shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday 30 January 2016

BANA KAUNARKA!!! 11

bana-kaunarkajpg.jpg

BANA KAUNAR KA!!!



11


MUHD-ABBA~GANA

ya harare ni ban sani ba ya sassauta murya wahida kome ya fito daga bakinki zan iya cinsa har in nemi kari nai tsaki ni dana ji ance sojoji zuciya gare su ko wannan bashi da zuciyane nai tsaki a fili nace bani da lokacin aure amma ka like kamar tsohon maye ina gama fadar haka na bar masa dakin,yau ma ina zaune ya shigi yana shigowa ya tsugunna yace good morming my sweet heart na mike cikin fushi kai tsaya kaji BANA KAUNARKA dama haka kake son in fada to na fada BANA KAUNAR KA so what? ya rike baki cikin mamaki nai tsaki tare da murguda baki na juya zan fita ya finciko ni na fada kirjinsa a hanzarce na dago cikin zafin nama na fidda hannu na sharara masa mari na ce kar ka kara taba ni ko an fada maka nima irin yan iskan yan matan nan ne niki ka mara wahida? an mare ka who are you? mahida ta shigo a fusace ta finciko ni ta kai min mari tare da hande ni tace shegiya mara mutunci don kinga yana sonki, da gudu na fita ina kuka nai dakin yaya amin,mahida tace don Allah shahid kayi hakuri hannu ya daga mata tare da ficewa ina shiga yace wa kuma ya taba ki? nai shiru mahida ta shigo yace mahida me kikai wa yar uwarki? yaya wallahi wahida bata da mutunci bata da kunya ya shahid fa ta mara mari wahida! shahid din kika mara? to me yasa zai dinga yi min naci nace bana kaunarsa dan me zai takura min ko ana dole a so ni wallahi.......tswa ya daka min cewa nai me yai miki? to meyasa zai dinga yi min naci shi kenan zan masa magana amma ki bar saurin marin babba ko zaki iya marina? na girgiza kai na ce na daina yaya ya mike ya shiga wanka na kalle take kuma munafika meye dalilin na marina na mare ki dan kuma na isa ne karki ga na kyale ki yanxu wallahi kika kara marina sai na ram........kan in karasa ta kuma marina,tuni fada ya kaure muka kama fada ya faruq ya shigo la! fada kuke yi ba za ku bari ba sai na zane ku ko da taga na sata kuka sai ta ruga gun mom tana kuka sosai mom tace zo auta me ya hada ku? nace mum marina tai nima na rama mum ita fa yaya shahid ta mara mari wahida? to me yasa zai takura min nace bana kaunarsa anya wahida baki da kunya to mom,mom ta ture ni ba ruwana dake mara kunya me zagin manya la! mom ba fa zaginsa nai ba tunda kika mare shi wata rana zaginsa zakiyi,Allah mom bazan kara batun daga wannan ran ban kara sa bom boy a idona ba ni kan hakan ya fiye min sauki ina falonmu mom tace wahida zo in aike ki gidan sister khadiya tana nufin gidan anti nace to mom mum ta bani sakon a motar mahida na tafi ina zuwa nai fakin na fito nai sallama falon yana kwance kan 3 sitter nai wuce wata dakin antin ina ji yana ba gaisuwa wahida? nai masa banza nai sallama dakin antin sai gashi ya shigo yana fadin anti bata nan na juyo zan fita sai ya tare kofa bana son wula............



MUHD-ABBA~GANA

www.abbagana.pun.bz
Share:

Thursday 28 January 2016

BANA KAUNARKA!!! 10

bana-kaunarkajpg.jpg

BANA KAUNAR KA!!!





10





MUHD-ABBA~GANA


bayan kwana biyu da yin maganar ina zaune dainmu ina karatun wani littafin addu'o'i ya shahid yai sallama na amsa ciki-ciki'domin yanzu haushi yake bani ya zauna kusa dani bai magana ba sai da ya shafe kusan minti goma sannan ya kalle ni 'ba ki iya gaisuwa ba ne ?na dago " sorry na manta ka tafi lafiya? gani nan lafiya ba lafiya ba lafiya nan da sauki wahida ina son muyi wata muhimmiyar magana okey ina jinka wahida kin san ina sonki ko? what nikake so? wahida me yasa kike son wahalar da dan uwanki...? ban gane nufin ka ba kin san mahida ta zabi dan uwana a matsayin abokin rayuwarta ina so kema ki sauke ra,ayin son karatu ki amince min billahillazi nayi alkawarin barin ki ki ci gaba da karatunki nai murmushi shahid kenan na fada maka bani da lokacin soyayya kwata-kwata ba zan iya hada karatu da soyayya ba shikenan zan iya jiranki ko nan da shekara goma ne no ka nemi wata kawai wahida kin san kuwa irin azabar da nake ji? oho kai kaso ka don haka bbu abinda ya demeni domin na fada maka gaskiya wahida nifa dan uwankine wahida me yasa ba kya sona in wani hali nake dashi wanda ba kya so dan girman Allah ki fito ki fada min kaga na farko bbu abin dana tsana irin shan taba kai kuma kana shan taba,maganar gaskiya ina zarginka da abubuwa da dama shahid ko ba haka ba dama ance sojoji suna shaye shaye kuma suna neman mata wa'iyazu billahi yace tare da mikewa ya cillo min kati gashi nan na baki cikakken sati kiyi bincike a kaina bayan taba me take sha tabar ma koki ka sank sha amma insha Allahu daga yau na barta har abada yana gama maganar ya fice jiki babu kwari.tunda wannan lokacin na shiga bincike kan bom boy har har sati biyu amma ban ga wani aibunsa ba in ban da da yake samu gun jama,a da dama sai dai wani abu ko kadan bana jin sonsa sai ma hausinsa da nake kara jiba kamar in na tuna shi soja ne kuma mugu ne na karshe domin bana mantawa ina karama mugun tsoransa nake innai abu aka ce za a fada wa shahid na kanyi kuku domin ban bashi da wasa gashi da girman kai rashin son magana yanzu ne fa da yake sona yake sakar min iska ni na san yana aurata zai daina sakar min fuska koda dama ance matar soja sai hakuri.kamar kullum ina zaune ya shigo da sallama tun kan ya karaso kamshin turaransa ya cika dakin kai gaskiya ina son turaransa haka nan kamshin kan sani farin ciki ko da kuwa ina cikin bacin rai gashin ban san sunan turaran ba bare in siyo gashi ina ganin kamar zubda ajine in tambaye shi sunan turaransa,kamar kar in amsa sallamar sai kuma na tuna girman sallama da darajarta sai na amsa ciki ciki na janyo remote na kunna T.V domin ta taya shi hira na mike domin in bar masa dakin suyi hirar da T.V caraf ya kamo hannuna sai naji hannunsa dumi ga wani irin taushin ji nai kamar in kwace hannun don wani irin sanyi dadi naji yana ratsa zuciyata na daddage na tofa masa yau a hannu ya daga hannun a tunanina mariina zai ko ya goge min yawun a jikina amma sai naga akasin haka domin ganina yasa harshe ya lashe yau din yace baki san yawunki yafi ice cream ba a gurina na yamutsa fuska ashe kai kazami ne??


MUHD-ABBA~GANA

www.abbagana.pun.bz
Share:

Wednesday 27 January 2016

BANA KAUNARKA!!! 9

bana-kaunarkajpg.jpg

BANA KAUNAR KA!!!




9




MUHD-ABBA~GANA



tana miki sannu ina amsawa baku biya ta gidanmu ba? mun biya mom da anty sunan nan zuwa ya haidar don Allah ku bani sallama naji sauki sai gobe na tura baki ni wallahi tafiya ta zanyi ki fita mana mu gani asibiti din da karnuka cinye ki basai in ari bindiga gun ya shahid ba in sn biyo ni in harbe su dariya suka dinga yimin ya shahid ya zauna bakin gadon kusa dani ya janyo ledar da suka shigo da ita ci mata ce tarkacan kayan zaki aikuwa tuni na shiga lashe-lashe haidar yace um su wahida ba dai kwadayi ba bom boy ya kai masa duka tare da fadin akwai wacce takai mahida kwadayi yarinyar da take cin faea naga alamar ka raina wahida,wahida fa antinka ce Allah ko Allah matar yayanka ce tunda ga lokacin ban kara magana ba har suka karaci surutunsu suka fice,koda naji shiru gashi ni kadai tsuru ai sai na zari mayafina na fice nayi sa'a likitocin bbu wanda ya ganni na zagaya ta baya kamar wadda tazo dubiya na fice ina fita na samu me adaidaita sahu na shiga sai gida ko kudin ban bashi ba na fice sai me gadi na ya bashi ina shiga na tadda suna shirin fitowa har anty tazo ina shiga mahida tace mom kinga wahida ta dawo da sauri suka fito wahida wa yace ki taho? to mom sai a barni ni kadai ni kuma naga naji sauki nai tahowata ai shikenan ke da al,amin.bayan kwana biyu abba ya tara mu yana son jin ra'ayin kowa,ya amin yace ni dai abba ba yanzu zanyi aure ba asali ma niko budurwa bani da itw ai min afuwa zuwa nan gaba Abba yace faruq ya faruq yace abba aure zanyi don na samu wadda nake so wacece a ina take? abba mamy ce yar baba rabi,u da kyau inji Abba mahida ina jinki nima abba na samu wanda nake so haidar din anty da kyau wahida ina jinki tuni nai raurau hawaye ya soma shatata,abba yace ban da kuka cikin rawar murya nace Abba ni karatu zanyi ya faruq yai farat yace ba wani karatunda shahid za,a hada ku ai kuwa na saki kuka ni wallahi bana sosa karatuna zanyi abba yace yi shiru bbu me yi miki dole yadda kowa ya ce ga wacce yake so ke ma sai kin furta sannan zan hada ki da wanda kike so abba kana ji ya faruq yace da ya shahid za,a hada mu rabu dashi bbu me yi miki auran dole ni a ra,ayina bani da niyyar tauye muku hakkinku duk da ina da right din da zan zaba muka maxan da suka dace daku amma nafi son ku kawo da kanku tunda kin zabi karatu Allah ya bada sa,a Allah kuma yai muku albarka amin ya faruq bai so haka ba domin so yai ko ina so ko bana so a aura min bom boy,koda abba ya tara yan uwansa ya fada musu ra,ayin ya,yansu sunyi farin ciki ainun sai dak sun so ace wahida ta zabi shahid ko da abba ya fada musu ra,ayin wahida na son karatu sun yi na,amm sannan sunyi mata fatan alkairi shi kanshi yaji dadin yadda yan uwan nasa sukayi na,am da ra ayin wahidar dama su yake ji domin in sun tubure sai wahidar ta amince da shahid din dole na ta amince ko bata so domin yayansa alh.rabi,u zai iya cewa ba a isa ba dole abi son ransa.



MUHD-ABBA~GANA


www.abbagana.pun.bz
Share:

BANA KAUNARKA!!! 8

bana-kaunarkajpg.jpg

BANA KAUNAR KA!!!



8




MUHD-ABBA~GANA


ya alamin ya zauna tare da cewa ke naki ba zai zo ba ne ,ni rufa min asiri ni bani da kowa asalima ni yanzu bani da lokacin soyayya yace kamar ni kin gani aure baya gana ni kan ba yanzu zan yi aure ba nima gaskiya nafi so nayi karati sosai gaskiyarki my sister amma naga shahid yana sonki sosai ko ba kya son soja ne? ni dai gaskiya yanzu bazan ce ina son shi ba domin karatu nasa a gabana to Allah ya taimaka mana,da safe kamar kullum na shiga dakin mom nagaishe ta nace mom ya zancan karatunmu? a,a sai dai ki tambayi abbanku na mike da sauri
[10:07AM, 1/27/2016] A.➖GANA: na shiga dakin abbanmu nayi sallama ya amsa min yana zaune kan abin sallah na zauna kusa dashi nace abba ina kwana lafiya lau sister usaina na bata rai gaskiya abba bana so acemin usakina to ya sunanki? ni sunana fa wahida abba ya zancan karatunmu? haba sister wahida wanne irin karatu kuma eh abba to kia min yar uwarki inji raayinta ina shirin fita ta shigo bayan ta gaida abba yace dama yar uwarki ce take so kuci gaba da karatu amma yaya kika gani? ta sunkuyar da kai sannan ta soma magana abba gaskiya ni aure zan........na zabura na mike mahida kina da hankali aure! aure fakikace? kuka ne ya kwace min ni kaina ban san dalilin kukan ba abba ne yai ta lallashina har nai shiru amma zuciyata kamar ta fashe don bakin ciki abba yace mahida menene hujjarki na kin karatun sannan batun aure wakike so? dan waye?aina kuma yake,abba munyi dashi zai barni na cigaba da karatuna nace waye shi? abba ya haidar ne dan anty....da kyau mahida Allah yai muku albarka. kefa wahida wallahi ni ba zan yi aure yanzu ba har nawa nake ni gaskiya karatu zanyi mahida ta katse ni da cewa abba wallahi ya shahid yana tsananin son wahida cikin kuka nace shi ya fada miki yana sona? don ni bamuyi dashi ba in ma ya fada miki to ki bashi hakuri dan bani da lokacin soyyaya a yanzu ina gama magana na fice wata dakinmu na shiga na kulle na fada gado kuka nake sosai me yasa mahida zatai mana haka? menene aibun karatun meyasa zata so aure akan karatu muddin ta tauye mana karatunmu wallahi ta cuce mu tuni wani irin rikitaccen zazzabi ya rufe ni kaina na sara min.maganar abba naji yana kiran sunana na mike jikina n karkarwa na bude ya amin yai saurin rike ni don ganin lokacin kankani na zafge abba yace wahida dama baki da lafiya natsunguna don kafafuna ba zasu iya dauka taba ya amin neya kama ni taso mu tafi asibiti abin ka da yar gatan al'amin tuni ya kaita babban asibiti inda aka bata gado hankalin al'amin bai kwanta ba sai da yaga ta samu bacci bayan azahar ina kwance dakin ni kadai sai ga ya shahid da haidar da yake a asibiti din ya haidar aiki sukai sallama na amsa da sauri bom boy ya karaso sannu sister yauwa ya shahid ina anti?



