shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday, 27 April 2016

SAUYIN RAYUWA 51___55

sauyin-rayuwa.jpg

[9:12PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 51 na BABY ZAHRA
Washe gari da safe ne akayi wuni, da yamma kuma akayi budan kai, ko wacce amarya aka kaita gidan ta, en uwan kuma suka koma gidan su muktar don su kwana zuwa ashe gari,

Abokanan sane suka rakoshi gidan nasreen, suna zazzaune a falo, akayi siyan baki, sannan suka danyi dan barkwanci daga bisani sukayi gaba, sallah ya umurce ta da su tashi suyi, bayan sunyi sallahr ne suka zazzauna a falor suka danyi ciye ciyen su, suka kunna TV suna kallo, tana kwance lamo ajikin sa sai soyayyar su suke sha, yana ta wasa da jikinta,daga bisani kuma suka tashi suka wuce cikin daki ( nidai a falon natsaya daga nan kuma na wuce gidan kaisa don inga halin da take ciki.. )
Aceen kuwa kaisa anakaita ta tashi ta rufe kofar gidan gabaya kasancewar tasan muktar ba zuwa zaiyi ba, duk da tasan ita yakamata yazo yafara kwana wa, saboda ita akafara daurawa aure da shi, amma tasan rashin adalci irin na muktar bazaisa yazo ya kwana mata ba, yabar nasreen acen, daga kafada tayi alamar ko ajikin ta, gyara kwanciyar ta tayi ta dada jan bargo zuwa jikinta, tayi baccin ta

Da asuba kuwa shiya taimaka mata tayi wanka, sannan suka sake komawa suka kwanta, tana kwance ajikin sa farin ciki yau Kamar zai kasheta, yau itace da muktar inta agado daya....
BABY ZAHRA
[9:12PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 52 na BABY ZAHRA
Misalin karfe 11:00am yatashi a firgice KAISA ce ta fado masa a ransa, a hankali yacire nasreen ajikin sa, toilet yashige yadan watsa ruwa, a gurguje ya sanya kayan sa...gidan kaisa ya nufa kasancewar gidajen a manne suke, katangane kawai yarabasu, tun daga bakin kofar falon yaji kamshin turaren wuta yana tashi, da sallama yashiga falon yaji shiru ya lalleka ko ina baiganta ba, uwar dakin yanufa, tana zaune bisa sallaya sallahr walaha tagabatar tana jan carbi tsayawa yayi sai da ya gama kallon ta sannan yayi mata sallama, a hankali ta amsa masa, saboda daman tunda taji motsi a falo da taso taje ta leka sai kuma taji anshigo tasan ba wanda zaiyi hakan inba shiba, bata juyo ba har saida ta gama tasbihinta, abakin gadon ya zauna, tajuyo tace ya muktar ina kwana,shiru yayi yanata kallon ta kusan 5sec kafin yace mata kin tashi lafiya, tashi tayi a inda take zaune, nade sallayar tayi sannan tayi taku daya biyu tace masa kalau nake, binta kawai yayi da kallo, yace ba akawo miki abin karyawa bane, tace mai ankawo fa, yace to zan iya samu indan ci, cikin tsiwa tace masa ae ba anan ka kwana ba, sake binta yayi da kallo tana bashi mamaki batsoro kwata kwata a idon ta take magana, tashi yayi ya nufi inda take
BABY ZAHRA
[9:12PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 53 na BABY ZAHRA
Tashi yayi ya nufi inda take, tana tsaye ajikin wadrop tana gyara kayan ciki, jitayi hannuwar sa sun zagaye kan kugunta, cikin firgici taso juyowa amma ina yayi mata mummunar kamu, gabantane yake mugun faduwa, cikin tashin hankali tace masa ya muktar meye kuma haka, don Allah nikam kasake ni, cewa yayi in ankifa, shiru tayi tanata murkususuwa tana son kwace kanta, amma ina, sai ma ce mata da yayi, kin san Allah in kikayi wasa yanzu zanyi maganin wannan rashin kunyarkin, cikin tsiwa tace masa to to ni me namaka, daukar ta yayi cak ya wurga kan gado, ya hau ruwan cikinta, ihu tasaka masa mai karfi, da sauri ya lalumo bakinta yasaka a nasa, sai murkususu take tana son ture shi amma ina ko motsi bayayi, hankalin kaisa duk yagama tashi, hawaye ne kawai suke gangara ta gefen kumatun ta,
Nan da nan zuciyar shi ta rayamasa cewa kamance da alkawarin da kawa nasreen ne, na bazaka taba kusan tan kaisa ba.....cikin sauri yamike akan kaisan cikin huci ya fito falo, wayar sa ya dauka missed call in nasreen ne yafara arba da shi, 20 missed call yagani, tsaki yajaa sannan ya fito daga gidan
BABY ZAHRA

