shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday, 27 April 2016

SAUYIN RAYUWA 56____60

sauyin-rayuwa.jpg

[9:12PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 56 na BABY ZAHRA
Tashi yayi ya nufi dakin, wow yace gsky dakin yayi kyau ga kamshin turaren da ke tashi a dakin ga wani sanyin a/c wanda ya hadu da kamshin turaren sai yabada sanyi mai dadin kanshi, toilet in ya nufa shima nan yayi kusan 5mnt yana kallon bayan gidan daga bisani ya soma abinda yashigo dashi,
Ita kuwa kaisa tana ganin yashige itama ta tashi tayi nata dakin ta sanya key, tayi kwanciyar ta abinta,
Bayan yafito daga wankan ne yasanya kayan bacci, yafito falon sai kuma bai ganta ba amma kuma tv yana kunne , zama yayi ya dauka ko itama tashiga wankan ne har yanzu bata fito ba, zaman jiran ta yakeyi, har tsawon 30mnt amma yaji shiru tashi yayi yanufi kofar dakin tan yadan murda hannun kofar, yajita gamm, tsaki yayi sannan ya nufi nashi dakin, ranshi a bace ya kwanta, yanata juye juye, wata zuciyar ce tace masa to kai naka a wanne daman so kake ku kwana tare kome, ko ka mance baka son tane, tsaki ya kumayi akaro na biyu, yaja bargo ya gyara kwanciyar sa, da kyar bacci ta dauke shi.
BABY ZAHRA
[9:12PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 57 na BABY ZAHRA
Washe gari da safe kafin yatashi ta gama masa komai na abin karyawa, yana fitowa yayi arba da ita cikin wata riga da wando 3Quetta tadan kama kanta da ribon tanata goge gogen su tv, ya fito yayi kusan 10mnt yana tsaye ya harde hannuwar sa yana kallon ta....haka kawai taji ajikin ta kamar ana kallon ta, a hankali ta Juyo... ido biyu sukayi da shi, irin kallon da yake mata ne yasakata taji kunya amma sai ta batsar, har kasa ta tsugunna cikin ladabi tace ina kwana yaya....karkiso kiga bakin muktar har kunne yana amsawa, hummm dariya yabata amma sai taci fuska bata gwada masa ba,(ashe fa gskyr rukky kobi ce, don ita tabata wannan kissan), cikin kisisina tace masa ga abin breakfast inka nan akan dining table, cikin annashuwa yace to bismillah muje, tana gaba tanata girgiza mazaune shikuma yana binta abaya kamar bunsuru duk hankalin sa yatashi, ita ta jawo mai kujera ya zauna, sai da yazauna sannan tafara zubamai abincin, itama kuma ta zauna don ta deba masa kewa, farinciki yagama kama muktar don ganin yau kaisa tasake mai fuska, dibo soyayyiyar dankali yayi, yamika mata a bakinta, ko kunya bata jiba tasa baki ta karba, farinciki yagama kasheshi a zaune
BABY ZAHRA
[9:12PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 58 na BABY ZAHRA
Allah Allah yake yagama cin abincin.... kaisa tagama fuskantar inda ya dosa, cikin nutsuwa da kissa ta tashi tsaye, cikin sauri yace mata ina kuma zaki bayan kuma bamu gama ba, cikin sassanyar murya tace masa, wlhy kaina yake ciwo zan dan kwanta, nan da nan hankalin sa yatashi, yace to kije ki shirya muje asibiti ko, cikin kissa tace masa a'a wlhy ae nasha magani bacci kawai nake bukata, tashige tayi dakinta, danna key tayi sannan tayi dariyar mugunta,tace hummm yafara shiga hannu, kadan kafara gani ae wlhy sai na gara ka.......kwanciyar ta tayi abinta tanajin shi yana murda hannun kofar, amma tayi banza da shi haryagaji yayi gaba, har bacci ya dauketa, misalin karfe 12:00pm ta tashi abincin rana ta daura, tana cikin yanka carrot ne, taji hannaye sun zageye mata kugu, gabanta ne yafadi sosae amma