MUHD-ABBA~GANA

www.abbagana.pun.bz
Share:

Tuesday 26 January 2016

BANA KAUNARKA!!! 7

bana-kaunarkajpg.jpg

BANA KAUNAR KA!!!

7




MUHD-ABBA~GANA


mom fada suke yi shine na mike mom ya faruq ya tsane ni baya kaunata baya son bude ido ya ganni ni wallahi gidan zan bar masa mahida tace wallahi nima bin ki zan yi mom ita tai ta lallashinmu da kyar ta shawo kanmu ya faruq ne ya shigo da gudu mom na shiga uku kunama a dakina oho kai ka jiyo alhakin yaranan ma ai ya ishe ka wahida mahida kuyi hakuri abu kamar wasa har abba ya dawo kunaman nan suna nan yai tai wa abba magiya yazo ya cire masa amma abba yace bbu ruwansa,kuma kar ka sake ka kashe su tun daga wannan lokacin muka samu saukin cin zalin da yake mana washe gari ina zaune dakin ya amin shahid ya shigo ya tsunguna gabana ya zuba min ido na kalli kaina ni ban ga abin kallo ba shi dai haka Allah ya yo shi da kallo yaya me yasa kake kallona? gani nai kin girma kinyi kyau nai murmushi na mike na tafi dakinmu a falo na same ta ita da small boy suna hira abinsu kamar su cinye juna dan sona gaishe shi na wuce daki na kwanta ya amin ya shigo sister me ke damunki? me kaga ni gani nai kin kwanta bbu abin da yake damuna to tashi kije inji bom boy na narke ina faman lumshe ido ni wallahi bacci zanyi ki daure kijr kinji kanwata na mike zan fita ya janyo hannuna dawo kisa hijabi ya fice na kallo kaina riga da wando ne ruwan madara rigar ta dan kama jikina gashi masha Allah kirjina ya tumbatsa na yafa mayafi na fita nai sallama ya zuba min manyan idanunsa na sunkuyar da kai sai daya gama jan ajinsa ganin bani da niyyar magana yace min kin wuni lafiya? lafiya ina antinmu? tana gaishe ki ina amsawa na mike ina kuma zaki ba lumshe ido ya shahid bacci nake ji ya miko min wata karamar akwati na amsa nace an gode Allah kara mana dankon zumunchi yace amin,nima na gode da addu'arki gare mu Allah ya amsa,ina shiga daki na bude kayan make up masu tsananin kyau da tsada sai dogayan riguna da takalmi da jaka gaskiya na yaba na kuma gode wa yayana bom boy.ina kwance mahida ta shigo ta zauna kusa dani sister ara min kaset din ki nace gata can dauki ta dauka ta dawo ta zauna hello,ta fada cikin kwantar da murya haba my love kai fa kace min gaka nan kuma naji shiru kiyi hakuri my dear kin san akwai cinkosan ababan hawa amma yanzu na iso ina nan shigowa okey Allay ya kawo ka ta sumbaci wayar tare da fadin i love you,i love you na kalle ta waye kuma my love? wakika sani banda masoyina ya haidar kin san shine zaina shina zaba a matsayin aboki....ya ishe ni tashi ki fita tai dariya wahida kenan ke wa kike so? ya al'amin nake so ko nayi karya? keso fa nace so din al,amin nakeso keso fa na aure nake nufi,oh sai dai a tambayo wa kuka za,a tambayo alhalin kece abar tambaya? ohi miki ya al'amin ya shigo ke mahida small boy na kira kai yaya sunansa fa haidar to ni small naga damar cewa ta kara gyara fuskarta ta fita tana fadin duk ke kika shantakar dani zaki sa in batawa my love nabi ta da kallo baki bude,,



MUHD-ABB~GANA


www.abbagana.pun.bz
Share:

BANA KAUNARKA!!! 6

bana-kaunarkajpg.jpg

BANA KAUNAR KA!!!





6



MUHD-ABBA~GANA




TA rungume mu tana shafar tattausan gashin kanmu ta kalli mahida waya taba min ke? ba wahida bace ta mareni ke wahida ba antinki bace kike dukanta mon fada sukai duk da haka in kun kuma sai na fadawa abbanku nai raurau,Allah mom na daina tace yauwa autata ya amin gaba daya muka fada masa ya rungume mu yana fadin I miss u la! mahida me akayi miki kila yi kuka? ba wahida vace ta duke ni wahida ashe baki da kunya lalle zan miki bulala yaya tsaya kaji fada fa sukai a makaranta mom ce ta kwala mana kira da gudu muka fito ku zo kuci abinci bana so yunwa ta kama min ku nace mahida jekiki dauko mana abincinmu lalle ma wallahi sai dai in kar aci wacece babba? mom ai dai nice babba ko? mom ta girgiza kai tace kinga mahida aka fara haifa ita a gida ke kuma sai da muka je asibiti mahida ta shiga tsalle na mike ina zumbura baki dakin ya alamin na koma yana zaune yana cin abinci na zauna kusa dashi ya kalleni me kuma aka yi miki? ba mom bace tace a hospital aka haifeni shine kuma abin jin haushi yi hakuri zomuci abinci na dau dan spoon ya janyo flet gassassun kajine ya dinga yagowa yana daura mana kan abinci sai dana ji nai hani an ya zuba min madara me sanyi nasha tuni sanyin AC ya kwashe ninna kwanta bacci me nauyi yayi awon gaba dani Al'amin ya kalleni yayi murmushi yace wahida sarkin rigima kenan.

BAYAN SHEKARA TAKWAS lokacin da mukayi candy gaskiya mun fito da sakamako me kyau don haka mun samu kyaututtuka gun yayanmu da iyayanmu a bangaran arabic kuwa munyi sauka yanzu hadda mukeyi.
wayar mahida ce ke ta ruru ina dubawa naga yaya Al'amin salamu alaikum wa alaikas salam,yaya al'amin kaki dawowa ko oh sister bako gaisuwa? la! na manta kina so in dawo ko? eh mana to kizo airport da gaske? eh mana to kizo gobe airport da gaske? mahida ta warcewa yar ya amin da gaske in sanar da mom eh ki sanar mata insha Allahu gobe zan dawo shahid ma yayo min waya wai iya suka zauka amma yana legas sukayi sallama ta kalleni ke shahid ya dawo to ina ruwana,ta kai min duka kar kiyi ruwan,da guduna ina fadin wallahi sai na rama dakin ya faruq taje ta kankame shi tana fadin yaya ka mata magana ya buga min haraea tare da fadin ki kazo nan sai nayi boll dake,wallahi sai na rama wayace a dokeni duk kurarinsa sai da naje na kai mata duka ya dauko belt ya shiga lafta min ina kuka mahida ta rike belt din haba yaya me yasa zaka dinga dukata wallahi kai mugune what nine mugu?? mahida ta tsunguna kalli yadda kaji mata ciwo sai kawai tasa kuka muka dinga kuka yai mana banza ganin kukan namu bbu sauki sai ya daga niyi shiru kinji wahida ta mom ta shigo wai faruq me kai wa yarannan mom wai danna duki daya shine dayar ma ta kama kuka to me dayar tai maka??





MUHD-ABBA~GANA




www.abbagana.pun.bz
Share:

Monday 25 January 2016

BANA KAUNARKA!!! 5

bana-kaunarkajpg.jpg

BANA KAUNAR KA!!!




5

MUHD-ABBA~GANA



SAHURA ta cabe ai ina ganin ko kujerar makka ba zata yiwa rawar kai kamar....kar ku takura min ba dole inyi murna mutumin daya tafi tun ina yar mitsitsiyata yace kixo na mike muka jera nai sallama yana zaune a mota na bude na shiga yaya sannu da zuwa ya zuba min ido ko meye abin kallo a jikina,oho nace ya shahid gani kaina rame ko? ai zazzabi nai.



WACECE WAHIDA??


wahida yarinyace kyakkyawa ajin farko domin mahaifinsu bafulatani ne mahaifiyarsu ma bafulatanar kamaruce a wajen ta kuma suka samo tsantsar kyau tana da manyan idanuwa masu tsananin haske kamar takadda tana da hanci sannan tana da wadataccen gaashin gira baki sidik zara zaran gashin idanu,karamin baki mai dauke da jajayan lips hakoranta masu daukar hankali tana da gashi sosai sannan tana da kyandiri son bata ki ba amma akwai abubuwan jan hankalin namiji kai a takaice de zan iya cewa irin sune qurun ini na duniya inka samu ka huta,(amma fa idan mai hankakice),hannunta ya kamo taushin hannun kar flourn dangote wanda yakan gamsar da mutum, a hankali yace waya yi miki kunshinnan mom ce tai mana nida mahida duk abin dana lissafa muku wahida nada shi to mahida ma haka domin kamarsu daya ko malamansu basa gane su sai dai banbancin su nutsuwa,mahida tafi wahida rawan kai wahida akwai langwai da jan aji sannan tsiwa ita kuma mahida tsokana.wahida kina jina wahida ta daga kyawawan idanunta ta kalleshi ya shahid ka fasa zama sojan? yayi murmushi wahida kenan kina so in zama? ta girgiza kai ina tsoran soja la! daga yau ki bar tsoron soja domin yayanki ma soja ne yaya amma dai baka harbin mutane ko? ina harbin masu laifi mana.....karararrawar da aka kada ne yasa mahida fita da gudu tana fadin nina tafi wahida sai kin taho wata leda ya dauka yace gashi ku raba na amsa nai masa godiya naceya shahid ka gaisar min da anti zata ji ina tsaye har motarsa ta kule ina shiga class na tadda malami yace zo nan daga ina kike? kan in yi magana mahida ta taso taja hannuna muka wuce malamin ya girgiza kai haka nan yaran suna birge shi.ana tashi direba yazo daukar mu na nemi mahida na rasa koda na tambayi kawarta a ina sai ta ce min suna ofis fada sukayi ita da wata haushi ya kamani ina fita na nufi ofis din ina shiga na gansu tsungune gaban malamai na finciko ta na wanke ta da mari nace wallahi kamar a kunnen abba abba fada ko zaki sani nina tafi in kun gama fadan kya taho kuma wallahi zan cewa direba kar ya sake ya dawo daukarki na juya ina jin guntun kukanta malam ne ya kirani zo wahida ki tsaya ta fada mana gaskiya mallam ba zan iya tsayawa ba zan fadawa ya faruq yazo ya dauke ta to shikenan ku tafi gobe kwa dawo. a mota tace wahida don Allah karki fadawa abba kin ga fa ita ce fa ta fara jana,dallacan rufe min baki da dai ace ban san halinki bane ni dai karki fadawa abba ai kuwa sai na fada masa muna zuwa bangaranmu muka wuce mukai wanka mukayi sallah sannan muka nufi dakin mom da gudu muka karasa muka fada jikinta,


MUHD-ABBA~GANA

www.abbagana.pun.bz
Share:

Sunday 24 January 2016

BANA KAUNARKA!!! 4

bana-kaunarkajpg.jpg

BANA KAUNAR KA!!



