shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Tuesday, 12 January 2016

NA DAINA SO!! 38

na-daina-so.jpg

NA DAINA SO!!! 38


Muhd-Abba~Gana


ajiyar zuciyata tayi sai lin da ta tuna cewa har yanzu kabir bai yi aure bs mene ne dalilin daya sa yusuf zaiyi mata haka? duk bayan yan mintina wannan tambayar na yawan bujuro mata har yanzu ta rasa takamaimai yadda zata ta amsa tambayar cin amana? to mene ne dalilin dayasa mijinta zai ci amanarta? saboda ya tafi birni? to ai shi ba bakon birni bane tun da a can yaje ya yi karatu..... saboda ya gano cewa ni yar kauye ce? saboda ni mummuna ce? saboda ni ban waye ba? saboda ni jahila ce? saboda bana yi masa biyayya? ta tuna irin yadda takeyi masa biyayya sau da kata ko wani abu zata bashi ko kuma zata karba da hannunsa sai ta durkusa duk sa'ilin da zata yi magana sai ta tausasa murya kamar wacce zata rera wakar jimami kafin ya tashi daga bacci ta gama shirya abincin safe kafin ya ankara ta kai masa ruwan wanka bandaki a duk sanda zai fita sai ta raka shi har wajen kofa idan ya dawo kwankwasa daya idan yayi kafin yayi ta biyu zata nufi kofa a guje taje ta bude masa ta karbi abin da ke hannunsa bayan tayi masa sannu da zuwa idan babbar riga ce a jikinsa ita take cire masa ta tuna irin yadda take rawar jiki don ganin ta girka masa irin abinci da yafi kauna hannayenta har kanta suka yi saboda daka doya a kokarinta nayi masa sakwara ta tuna da irin yadda a lokuta da dama ba tare da ya sani ba.
Muhd-Abba~Gana
www.abbagana.pun.bz
Share:

0 comments:

Post a comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).