NA DAINA SO!! 10
NA DAINA SO! 10 muhd abba gana muryoyi ne barkatai suka yi ta faman kutse a kwakwalwar mairamu tana mai hasahen irin abin da mijin nata zai fada mata ta san dole zai zo ne yana mai yin fara'a kanar yadda ya saba irin yadda take dokin ganin sa ya sa ta yafe masa laifin da yayi mata duk da cewar bai ma zo ba balle ya roki afuwa ko abinci bata ciba baya ga kokon safe a yadda ta tsara yau tare zata ci abinci da mijinta amma tana sa ran matukar farin ciki ba zai iya barin ta iya cin abinci ba ta tuna da irin yadda a da suke cin abin ci tare wannan yasa wa wannan a baki wannan yasa wa wannan a baki har su koshi ta tuna da irin yadda suke sudewa juna hannu kafin su wanke da ruwa { hmmm aure ni'imar Allah } ta tuna irin yadda a lokuta da dama mijinta ke goya ta yayi ta sukuwa da ita a tsakar gida ta tuna irin yadda suke wasan buya da wasan yar burum-burum a wasu lokuta har da wasan yar carafke,suna matukar son juna sun jima da amanar cewa dayansu ba zai iya gudanar da rayuwarsa daidai ba idan har ba tare da dayan ba. Muhd-Abba~Gana www.abbagana.pun.bz
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.