4





MUHD-ABBA~GANA






KODA mum ta dawo tace ina auta? mahida ta kwashe labarin duk yadda akayi ta fada mata ran mom ya baci tace shikenan shida abba koda abba ya dawo mahida taje yi masa sannu da zuwa yace ina wahidar? mahida ta fede masa biri har wutsiya ya girgiza kai shikenan maza kije gidan sister khadija ki gano ko tana nan mahida ta shirya tsaf sai gidan anty bata same ni ba daga nan tai gidan baba rabi'u nan ma bana nan a gidan atu muna zaune da mamy muna hira ta fado tayi wujiga wujiga domin bata kawo zata same ni gidan atun ba,duk a tunaninta ko na gudu katsina,ta fado jikina dalla can ni kin ban wahala, wallahi ban zaci kina nan ba nice har gidan su mamy.........to ni na aike ki ta kalli mamy tace anti mamy yarinyar nan bata da kunya kin ganta ko yaya faruq bata ragawa ba mamy tace in an bi ta barawo to fa abi ta mabi sahu, in wahida nada laifi ya faruq na da laifi.....ki daure mata gindi nan kenan to ai shikenan abba ne ya turo ni ki tashi mu tafi na mike wallahi babu inda zani in kin ganni a gidannan to dan uwana ya dawo....haka kika ce? yes bbu inda zani shikenan mamy na tafi oho ki gaishe su umma ta gaida aisha zasu ji amma ki sani abba na nan zuwa tai ficewar ta ina jin tashin motarta da yamma muna zaune nida mamy muna hira sai ga su bom boy shi da small boy muna gaisawa na tashi na shige dakin atu ai kuwa banyi cikakken minti goma ba ya shigo ya ya tsunguna gabana yayi kusan minti goma na dago lafiya nace cikin sanyin murya,hannuna ya kama ya murza "my sweet heart, na lumshe ido tare da zare hannuna tunaninme kikeyi?,tunanin big brother okey ni ba kya tunanina haba dai gaka me zai sa inyi tunanin ka shima don baya nan,anya sister har yanzu ba kya sona? haba kana dan uwana in ki sonka ina sonka ainun,zaki aure ni kenan? tambayar tayi min tsauri nace haba dai kana yayan nawa? oh my god me yasa kike wahalar dani kina wahalar min da......" kai dai kaso ka wahalar da kanka domin ban mumafice ka ba na fada maka gaskiya ya dafe kansa wahida gaskiya na ji dadin yadda ya furta sunan kamar a bakinsa aka rada min sunan.

please help me wahida,help me,billahillazi ina tsananin sonki son ki zai iya zama sanadi ajalina.......bana fata kayi hakuri bom boy bani da niyyar yaudarar ka domin sam a yanzu bani da lokacin soyayya asalima ni karatu nasa a gaba ban jira ya kara magana ba na barshi a nan.kwance nake ina tunanin irin son da bom boy ke min tun ina mitsisiya ta har kawo yanzu ba zan taba mantawa ba lokacin muna makaranta primary 5 lokacin ina da shekara tara min fito breakfast a wannan lokacin shekara shida ya shahid baya nan yana kasar Rasha,ina zaune ni da wata yar class dinmu sahura mannir sai ga mahida da gudunta wahida ga yaya shahid wallahi ya dawo gashi can yazo ganinmu na kalle ta shine kike wannan uban gudun kamar wadda akaiwa bushara da kujerar makka??"

-------------------------------------------------------------------
gargadi: ban yarda wani koh wata ya canza koh ta canza wani wani abu diga cikin littafinnan ba, kari koh ragi yin hakan din Almuntahana ne wato haramcaccene, kuma duk wanda yayi ba tare da izinina ba ba,Allah ya isa ,ban yafeba, kuma bazan yafeba. sai sa nake alfahari da tall gate dan Zamu hadu a candin da matashin/budurwar.kuma sai an saka min...



MUHD-ABBA~GANA




www.abbagana.pun.bz
Share:

Saturday 23 January 2016

BANA KAUNARKA!! 3

bana-kaunarkajpg.jpg

BANA KAUNAR KA!!


3






MUHD-ABBA~GANA






KE malama rufe mana baki ina kuma binsa zaki yi mu samu labari na tabbata da nine zan tafi ko kishi ba zaki yi ba mahida tace ya faruq muje gidan su small boy tana nufin gidan su shahid nai tsaki ni gaskiya ba zani ba ai kuwa jin nace ba zani ba yace ai kuwa sai munje koda muka isa gidan kin fitowa nayi nace kaina ke min ciwo sukai ficewarsu shahid da haidar da mamansu wadda suke kira anty suna zaune a falo suna (break fast) anty tace a,a mahida faruq sannunku da zuwa shahid yace ni ban muku magana ba tunda baku zo da wahida ba tare muke tana mota wai kanta ke ciwo da sauri ya mike bari in shigo da ita tasha magani ina zaune na kifa kaina kan sitiyarin ya bude motar ya shigo da sallama tuni kamshi turaransa ya cika ni banda gobe shiru na minti goma na san in na biye ta miskilin mutumin nan sai muyi minti hamsin na dago abin mamaki idonsa fea a kaina cikin sakan biyar na masa kallo sanye yake da farar t-shirt da wando (3 coter) kin tashi lafiya? nace lafiya na maida kaina na kwanta ya kalleni ba zaki shigo ku gaisa da anti ba? banyi magana ba wahida? mahida tace eh kanta ne yake ciwo oh sannu kinji na zauna kan (carpet) ina gaida anti,anty ta ce wai ina Al'amin ne? yanxu muka raka shi airport ya tafi china bom boy yace oho shi yasa wahida take kuka anty tace bom boy kawo mata paracitamol,ya kawo min magani tuni na soma hawaye domin bana son shan magani kasancewar duk sun san halina sai ya ajiye maganin ya kama min kan
koda muka koma gida abba baya nan kuma mon ta tafi unguwa muna zaune muna hira mahida tace gaskiya sister ina son small boy...nai saurin katse ta ai ki ta sonsa ni dai nace bana son bom boy amma kin san aure tsakaninku bbu fashi.........to Abba sai ka aura masa ni kamar kin sani ko ban aura masa ke ba zan sanar da abba irin matsannancin son da bom boy.........kan ta karasa na finciko ta na tsinka mata mari maganar ya faruq naji la! la!! la!!! kika mare ta me tai miki? dan me zata dinga raina min hankali cool down wahida da kyau wai ke wacce irin yarinyace mara kunya iye! mahida ba yayarki bace? ke wallahi ko sunanta naji kin kara fada sai na babbala ki"...to ai saika fada min shekara nawa ta bani ko wata nawa ko kai ba ka fadar sunan ya amin.....da sauri ya finciko wayar soket abin haushi ko gezau ba tai ba ya finciko ta ya cilla kujera ya shiga dukanta tana ihu tana kiran mominta mahida kankame ta tai suka shiga kukan tare, by muhd abba gana, na mike ina fadin wallahi ba gaji gidan zan bari don an ga ya amin baya nan dole aci zalina ina kuka na hada kayana na datse na shiga jan akwati mahida naja gidan kakarmu na nufa wadda ta haifi babanmu ina shiga na tadda mamy' yar baba rabi,u tazo hutu da gudu muka kankame juna,atu kakarmu ta shiga murje ido wa zan gani kamar wahida? atu kenan ni sunana mahida!!!






MUHD-ABBA~GANA





www.abbagana.pun.bz
Share:

BANA KAUNARKA!! 2

bana-kaunarkajpg.jpg

BANA KAUNAR KA!!




2




MUHD-ABBA~GANA






KAYI hakuri abba insha Allahu ba zan kuma ba shi kenan Allah yai muku albarka mon tace "wai ya amin ya fasa tafiyar? ai kin san jirgin sha biyu zai hau ko da naji

WAYE NE ALH SULAINMAN WATO MAHAIFIN WAHIDA DA MAHIDA??


** * *** **
alh, sulainman haifaffan katsina ne kasuwanci ya kawo shi garin kano kasancewar Allah ya sawa abin albarka cikin kankanin lokaci alh sulainman yayi gidan kansa sannan ya gina wani gida daban kasancewar mahaifinsa ya rasu sai mahaifiyarsa nana Aishatu da kanwarsa nana khadija sai yayansa mohd rabiu da kyar ya shawo kan mahaifiyarsa ta yadda ta dawo garin kano shi kuwa dan uwansa wato yayansa dama tuni ya saida shanunsa da gonakinsu shima yaja jari, alh sulainman ya hadu da matarsa haj, maryam can garin kano sun kulla soyayya wadda ta kaisu ga yin aure haihuwarta ta farko ta haifi yaya biyu hassan da hussaini,hassan shine (al,amin) inda usaini yaci (faruq) shekara goma sha shida ta kara haifar biyu hassana (mahida) inda usaina kuma suke kiranta (wahida) sai yayan alh sulainman mai ha daya jal wadda aka sa mata sunan kanwar alhaji sulainman wato khafiya suna kiranta mamy sai kanwarsa khadiya ma wadda take auran wani babban ma,aikacin gwamnati mai suna alh aliyu haidar, haifuwarsu daya jal inda ta haifi yaya biyu hassan shine (shahid) usaini kuma suna kiransa haidar amma sunan ubansa gare shi tsakaninsu Al'amin da su shahid tsiran kwana goma ne dukkanin yaran sun taso cikin tsantsar kulawa sannan sun samu ingantaccen ilimi inda al'amin yake matsayin dan kasuwa domin sana'ar mahaifinsu ya fada sa faruq ma'aikacin kwastam (costom) a turanche shahid soja yake son zama,haidar doctor,sai matan mamy wadda take bautar kasa,mahida da wahida kuma karatun likita suke sai dai yanzu sun dakata ko meye dalili kwaji nan gaba.
mahida ta kalleni kema duk abin da akai miki keki kaja,wai me yasa ba kya son shahid din? kinga mahida kai ki dameni bana sonso ko ana dole a so..? ya Al'amin ne ya shigo yayi shirinsa tsaf ya zauna kusa dani sister zan tafi na kalle shi cikin kulawa yaya sai yaushe kuma zaka dawo? sati biyu zanyi ku taso ku raka ni air port na mike muka daura after drees akan kayan jikinmu muka rufe dan kwalin rigar ya faruq shi yai mana direba domin shi da mahida suna gaba nida ya amin muna baya ya kalleni ni me zan siyo miki? yaya irin man wanke kan nan da ka siyo min wancan zuwan sai kuma sabulai masu kyau koda zai tafi kuka na dinga yi ya rungumeni yana lallashina da kyar muka rabu a motar ma ban yi shiru ba ya faruq ya daka min tsawa.






MUHD-ABBA~GANA





www.abbagana.pun.bz
Share:

Wednesday 20 January 2016

BANA KAUNAR KA!! 1

bana-kaunarkajpg.jpg

BANA KAUNAR KA!
1


MUHD-ABBA~GANA




09039016969


WAHIDA! WAHIDA!! na"am gani nan d sauri na isa "salamu alaikum,yaya gani zauna magana zamuyi da ke na zauna ina kallonsa wahida tsakaninmu babu boye-boye babu munafintar juna saboda Allah me yasa ba kya son yayanki dan uwanki shahid (bom boy)? na sunkuyar da kai yaya zan iya fitowa in fada wa ya al'ami shahid na shaye-shaye?no ba zan iya ba na dago ganin yana kallona duk saina dabarbarce nace haka nan bai kwanta min ba ba kya sonsa kenan? na daga kai...magana zaki yi ni gaskiya bana sonsa...aka banko kofar yaya faruk ne cikin karaji yace ai kuwa dole kiso shahid ko kin ki ko kin so sai....ni dai gaskiya BANA KAUNARSA haka kurum sai a tura min ni wallahi...a fusace yayo kaina da gudu (bedroom) din yaya al,amin ina fadin yaya kai masa magana wayyo yaya al,amin yace kar ka duke ta faruq kar ka taba ta amma ina ya finciko ni yayi bool dani na wuntsila ya kuma kai min kafa al,amin ya rike shi da gudu na fita ina rusar kuka dakin abbanmu na nufa suna zaune suna kallon nigerian film ,mahida tai saurin mikewa ta rike ni sister waya taba ki? jikin mom na fada ina kuka tuni sister mahida ma ta kama kuka da kyar abba ya shawo kaina please i,m sorry baby waya taba ki? ba ya faruq bane mahida maza kira min faruq ta mike da sauri ta tafi ya kazo inji abba wata tsawa ya daka mata ke fita min daga daki ba zan zo ba wato keme yar uwa dan an dole tashi ne za ki shigowa mutane daki bako sallama to koma kiyi sallama ko in ci ubanki mahida ta juya tana gunguni koda tazo sai ta cewa abba ya ce yana zuwa ai kuwa ba ayi cikakken minti goma ba sai gashi yana zuwa yayi sallama abba ya kalle shi faruq me wahida tayi maka? nan take yaya ya fadi duk abin da ya hada mu abba ya kalleni wahida baki da gaskiya dan me zaki masa rashin kunya alhalin shine sama dake? nai shiru maza ki bashi hakuri ko in bata miki rai na durkusa don Allah ya faruq kayi hakuri yai murmushi dana fassara shi murmushin mugunta mahida ta kamo hannuna muka bar dakin suna fita alhaji sulainman ya kalli faruq yace abin da kake yi baka kyautawa ummaru yarinyar nan ka maida ita kamar jaka koda wanne lokaci kana dukanta me yasa? abba wallahi wahida bata da kunya tayi mugun raina ni to ai kai kaja ta rana ka tunda kai kuke wasa dasu me yasa basu raina al,amin ba? kaga ko kadan alamin baya dukansu."





MUHD-ABBA~GANA



www.abbagana.pun.bz
Share:

Monday 18 January 2016

WASIYOYI GUDA BIYAR

shyk-muktar.jpg

WASIYYOYI 5 DAGA MANZON ALLAH (S.A.W).
Manzon Allah (s.a.w) yace:
"Waye zai karbi wadannan kalmomi guda 5 daga
gareni, yayi amfani da su koya sanar da wanda
zaiyi amfani dasu ???"
Sai Abu Huraira (r.a) yace Ni zan karba ya Ma'aikin
Allah.
Sai Manzon Allah (s.a.w) yariqe hannu na ya
maimaita minsu sai yace;
1. "Ka guji aikata sabo, zaka zamo wanda yafi
kowa bauta a cikin mutane.
2. "Ka yarda da abinda Allah Ya baka, zakafi kowa
arziqi cikin mutane.
3. "Ka kyautatawa maqobcin ka, zaka zamo
(cikakken) Mumini.
4. "Kasowa mutane abinda kake sowa kanka, zaka
kasance (cikakken) Musulmi.
5. "Kada ka yawaita dariya, domin yawan Dariya na
kashe zuciya.
SILSILATUL AHAADIISUS SAHIHA 930.
MANZON ALLAH (S.A.W) YACE KA RIQESU KOKA
SANAR DA WANDA ZAIYI AMFANI DA SU.
IDAN KA TURAWA YAN'UWA MUSULMAI BAKASAN
WA ZAI YI AMFANI DA SU BA, KAGA KASAMU
LADAN MUTANE MASU TARIN YAWA.
Share:

NA DAINA SO!!! 48 49 & 50 (KARSHE)

na-daina-so.jpg

NA DAINA SO!!


