[9:11PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 36 na BABY ZAHRA Daga cen nesa ya hangota ta nufo inda ya ke hijab ne ajikin ta har kasa rungume da al Qur'ani a da wasu littafai a hannun ta da alamu dai daga makaran ta take, sai da tazo daf da shi har zata wuce sai kuma yaga alamar bata ganshi ba, cikin mulki da kasaita yace ke daga ina kike, Gaban tane yayi mummunar faduwa arazane tajuya don ganin mai wannan muryar, Allah Allah take Allah yasa ba wanda take zato bane.....ya ilahi ta furta acikin zuciyar ta, wannan kuma meya kawo shi nan kuma..... ya katse mata tunanin ta da cewa bada ke nakeyi bane, cikin bacin rai fuska ba wal wala tace daga makaranta, yace wacce makaranta kuma, tace islamiyya, gyaran murya yayi sannan yace zo ki dauki kaya a both, a hankali ta juya tare da shi suka jera zuwa gurin both in, yana nuna mata wa enda zata dauka, a hankali yace bakiji dadin ganina ba ko, shiru tayi bata ce mai komai ba, sannan yace to ai ni inma inda nasan zan zo insameki a nan da banzo ba, cikin tsiwa kaisa tace to ai yanzu ma bai baci ba zaka iya tafiya, a hankali yace to ae ba gurin ki nazo ba ko, kibari duk randa kikayi gidan kanki in kika ganni a gidan sai ki koreni amma yanzu nazo gurin uwata ce, har falon suka shiga suna gayawa juna magana, goggo indo ce tace ke kaisa ke da waye, lekowar da zatayi sukayi ido biyu da muktar tace ahhh lalle fa yaron abba Kaine a gidan nan BABY ZAHRA [9:11PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 37 na BABY ZAHRA Murmushi yayi yace eh wlhy goggo nine yau a gidan ki, goggo indo tace wato don kaji matar ka tana nan shine ka kwaso kafa kazo ko, yaushe rabon ka da gidan nan, cikin kunya muktar yace laaa goggo ba haka bane, hasalima niban san tana nan ba, a kofar gida muka hadu shine ta hada fuska tafara gaya min magana wai bata so zuwa na ba, goggo indo ce tace lallai agaishe ki kaisa, to gwanda ma kina sakawa kanki cewa mijin kine shi yanzu, kaisa ce tace wlhy goggo indo ba haka mukayi da shi ba.... cikin masifa yace dalla kiyiwa mutane shiru manya suna magana zaki sa baki, goggo indo ma ta biye wa muktar sukawa kaisa caaa aka, goggo indo ce tace maza tazo har gaban sa tabasa hakuri, baki zunbure ta taso tazo gaban sa ta tsugunna tace don Allah ya muktar kayi hakuri da abin da na maka.....sai wani shan kamshi yakeyi yana wani daga kai sama nan da nan mulkin ta motsa, da kyar ya iya cewa karki damu, tashi tayi ta shige cikin daki tayi kwanciyar ta BABY ZAHRA [9:11PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 38 na BABY ZAHRA Gsky zuwan ya muktar ba karamin takurawa kaisa yayi ba, yana zaune komai sai an masa, gashi goggo indo sai goya mai baya takeyi yana mata abinda ran shi yake so, Allah Allah take yasamu ya koma... Sallama akayi akofar dakin kafin suka shigo, da gudu ta tashi taje ta rungume su kawayen tane na skul suka zo mameey yahya da ruwaeda, bakin gado suka samu suka zauna, bayan sun gama gaisawa ne da dan tade taden da suka saba na skul, sannan suka mika mata kudin ashoben su daman abinda ya kawo su kenan, mikewa tayi tsam don taje ta dakko musu ashoben a dakin goggo indo, kicibiss sukayi da shi abakin kofar dakin ta, har sai da jikin su suka gogu da juna,hakan bakaramin fadar mata da gaba yayi ba, nan da nan ta hade rai, takama neman hanya ta gefen shi zata wuce, tare hanyar yayi shima ransa abace, yace ke wai bakisan yakamata bane da bazaki kawo min abinci naba, kanta akasa tace ae bansan ka dawo bane, yace tayaya za ayi kisan na dawo tunda kin sami wa enda suka fini kin bude musu baki kunata shashanci, ko kallon shi batayi ba balle tace mai wani abu gefen shi ta goga sannan ta wuce abinta, shekeke ya tsaya yana kallon ta, aaa lalle fa wannan yarinyar ta