shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday 20 April 2016

SAUYIN RAYUWA 1-2-3-4 & 5

sauyin-rayuwa.jpg
[9:09PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA page 1 na BABY ZAHRA Kayatatciyar daki ne mai dauke da ko mai na more rayuwa, alarm ce ke bugawa agefen wani hadaddan gado na alfarma, mika hannunsa yayi na dama ya danna alarm in ta mutu, mikewa yayi zaune yazaro dogayen kafafunsa kasa yayi dan mika sannan ya tashi yashige toilet, fitowa yayi sanyi da towel ajikin sa da kuma karama na goge kai da alamu dai wanka ya yi, zaunawa yayi akan er karamar kujerar da ke gaban madubin yadan shafa mai yamike yasanya kayansa, sauri sauri yake abun kasancewar yayi lattin zuwa office, a gurguje ya sakko kasa mai aikin shi yafara arba dashi yadakko mai kayan karin kumallo, hannu kawai yadaga masa alamar ya koshi,dakin momy ya nufa yana murda kofar dakin sukayi kicibis da kanwar sa zahra da sauri tace yaya ina kwana dakyar ya budi baki yace fyn yayi shigewar sa, daga kafada zahra tayi inda sabo ta saba da halin shi ita dai wannan kasaita na yayan nata yana matukar damun ta wai har wa itama da suke ciki daya yanayiwa, tsaki kawai taja tayi gaba abinta, zaune yake akasa kansa na kasa yana gaishe da mahaifiyar shi, kanshi ta dafa sannan tasanya masa albarka tace yatashi yaje kuryayi latti dayawa mutane suna cen suna jiran sa, mikewa yayi cikin kasaita kafin yafito, yana fitowa yasamu an wanke masa motar sa da zai fita da ita, masu aekin gidan ne suke mika masa gaisuwar su amma hannu kawai yake daga musu alamar ya amsa, Inda sabo suma sun saba, shiga motar yayi yajata shida Kansa, kai tsaye companyn sa ya wuce yana shiga tun daga bakin gate akafara mika masa gaisuwa, yanda yasa bannan dai hakan yayi, yayi wucewar sa, masinjan sa ne yazo da sauri yakarbi jakar laptop inda ke hannunsa kaitsaye office yashige yafara aiyukan da ke gaban sa, masinjan ne yashigo yake sanar masa akwai bakinda ke jiran sa tundazu, dakyar ya iya budar baki yace sujirashi zuwa anjima........MUKTAR USMAN JAJERE kenan yaro Dan kwalisa ga kyau ga kudi dogone shi mai matsaikaicin tsayi shi ba fari bane kuma ba baki ba chocolate yake kyakykyawane ajin farko,har wani doro yayi don rigama emmata rushing suke akan sa amma baya kula su, don shi arayuwar sa yafison mace tagani afada er gidan masu dashi sosae sannan yafison er gidan sarauta shiyasa haryanzu budurwar sa kwaya daya ce kuma ita yake shirin aura
Wanene MUKTAR muktar dan gidan ALHAJI USMAN SHEHU JAJERE ne alhj usman su en garin jajere ne dake jahar jalingo yana tare ne da matar sa hajiya hafsatu hjy Hafsat macece er kwalisa da kuma kasaita, kusan sai ince duk wata mulki da kasaeta 'ya'yanta ita suka biyo yaransu biyu ne rak aduniya MUKTAR da kanwarsa ZAHRA suna da kudi na azo afada, suna zaune ne agarin abuja a unguwar maitama BABY ZAHR [9:09PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA page2 na BABY ZAHRA gata na duniyar nan sun samu shiyasa ma wani sa in zakaga kamar basu da tarbiyya idan kaga irin abinda sukewa hajiya Rukayya wato matar da Baban su ya aura kwanan nan rashin kunyar dunuyar nan babu irin wanda muktar da kanawar sa Zahra basa mata da kuma daurin gindin Momy, shiyasa ma bata fiya shiga harkar su dayawa ba, takanyi damuwar gabanta ne kawai, kakan iya zuwa gida ka wuni batare da kasan akwai wata matar agidan ba, kasancewar gidan nasu gidan sama ne babba, a babban falo kawai suke haduwa, banda wannan falon kuwa kowa nata falon da daki da kicin adakin ta, gidan anmusu shine kamar mu hadu afalo, kofofi zakagani acen samar bene acikin falon inka shiga kuma zakaga kowa da wani falon ta da daki aciki, wannan babban falon an mayar da shi ne kamar falon baki, inzaka fita ne ake ganin fitarka amma zaka iyayin sati adakin ka batare da kunga juna ba, sannan kuma kowacce danata masu aekin, shiyasa ma takanyi rayuwar ta ita kadan ta, inda alhj yabi na