48-49-50
{KARSHE


Muhd-Abba~Gana





WASHEGARI ban dade da tashi ba sai naji kiran mahaifina bayan naje na durkusa na gaisheshi sai ya fara magana wanda yayi matukar tayar min da hankali mairamu jeki ki shirya yau kotu zamu wajen raba auren ku da yusuf a take naji wata mugun faduwar gaba amma ban bari ya gane ba ,da gudu nashiga daki ina shiga wani kuka ya zomin mai karfi nayi kamar minti 20 zuwa 30 na fito bayan na goge fuskata.

A wannan rananne aka raba aurena da yusuf ma yaudari gaskiya nayi kukan zuci da takaici kuma aka sankaya aurena da ya kabir wata juma,a mai zuwa a kwana biyunan na zama shiru shiru da faruwar al'amarinan amma duk da ba komai nayi farin cikin aurenmu daya kabir haka dai ya cigaba da bani kulawa ta musamman dan na dawo daidai har na fara mantawa da duniyar yusuf.

RANAR JUMA,A ne aka daura auren mairamu da ya kabir Alhamdullilah mutane da dana sun halarci daurin aurensu,kai a yauzu de da alamun tayi dacen miji inji wata tsohuwa ta unguwarsu, a wannan daren a ka kai mairamu dakin mijinta aka wuce aka barta tana ta kukan rabuwa.
bayan shekaru takwas da auren su Allah ya albarka ce su da yara uku mata biyu maza biyu,MAIRAMU DA KABIR SUN ZAUNA CIKIN JIN DADI DA WALWALA.

ALHAMDULILLAH


godiya ta tabbata ga sarkin da ba ayi masa dole,mawadachi,mayalwaci, mai kowa mai komai shine Allah (S,W,T) amincin Allah ya tabbata ga shugaban masu numfashi da sanda rarru shine annabinmu mai cetonmu muhammadu radullulah (S.A.W)


INA KAUNARKU YAN UWANA DA MAKARANTANA NA GODE DA SOYAYYARKU A GARE NI.


muhadu a wani sabon littafina mai suna

"BANA KAUNARKA"


naku har kullum har abada,jikan marubuta, MUHAMMAD ABBA GANA (sharifin~Zamani)! For
correction and advice call me/ whatsapp me @ (09039016969)


Sadaukarwa: AUWAL YUSUF BAUCHI ( DR DAN LELE)

wish you long life and prosperity. Godia ga
dukkan yabo ga sis Aminat & aishat (admin
hausa book page) on facebook! Jinjina gareku
members na::



-Duniyar marubuta Hausa

-novels!


-home of hausa novels


-HAUSA NOVELS

-rayuwan kwaraii

-HAUSA NOVEL

-presdintial villa

-soyayya jigon rayuwa

-sirrinmu

-zumunchi

- hausa literature

-takaicin rayuwa

-novelss

da de wayanda bansamu lissafowa ba love u oll!

Ban manta daku ba members na groups dina
house of novels (1,2,3 & 4)

A karshe Allah yajikan
yan uwa musulmi
dasuka rigamu gidan gaskia! Love You all my well
wishers.
Share:

NA DAINA SO!! 45 46 & 47

na-daina-so.jpg

NA DAINA SO! 45-46-47


Muhd-Abba~Gana



bana shakka amma ba zan yarda ka aure ni ba saboda me? saboda wasu dalilai guda biyu wadanne dalilai......? kyKkyawa ya dace ka nema yar birni ba yar kauye ba kuma budurwa ba bazawara ba mairamu ko da ace kin fi kowa tsufa da kauyanci to ina sonki a haka amma kuma ni........ amma kuma ke me? NA DAINA SO!! NA DAINA SO!! ba komai tunda ni ina sonki......
NA TSANI DUK WANI NA MIJI KUMA NA DAINA SO!! NA DAINA SO!! a guje ta bar wajen tana kuka shima hawaye ne a fukarsa..ai kuwa jikina yayi sanyi kuma naga rashin dacewar abinda na furta na kuma yi alkawarin zan yi kokarin na mance da komai,bayan kamar kwana biyu da misalin karfe goma na rana shigowar ya kabir ne ya kaste ni diga duniyar tunanin da nake bayan mun dan gaisa na danyi shiru sai ya fara maganar sa kamar haka : ki tashi mu tafi kotu wajen raba auren ku da yusuf,a take naji wani takaici ya lullubeni na tashi na fita na barsa a wajen, na tsaya a kofar fita takun sawunsa naji da alamun biye dani yake yaci gaba da cewa Dan Allah mairamu kiyi hakuri ki yarda a raba aurenki da yusuf duk danasan zafin radadin da kike ji na zaman shekarun da kikayi na jiran mijin naki ,a zuciyata na fahimci sonda ya kabir yake min amma a zahiri shiru nayi ina kallonsa kawai yaci gaba da suburbuda zancensa shin mairamu kin san tsananin sonda nake miki kuwa koh ba komai ki yarda a raba auren kuma ki manta da abinda ya wuce sai a lokacin naji bakina yana son magana shin zaka iya dawormin da farin cikin rayuwata? koh zaka iya maida mun shekarun da na kwashe ina jiran dawowarsa ni a gaskiya bazan sake aure a rayuwata ta duniya ba,a fusace yayi magana kada ki kara furta wannan zancen yanda yayi maganar nasan ranshi ya bacci sannan kamar hujjata bata gamsar dashi ba na kyale shi kawai nayi tafiyata ban yanke wani hukunci ba,daga basina shima de wucewarsa yayi sai kuma jikina yayi sanyi amma ban daina jin kunci da takaici a rayuwata ba.


Muhd-Abba~Gana


www.abbagana.pun.bz
Share:

Sunday 17 January 2016

NA DAINA SO!! 43 & 44

na-daina-so.jpg

NA DAINA SO! 43



Muhd-Abba~Gana


duk irin kokarin da mairamu keyi don ganin ta kawar da tunanin yusuf abu ya faskara tunaninsa ne abu na farko da take yi idan ta farka daga bacci kuma tunaninsa ne abu na karshe da take yi kafin bacci yaci nasarar sure ta ita da kanta ta gamsu cewar tana bukatar taimakon gaggawa tun kafin al,amarin ya kai ga wargaza kwakwalwa. by muhd abba gana

** ** **

a wani yammaci kabir ne da mairamu zaune a gefen kogi kan wasu duwatsu mairamu ina mai ba ki hakuri hakurin me? hakuri bisa laifin da nayi wanne laifi kayi? da tun da farko na goyi baya har yusuf ya zama mijinki wannan ai ba laifi kayi ba taimako na kayi na samu abin da nakeso laifi nayi mana tun da na san cewa yusuf ba mutumin kirki bane mai kake son cewa? sannin kanki ne cewa tare muka yi karatu da yusuf abin da kusan duk mutanen kauyen nan basu sani ba shine bai kammala karatun jami'a ba korarsa akayi....... saboda me? saboda wani laifi da yayi wanne laifi? sai da ya dan yi jim kafin ya bata amsa "wata budurwa ya yiwa ciki"


Muhd-Abba~Gana


NA DAINA SO! 44


Muhd-Abba~Gana


duk shiru sukayi kamar ruwa ya cinye su mairamu ce ta katse shirun ba kayi laifi ba yaya kabir don a lokacin ko da ace ka yi min wannan bayanin ba zan fasa aurar yusuf ba watakila ma naji haushinka mai yiwuwa nayi tunanin cewa ko bakin ciki kakeyi min saboda makahon so nakeyi wa yusuf kuma ba zan iya .....kasa karasa maganar tayi ina son ki saurari wata magana wacce magana? ki shirya gobe da safe muje kotu ayi me? a raba auren ki da yusuf raba aurena da yusuf zai dawo min da shekarun dana salwantar? raba aure na da yusuf zai kankare bakin cikin da ya kunsa min raba aure na da tusuf zai dawo min da farin cikin dana rasa a rayuwata? mene ne amfanin raba auren? saboda ki fuskanci sabuwar rayuwa ta hanyar sake yin wani aure? kwarai kuwa wallahii wallahi ba zan kara yin wani aure a rayuwata ba ki daina fadin haka to ai gaskiya ce wannan ba gaskiya bace to wane ne zai yarda ya aure ni? nine kai?? shakka-babu ko kina shakka a bisa irin so da nake yii miki?



Muhd-Abba~Gana


www.abbagana.pun.bz
Share:

Friday 15 January 2016

NA DAINA SO!! 41 & 42

na-daina-so.jpg

NA DAINA SO! 41




Muhd-Abba~Gana



amma zata ji dadi kuwa idan aka ce yusuf mayaudarine? shin yusuf zai dawo? wata rana zai tuna da ita ya dawo? idan ya dawo zai nemi gafararta? idan ya nemi gafararta zata iya yafe masa kuwa? babban abin da yafi ci mata kawo a kwarya har yanzu tana son yusuf kuma tana ji a jikinta kamar ba zata iya daina son shi ba lalle so babbar cuta! kiyi hakuri mairamu na san cewa nayi laifi babba don Allah ki yafe min yusuf ne ya durkusa a gabana yana bata hakuri nima wannan al,amarin ba,a son raina ya faru ba har da hawaye a fuskarsa na yafe maka.........na yafe maka....tana mai kuka ta fadi hakan a daidai lokacin ta farka daga barci cikin talatainin dare sharkaf! jikinta ya jike da gumi takaici ya lillibeta bayan data tuna da mafarkin da tayi tana sa ran wata rana mafarkinta zai zama gaske tana sa ran kwananta ya kusa karewa WASHE GARI DA SAFE tana cikin wanka taji an kwala mata kira tsayawa tayi cak! muryar irin tasa ce.......a,a ba irin muryarsa bace
... muryarsa ce mana kiranta a ka kuma yi a karo na biyu daga can daki ake kiranta hakika muryar yusuf taji.






Muhd-Abb~Gana





www.abbagana.pun.bz

NA DAINA SO!42



Muhd-Abba~Gana


yusuf ya dawo! ya dawo bata hakuri bata damu da wanke kumfar da ke jikinta ba zani ta daura ta fito a guje daga bandaki ta nufi daki arba tayi da kabir tsaye a kofar falo lafiya ya tambaye ta a razane ya...ya..da..wo?? ta tambaye shi a rude sannan kafin yace wani abu taci gaba da magana yayin da numfashinta ke neman dukshewa daga jikinta kamar mai fama da ciwon asima na....na...na jiyo muryarsa ba muryarsa bace muryata ce inji kabir a guje mairamu ta karasa cikin daki don ta tabbatar ba kowa a dakin karo na farko da kabir yaji tsoron kada mairamu ta haukace a sanadiyyar cin amanar kauna a ranar bayan da mairamu ta idar da sallar la,asar lekawa tayi kofar gida a in da ta hangi yusuf tsaye yana yi mata murmushi na san dama zaka dawo kusan da karfi ta fadi hakan yayin da ta nufe shi a guje rungume shi tayi tana kuka ture ta yayi cira kai tayi ta kurawa fuskarsa ido sai a lokacin ta kula mutumin da ta rungume ba mijinta bane kuma ba mijin surayya bane sunansa kallamu kusan duk sa,ilin da mairamu ta kwanta bacci sai tayi mafarkin yusuf a wasu lokuta yana bata hakuri yayin da a wani sa'in yake yi mata wulakanci iri daban-daban jefi-jefi surayya a mafarkin sau da yawa tana kyalkyala mata dariya.



Muhd-Abba~Gana



www.abbagana.pun.bz
Share:

NA DAINA SO!! 39 & 40

na-daina-so.jpg

NA DAINA SO 39



Muhd-Abba~Gana


take tattara tufafinsa wadanda suka yi datti ta wanke masa ta tuna irin yadda take tarairayar mijinta irin yadda take ji da shi kamar tsoka daya a miya amma kuma......... sauri tayi ta dafe gefen kanta sakamakon ciwon da ya soma yi to amma ba yadda zata yi ta hana tunane-tunane kutsawa cikin kwakwalwarta tun bayan yin bikinsu da watanni shida yusuf ya hadu da wata irin rashin lafiya mai zafin gaske kusan duk wani abu da mairamu ta mallaka sai da ya kare a hanyar nema wa yusuf magani akwai wata gona da ta gada daga wajen mahaifinta mutumin da bata taba gani ba saboda ya rasu ne kafin a haifeta har gonar sai da ta sayar don ganin mjinta yusuf ya samu lafiya sannan kusan komai ita take yi masa sakamakon tsamarin da rashin lafiyar tayi sai dai a kwantar a tayar daga karshe dai ya warke daga cikin kashi uku na kudin gonar kashi daya ya tafi a kudin magunguna kashi daya kuma ya salwanta a kudin abinci da kayan cefene yayin da kuma taba shi kashi daya ya ja jari mairamu bani da kalmomin da zan iya amfani da su wadanda zasu iya biyyana hakikanin irin farin cikin da nake yi da Allah ya bani ke a matsayin mata abin da kawai na sani shine ina daya daga cikin wadanda sukayi dacen samun mace ta gari kuma ina yi miki godiya a bisa kokarin da kikeyi min Allah ya saka miki da alkairi shin mai kike so a waje nâ?


