shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Monday 27 November 2017

SIFFOFIN UWA TAGARI 5


LALLE

Yar’uwata ki sani lalle kwalliyace ga duk ya mace kuma mace idan ta bar hannunta ko kafarta ba lalle to ba’a iya banbance ta da namiji. Kuma kowace irin kalan lalle da mata sukeyi kema kiyi da zaran ya goge sai ki biyoshi da wani kala domin cika siffarki ta ya mace.

BANGAREN ADO

Yar uwa ki sani kirkire kirkiren adon zamani wajibine akanki a gidan mijinki harma da irin naki salon adon, kuma duk wata dressing da mata sukeyi a duniya dolene ki rinka yiwa mijinki matukar bai sabawa addinin musulunci ba, sannan kiyi masa ado da duk irin kayan da kika mallaka.

KISISINA DA KARERAYA

Ya yar’uwata mace bata cika mace ba idan bata iya kisisina irin ta mata ba, kamar su kareraya, yanga da rigima. Kuma ki sani irin wadannan dabi’un su suke daukaka martabar mace a wurin mijinta acikin dukkan alamuran su, Magana ko tafiya ko kallo da makamantansu.

DAMUWA DA DAMUWARSA

Yar uwa wajibine ki karanci halin mijinki sosai kisan mijinki acikin halin farin ciki da kuma bakin ciki kuma ki lura da yanayin sa a lokuta kamar haka:
Ø     Lokacin fita nema
Ø     Lokacin dawowa daga nema
Ø     Lokacin gajiya
Ø     Lokacin farin ciki
Ø     Lokacin bakin ciki

Ø     LOKACIN FITA NEMA: A wannan lokaci yar’uwata ki sani dolene ki tabbata mijinki ya fita daga gida cikin kwanciyan hankali da natsuwa. Akwai wani dabi’a da matan magabata sukeyiwa mazajensu, su kan shirya bayan sunyi wanka da kwalliya sannan sai su raka mazan su har kofar gida ko kofar daki, sannan suna tafiya suna taku daddaya da rangwadi kuma su kan yimusu addu’a sannan su basu wasiyan cewa idan Allah yasa ka samu halal ka kawo mana, idan kuwa baka samu ba zamuyi hakuri da azabar yunwa akan azabar Allah. Bayan ya fita yayi nisa sai ki kirashi da wani sunan soyayya mai dadi sai kiyi masa Kiss da hannunki. Sai kice masa Allah ya bada sa’a. Allah ya sa mudace Ameen.

Ø     LOKACIN DAWOWA DAGA NEMA: Ki sani yar’uwata miji yana dawowa gida a halin gajiya kafin ya dawo kin shirya ma dawowarsa.

Ø     LOKACIN GAJIYA: A wanna lokaci ki sani zaki nemi ruwa mai dumi a lokacin sanyi idan kuma lokacin zafine, sai kinemo ruwan sanyi ki kai masa wurin wanka bayan ya gama wankan ya dawo daki ki bashi abinci

Ø     LOKACIN FARIN CIKI: Yar’uwata a wannan lokacine zaki baje kolin shagwabar ki da rungumarsa

Ø     LOKACIN BAKINCIKI: Yar’uwata a wannan hali babu wasa babu tsokana a tsakaninku har sai kinji mai ya bata masa rai, idan ya fita bai samo bane sai ki kwantar masa da hankali, sai ki nuna masa kullum Allah yana basa sai kawai don yau baka samo ba sai muyi hakuri mu godewa Allah. Idan kuwa wani ne ya bata masa rai, sai ki bashi hakuri da kuma kwantar masa da hankali, sannan idan ya dawo miki cikin tashin hankali sai ki warware masa bayan kinji mai ya faru dashi. Idan ba zaki iya warware masa ba sai ki kaishi inda za’a warware masa damuwarsa.

1. MACE TAGARI ITACE WACCE IDAN MIJINTA YAYI RANTSUWA AKANTA ZATA BARRANTAR DASHI: Yar’uwata ki sani wajibine idan mijinki yayi miki rantsuwa sai ki barrantar dashi misali idan yace wallahi yau sai kin yafe min laifin da nayi miki, kawai sai ki yafe masa don ki barrantar dashi.

