shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday, 6 January 2016

NA DAINA SO!! 26 & 27

na-daina-so.jpg

[8:19PM, 1/4/2016] abba gana: NA DAINA SO 26


Muhd-Abba~Gana


kin tabbata? shakka bbu na tambaye ki mana Allah yasa na sani sai da ya dan yi jin kafin yayi magana tun yaushe kika fara son yusuf? gaskiya an dade tun lokacin da kuke karatu a birni amma ya akayi ban sani ba? ba tare da ya shirya ba kawai ya ji yayi wannan tambayar saboda yawanci a hanya muke haduwa kin tabbata kina sonshi sosai? ina son shi fiye da yadda nake son rayuwata a zuci taso ta furta hakan amma muryarta taci amanarta yaya kabir ina so ka taimake nina auri yusuf domin ina kaunarsa fiye da yadda kake zato ina alfahari da kai na san cewa bani da dan uwa kamar ka mai kaunata kuma mai kaunar abinda nake kauna don haka ka taimaka ka tsaya kai da fata don ganin cewa yusuf ya zama mijina don idan ba yusuf ba.......' kasa karasa maganar tayi to amma alamun da kabir ya gani a fuskar mairamu ya taimaka masa wajen karasa maganar a zuciyarsa .....idan ba yusuf ba zan taba yin aure ba idan ba yusuf ba ba zan taba jin dadin rayuwar nan ba ...........idan ba yusuf ba mutuwa zanyi"" kabir baya son ganin rayuwar kanwarsa cikin tashin hankali a bisa wannan hujja ne kabir ya fasa bayyana wa mairamu sirrin dayayi niyyar fada mata game da rayuwar yusuf.Muhd-Abba~Gana


www.abbagana.pun.bz
[8:19PM, 1/4/2016] abba gana: NA DAINA SO 27

Muh'd-Abba~Gana


yana fatan Allah ya shiryi yusuf duk wanda ya rufawa wani asiri to shima Allah zai rufa masa kuma mairamu na matukar son yusuf mairamu kin tabbata shima yusuf din yana sonki sosai? kwarai kuwa wani irin tausayi ne ya lillibe kabir tausayin mairamu rashin sani yafi dare duhu inji yusuf a zuciyarsa da ace mairamu ta san ko wane ne yusuf bala........ da ace mairamu tasan dilin da yasa aka kori yusuf bala daga jami'a lokacin da suke tsakiyar karatu...da ace......... a lokacin da mairamu ta bayyana cewa yusuf take so haka kawai mutanen gida suka ji basa son saurayin haka kawai ni saurayin bai kwanta min a rai ba mahaifinta ke fadawa mahaifiyarta saboda me? yana da wani abune? yana ma daga cikin samarin da ake yabawa da halayen su tun da tare da kabir sukayi karatu a birni.

Muhd-Abba~Gana

www.abbagana.pun.bz
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).