shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Friday, 1 January 2016

NA DAINA SO!! 11 & 12

na-daina-so.jpg NA DAINA SO 11 Muhd-Abba~Gana shin hakan na nufin duk tsawon shekarun da aka shafe baya gudanar da rayuwarsa cikin walwala da jin dadi? miramu ta tambayi kanta ko dai al'amura sun sauya? ganin har karfe sha biyu rana bai iso ba yasa ta yin tunani ko sai wajen azahar zai iso tana da tabbacin cewa yanzu yana ciki mota akwai nisa sosai tsakanin kauyen da birni don sai an ratsa ta tsakanin wasu dajijjika kuwa hanyar akwai kwazazzabai don haka duk wanda ya bi ta hanyar dole ya gaji koda kuwa a cikin mota yake tafiya bayan da tayi wannan tunanin ne ta tanadarwa mijin nata ruwan wanka zama tayi a kan kujera ta ci gaba da jira tana mamakin irin tunanin da mijin nata keyi a halin yanzu ,WACE CE MARIYA?? an haifeta marainiya a cikin wani kauye mai suna kantafarfara mairamu ta taso a gaban mahaifiyarta wacce itama ta rasu sa ilin da take shekaru shida a duniya wata kanwar mahaifiyarta ce ta rike ta har ta girma a gabanta mallam nasiru malami ne mai almajirai shahararren mutun ne a fadin kauyen sunan matarsa dije mutane ne masu mutunci da girmama jama'a kusan kowa a kauyen yana kaunarsu sune suka rike mairamu cikin aminci da rashin nuna wariya a tsakaninta da sauran yayan ukun da suka haifa. NA DAINA SO! 12 Muhd-Abba~Gana wannan ne dalilin da yasa da yawa mutane ke zaton cewa su ne iyayenta na asali kabir shine babban da ga mallam nasir sai kuma kannensa mata guda biyu rukayya da zainabb rukkayya itace sa'ar mairamu don haka suka taso kawaye kuma aminan juna kusan komai tare suke gudanarwa saboda ko yaushe suna tare da ba don bambancin tsayi da kyaun fuska da mairamu tafi zainab ba to da babu abin da zai hana a kira su da suna tagwaye sun samu kyakkyawar tarbiyya irin ta addini islama kusan kowa na kaunarsu a duk fadin kauyen babu makarantar boko wannan ne dalilin daya sa basu samu ilimin zamani ba a lokacin da suka zama yan mata ne aka soma rububin su (kamar kayan gwanjo) kowa na burin ya samu mace ta gari musammanma mairamu domin Allah yayi mata farin jini fiye da yadda aka saba gani a kan sauran yan mata don ita har daga makwabtun kauyuka ake zuwa neman aurenta attajirai da yayan attajirai shahararrun manoma da mafarauta har izuwa kan yayan masu rike da sarautun gargajiya duk sun yi takara wajan neman aurenta amma ita mairamu tuntuni tayi nata zabin.....dogo ne siriri baki mai dan faffadan hanci baya ga kama a zahiri daya yi da mahaifinsa ya gado mahaifin nasa wajen kyawawan dabi'u musamman ta fuskar zamantakewa da jama'a. MUHD-ABBA~GANA www.abbagana.pun.bz
Share:

1 comment:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).