2. MACE TAGARI ITACE WACCE IDAN MIJINTA BAYANAN KOKUMA YAYI TAFIYA SAI TA KIYAYE KANTA KUMA TA KIYAYE DUKIYARSA: Yar’uwata ki sani idan mijinki bayanan dolene ki kiyaye kanki da dukiyarsa, kuma karki yarda ki nuna adonki ko kwalliyarki ma wani kuma karkiyi almubazarranci da dukiyarsa. To yar’uwata idan kika cika wadannan sharuda wallahi kin zama mace ta gari injin Manzon Allah (S.A.W). da fatan Allah (S.W.T) ya baki ikon cika wadannan sharuda Ameen.
Share:

Saturday 18 November 2017

SIFFOFIN UWA TAGARI 4SIFFOFIN MACE TA GARI

Yar uwa mai karatu ga kadan daga cikin siffofin mace ta gari, idan kuwa baki da wadannan siffofin, to sai ki rungumi wannan su zamo dabi’unki. Allah yasa mu dace Ameen
1.                       Itace idan mijinta yayi mata umurni zatayi masa biyayya.
2.                       Itace idan mijinta ya kalleta zata farantamasa rai.
3.                       Itace idan mijinta yayi rantsuwa akanta zata barrantar dashi.
4.                       Itace idan mijinta yayi tafiya zata kiyaye kanta da dukiyarsa

1.                       MACE TAGARI ITACE WACCE IDAN MIJINTA YAYI MATA UMURNI ZATA YI MASA BIYAYYA: Yake yar’uwata ki sani duk irin umurnin da mijinki yayi miki to wajibine kiyi masa biyayya matukar bai sabawa Allah ba. Kuma acikin kowani hali kika samu kanki ba tare da yamutsa fuska ba. Balle jan aji, kuma yar’uwa ki sani jan aji haramunne idan mijinki yayi miki umurni, wajibine ki zamo mai bin umurninsa. Allah ya baku ikon bin umurninsa Ameen.

2.                       MACE TAGARI ITACE IDAN MIJINTA YA KALLETA ZATA FARANTA MASA RAI: Ya yar’uwata mijinki ba zai taba kallonki har ki faranta masa rai ba, face kin dauwama a siffarki ta ya mace.
GA WASU DAGA CIKIN SIFFOFIN KAMAR HAKA KWALLIYA DA GAYE: Yar’uwata ki sani yana daga cikin asalin hallitar mace akai shine kwalliya, don haka ba’a son mace cikin sahun mata idan batayin kwalliya, anan wajibine ki kasance zinariya a gidan mijinki ko wani lokaci da irin salon kwalliyan da zaki yiwa mijinki acikin lokuta guda hudu kamar haka:
i-                        LOKACIN SAFIYA: Yar’uwata bayan kinyi Sallah wajibine kiyi wanka kiyi kwalliya irin kwalliyar Amarci.

ii-                     BAYAN BREAK FAST: Idan kin gama wanke kwanukan da aka ci abinci kinyi shara sai kiyi wanka kiyi kwalliya, yar’uwata kar ki yarda mijinki ya dawo ya sameki a hargitse, kamar yadda wasu mata sukeyi, abin kunya wai suna da zanin zaman gida kuma suna da zanin fita anguwa, wallahi wannan mummunar dabiane a dena.

iii-                   BAYAN ABINCIN DARE: Yake yar’uwata anan ma ya zama dole ne kiyi masa kwalliya irinta zamani wadda zaki kayatar dashi.
iv-                   LOKACIN BARCI: Yar’uwata anan kuma wajibine zaki yiwa mijin ki kwalliya da shara sharan kaya wadda zasu rikita mijinki.


do you want to learn how to blog and also make money online check this site
Share:

Saturday 11 November 2017

SIFFOFIN UWA TAGARI 3


MACE TAGARI

Mace ta gari za a same ta da:
1.                       KAMEWA: Daga duk wani abu da zai sosa wa maigidan ta rai, a kanta ne ko gidansa ko abincinsa da sauransu.

2.                        GASKIYA: In za ta yi magana ba ta qarya, domin samun riqe gidan gaba daya.

3.                       AMINCEWA: Duk abin da yake so ta yi ta amince, don yarda da cewa ba zai halakar da ita ba, tana qaunarsa.

4.                       TAWALU'U: Ta qanqar da kai gare shi koda kuwa tana da ilimi, arziqi da shekaru sama da shi, kamar dai Khadeejah R.A da Annabi (S.A.W)

5.                        NATSUWA: Kar ta riqa tuno abubuwan da suka gabata, kuma ta dena tsoron masu zuwa.

6.                        KUNYA: Ta riqa jin kunya, wannan ado ne gare ta, masamman in tana tare da mijinta a cikin jama'a, wannan zai qara masa kaunarta.