girma wato har tasan ta gogi jikin sa sannan ta wuce tabb lalle yarinyar nan zata sani, bari ta shiga hannuna zatayi bayani, ita kuwa kicin ta nufa ta har hada mai abincin nasa akan babban plat don haka goggo indo tace tana masa, wai tafara koya tun yanzu, a palour tasame shi shame shame Kamar wani mai jiran mai aikinsa takawo mai abinci, ajiyewa tayi a kan table inda yake gaban sa sannan tajuya zata tafi yace mata ke zonan BABY ZAHRA [9:11PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 39 na BABY ZAHRA Juyowa tayi batare da tadawo ba tace ya ne, yace zoki zuba min, nan take tace mai ina da abinyi yanzu, bata ko tsaya taji mai zai ce mata ba tayi gaba, bakaramin tashi hankalin muktar yayi ba wato har yakai stage inda kaisa zata fara masa rashin kunya, to insha Allahu yayi ma kansa alkawarin ba zai sake kulata ba koda abincin ne ya gwammace yana shiga kitchen shi da kansa yana dakko wa, insha Allahu yayi makansa wannan alkawarin,
Kwana daya biyu uku kaisa taga muktar baya ko kallon inda take, daga farko tayi farin cikin abun don ganin yanzu baya takura mata, amma daga baya kuma sai abin yadame ta gashi gobe wai zai koma abuja, kai wai menayiwa yaya muktar ne yayi irin wannan mummunar fushin da ni, tunowa tayi tayi metamasa na karshe, nan da nan gabanta yafadi sakanakon tuno da rashin kunyar da tamasa na karshe, kai gsky ban kyauta ba yakamata insa meshi in ba shi hakuri, to taya ya ma zan fara mutumin da ko murmushin shi na daina gani yanzu, yanzu ya koma asalin muktar usman jajeren shi, tana cikin tunanin nema sai taji sallamar sa yashigo falon da sauri tace sannu da dawowa ya muktar, bai ko kalli inda take ba balle ya amsa HANNU yadaga mata alamar ya amsa, nan da nan gaban ta ya fadi tace tabb ya muktar an koma DA kenan, kai tsaye kitchen ya wuce yakama zubama kansa abinci da sauri tazo tasame shi tace yaya kawo in saka maka, kai kawai ya girgiza mata, bakaramin tashi hankinta yayi ba fatan ta daya shine kar goggo indo tazo tasame shi a kitchen shi da kansa yana debawa kansa abinci, ai bakaramin tashin hankali yajawo mata ba. BABY ZAHRA [9:11PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 40 na BABY ZAHRA Binshi takeyi a baya kamar jela suka sake komawa falon, yana zama itama ta zauna shiru shiru ba wanda yacewa kowa kala har sai da yagama sannan yayi gyaran murya yace meye da meye zakiyi na event in bikin ne, a hankali tace walima zanyi, yace to ga wannan 300k yaba ta kamar yarda yabawa nasreen,arazane ta kar bi kudin wannan uban kudin me zatayi da shi, cikin sauri ta dan zari kadan aciki tace masa ga wannan karike, wannan ma ya isa, bambarakwai yaji abin abinda baisaba ji agurin nasreen ba, amma sai yaci fuska bai gwada mata kamar yaji mamaki ba, ko kallon ta baiyi ba balle yasan me take fada, yaci gaba da bude ledar da ke gaban sa, waya ya ciro a kwalinta ya mika mata tasaka hannu ta karba cikin murna da farin ciki tace nagode YAYA NA! Wani yarrr yaji ajikin sa da sauri ya kalleta yaga ita bata Masan ta furta wannan kalmar abakin taba, har cikin ransa yaji dadin kalmar, sai kuma wata zuciya tace mai to meye nawani jin dadi don yarinyar da baka SO takira ka da yayanta ga nasreen inka nan tana kiran ka da sweeet ma ba wani yayan ta ba, tsaki yayi acikin ransa ya mike yafita, bude wayar tayi TECNO PANTOM ce da gudunta ta shige dakin goggo indo ta dira akanta tana ihu da sauri goggo indo ta tashi tace ke lafiya, kefa baki da hankali wataran mika mata wayar tayi da sauri tace ya muktar yasai mun waya, eyye goggo indo tace a'a gsky waya kam yayi kyau ina shi muktar in yake tace yafita yanzu, sake miko mata kudin daya bata tayi tace gashi wai yaban inyi event da shi, ni inaganin kamar kudin yayi yawa ko
tnxs
ReplyDelete