shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Friday, 22 April 2016

SAUYIN RAYUWA 31__35

sauyin-rayuwa.jpg

[9:11PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 31 na BABY ZAHRA Cikin murna da zumudi ta tashi ta zauna sosae Dr Adam ne da falmata suka shigo da sauri nasreen ta fincike karin ruwan ta tashi da gudu taje ta rungume falmata tace mata nagode falmata da shawarar da kika ban gashi har mai Martaba ya amince da bukata na, nagode sosae sosae, ta juya takalli Dr adam tace mai nagode kaima Dr naji dadin abinda kamin, tajuya ta kalli falmata tace kibude site drawer zakiga kudi kibawa Dr, da sauri falmata tace to, ta dakko mai kudi mai tarin yawa, wanda ita kanta nasreen in batasan nawa bane a gun, aka mika mai, godiya yayi sosae Kamar zai yi mata sujjada don murna, ta sallame shi yayi tafiyar sa....haka nan dai fulani tayi hakuri da zancen auren nasreen da muktar ta dangana abin a matsayin kaddara don haka aka ci gaba da shirye shirye Tsakanin gidajen uku ko ina shirye shirye akeyi ba kakkautawa, kasancewar dukka 'ya'yan fari za a aurar..... Akwana atashi har biki saura sati biyu don haka shirye shirye sai ci gaba takeyi........ Haka kawai yau yatashi yaji yana dan kewar kaisa ko meyasa haka oho, dan zaman da yayi a jajere yasa yadan saba da ita amma ba sosae ba don ma dai kullum fada ne ke hada su, to amma bari dai yagani ko zai iya shiga jalingo yau, wayar sa ya dauka yakira ahmad abokinsa ne dake aiki a airport bayan sun gaisa ne yake tambayar sa ko zan samu ticket in jirgin da zanje jalingo da safen nan, acen bangaren Ahmad ne yace mai kar ka damu abokina zaka sami na karfe goma 10:00am, farincike ne yakama muktar yace to shikenan bari in shirya ina zuwa, sannan yakashe wayar yashige wanka. BABY ZAHRA [9:11PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 32 na BABY ZAHRA Tsaff ya shirya bai ko gayawa kowa zaiyi tafiya ba sai da yagama shirin sa ya dakko kayan sa sannan ya sakko kasa su abba yagani dukka su suna zaune ya gaggaishe su bayan sungaisa ne, ya dubi abban shi yace abba yau ina son in je jajere fa, abba yace lafiya zakaje tafiya ba shiri, murmushi muktar yayi yace ina sone inje saboda inji ko kaisa tana da matsala na kudi, kuma bata da waya balle muna communication da ita, shine yau nashirya nace bari dai inje inji, nan da nan abba ya wangale baki yana dariya dadi ya kama shi, nan da nan yakama sakawa muktar albarka yace ubangiji Allah ya kaika lafiya ya kuma dawo da kai lafiya idan kaje ka gaida min da dan uwana sosae sosae, to abba zasuji insha Allahu, nan kuwa idan ran momy yayi dubu to ya bace, me yaron nan yake nufi da zaije duba kaisa, karfa yace min yakamu da son yarinyar nan ne, ko kuma dai maganar abba gsky ne dayace shi yazo yace masa yana son kaisa shiyasa yabashi ita, lalle kuwa zanci masa mutunci, bari yaje ya dawo, abba ne ya katse mata tunaninta da cewa yanzu sai yaushe kenan zaka dawo, yace eto abba inaga dai bazan yi sati ba, saboda nima inzo inkarasa nawa shirye-shiryen anan, toto shikenan ae cewar abba to Allah ya kiyaye hanya ko agaggaishe su, yace amin, yace to momy, aunty nikam natafi!!! ,ba aunty rukkaya ba harta su momy sun sha mamakin yanda akayi yau kuma muktar yayiwa aunty rukayya magana kuma cikin lafazi mai dadi, to Allah ya kiyaye maka hanya muktar agaida mun da su innan kaisa, cewar aunty rukaiya, insha Allahu ya fada cikin nishadi, yakee momy tayi tadan saki fuska tace agaida min da surkata sosae sosae, gashi banda abu yanzu ai dana baka ka kaimata, kai innema da tafiya ba shiri, ko dai ita tayi kiran ka ne, kowa afalon sai da yayi dariya, sannan tace to Allah ya kiyaye hanya ko agaggaishe su sosae, to insha Allahu yace mata sannan suka rakashi har bakin motar ya shiga driver yaja suka tafi BABY ZAHRA [9:11PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 33 na BABY ZAHRA Misalin karfe 11:00am yana zaune a falon karbar baki na gidan su nasreen, soyayyar su suke ci sosae, sai zuba masa shagwaba take, tana narke a jikin sa, abinda yasa muktar yake kara son nasreen kenan saboda yana son mace mai shagwaba gashi nasreen inshi ta iya sosae, shiyasa yake Allah Allah sati biyun nan yayi saboda yasamu ya mallaketa har abada..... agaban sane yayi mummunar faduwa sakamakon tunowa da kaisa da yayi, baisan me yasa ba kwana biyun nan idan har yatuno ta sai yaji bagan