Muhd-Abba~Gana





www.abbagana.pun.bz

NA DAINA SO 40






Muhd-Abba~Gana





kayi min alkawarin cewa har abada zaka rike amanata wannan ne kawai burinki? kwarai kuwa na sha yi miki alkawari kuma ina mai kara jaddada miki cewa you are the one and only one' i love you more (kalmar wani i love u karyane injini) shi duk ire iren wadannan kalam da yusuf ya sha fada mata kanzon kurege ne? mai yasa zai yi mata haka ? kudin da ta bashi da shi yayi kasuwanci har kasuwancin nasa ya bunkasa ya yanke shawarar zai je birni ya nemi wani aiki sannan ya ci gaba da bunkasa jarinsa watakila da yaje jarin nasa ya bunkasa watakila a cikin jarinne har ya samu ya auri surayya daga bisani sai data nemi wannan mujallar ta karanta a boye duk da ta san cewa yin hakan ba karamin karin takaici da bakin ciki ba ne a gare ta abin dayafi dugunzuma tunaninta lokacin da dan jarida ya tambayi yusuf cewa shin ya taba yin aure? ban taba yin aure ba!! kuma ba zan kara yi ba! surayyace kadai matata ta haddace maganar daya fada furuci mafi tayar da hankali a shekara shin hakan na nufin yusuf ya manta dani? mairamu ta tambayi kanta a karo na barkatai bata tsammani hawaye a idanunta sai dai hawayen jini..... wanda yace namiji uba ne to tabbas zai mutu maraya.............namiji ba dan goyo bane .........maza kwandon zawo........maza tabarmar kashi.......maza mayaudara .......maza maha'inta!!! ( wallahhi bandan)





Muhd-Abba~Gana





www.abbagana.pun.bz
Share:

Tuesday 12 January 2016

NA DAINA SO!! 38

na-daina-so.jpg

NA DAINA SO!!! 38






Muhd-Abba~Gana






ajiyar zuciyata tayi sai lin da ta tuna cewa har yanzu kabir bai yi aure bs mene ne dalilin daya sa yusuf zaiyi mata haka? duk bayan yan mintina wannan tambayar na yawan bujuro mata har yanzu ta rasa takamaimai yadda zata ta amsa tambayar cin amana? to mene ne dalilin dayasa mijinta zai ci amanarta? saboda ya tafi birni? to ai shi ba bakon birni bane tun da a can yaje ya yi karatu..... saboda ya gano cewa ni yar kauye ce? saboda ni mummuna ce? saboda ni ban waye ba? saboda ni jahila ce? saboda bana yi masa biyayya? ta tuna irin yadda takeyi masa biyayya sau da kata ko wani abu zata bashi ko kuma zata karba da hannunsa sai ta durkusa duk sa'ilin da zata yi magana sai ta tausasa murya kamar wacce zata rera wakar jimami kafin ya tashi daga bacci ta gama shirya abincin safe kafin ya ankara ta kai masa ruwan wanka bandaki a duk sanda zai fita sai ta raka shi har wajen kofa idan ya dawo kwankwasa daya idan yayi kafin yayi ta biyu zata nufi kofa a guje taje ta bude masa ta karbi abin da ke hannunsa bayan tayi masa sannu da zuwa idan babbar riga ce a jikinsa ita take cire masa ta tuna irin yadda take rawar jiki don ganin ta girka masa irin abinci da yafi kauna hannayenta har kanta suka yi saboda daka doya a kokarinta nayi masa sakwara ta tuna da irin yadda a lokuta da dama ba tare da ya sani ba.




Muhd-Abba~Gana




www.abbagana.pun.bz
Share:

NA DAINA SO!! 37

na-daina-so.jpg

NA DAINA SO! 37






Muh'd-Abba~Gana






kusan kullum safe da yamma kabir kan ziyarce ta kamar yadda ya saba tun a baya har soyayya na musamman yake yi mata kasancewar yana da mota ya sa tun bayan da al'amarin ya faru daga lokaci zuwa lokaci ya kan je ya dauki mairamu su fita yadan zagaya da ita wani sa'in har bayan gari suke tafiya su zagaya gona ko su wuce bakin kogi ya kan yawaita yi mata hirarrakin al'amura masu nishadantarwa da ban dariya duk a kokarinsa na ganin mairamu ta manta da abin da ya faru wanda suke karanta a mujalla, har kaset wani abokinsa da ke birni ya aiko masa kasaet din dake kunshe da walima ta musamman da aka yi na bikin yusuf da surayya cikin talatainin dare kabir ya kalli kaset din a inda ya tabbatar da cewa yusuf mijin mairamu mutumin da yayi watsi da matarsa ya tafi birni shine ya auri jaruma surayya bayan da ya gama kallon kaset dinne ya ragargaza shi tare da fatan cewa Allah yasa ka da mairamu ta samu kallon irin wannan kaset din har abada domin yana tunanin idar har ta kalla toba suma zata yi ba rasa ranta zatayi gaba daya abin dake damun kabir kodaya ci nasarar bawa mairamu dariya da zarar ta kammala dariya kawai sai ta fashe da kuka ko kuma a wani sa'in dariya ta rikide ta zama kuka ko a yau kuma a yanzu da mairamu ke zaune ita kadai a falo tana sane da irin fudumuwar da kabir ke bayar wa na son ganinta cikin farin ciki koda kuwa hakan na nufin shi zai zama kyandir ya haska rayuwarta shi kuma rayuwarsa ta lalace.







Muhd-Abba~Gana






www.abbagana.pun.bz
Share:

Monday 11 January 2016

NA DAINA SO! 36

na-daina-so.jpg

NA DAINA SO 36






Muhd-Abba~Gana






makwanni hudu da faruwar al'amarin har yanzu ganin abin take yi kamar wani mugun mafarki mai tsayi wanda har yanzu ta kasa farkawa ta wani bangaren kuma abin yafi kama da mummunan tunanin al'amarin da ba zai taba faruwa a gaske ba sai dai ko a cikin ire-iren tatsuniyoyin mutane masu ikirarin kare hakkin mata ta wani bangaren kuma labarin na kama da ire-iren labaran da ake nunawa a cikin wasannin kwaikwayo na zunzurutun cin amanar mata da mazaje keyi a wannan zamanin abin da har yanzu take yawan tambayar kanta game da wannan al'amarin shin gaske ne mafarki ne, tunanine,tatsuniya ce ko kuma al'mara? sanye take cikin wata doguwar riga har kasa mai launin sararin samaniya kanta babu kallabi zaune take a kan kujera tayi jugum! kamar wacce aka sanar da ita adadin kwanakin da suka rage mata a duniya ta rame sosai saboda rashin cin abinci yadda ya kamata kuma ga tunanin wannan al'amarin kusan ko yaushe na barazanar wargaza mata kwakwalwa kusan tun ranar da wannan mummunan al'amarin ya faru na samu labarin yusuf yayi aure a birni gidan baya rabo da mutane don likita ya bar da shawarar cewa a daina barinta ita kadai ko yaushe gidan cike da jama'a a nata faman raha da barkwanci kamar yadda likita ya bayar da umarni sai dai ita kwata-kwata bata son yin magana balle a je ga batun yin raha duk kuwa da irin kokarin da mahaifiyar da kuma yan uwata suka dinga yi don ganin hankalinta ya kwanta don ganin ta manta da rayuwar yusuf kwata-kwata.






Muh'd-Abba~Gana






vwww.abbagana.pun.bz
Share:

Saturday 9 January 2016

NA DAINA SO!! 29-30-31-32-33-34-35

na-daina-so.jpg

[5:47PM, 1/9/2016] Bana: NA DAINA SO 34






Muhd-Abba~Gana





daga cikin bayanan da yusuf yayi kwata-kwata bai nuna cewa ya taba yin aure ba balle yace ya baro mata a kauye kawai dai yace shi dan asalin kauyen kantafarfara ne wani irin bakin ciki ya kai farmaki zuciyar kabir yayin da ya tuna da irin so da kaunar da mairamu ke yiwa yusuf ya tuna da irin dagewar da tayi don ganin yusuf ya zama mijinta to so shi a lokacin da bashi da komai ya tuna da irin yadda mairamu taki yarda a raba aurenta da yusuf bayan daya koma birni da zama ya barta a kauye,ya tuna da irin shekarun da mairamu ta shafe tana jiran dawowar mijinta amma daga karshe abin da zai yi mata kenan? mene ne dalili? kabir bai yi aure ba sai tsintar kansa yayi yana zubar da hawaye hawayen bakin ciki da takaici hawayen tausayin rayuwar mairamu hawayen bakin ciki shekarun da mairamu ta salwantar tana jiran dawowar wanda ba zai dawo ba hawayen nadamar goyon baya da yayi tun a farko har aka yi wannan aure hawayen rashin sanin ta hanyar da zai bi don ganin ya kankarewa mairamu bakin ciki da bacin rai na shekara da shekaru hawaye abin da ya faru hawayen abin da ke faruwa,by muhd abba gana,hawayen abin da zai faru lamari irin na kauye.





Muh'd-Abba~Gana





www.abbagana.pun.bz
[5:47PM, 1/9/2016] Bana: NA DAINA SO 29






MUH'D-ABBA~GANA






HABA yaya ka...kabir kamar yadda ka ka boye sona a cikin zuciyarka haka zaka boye abin da nake gani a zahiri dukkaninsu shiru suka yi na tsawon wasu tsirarin sakanni yaya kabir don Allah ka daure kaima kayi aure baice komai ba babu kalmomin da zan iya amfani dasu wajen yi maka godiya game da irin dawainiyar daka yi min a rayuwa,amma abin da zan ce kawai shine Allah ya saka maka da alhairi ya saka mana gaba daya ina yi miki fatan alkairi Allah ya baku zaman lafiya ke da mijinki......
ba karamin farin ciki kabir yayi ba yayin da ha ga ma'auratan sun zauna lafiya sai dai shi ya kasa yin koda soyayya balle a je ga batun yin aure ba karamin kaduwa yayi ba sa'ilin da ya samu labarin cewa yusuf zai je birni yana tsoron zuwansa birni saboda..............a'a ai ya shiryu.Allah ya shirye shi ya daina lokacin da aka debi tsawon watanni takwas zuwa tara ba tare da yusuf ya dawo gida ba kabir ya tsinci kansa cikin matsanancin damuwa saboda tunani daya yi na cewar mai yiwuwa yusuf ya koma gidan jiya. karo na farko da kabir ya gane cewar yayi kuskure daya goyi bayan mairamu har ta zama matar yusuf.








MUHD-ABBA~GANA





www.abbagana.pun.bz
[5:47PM, 1/9/2016] Bana: NA DAINA SO 33






Muhd-Abba~Gana





WATA firgitacciyar kara ta kwalla kafin ta dafe kokon kanta da hannu biyu bayan addu'o'in da aka yi ta tofa mata sai da aka kira wani likita yazo yayi mata allura kafin bacci ya ci nasarar sace ta ganin irin yadda jikin nata ke ci gaba da daukar zafi kamar kwanon tuyar da aka dora a kan wuta ya sa da sassafe a ka dauke ta zuwa asibiti asibiti daya ne a kauyen har ruwa aka kara mata kwanakinta uku a asibitin kafin a sallame ta da magunguna baya ga allurai lokacin da mairamu ke kwance a gadon asibiti kusan duk sa'ilin da ta bude ido sai tayi tsammanin ko zata ga mijinta yusuf a kusa da ita ya dawo daga birni bata ganshi ba kabir ya yi matukar girgiza daya samu labarin sanadin wannan rashin lafiyar shima da ya nemi mujallar ya karanta labarin ya bashi tsoro matuka saboda tunanin halin da mairamu zata tsinci kanta a ciki,by muhd abba gana, tabbas yusuf ne! mijin mairamu ya auri jarumar fina-finan hausa! bayan tafiya dayayi ya bar matarsa tsawon shekaru ba tare da ta ji duriyarsa ko da sau daya ba karo na farko da aka samu cikakken labarinsa shine yayi aure a birni har hira da akayi da yusuf a mujallar,sai da kabir ya karanta.