7.                        KWANCIYAR HANKALI: Mantawa da matsalolin rayuwa da qoqarin tura farin ciki ga mai gida koda suna cikin matsala.

8.                        GODIYA: Duk abin da ya zo da shi a nuna masa jin dadin zuwa da shi komai girmansa komai qanqantarsa.

9.                       HAQURI: A kan duk abin da zai bayyana daga miji (wannan ne kawai muka dauka alhali suna da yawa)

10.                  TSAYUWA QYAM: A wajen bauta da qarfafa mijin da 'yayan su.

11.                  AMANA: Ta zama mai amana, kar ta yarda maigidan ta ya ga ha'incinta koda kuwa sau Daya ne, ta riqa gaya masa abin da za ta yi domin maganin shedan. ‎
Wadannan abubuwa guda 11 su suke nuna mace nagari, dan uwana kada ka riqa binciken qyalqyal banza, ke ma yar uwa ki dai na kallon kudi ki duba rayuwarki idan kin shiga gidansa, komai kudinsa in ba kwanciyar hankali ba za ki ji dadinsu ba. Biyayya ga miji ba mai iya wa sai mace ta tagari, da yawa mata suna so a ce su ne wadan da Annabi (S.A.W) ya sifanta dinnan da (Nagari) sai dai biyayyar ce ta yi qaranci, ko za’a yi sai dai a gabansa in ya matsa an watsar kenan.

           Mace ta gari takan yi qoqarin ta zama wa mijinta aljannarsa ce, ba ta son ta ga gazawarta a idanunsa, don haka takan yi farin ciki in taga murmushinsa, takan damu matuqa in ta ga fushinsa ko da ba da ita yake ba, ba ta jinkiri a wajen abinci, kuma ta iya dafawa ba tare da almubazzaranci ba, ita ce amin taccen abokin shawararsa, mai iya riqe masa sirri, ba ta yarda wani ya sani ko waye kuwa, sannan ga taimako.

do you want to learn how to blog and also make money online check this site
Share:

Thursday 2 November 2017

SIFFOFIN UWA TAGARI 2

SIFFOFIN UWA TAGARI

Kalmar macce abu ne mai matukar girma sabida daraja da kuma kima da Allah ya bata, Yaku mata kada ku shagala da jin dadin rayuwar duniya kuyi biris da baiwar da Allah ya yi muku kusani cewa duk wata jin dadin matukar baki kame kanki daga aikata fasadi ba yazama na banza kuduba kugani yanxu Rayuwar da muke ciki a bin haushi matan aure basa fita irin wadda Addini ya umurcesu dasuyi wa'iyazu billah haba mata, Ina kuka baro Hijabinku suturar ku wadda Allah ya ce ku lulluba da ita...??? Wai ace matar aure zata fita unguwa saita kashe makeup tamkar zataje gasar sarauniyar kyau amma abin haushi In ka tarar da ita A cikin gidanta tamkar yar aiki, Wai bazatayi wanka da tsaf ta ba sai in zata gidan biki ko asibiti ko wani abin to wallahi kisani duk wanda zaiga adonki ya yaba matukar ba mijinki bane kinyi a banxa. Wani abin haushi abin takaici Wai yanxu mata basu sallah cikin lokaci sabida an miki kwalliya karkije alwala ta goge Innalillahi wa'innah illaihirraju'un kenan kin xabi duniyarki a bisa lahira ko....?? wace riba gareki idan Allah ya dauki ranki kina cikin irin wannan halin...?? mezaki ce da mahaliccinki..?? kokinsan cewa mutuwa kowane lokaci zata iya yi miki bazata gaskiya mata a gyara yakamata ace duk wani abu komai mahimmancinsa ki hakura dashi har sai kin gana da mahaliccinki (SALLAH) , Adaure ayita cikin lokaci kuma bada garaje ba dan naga wasu ma sallar basusan yanda zasuyita cikin nutsuwa sabida kawai dadin duniya ya shagaltar Dasu. Allah ya sawwake. Ameen!!
Da farko yake yar’uwa ki sani aure bautan ubangiji ne. To amma mai yasa ku mata kuke banbanta yanayin zaman aurenku bayan Annabinmu dayane, domin da yawa daga cikin yan uwa mata basu dauki aure a matsayin bautaba wallahi. Bayan aure itace babban hanyar shigarki Al-jannah idan kikayi hakan kuma kika yarda da hakan to kinci riban duniya da kuma lahira. Allah yasa haka Ameen. Sannan ki sani yar’uwa duk wata ibada tana tareda jarrabawa musamman ma aure, domin zamane da ya kunshi farin ciki da bakin ciki, dadi. da mara dadi, hakuri da rashin hakuri, da sauran wasu abubuwan da basai na ambacesu ba, Yake yar’uwa ki sani aure anayinsa saboda wasu abubuwa da dama amma babban su shine natsuwa. Kuma natsuwa baya samuwa sai idan mace ta zama tagari shiyasa da yawa daga cikin maza basuda natsuwa saboda matansu ba nagari bane. Manzon Allah (S.A.W) yace duniya abin jin dadi ne, amma mafi alkhairin jin dadin duniya shine mace tagari, don haka ya yar’uwata idan harke ba mace tagari bace to ki sani baki da amfani a zaman gidan aurenki da mijinki idan kika sake baki gyara zamanki da mijinki ba, to wallahi zaki samu mummunana sakamako a wurin Allah. Allah ya karemu Ameen.