nata kamma da tun tuni ya sake ta, to yaki sakin tan kasancewar er uwarsa ce ita, shiyasa kawai take zaman hakuri agidan Bakin kogine mai cike da iska mai dadi, tsugunne suke bakin gogin diban ruwa sukeyi acikin tulun su tadi sukeyi sosae, wanda ta shammacesu har basu ma san an tsaya akan su ba, hannuwar sa ya hada guda biyu ya tafa su,a dai dai kunnuwar su arazane suka mike harara rakiya tasake masa tace haba mana IRO yaza ayi ka wani kama karazana mu, hakuri yabasu sannan yajuya da murmushin shi ya kalli dayan gefen itama murmushin tamai, yace to kawo in rike maki tulun ko mikamai tayi suka jera suna tafiya, rakiya ce ta katsar da su da cewa nikam nayi gaba kisameni agida don Ku in kuka hadu kukan mance da kowa sai kan ku don haka nikam nayi gaba
SAUYIN RAYUWA page Murmushi kawai suka mata rakiya kenan iyayen tsiwa, ahankali suke tafiyar har suka iso gidan tulun ruwanta yabata, sukayi sallama tawuce gida,da sallama tashiga inna tagani tana shara da sauri taje ta juye ruwan a randa tazo takarbi sharar, inna ta aa jeki ki dau abincinki kici, ki tayi har sai da ta karbi sharar ta share gidan tass sannan tazo tanemi abinci taci, KAISA AHMAD MALAMI JAJERE kenan, kaisa yarinya ce mai nutsuwa ga sanin yakamata haddan Al'Qur'ani izzu sittin ne akanta baban ta MALAM AHMAD SHEHU JAJERE wanda akafi sani da MALAMI babban malami ne agarin jajere sananne akan addini ana ji dashi agarin jajere su uku tak agun mahaifan su USMAN shene babba sai shi MALAMI sai er autar su AISHA wanda akafi sanin ta da INDO yaran kuma suna kiranta da GOGGO INDO [ SAUYIN RAYUWA page4 na BABY ZAHRA goggo indo tana matukar son 'ya'yan yayyan ta kasan cewar ita bata sami haihuwa ba shiyasa ma t 9:10PM, 3/18/2016] baby zahra: a dauki kaisa take zama agaban ta, ita tana aure agarin jalingo agurinta kaisa take karatu, kasancewar acikin su malami ne kawai mai Yaya dayawa shine mai yara hudu acikin su maza biyu mata biyu fatima ce Babba mai sunan mamar su, ana kiranta da KAISA sai kanin ta USMAN mai sunan yayan shi anakiran sa da yaya, SHEHU mai sunan babbansu anace mai abba, da kuma AISHA mai sunan goggo indo, aduk acikin su malami ne kawai baida wadata amma kuma suna bakin kokarin su gurin kyautata mishi, alhj usman wanda suke kira da abban abuja yayi yayi da kaisa ta dawo gurin shi ta zauna amma taki, ba don sabida komai ba sai don yaya muktar da zahra saboda irin wulajancin da suke mata inta je gidan shiyasa ma bata zuwa, goggo indo kuwa saboda irin wulakanci momy yasa kwata kwata basa shiri da ita KAISA yarinya ce kyakykyawa son kowa kin wanda yarasa bakar bafulatana ce ita wato chocolate colour bata da tsayi kuma ita ba guntuwa bace kwata kwata shekarunta 20yrs ne a duniya yanzu haka ta gama diploman tane a polytechnic inda ke jalingo...... Wannan kenan Kwance take a wani kayatattacen falo na alfarma kuyangunta ne sukeyi mata danna a kafa hannunta kuwa rike take da wata hadaddiyar waya dannawa takeyi hankalinta ya karkata kan chart inda takeyi da masoyin ta abin alfaharinta, jakadiyace ta katse mata nishadin ta tace ran gimbiya shi dade antashi lafiya, sae da takai kusan 5mnt kafin tadan daga kanta alamar ta amshi gaisuwar ko ido bata daga ta kalli jakadiyar ba, cen sai jakadiya tace gimbiya dama fulani ce ta aiko ni, ido kawai tadan daga mata alamar tana sauraren ta, da sauri jakadiya tace fulani tace tana son ganin ki yanzu, kai ta girgiza mata alamar taji,sannan jakadiya tamike tace nabarki lafiya ta fita,cen kimamin 15mnt kafin ta tashi taje kiranda mahaifiyarta tamata....to NASREEN MUHAMMAD LAMIDO kenan yarinya er kwalisa mai ji da kanta er sarauta jikan sarauta fara ce ita mai matsakaicin tsayi kyakykyawa ajin farko er gata gaba da baya wannan shekarar tagama university inta a London, acen ta hadu da MUKTAR inta tana tsananin son shi shine abin alfaharin ta
Share:

4 comments:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).