Muh'd-Abba~Gana





www.abbagana.pun.bz
[5:47PM, 1/9/2016] Bana: NA DAINA SO 30






Muhd-Abba~Gana






BAYAN da mairamu ta bude kofar ne ta tsaya turus!! kamar wacce tayi mugun gamo ba mininta bane ya dawo wata gajeriyar mata ce tsaye a kusa da kofar ba yau ta fara ganinta ba kuma jiya ba karewa ma makota ne babarbariyace ce ana kiranta da hajja gana shi ya sa ta tambaye ta a kidime hajja gana lafiya?? shiru ta dan yi kafin ta soma magana kin tuna kanina mas'ud da ya tafi birni satin da ya wuce? eh na tuna to dazu ya dawo daga birni? ehhhhh shin ya hadu da yusuf ne? hajja gana batace eh koh a'a ba wanda wannan ya taimaka wajen karasa tayarwa da mairamu hankali tabbas hajja gana tafe take da wani mugun labari mairamu ta raya a ranta kuma ga dukkan alamu labarin ya shafi yusuf wani abune ya same shi? hatsarin mota ne ya ritsa da shi? yan fashine suka tare shi? rashin lafiya ce ke damun sa? mene ne wai kam?






Muhd-Abba~Gana






www.abbagana.pun.bz
[5:47PM, 1/9/2016] Bana: NA DAINA SO 32






Muh'd-Abba~Gana





TABBAS jarumar film ce sunanta surayya to mene ne hadin wannan fisararriyar buduwar da mijina? cikin daga murya mairamu ta fadi hakan bayanin ba shi da dadi" fada min ko mene ne aure suka yi da yusuf ta soma ja da baya kamar wacce ake nunawa mutuwa yau satin su biyu da aure inji hajja gana karyane!! karyane!! karyane!! wallahi karyane! yusuf ba zai min haka ba babban burinta a wannan lokacin shine kawai kasa ta dare ta fada ko kuma rufin gidan ya ruguzo mata a kwanya to amma ko ba komai tayi farin ciki sa'ilin da wani matsannancin duhu ya soma lilliba bargo a kwakwalwarta lokaci guda numfashinta ya soma dakushewa daga jikinta har ta kai ta kawo ta gaza ci gaba daja da bays abu na karshe da zata iya tunawa shine hajja gana ta nufo ta da hanzari da zummar ta ringumeta don hana ta faduwa amma ta makara

* * ** **


cikin talatainin dare mairamu ta bude ido farfadowa tayi daga dogon suma?ko kuma farkawa tayi daga bacci mai dauke da mugun mafarki? kwance take a kan gado mutane kewaye da ita ga dukkan alamu addu'oi ake karanta mata yayin da mahaifiyarta ke karanta Al-KUR'ANI.hakika abin da ya faru ba mafarki bane babban takaicinta a cikin jama'ar dake wajen bata ga mijinta yusuf ba yayinda ta tuna da hoton bangon mujallar nan take kanta ya soma yin wani irin ciwo yayin da a sa'i guda matsanancin zazzabi ya lillibe ta maganganun hajja gana ne suka soma sintiri suna barazanar wargaza mata kwakwalwa a cikin mujallar nan aka yi bayani tun sati biyu da suka wuce aka daura auren wannan shahararriyar jarumar......ya aure ta ya ma riga ya aure ta ya aure ta!! ya aureta!! ya aureta!!!






Muhd-Abba~Gana





www.abbagana.pun.bz
[5:47PM, 1/9/2016] Bana: NA DAINA SO 31






Muh'd-Abba~Gana






fada min mai ya faru? ya hadu da yusuf ne? a'a bai badu da shi ba amma....... amma me? kiyi min bayani mana wata mujjaa ya siyo......mujalla? shi mas'udun? eh a daidai lokacin hajja gana ta mikawa mairamu wata mujjalla cikin rashin fahimta mairamu ta karbi n
mujallar ta duba bangon hoton data gani a jikin bangon ne yasa saura kiris mujallar ta subuce daga hannunta hoton mijinta ne!!!!! dogo mai doguwar fuska fari mai fararen idanu siririn saje da dan madaidaicin gashin baki daya bari ne ya nemi ya mayar da shi jami'in tsaro yayi matukar kara kyau fiye da yadda ta san shi idan har akwai abin da bai sauya ba a tare da shi to bai wuce irin murmushinsa ba hoton da ta gani a kusa da yusuf ne ys sata ji kamar an doka mata tabarya a kirji domin hoton wata kyakkyawan budurwace mai siffa irin ta larabawa itama budurwar murmushi takeyi kamar yadda yusuf dinke murmushi sai daga bisani ta lura da cewa yusuf din rike yake da hannun wannan budurwar......shin a ina ta taba ganin fuskar wannan budurwar? rudewar da tayi ba zai iya barinta tayi wani kyakkyawan aiki da kwakwalwan ba hajja ga.....gana.me....mene wannan? kin gane wannan budurwar ? ba....ban gane ta bs wa cece???????






Muh'd-Abba~Gana






www.abbagana.pun.bz
[5:47PM, 1/9/2016] Bana: NA DAINA SO!35






Muhd-Abba~Gana





cikin kankanin labari ya karade mutane da dama sun girgiza da samun wannan labari wasu ma har da zubar da hawaye saboda tausayawa ga mairamu yayin da kuma wasu ke korafin cewa laifintane data riki namiji uba , tuntuni an bata shawara taki yarda inji wata mata a taron biki, yanzu ai ta gane cewa namiji ba dan goyo bane inji wata tsohuwa,to yanzu ya zatayi?,wani mai sayar da itace ya tambayi abokinsa amma har yanzu fa bata tsufa ba, cewar wani saurayi a majalisar yan zaman kashe wando,amma gaskiya yaci amanar yarinyar nan wani dattijo ke fadawa abokinsa a kan hanyar su ta zuwa masallaci idan yar uwata ce har birni zan tafi naje na yi masa mugun duka inji wani mafarauci nida za ta amince ma ai da sai na aure ta inji wani mafi talauci a kauyen haka dai labarin mairamu yazo kanun labarai kusan ko'ina tun daga cikin masallaci zuwa kan hanya majalisun samari da dattawa balle kuma taron dake hada mata ko kuma yan mata tun ina budurwa mijin nata ya gudu ya barta watar mata mai yaya hudu take bawa wasu yan mata labari amma ga dukkan alamu ya zama mai kudi inji wata daga cikin wadanda ake bawa labarin mai yasa kika fadi haka? mai magana ta farko ta tambaya, saboda jarumar film din ya aura ni abin ma daya fi bakanta min rai kenan karo na farko da wata daga cikin wadanda ake bawa labarin tayi magana aduk fadin birnin ya rasa wacce zai aura sai mai yin wasan kwaikwayo" kusan duk inda mairamu ta tafi ana zundenta wasu ma har dayi mata jaje kamar wacce aka yiwa gobara a kan haka ta yanke shawarar daina fita ko'ina sai in da wani kwakkwaran dalili.






Muhd-Abba~Gana






www.abbagana.pun.bz
Share:

Thursday 7 January 2016

NA DAINA SO!! 28

na-daina-so.jpg

NA DAINA SO!!28






Muhd-Abba~Gana





da farko kusan duk gidan basa kaunar al'amarin to amma sai kabir ya tsaya kai da kafa har ya bayar da shaida a kan cewa yusuf mutum ne na gari tun da tare sukayi katun jami'a a birni kuskure mafi girma daya yi a rayuwarsa kawai don ganin mairamu ta samu abin da take so.by muhd abba gana



* * * * *
bayan daura auren YUSUF DA MAIRAMU daren tarewa kafin yan kai amarya su zo mairamu ce ta shiga dakin kabir a inda ta iske shi zaune a kan kujera yayi tagumi ga dukkan alamu yana cikin wani yanayi na damuwa yana ganin taya sauke tagumi da yayi sannan yayi kokarin nuna alamun farin ciki ta hanyar sanya fara'a a fuskarsa amma idanunsa sun tona masa asiri amarya mai...mairamu amarya ba kya laifi ko kin kashe dan masu gida......ba shi da zabi illa yayi shiru saboda ba zai iya ci gaba da magana ba zumbur! ya mike tsaye yayin da yaga hawaye a fuskar mairanu me...mene ne kuma abin yin kuka? ba...bayan yau ranar farin ciki ne? to ai kaima kuka kakeyi yana taba fuskarsa kuwa ga mamakinsa sai ya ji hawaye ba.....ba hawaye ba"






Muhd-Abba~Gana






www.abbagana.pun.bz
Share:

Wednesday 6 January 2016

NA DAINA SO!! 26 & 27

na-daina-so.jpg

[8:19PM, 1/4/2016] abba gana: NA DAINA SO 26






Muhd-Abba~Gana






kin tabbata? shakka bbu na tambaye ki mana Allah yasa na sani sai da ya dan yi jin kafin yayi magana tun yaushe kika fara son yusuf? gaskiya an dade tun lokacin da kuke karatu a birni amma ya akayi ban sani ba? ba tare da ya shirya ba kawai ya ji yayi wannan tambayar saboda yawanci a hanya muke haduwa kin tabbata kina sonshi sosai? ina son shi fiye da yadda nake son rayuwata a zuci taso ta furta hakan amma muryarta taci amanarta yaya kabir ina so ka taimake nina auri yusuf domin ina kaunarsa fiye da yadda kake zato ina alfahari da kai na san cewa bani da dan uwa kamar ka mai kaunata kuma mai kaunar abinda nake kauna don haka ka taimaka ka tsaya kai da fata don ganin cewa yusuf ya zama mijina don idan ba yusuf ba.......' kasa karasa maganar tayi to amma alamun da kabir ya gani a fuskar mairamu ya taimaka masa wajen karasa maganar a zuciyarsa .....idan ba yusuf ba zan taba yin aure ba idan ba yusuf ba ba zan taba jin dadin rayuwar nan ba ...........idan ba yusuf ba mutuwa zanyi"" kabir baya son ganin rayuwar kanwarsa cikin tashin hankali a bisa wannan hujja ne kabir ya fasa bayyana wa mairamu sirrin dayayi niyyar fada mata game da rayuwar yusuf.







Muhd-Abba~Gana






www.abbagana.pun.bz
[8:19PM, 1/4/2016] abba gana: NA DAINA SO 27





Muh'd-Abba~Gana






yana fatan Allah ya shiryi yusuf duk wanda ya rufawa wani asiri to shima Allah zai rufa masa kuma mairamu na matukar son yusuf mairamu kin tabbata shima yusuf din yana sonki sosai? kwarai kuwa wani irin tausayi ne ya lillibe kabir tausayin mairamu rashin sani yafi dare duhu inji yusuf a zuciyarsa da ace mairamu ta san ko wane ne yusuf bala........ da ace mairamu tasan dilin da yasa aka kori yusuf bala daga jami'a lokacin da suke tsakiyar karatu...da ace......... a lokacin da mairamu ta bayyana cewa yusuf take so haka kawai mutanen gida suka ji basa son saurayin haka kawai ni saurayin bai kwanta min a rai ba mahaifinta ke fadawa mahaifiyarta saboda me? yana da wani abune? yana ma daga cikin samarin da ake yabawa da halayen su tun da tare da kabir sukayi karatu a birni.





Muhd-Abba~Gana





www.abbagana.pun.bz
Share:

NA DAINA SO!! 25

na-daina-so.jpg

NA DAINA SO 25





Muh'd-Abba~Gana






"eh"ta ba shi amsa tana mai sunkuyar da kai aina san shi..... ya fada min tare kukayi makaranta a birni tabbas haka ne amma a zuciyarsa sai yace na san bai fada miki bin kunya daya taba yi ba wanda ta dalilin haka aka kore shi daga jami'a yaya kabir! ta tari hanzarinsa na'am mai yasa a gida baka fadi gaskiya ba? gaskiya game dame? sai da ta dan kawar da kanta ba cewa matsalar daga.......daga ......ni ai wannan ba matsala ba ce mairamu ni mai son abin da kike sone kuma ba naso aga laifinki duk da cewar don baki amince kin aure ni ba ba wani laifi kikayi a addinance da al'adance ba to amma kin san yadda mutane suke yanzu nan sai wasu su fara yin wata irin fassara amma yanzu kin ga cikin hikima da azanci na janye maganar ba tare da anyi ta gutsuri-tsoma ba to shin da gaske akwai wacce kayi alkawarin aure kamar yadda ka fada? bbbu to amma dai ai kana da budurwa ko? naso nayi budurwar amma na kasa yi ( ashe muna daya dan uwa) saboda me? saboda ke nake so ya fadi a zuciyarsa amma a fili sai yace saboda ba yanzu zan yi aure ba sai na samu wacce take sona sosai.......ai zaka samu,, hmmmm! a matan yanzu kam zayyi wuya





Muh'd-Abba~Gana





www.abbagana.pun.bz
Share:

NA DAINA SO!! 24

na-daina-so.jpg NA DAINA SO 24 Muh'd-Abba~Gana kuma makaranta daya suka yi ti shin mene ne abin yi? yaje ya gamu mAiramu ya sanar da ita gaskiyar lamari game da mutumin da take so ko kuma kawai yaja bakinsa yayi shiru? idan ya fada mata zata yarda kuwa? bazata yarda ba saboda irin son da take yi masa wata zuciyar ta gargade shi watakila tayi tsammanin cewwa tsananin kishi ne ya sa ka yiwa abokinsa kaxafi don kawai tayi watsi da shi watakila kuma daga lokacin ta daina ganin mutuncinka har abada, ba karamin dogon lokaci kabir ya selwantar yana tunani ta hanyar da zai bi don ganin wannan al'amarin bai tabbata ba to amma dai daga karshe ya yanke shawarar zai tunkari mairamu da maganar ta wata sigar don ko a mafarki ba zai so ganin mutum mai irin wannan halin ya auri kanwarsa ba babban abin da yafi daurewa kabir kai shine rashin sanin ta yadda aka yi mairamu ta zurfafa son wannan saurayi cikin kankanin lokaci ba tare da shi kabir din ya sani ba to amma lokaci bai kure ba akwai mafita wata rana a gefen wani lambu kabir da mairamu mairamu dama yusuf bala ne masoyin naki? www.abbagana.pun.bz
Share:

