shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday, 30 January 2016

BANA KAUNARKA!!! 11

bana-kaunarkajpg.jpg

BANA KAUNAR KA!!!11


MUHD-ABBA~GANA

ya harare ni ban sani ba ya sassauta murya wahida kome ya fito daga bakinki zan iya cinsa har in nemi kari nai tsaki ni dana ji ance sojoji zuciya gare su ko wannan bashi da zuciyane nai tsaki a fili nace bani da lokacin aure amma ka like kamar tsohon maye ina gama fadar haka na bar masa dakin,yau ma ina zaune ya shigi yana shigowa ya tsugunna yace good morming my sweet heart na mike cikin fushi kai tsaya kaji BANA KAUNARKA dama haka kake son in fada to na fada BANA KAUNAR KA so what? ya rike baki cikin mamaki nai tsaki tare da murguda baki na juya zan fita ya finciko ni na fada kirjinsa a hanzarce na dago cikin zafin nama na fidda hannu na sharara masa mari na ce kar ka kara taba ni ko an fada maka nima irin yan iskan yan matan nan ne niki ka mara wahida? an mare ka who are you? mahida ta shigo a fusace ta finciko ni ta kai min mari tare da hande ni tace shegiya mara mutunci don kinga yana sonki, da gudu na fita ina kuka nai dakin yaya amin,mahida tace don Allah shahid kayi hakuri hannu ya daga mata tare da ficewa ina shiga yace wa kuma ya taba ki? nai shiru mahida ta shigo yace mahida me kikai wa yar uwarki? yaya wallahi wahida bata da mutunci bata da kunya ya shahid fa ta mara mari wahida! shahid din kika mara? to me yasa zai dinga yi min naci nace bana kaunarsa dan me zai takura min ko ana dole a so ni wallahi.......tswa ya daka min cewa nai me yai miki? to meyasa zai dinga yi min naci shi kenan zan masa magana amma ki bar saurin marin babba ko zaki iya marina? na girgiza kai na ce na daina yaya ya mike ya shiga wanka na kalle take kuma munafika meye dalilin na marina na mare ki dan kuma na isa ne karki ga na kyale ki yanxu wallahi kika kara marina sai na ram........kan in karasa ta kuma marina,tuni fada ya kaure muka kama fada ya faruq ya shigo la! fada kuke yi ba za ku bari ba sai na zane ku ko da taga na sata kuka sai ta ruga gun mom tana kuka sosai mom tace zo auta me ya hada ku? nace mum marina tai nima na rama mum ita fa yaya shahid ta mara mari wahida? to me yasa zai takura min nace bana kaunarsa anya wahida baki da kunya to mom,mom ta ture ni ba ruwana dake mara kunya me zagin manya la! mom ba fa zaginsa nai ba tunda kika mare shi wata rana zaginsa zakiyi,Allah mom bazan kara batun daga wannan ran ban kara sa bom boy a idona ba ni kan hakan ya fiye min sauki ina falonmu mom tace wahida zo in aike ki gidan sister khadiya tana nufin gidan anti nace to mom mum ta bani sakon a motar mahida na tafi ina zuwa nai fakin na fito nai sallama falon yana kwance kan 3 sitter nai wuce wata dakin antin ina ji yana ba gaisuwa wahida? nai masa banza nai sallama dakin antin sai gashi ya shigo yana fadin anti bata nan na juyo zan fita sai ya tare kofa bana son wula............MUHD-ABBA~GANA

www.abbagana.pun.bz
Share:

6 comments:

 1. We haven't seen a post yau. Yaushe za a mana? It's a nice novel. Good job

  ReplyDelete
 2. khairatt abdulganihu3 February 2016 at 07:18

  wooow

  ReplyDelete
 3. Sabon post please. Muna ta jira. Hope komai lfy

  ReplyDelete

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).