[9:12PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 54 na BABY ZAHRA
Yana fita da sauri tabiyo bayansa ta kulle kofar gidan gaba daya, kaii gsky yau muktar yayi mugun razata, ko me yatunone yafasa aika aikan da yake shirin mata, ummm koma dai me yatuna nikam dai yataimake ni, Kutt kullum ana ce min maza basu da kunya ban taba yarda ba sai yau, yanzu ashe ya muktar har zai iyayi min haka, to ni yanzu da wani idone ma zan kalle shi, duk yanzu yabi ya daura min kunyarsa a rai, kai Allah dai ya kyauta....ae kuwa tun daga ranan kaisa tafarawa muktar wasan en buye buye, shi kuma duk hakan ya dame shi amma bai gwada mata ba, kullum da safe zai zo su gaisa, har kwana bakwai in nasreen yacika,
Kuka takeyi shar shar tace haba sweet kwana 7 zanyi batare da kaiba, bayan kuma kasabamin da kwanciya ajikin ka, don Allah sweet Kaduba dai kagani, cikin mulki yace mata to ae itama haka tayi hakurin kwana 7 in batare da ni ba, kuma itace karama a gangan ki, haba sweet amma fa kai da kanka fa kamin alkawarin bazaka taba kusan tar taba, cikin nutsuwa yace mata to ae don na kwana agidan ta ba wai shine na kwana akanta ba, tana da dakinta ina da nawa, haka kowa zaina kwana anasa dakin, ko kuma kinaso ne ran lahira intashi da shanyayyar jiki, saboda bana adalci agurin matana,
BABY ZAHRA
[9:12PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 55 na BABY ZAHRA
Dakyar ya shawo kan nasreen tabarshi yatafi, kasancewar tana da masu aiki da aka kawota da su su biyu, falmata ce da rabi, aka hadota da su daga fada, amma duk da haka sai da yakira zahra don tazo ta taya ta kwana,
Misalin karfe 8:00pm na dare ne ya shigo falon kaisa da sallama, a falo ya taddata tana kallo, tana ganin shi taji gaban ta yafadi,bata zaci zaizo ba, zama yayi akan kujera, tajuyo a hankali tace masa ina wuni ya muktar, idon sa yana kallon tv yace mata lfyklw, tashi tayi ta shige kitchen ta hado masa abinci akan tire, ta kawo masa, ita da kanta tazuba masa sannan kuma ta zauna agurin tana zaman jiran shi yagama, a hankali yace mata kizo muci, kai kawai ta kada masa alamar aa , daga kafadun sa shima yayi alamar ko ajikin sa, yacigaba da cin abincin, abincin yayi masa dadi sosae don tuwan semo ne da egusi soap yaci abincin sosae, yana gamawa ya wanke hannun sa, ita kuma ta kwashe tayi kitchen,bayan ta dawo falon ne tashiga dakinsa dama already ta gyara tasaka turarurruka masu dadi, toilet ta nufa ta hada masa ruwan wanka, tasaka turaren wanka aciki, sannan tafito falon tace masa na hadama ruwan wanka, cikin jin dadi yace mata too.
BABY ZAHRA
Share:

0 comments:

Post a comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).