NA DAINA SO!! 23

na-daina-so.jpg NA DAINA SO 23 Muhd-Abba~Gana AKWAI wani abu a kwakwasar daya sa ta mikewa tsaye zunbur! kwankwasar ta bambanta da wace take ji a kullum ta jima rabon ta ji wannan kwankwasar tun yaushe? tun shekaru shida baya tabbas shine!! tabbas shine ya dawo! a guje ta nufi kofar gidan bata damu da karon data tsinci kanta tana mai yi da dukkannin abin da ta riska a gabanta ba burinta kawai ta kai ga bude kofa,don gannin tayi ido biyu da burin rayuwarta...tana sa ran ya gama warkewa daga rashin lafiyar data addabi rayuwarsa ta baya tana sa ran ya kara kyau fiye da yadda ta sanshi a baya tana sa ran gannin kyakkyawar fuskarsa cike da annuri tana sa ran tun a kofar gida zasu rungume juna tana sa ran idan ya shigo cikin gida ba zai kara fita ba balle har ya sake yin kwatankwacin wannan doguwar tafiyar tana sa ran.........tana sa ran......tana sa ran......by muhd abba gana ****************** ba karamin girgiza kabir yayi ba sa'ilin daya gane masoyin mairamu ba wai don kishi ba kuma ba don yana bakin ciki ba face sai don wani sirri da ya sani game da masoyin nata wanda ita ba ta sani ba bama itace kadai ba ta sani ba kusan duk mutanen kauyen babu wanda ya san sirrin idan ba kabir ba kuma shima ya sani ne saka makon cwwa tare suka yi karatun gaba da sakandire a birni. www.abbagana.pun.bz
Share:

Tuesday 5 January 2016

NA DAINA SO!! 21 & 22

na-daina-so.jpgna-daina-so.jpg NA DAINA SO 21 Muh'd-Abba~Gana 09039016969 NASAN kina tunanin kamar zan ga kina yi min rashin mutunci to ina mai tabbatar miki da cewa bana daga cikin samari masu karamar kwakwalwa na dauki alkawarin zan ke yi miki addu'a a kan Allah ya tabbatar da alkhairi tsakaninki da wanda kikeso yasa ya zama miji na gari wanda zai ke kula da hakkokikin ki ki cire damuwa daga zuciyarki ki kwanta kiyi bacci sai da safe har ya isa wajen kofa da zummar ficewa daga dakin ya tsaya sakamakon kiran sunansa da tayi yaya kabir na'am to...ka kana da wata budurwar ne? murmushi yayi ba tare da ya bata amsa ba ya fice daga dakin sai dai kafin ya fita sai da mairamu taci nasarar ganin hawaye a fuskarsa. kwanaki biyu da faruwar al'amarin kabir ya bayyana wani labari a gida labarin da ya girgiza kusan kowa domin mahaifiyarsa ya fada wa cewa ya janye maganar son mairamu a yayin data nemi dalilinsa na daukar wannan matakin kawai ji nayi na fasa.....kuma na tuna akwai wata da muka taba yin alkawarin aure a birni ya kawo wannan uzirin ne don gannin bai dorawa mairamu laifin komai ba itama ta fuskanci haka a zahiri ya hakura amma a badini ba zai iya ba babu irin kokarin da kabir bai yi ba don ganni ya cire son mairamu daga zuciyarsa amma abu ya faskara kusan ko yaushe kuma a duk inda yake akwai tunanin mairamu a tare dashi har kokarin yin wata budurwar yayi don ganin ya shafe babin rayuwar mairamu daga zuciyarsa da rayuwarsa gaba daya to amma daga bisani ya gano cewa babu gurbin da wata zata iya samun mafaka ko da ta siyasa ce a zuciyarsa saboda yadda mairamu ta yi mamaya yana ji a jikinsa idan har ba mairamu ba to ba zai iya yin aure a rayuwarsa ba zai mutu tuzuru NA DAINA SO 22 Muhd-Abba~Gana har bayyan sallar magariba ba wani labari shin ko fitowar yamma yayi? mairamu ta tambayi kanta bayan da ta idar da sallar magariba tun la'asar cikita ke gugi saboda azababbiyar tunwar dake addabarta amma ta ki yarda taci komai don ta tsara cewar da mijinta zasu ci tare duk da cewar tana sa ran murnar ganinsa ma kadai zai iya hana ta cin abinci mai yasa har yanzu bai iso ba? karfe takwas na dare agogon dake manne a jikin bangon dakin ya nuna mijinta bai dawo ba to ko fitowar dare yayi? ko motace ta lalace musu a hanya? ko hatsari suka yi? ko yan fashine suka tsare su? bata yi aune ba sai taji hawaye na barazanar fitowa daga idanunta sannan al'amari ne cewar hanyar shigowa kauyen bata da kyau ana yawan yin hadarirrika baya ga yan fashi dake tare mutane daga lokaci zuwa lokaci hadari? yan fashi? tana faran ba daya daga cikin wadannan al'amuran ne......rashin fitowa da wuri? amma mai yasa bai fito da wuri ba? kuma ma...........tunanin dake kwakwalwarta ya datse kusan a lokaci guda numfashinta ya nemi daukewa sakamakon kwankwasa da taji an soma yi. www.abbagana.pun.bz
Share:

NA DAINA SO!! 15-16-17-18-19 &20

na-daina-so.jpg [11/19/2015, 5:01 PM] Äbbä Gãñā: NA DAINA SO 15 Muh'd-ABBA~GANA SHIN mene ne dalilinsa na kin sanar da ni kafin furta maganar a gida? tambaya da ta yi ta munta don a kwanaki biyun nan ko isasshen bacci ba ta samu to amma ko ba komai tana ganin yanxu ne lokacin da zata samu amsar tambayar da ke addabar kwakwalwarta mairamu ya kira sunanta a tausashe na'am ta amsa a sanyaye kin yi mamaki samun labarin? eh mai ya sa ki ka yi mamaki? batace bamai ba nayi mamakin abin da zai saki yin mamakin jin cewa ina sonki a gaskiya mairamu tun kafin na mallaki hankali sosai ina nufin tun iya yaro lokacin dana fara ganin ki naji a jikina cewa ko ba dade ko ba jima wani al'amari zai faru a tsakaninmu na tsinci kaina cikin wani yanayin na son kasancewa tare da ke so ganin fara'a a fuskarki son ganin samun dimbin nasarori a rayuwarki daga bisani na fahimci sunan yanayin da nake ciki so kuma ba son kowa ba face ke na jima ina tunanin ta hanyar da zan bi don ganin na bayyana miki sirrin dake zuciyata na jima ina hasashen ranar daza ta zo na nemi alfarmar samun wani matsayyi na musamman a zuciyarki na kwashe shekara da shekaru ina laluben kalmomin da zan yi amfani da su wadanda za su iya gamsar da ke irin gagarinmin matsayi da martabar da kike da ita a rayuwa ta na so ace akwai yadda zanyi na bude miki ki ga irin yadda kika yi sansani a harabar xuciyata. Muhd-Abba~Gana www.abbagana.pun.bz [11/19/2015, 5:37 PM] Äbbä Gãñā: NA DAINA SO 16 Muhd-Abba~Gana shiru ya dan yi yana mai ci gaba da kallon daguwar kyakkyawar fuskarta mairamu a takaice dai ina mai farin cikin bayyana miki cewa ina so ki so ns hakika son da ban taba yiwa wata ba kuma koda wasa ba zan yi wa wata irinsa ba ina so ki amimci ki zama abokiyar rayuwata ki zama matata nayi alkawarin zaki same ni miji na gari mijin da zai ke kula da hakkin matarsa nayi alkawarin faranta miki rai zan kasance mai nisantar duk wani abi da zai kai ga bata miki rai zan ke tausaya kasance mai nisantar duk wani abin da zai kai ga bata miki rai zan ke tausaya miki zan kasance mai..... yaya kabir karo na farko data kira hanzarinsa tun sa'ilin da ya soma bayani duk da cewar cikin sassanyar murya ta kira shi amma akwai wani abu a muryarta daya nemi dakatar da bugun zuciyarsa na"am ya amsa na tambayeka ? mai zai hana kaba ni izini? nabaki izinin jan ragamar rayuwata don haka zaki iya tambayata komai don Allah mene ne dalilin da yasa tuntuni ba ka taba fada min wannan bayayyan sirrin da ke zuciyarka ba? ga mamakin kabir sai ya ji tambayar kamar ta dan yi masa tsauri sai daya dan yi jim kafin ya gano cewa wannan ita ce tambaya mafi sauki da aka taba yi masa a rayuwarsa saboda babu kalamomin da a hakikanin gaskiya zasu iya bayyana irin matsayin da kike da shi a rayuwata saboda ina ji a jikina cewa ke ma kina jin abin da nakeji saboda in da tabbacin cewa ko yaushe na nemi alfarma a wajen janwata ba zan rasa ba saboda yanzu ne lokaci saboda...saboda...saboda...saboda mairamu dalilan na da yawa daya daga ciki muhimman dalilan da sukasa a yanzu na bayyana maganar saboda la'akari da nayi cewar idan na tsaya kallon ruwa babu abinda zai kana kwado yayi min kafa kuma bazan yarda bishiya ta fito a gidanmu ba amma kuma wani a can gefe yafi ni shan inuwarta dadin dadawa ina tsoron ka da wankin hula ya kai dare mairamu da fatan zan samu masauki sauran furucin ya makale a fatar bakinsa sannan a lokaci guda murmushi murmushin da yake yi ya rikide zuwa wani irin yanayin da aka fi gani a fuskar mutumin dake fama da ciwon hakori hakan kuwa ya faru ne sakamakon alamar daya gani a fuskar mairamu babu fara'a fuskarta....baya ga haka kuma akwai daya fi tsorata shi tagwayen hawaye ne ke zuba daga idanunta kafin ya samu damar cewa wani abu tuni har ta juya a guje ta bar wajen MAIRAMU!!! MAIRAMU!!! MAIRAMU!!!! Muh'd-Abba~Gana www.abbagana.pun.bz [11/21/2015, 9:02 AM] Äbbä Gãñā: NA DAINA SO 17 Muhd-Abb~Gana kwalla mata kira yayi ta yi bata tsaya ba batw waiwayo ba bata amsa ba karo na farko data taba yi masa irin wannan tun a lokacin ya gane cewa akwai matsala karo na farko da wani tsohon ciwon kansa ya dawo masa tun bayan shekaru biyu da warkewa al'amura sun rikicewa mairamu mai yasa tuntuni yaki sanar da ita? sai yanzu bayan ta riga ta kamu da son wani daban hakika duk abinda yaya kabir ya fada na game da irin son da yake yi mata ta amince dari bisa dari musamman datayi ta tunawa da wasu al'amura da suka yi ta faruwa tun a shekarun baya,ta tuna irin yadda tun suna yara yake fifita ta a kan sauran kannensa to mai yasa tun a lokacin bai fada mata ba? mai yasa tun a lokacin ita bata gane ba? rashin sanar da ita laifinsa ne rashin daukan haske laifinta ne kasa bacci tayi a daren ranar cikin talatainin dare ta farka a gefen katifa ta zauna gami da rafka tagumi yaya kabir duk wata budurwa zata so ace ta samu miji kamar kabir saboda kyawawan halayensa ita kanta mairamu zata so yaya kabir ya aure ta da ba don wani kwakkwaran dalili ba ita tana daukansa ne a matsayin wanta dan'uwanta............amma wannan ba dalili bane. www.abbagana.pun.bz [11/21/2015, 9:10 AM] Äbbä Gãñā: NA DAINA SO 18 Muhd-Abba~Gana akwai dalili akwai wanda take so kuma sun yi alkawarin aure kawai dai basu bayyana a fili ba to shin zatace da yaya kabir yayi hakuri? ya nemi wata? mene ne dalili? saboda ni bana sonka......a'a ba haka zata ce ba ya nemi wata,saboda ita tana da wanda take so...an ya zata iya fadar haka kuwa? idan ta fada mai zai faru? idan bata fada ba mai zai faru? ta tuna da irin yadda kabir yake kaunarta ta tuna da irin yadda iyayensa suka rike ta tun tana karama kuma suke ci gaba da rike ta ba tare da sun taba nuna wani bambanci s tsakaninta da yayan da suka haifa ba to ta wacce hanya zata ce bata son dan da suka haifa? ina mafita? kifa kanta tayi a kan katifa tana kuka kafin wani tattausan hannu ya dafa kafadarta da farko tayi tsammanin ko rukayya ce ta farka a sanadiyyar jin gunjin kukan da take yi to amma sa'ilin data dago kai ga mamakinta sai taga kabir ne. www.abbagana.pun.bz [11/21/2015, 9:23 AM] Äbbä Gãñā: NA DAINA SO 19 Muhd-Abba~Gana yaya.....yaya ka...birrr! karkarwa baya ga in'inna a tare da muryarta "mairamu" ya kira sunanta cikin sassanyar murya tabbas shine! ta fadi a zuciyarta toya aka yi har ya turo kofa ya shigo ba tare da taji motsin shigowarsa ba? dadin dadawa a wanne dalili zai shigo musu daki cikin talatainin dare? kasa cewa komai tayi face kura masa ido kamar tana sa ran daga sama ya fado a hankali ya zauna a gabanta fuskantar juna sukayi ki kwantar da hankalinki ba aljani bane don naga irin kallon da kike yi min amma duk da haka kin cancanci a baki lambar yabo saboda jarumtar dakika nuna bakiyi ihu ba kuma baki ji yunkurin gudu ba kasa-kasa yake yin magana saboda yanayin dare nima kasa bacci nayi kuma naji a jikina cewa kema kin kasa yin bacci wannan ne dalilin daya sa na zagayo sai dai bambanci na da ke shine ni bs kuka da hawaye nake yi ba kukan zuci nake yi kuma ina da dalilina nayi hakan.by muhd abba gana ban yi niyyar shigowa cikin dakinku ba to amma kukan da naji kina yi ne yasa ni sauya shawara shiru ne ya dan biyo baya a dan wannan tsakaninne ta sharce hawayen dake fuskarta ""mairamu"" 'na'am ina sonki ki bani amsar wasu yan tambayoyi da zan miki kuma gaskiya na ke son kifada min ba tare da kin boye min komai ba shiru ne ya kuma biyo baya na tsawon wasu tsiraran sakanni. www.abbagana.pun.bz [11/21/2015, 9:35 AM] Äbbä Gãñā: NA DAINA SO 20 Muhd-Abba~Gana mairamu "na'am" a wanne matsayi kike daukata? yaya na kuma dan uwana to ina so ki ci gaba da daukata a wannan matsayin a matsayina na dan uwanki mai kaunarki zan so ace na gan ki cikin farin ciki da walwala duk wanda zai takura miki a duniyar nan to ni abokin adawarsa ne don haka na gano rashin adalci na hukuncin dana zartar dana fada a gida cewa ina sonki ba tare dana tuntube kina ji ra'ayinki game da lamarin ba hakika ban kyauta ba nice ban kyauta ba' ta wacce hanya? da tuntuni na kasa fahimtar cewa kana so na har sai yanzu da......shiru tayi ta kasa karasa maganar "ki karasa maganar mana a maimakon haka kwalla ne suka cika idanunta mairamu nasan cewa ba so na ne ba kya yi ba kawai dai an riga nine shirun dana yine ya jawo min ba komai mairamu ki kwantar da hankalinki ni mutum ne mai saurin fahimta na janye wannan maganar amma har yanxu dan'uwanki ne ni wanda ko yaushe a shirye yake ya tallafi rayuwarki. www.abbagana.pun.bz
Share:

