SIRRIN ZAMA DA MIJI
{KASHINA 7}
(KIYAYE DUKIYARSA)
BY
MUHD*ABBA*GANA 09039016969
yazo a cikin siffofin salihar mace cewa manzon Allah (SAW) yake cewa: ita ce matar da take kiyaye kanta kuma ta kiyaye dukiyar mijinta a lokacin da yake a gida da kuma lokacin da baya gida. don haka dukkan mace ta gari itace wacce take kiyayewa tare da taimakawa mijinta a cikin sha'anin tattalin arzikinsa. bayan haka yana da kyau mace ta kare kanta daga barin yawaita tambayar mijinta domin aikata haka yana janyo mata zubewar kwarjininta a idon mijinta don haka yana da kyau mace ta kiyaye wadannan abubuwa domin samun kyakkyawar zamantakewa mai aminci a tsakaninta da mijinta. Allah ya baku ikon gyarawa, naku har kullum jikan marubuta muhd abba gana
tnxs
ReplyDeleteAllah kara basira.
ReplyDelete