sai ta batse,tayi murmushin karfin hali, tace yaya na harka tashine, cikin jin dadi yace mata ya ciwon kan dai, tace lfyklw na warke, cikin tsokana yace mata wato shine kika kulle min daki ko, hummm tace masa, cikin faduwar gaba tace ae kasan kaina ke ciwo shiyasa, yace to ae yanzu an warke ko, tace ehh, yace to ae baza akulle min da daddare ba ko, humm kawai tace masa cikin kunya, yace mata ya da humm kuma, tace babu, yace to ya baza akulle min ba ko, ce mai tayi Allah ya kaimu, cikin annashuwa yace amin, sunbatar ta(kissing) yayi a kumatu,sannan yasake ta yace bari in je gida abba yana son ganina, har kofar falon ta rakoshi, tamai addu'ar fatan alkhairi
BABY ZAHRA
[9:12PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 59 na BABY ZAHRA
Bai gama da abba ba har sai bayan sallahr ishsha, duk hankalin sa ya gama komawa gurin kaisa, sai da abba yalura da hankalin shi baya gurin ne shine ya sallameshi, yana zuwa gidan nasreen ya dosa, don yayi mata sai da safe.....a falo yatarar da ita daga ita sai dan gajeren wando iya cinya, sai 'yar riga fale fale ya manne ajikin ta gashi shara shara, kuma ko bra babu ajikin ta komai najikin ta ana gani..da sauri tamike taje da gudu ta rungume shi tace sweet wato yau kashare ni ko don kaje gurin amaryar ka, tunda safe fa nake jiran ka, cikin shagwaba tayi maganan, shafa gashin kanta yayi sannan ya yi kissing inta yace yi hakuri sweet wlhy yanzu ma daga gurin daddy nake tun safe ya rike ni sai yanzu...jawo shi tayi dakinta, ta kwanta akansa ta soma romantic insa tun yana ki har yaba da kai........misalin karfe 12:00pm ne na dare ina zaune abakin gado raina idan yakai million to yabaci wato ni muktar zai wulakanta ko, yasa namasa girki amma baizo yaci ba, yau ranar kwana na amma ya kaiwa nasreen, hummm dogon numfashi ta jaa sannan ta kwanta ta jawo bargo, amma dakyar bacci ya dauketa.
BABY ZAHRA
[9:12PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 60 na BABY ZAHRA
Misalin karfe 4:00am na asuba ne ya farka daga nannauyin baccin da yayi, KAISA! abinda zuciyar shi tafara ambato kenan, a firgice yatashi wanda har sai da yasa nasreen itama ta farka a razane, lafiya tace masa, da sauri yace mata kaisa, bai masan lokacin da ya furta mata hakan ba, cikin bacin rai nasreen tace meye kuma wani kaisa, yace mata nasreen yau fa ranar kwanan kaisa ce nazo na kawo miki, haramtacciyar kwanciya fa mukayi, tsaki taja masa tace to sai kuma me don ka kwana agurina ranan kwanan kaisa, sau nawa ana haka, cikin tsawa yace mata baki da hankali ne nasreen, inda kece aka miki hakan yaya zakiji a ranki, cikin kissa tasaka masa kuka mai cin rai,tace ashe har lokaci yayi da zakafara wulakantani akan wata, tsaki yaja, baiyi niyar rarrashinta ba amma dayaga kukan nata dada yawa yakeyi shine yajawota jikin sa ya hau rarrashin ta, a hakan taso su sake komawa gado amma yaki, ranta idan yakai million to yabaci, ta dada tsanan kaisa a ranta, yaushe muktar ya soma son kaisa, da har zai fara nuna mata kulawa irin haka,to wlhy kuwa zanyi maganin su tafadi hakanne aran ta, haka muktar ya karasa kwana a zaune daya fita sallahr asuba ne bai dawo ba ya wuce gidan kaisa, mai gadi ne yabude mai gate ya shigo cikin hanzari yana gaishe shi ma amma bai tsaya amsawa ba kofar falon ta ya nufa
BABY ZAHRA
Share:

4 comments:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).