Saturday 2 January 2016

NA DAINA SO!! 13 & 14

na-daina-so.jpg NA DAINA SO 13 Muhd-Abba~Gana tun yana karami ba shi da abokin fada ko musu baya yi balle a kai ga tankiya ko yaushe yana zaune shiru-shiru kamar baya magana yana daga cikin tsiraran samari kauyen da iyayensu suka biya musu kudi suka je suka yi karatun boko a birni tun yana karamin mutum ne shi mai matukar jin tausayi don ko da babbar sallah ba ya iya tsayawa a wajen da ake yanka raguna don yanzu sai ya fara hawaye ba wai dabbobi kadai da tsintsaye yake tausaya wa ba har ma da mutane musamman mata yana daga cikin mazajen daba son ganin ana wulakanta mata,musammam ma ta fuskar tauye musu hakki a mu'amala ta auratayya ya jima yana takaici da tananin ta hanyar da zai bi don gannin an daina dannewa mata yanci a kauyen kantafara amma har yanzu hakarsa bai kai ga cimma ruwa ba daga cikin wadanda yafi tausayi a duniya akwai mairamu mairamu: kanwa a zahiri masoyiya a badini tun kabir na karamin yaro yake matukar kaunar mairamu wacce kusan kanwa ce a gare shi tun da mahaifiyarsa kanwa ce ga mahaifiyar mairamu tun suna yara sun shaku da juna mairamu tana daukan kabiru a matsayin dan'uwanta kuma yayanta domin tana kiranaa da irin sunan da sauran kannensa ke kiransa da shi wato yaya kabir yana daukanta a matsayin kanwa kuma masoyiya domin ya jima da yanke hukunci a kotun koli na zuciyarsa kan cewa mairamu ce zata zama matarsa idan lokacin yin aurensa yayi to amma a yadda ya tsaya ba zai sanar da mairamu sirrin dake zuciyarsa ba har sai lokaci yayi (KUSKURENE!!!) yana sa ran itama tana sonshi (GANGANCINE!!!) ko da bata sonshi to yana da tabbacin zata so shi idan ya nemi hakan ya kasance (HASASHE!!) lokacin da kabir ya kammala karatunsa a birni bayan da ya dawo gida ya ga irin tashen da mairamu take yi da irin yadda samari ke yawan yin hirarta wasu ma a cewarsu a tarihin kauyen kantafarfara ba a taba ganin budurwa da ta kai mairamu farin jini ba a kokarin sa na yiwa tufkar hanci kabir yana ganin yanxu ne lokacin da ya dace ya bayyana wa mairamu sirri da ya jima yana boyewa a zuciyarsa don ayi musu baiko musamman ma da yayi la'akari da abin da mahaifinsa yace na ya fito da wacce yake so kafin karshen shekara yayi aure tabbas yaba da zabi sunanta mairamu sai da ya fara sanar da mahaifiyarsa tayi matukar farin ciki da jin labarin da dan nata ya bata murna kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha tabbas kayi dace da mace ta gari abin da mahaifiyar tasa tace masa kafin taje ta sanar da mahaifinsa hannu biyu mahaifin nasa ya karbi abin don a cewarsa ya jima bai ji labarin farin ciki irin wannan ba nan da nan magana ta bazu a cikin gida na cewa yaya kabir yana son mairamu to amma sa'ilin da kabir ya tunkari mairamu da maganar al'amura suka rikice masa akwai wanda take so!!!! NA DAINA SO 14 Muhd-Abba~Gana HAR BAYAN AZAHAR BAI ZO BA shin ko bai fito da wuri bane? miramu ta tambayi kanta to mene ne ya hana shi fitowa da wuri? aiki ne yayi masa yawa? to wanne irin aiki? tsawon shekara shida bata sa shi a kwayar idonta ba kuma yau din ma da zai dawo gida shin ba zai zo da wuribane? da matsala miramu idan ina tare da ke komai na duniya kan zame min abu kyakkyawa babu wani aiki a duniya nan da zai iya shagaltar dani daga barin tunanin ki kece madubin zuciyata idan ban ganki ba bana jin dadi dadadan kalaman mijin nata yi ta tunawa wadanda a halin yanzu ta kasa gane matsayin su tsakanin zancen mafarki wakokin wasan kwaikwayo da kuma ire iren tatsunkyoyin mutanen farko sai dai har yanxu tana ganin ya dace taci gaba da ba shi uzurin na watsi da yayi da rayuwarta a'a ba watsi yayi da rayuwarta ba kawai dai mantawa yayi da ita a'a ba mantawa yayi da ita ba hasali ma ba zai iya mantawa da ita ba kawai dai rabuwa yayi da ita to shin rabuwa kawai ne? kuma har tsawon shekara shida duk yadda ta kai da son boye laifin mijin nata tana ganin wannan karon baza ta iya kare shi a babbar kotun da ke zuciyanta ba mai yasa yayi min haka? shi kadai ya san amsa har bayan sallar la'asar babu wani labari kusan sau shida a cikin awannni daban daban tana jin kwankwasa a guje take zuwa ta bude kofar gida amma ga karin takaici sai taga babu kowa daga karshe dai ta gano cewa kunnuwanta ne ke zolayanta a halin yanzu babu kuzari a tare da ita bayan gajiya data yi da kaiwa da komowa a tsakar gidan zama tayi a kan tabarma ganin da hada kai da gwiwa tunani ta soma yi na musanman a kokarinta na gano daga inda matsalar ta samo asali a can gefen kauyen nasu a bakin wani wani karamin rafi miramu ce da kabir ke fuskantar juna amma ita mairamu tafi sunkuyar da kai da kallon fuskar dogon saurayinta a lokacin kwananta biyu da samun labari a gida labarin da yayi matukar girgixa tunaninta labarin cewa kabir YANA SONTA!!! Muhd-Abba~Gana www.abbagana.pun.bz
Share:

Friday 1 January 2016

NA DAINA SO!! 11 & 12

na-daina-so.jpg NA DAINA SO 11 Muhd-Abba~Gana shin hakan na nufin duk tsawon shekarun da aka shafe baya gudanar da rayuwarsa cikin walwala da jin dadi? miramu ta tambayi kanta ko dai al'amura sun sauya? ganin har karfe sha biyu rana bai iso ba yasa ta yin tunani ko sai wajen azahar zai iso tana da tabbacin cewa yanzu yana ciki mota akwai nisa sosai tsakanin kauyen da birni don sai an ratsa ta tsakanin wasu dajijjika kuwa hanyar akwai kwazazzabai don haka duk wanda ya bi ta hanyar dole ya gaji koda kuwa a cikin mota yake tafiya bayan da tayi wannan tunanin ne ta tanadarwa mijin nata ruwan wanka zama tayi a kan kujera ta ci gaba da jira tana mamakin irin tunanin da mijin nata keyi a halin yanzu ,WACE CE MARIYA?? an haifeta marainiya a cikin wani kauye mai suna kantafarfara mairamu ta taso a gaban mahaifiyarta wacce itama ta rasu sa ilin da take shekaru shida a duniya wata kanwar mahaifiyarta ce ta rike ta har ta girma a gabanta mallam nasiru malami ne mai almajirai shahararren mutun ne a fadin kauyen sunan matarsa dije mutane ne masu mutunci da girmama jama'a kusan kowa a kauyen yana kaunarsu sune suka rike mairamu cikin aminci da rashin nuna wariya a tsakaninta da sauran yayan ukun da suka haifa. NA DAINA SO! 12 Muhd-Abba~Gana wannan ne dalilin da yasa da yawa mutane ke zaton cewa su ne iyayenta na asali kabir shine babban da ga mallam nasir sai kuma kannensa mata guda biyu rukayya da zainabb rukkayya itace sa'ar mairamu don haka suka taso kawaye kuma aminan juna kusan komai tare suke gudanarwa saboda ko yaushe suna tare da ba don bambancin tsayi da kyaun fuska da mairamu tafi zainab ba to da babu abin da zai hana a kira su da suna tagwaye sun samu kyakkyawar tarbiyya irin ta addini islama kusan kowa na kaunarsu a duk fadin kauyen babu makarantar boko wannan ne dalilin daya sa basu samu ilimin zamani ba a lokacin da suka zama yan mata ne aka soma rububin su (kamar kayan gwanjo) kowa na burin ya samu mace ta gari musammanma mairamu domin Allah yayi mata farin jini fiye da yadda aka saba gani a kan sauran yan mata don ita har daga makwabtun kauyuka ake zuwa neman aurenta attajirai da yayan attajirai shahararrun manoma da mafarauta har izuwa kan yayan masu rike da sarautun gargajiya duk sun yi takara wajan neman aurenta amma ita mairamu tuntuni tayi nata zabin.....dogo ne siriri baki mai dan faffadan hanci baya ga kama a zahiri daya yi da mahaifinsa ya gado mahaifin nasa wajen kyawawan dabi'u musamman ta fuskar zamantakewa da jama'a. MUHD-ABBA~GANA www.abbagana.pun.bz
Share:

NA DAINA SO!! 10

na-daina-so.jpg NA DAINA SO! 10 muhd abba gana muryoyi ne barkatai suka yi ta faman kutse a kwakwalwar mairamu tana mai hasahen irin abin da mijin nata zai fada mata ta san dole zai zo ne yana mai yin fara'a kanar yadda ya saba irin yadda take dokin ganin sa ya sa ta yafe masa laifin da yayi mata duk da cewar bai ma zo ba balle ya roki afuwa ko abinci bata ciba baya ga kokon safe a yadda ta tsara yau tare zata ci abinci da mijinta amma tana sa ran matukar farin ciki ba zai iya barin ta iya cin abinci ba ta tuna da irin yadda a da suke cin abin ci tare wannan yasa wa wannan a baki wannan yasa wa wannan a baki har su koshi ta tuna da irin yadda suke sudewa juna hannu kafin su wanke da ruwa { hmmm aure ni'imar Allah } ta tuna irin yadda a lokuta da dama mijinta ke goya ta yayi ta sukuwa da ita a tsakar gida ta tuna irin yadda suke wasan buya da wasan yar burum-burum a wasu lokuta har da wasan yar carafke,suna matukar son juna sun jima da amanar cewa dayansu ba zai iya gudanar da rayuwarsa daidai ba idan har ba tare da dayan ba. Muhd-Abba~Gana www.abbagana.pun.bz
Share:

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).