNAR KA

47

MUHD-ABBA~GANA Da Amrah

A 'bangaren su Bomboy kuwa da fita na mom tace "Zainab ai sai kuzo ku karya, nasan dai bakuci komai ba", Bomboy yace "wlh mom mun gode Alhamdulillah saida muka karya tukuna muka fito", Mom tace "ai sai kabari "yata ta bani ansa, nasan dai bazata qi cin girkina ba", Murmushi Zee baby tayi tace "mom wlh karki damu a qoshe muke, ai anan zamu yini dole zamuci girkin ki insha Allahu", Mom tace "tou shikenan, kuma gashi Wahida da zata taya ki firar ma ta tafi makaranta ko bankwana babu, amma da yake yau friday lecture daya kawai takeyi (10-12)", Zee baby a ranta tace "aikuwa bazamu shirya da wannan yarinyar ba, dan da alama 'yar rainin hankali ce, jifa yanda take kallo na tun daga sama har qasa, ba wai dan ta fini da komai ba kuma". A zahiri kuma tace "tou mom allah ya dawo da ita lafiya".

Haka nayi lecture cikin rashin fahimtar abnda lecturer'n ke fad'I, har ya gama ban san ya gama ba saida Hafiza ta ta'boni tukuna na zabura nace "ya akayi ne?", "Au baki ma san menene ba kenan? Tun dazu fa aka gama lecture har kowa ya watse, na sa miki ido ne inga iyakar ki dama", Jaka ta kawai naja tana tambayata "me yake faruwa dake ne Wahida?" Ban bi ta kanta ba na qara gaba, direct inda aka yanada domin ajiye motoci (parking space) na dosa kamar mahaukaciya nake jan motar da qarfi. A hankali maganar Shahid ke dawo mn, ina tuna furucinda dad yayi, da qarfi na doki sitiyarin motar nace "ohh shetttt! Na cuci kaina ni Wahida, me yasa na za6i kin bin umurnin iyaye na? Me yasana za6o karatun boko akan sunnar manzon Allah (SAW)? Me yasa nayi ZURFIN CIKI? Daga d'ayan 6aren zuciyata kuma tace mn ai Wahida mace dole sai tana da class, mace babu aji ai bata cika mace ba, ni d'in da maza ke bi suna so ina wulaqanta su taya zan iya nunawa wani soyayya ta?. Zafafan hawaye keta ambaliya a fuskata nace "qarya kike, baki isa ki zuga niba domin kuwa girman kai rawanin tsiya ne, "A'UDHUBILLAHI MINASH SHAIDANIR RAJIM, ALLAHUMMA AJIRNI FII MUSIIBATI, WAKHLIFNII KHAIRAN MINHA" Na fada tare da parka motata a bakin titi, saida na samu natsuwa sannan naja mota ta, har na kama hanyar gida kuma na tuna da Bomboy yace sai dare zasu tafi, corner nayi na kama hanyar gidan Mahida. Na sameta kwance bata da lafiya duk tabi ta qare cikun kwana biyu, a hankalu nake taku har na isa inda take, a kidime nace "sister me yake damunki?", Murya qasa qasa tace "wlh ciwo ne jiya jiyan nan na kamu dashi, sai fama da zazza6i nake, ga amai baya ko qaqqautaw.....", bata gama fadi ba saiga wani aman, dafe bakinta tayi tare da saurin zuwa toilet, acan na sameta tana ta nishi bayan aman data gama.

Bayan samun natsuwa sosai nace "amma fa sis psychologically kina dauke da juna biyu, duk da ba likita nake karanta ba kawai sai na karanto hakan, but ya kamata ki ziyarci dr. Yayi miki awon jini". Maheeda tace "sis ai ba sai naje asibiti ba, ko kin manta da miji na likita ne?" Ta qasara maganar fuskarta dauke da annuri. "Sis nidai sai inga kamar kina cikun damuwa, ya kamata ki fada mn damuwarki idan ina da mafita wlh zanyi bakin qoqari na dan ganin na fitar dake daga cikinta, d'azu mom ta kirani tace duk yanda zanyi ince kizo gidana in bincike ki saboda bata son ganinki cikin damuwa, cikin ikon Allag kuma sai gaki kinzo", A hankali na fara share hawayen daya fara bin kumatuna, tabbas nasan idan ban fadawa mahida damuwa ta ba tou babu wanda zan iya tunkara da Ita ciki kuwa harda mom.

ABBA GANA

AND

PRINCESS AMRAH

Share:

6 comments:

 1. Hm dakyau dan uwa amma rubutun yanayin kadan yakamata yakai ga gamsar da mai kara2

  ReplyDelete
 2. Hm dakyau dan uwa amma rubutun yanayin kadan yakamata yakai ga gamsar da mai kara2

  ReplyDelete
 3. Prince kana kokari ALLAH yakara basira.

  ReplyDelete
 4. Muna godiya amma don Allah adingayi kullum

  ReplyDelete
 5. muhammad abba gana16 April 2016 at 12:42

  insha Allah za,akokar ta@Zee Abdul,

  ReplyDelete

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).