sa ya fadi, cikin sauri ya janye jikinsa daga na nasreen, a hankali tace masa lafiya kuwa yace a'a lafiya kalau, kawai na tunone da aikan da abba ya ban, ya kamata in wuce jajere ne yanzu, cikin shagwaba tace haba mana sweet kabari sai da yamma, cikin kasaita yace wlhy nima naso hakan amma bazai yuyu ba, yanzu abinda za ayi kisa afitomin da motar ki da ita zan wuce, too kawai tace mai tayi waya tasa aka fito da motar, dubu dari biyu 200,000 yabata yace ga wannan kifara rage abubuwa da shi ina ce kince event hudu zakiyi tace ehh yace to ga wannan, tasa hannu ta karba tace sweet nawa ne a nan yace 200k ne tace gsky sweet ba zai wani isa ba event hudu fa, ya saka hannu a aljihunsa ya karo mata 100k yace to ga kari, ta karba tace to za dai afara managed insa amma shi inma ba isa zaiyi ba, ajiyar zuciya yayi abinda yake hada shi da nasreen kenan tun ba yauba ita a rayuwar ta bata iya godiya ba sai ma raina ko, sannan yace mata to shikenan ni kuma yanzu banda wani kudi a hannu na, sai naje bank don haka yanzu kam sai na tashi dawowa, too kawai ta ce mai ta tashi taraka shi har bakin motar sannan yatafi BABY ZAHRA [9:11PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 34 na BABY ZAHRA Karfe 2:00pm dai dai acikin garin jajere yayi mai, kasancewar bai sanar da kowa da zancen zuwan san ba, kai tsaye ya shige cikin gidan sallama ya kwada da gudu su nana sukazo suka rungume shi suna ga yaya muktar ga yaya muktar inna ce tafito tace aaaa lale marhaban da ba kon abuja, bismillah shigo ciki ko, da sallama ya shiga dakin ya nai mi guri a kasa ya zauna ya mika mata gaisuwar sa baisan meyasa ba yanzu kwata kwata kunyar inna yakeji, bai saniba ko don ta kusan ta dawo surukar sace oho, abinci inna ta kawo mai ta ajiye masa sannan ta juya tafice waje ta zauna saboda inna akwai kunyar nan tamu ta fulani balle kuma yanzu da take mai kallon surukin ta, sai sa ido yakeyi don yaga ta ina kaisa zata bullo amma yaji shiru ba ita ba labrin ta, cen dai ya dan rage murya yace nana ina auntyn ki take, tace ai aunty kaisa ta dade da tafiya jalingo gurin goggo indo, goggo indo ce tace wai za ayi mata wasu en gyararraki kafin ayi mata aure,yaya muktar inace zaka zo auren aunty kaisa ko, da sauri ya to she mata baki ganin tana maganar da karfi kar inna ta jiyo ta,saboda nana irin yaran nan ne masu shegen magana fadi ba atambaye kaba duk ta iya shi, kuma kwata kwata shekarunta hudu ne a duniya,da sauri yace ehh zan zo mana nana, wai gyara akaje ayi mata a jalingon, da sauri nana tace ehh wai gyaran biki za amata, wani munafurtacciyar murmushi muktar yayi wanda ni kaina na gagara gane me wannan murmushin ke nufi BABY ZAHRA [9:11PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 35 na BABY ZAHRA A gaggauce yaci abincin shima yacine don baya wuce tayin inna saboda dadin abincin ta, a hankali yafito daga dakin, inna ce tace bari insaka agyara maka cen dakin ko, da sauri yace a'a ai inna daman nashigo ingaishe kune, amma yanzu zan wuce, abban baya nan ne, inna tace ai abba ya tafi yola yau amma gobe zai dawo, da ka tsaya kajirashi ya dawo ae, amma kace wai zaka wuce, yace ehh wlhy inna akwai aikan da abbana ya bayar in kaiwa goggo indo ne, to ina ganin idan naje ta gidan tan zan kwana zuwa washe gari sai in wuce, inna tace ohh to ae shikenan, inkaje cen ma kwa hadu da kaisan acen don itama ta dade da zuwa cen in, fuska yaci sannan yace owk to shikenan, nidai zan wuce, inna tace to Allah ya kiyaye hanya, yaciro kudi mai tarin yawa yabawa nana yace babyna gashi kije kisayi alawa ko, yabata ne saboda yasan inya bawa inna bazata karba ba, har bakin mota su nana suka rako sa, yashiga yaja yatafi sai garin jalingo, bai shigo garin ba sai misalin karfe biyar na yamma 5:00pm sannan yashigo garin kai tsaye gidan goggo indo ya nufa, sai da ya isa dai dai kofar gate in gidan sannan ya tsaya, yakama tunani to wai meyasa ma na biyo yarinyar nan ne, wai me nake nufi da hakan, kaii karfa yarinyar nan ta raina ni fa taga kamar ita na biyo, kwana yayi da kan motar sa da niyar zai koma, sai kuma me.....zuciyar ce ta gagara tafiya don bazata iya tafiya batare da taga fuskar kaisa ba, kan starring motar ya buga da karfi, gsky bansan me yake damuna ba kwana biyun nan akan wannan kucakar yarinyar BABY ZAHRA

Share:

1 comment:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).