Ya kamata duk matar da ta tsinci kanta adakin aure, a wannan zamanin da muke ciki, ta gode ma Allah. Ba don komai ba, idan ta duba zata ga wasu 'yan-mata irinta, sunfi ta kyawun halitta da iya ado, amma har yanzu basu samu mijin aure ba. Don haka zai fi alkhairi agareki ki Qudurce acikin zuciyarki cewa GIDAN MIJINKI NAN NE WAJEN NEMAN ALJANNARKI Ki rike mijinki hannu bibbiyu, ki kula da tsaftar jikinki da tsaftar Muhallinku. Ki kiyaye MUGAYEN QAWAYE... Ba zasu rasa yi miki hassada ba. Tunda ke kin samu miji, su kuwa basu samu ba... Dole suyi miki hassada. Ki kiyaye sirrin mijinki, kar ki gaya ma kowa. Musamman ma kawayenki zasu so suji abinda yake faruwa. Don haka kar ki gaya musu Idan kuna da 'ya'ya to ki kula dasu, ki kula da tsaftarsu. in ma 'ya'yan kishiyarki ne, to ki kula dasu kamar yadda zaki kula da 'ya'yanki. Ki kiyaye dukkan amanonin mijinki. musamman ma iyayensa da 'yan uwansa da dukiyarsa. Allah Ya bamu ikon kiyaye Hakkin iyalan mu.
Share:

SIFFOFIN UWA TA GARI


SIFFOFIN UWA   TA GARI


NA

MUHAMMAD ABBA GANA
(09039016969)


GODIYA

Dukkan godiya su tabbata ga Allah (S.W.T) Ubangijin Talikai bisa ni’imominsa bayyanannu da boyayyu, wanda da ikonsa ne da yardarsa na rubuta muku wannan littafin, Allah nagode maka.

GAISUWA A GAREKU DA JINJINA

Dukkan gaisuwa ga yan uwa musulmai maza da mata Allah ya hada mu a Aljannah. Baran manta Daku ba:
Hajiya Saratu (Maman Abdallah)
Hajiya Fatsuma (Maman Iklass)
Hajiaya Fatima (maman salihu)
Hajiya Rukayya (Maman munir)
Hajiya Maryam (Maman dada)
Hajiya Fatima (Maman Shafiu)
Shamsiya aminu umar (maman usaimin)
Shamsiya shuaibu (maman islam)
Sakina umar (Maman Habibullah)

                                            INA KAUNARKU

ina kaunarku ‘yan uwana da masoyana, nagode da soyayyarku a gareni.


                                                     SADAUKARWA

Na sadaukar da wannan littafin ga kannena da ‘yan uwana da iyayena da masoya, Allah ya bar zumunci.

YA ZA’AYI IN MANTA DA KU?

Iyayena abin alfaharina a kullum addu’ata Allah yaja da ranku ya baku tsawon rai mai amfani. Hadiza Wahira da Mallam Abba Gana Kolo, Allah yasa Aljanna ce Makomarku, Ameen.

GABATARWA

Ina gabatar da wannan littafi wanda ya kunshi takaitaccen bayani akan iyaye mata. Domin a hakikanin gaskiya iyaye mata sun bambanta, Allah yasa mu dace, Ameen. Wannan wata fadakarwace ga yan’uwa mata zalla, ko zasu fadaka daga gurbatattun dabi’un da sukeyi a gidan aurensu. Muna rokon Allah ya daidaitamu bisa bin hanya madaidaiciya kuma ya shiryemu ya sanya mu cikin bayinsa salihai Ameen.

---------------------------------------------------------------------------------------------
do you want to learn how to blog and also make money online check this site
Share:

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).