WASIYOYI GUDA BIYAR
WASIYYOYI 5 DAGA MANZON ALLAH (S.A.W).
Manzon Allah (s.a.w) yace:
"Waye zai karbi wadannan kalmomi guda 5 daga
gareni, yayi amfani da su koya sanar da wanda
zaiyi amfani dasu ???"
Sai Abu Huraira (r.a) yace Ni zan karba ya Ma'aikin
Allah.
Sai Manzon Allah (s.a.w) yariqe hannu na ya
maimaita minsu sai yace;
1. "Ka guji aikata sabo, zaka zamo wanda yafi
kowa bauta a cikin mutane.
2. "Ka yarda da abinda Allah Ya baka, zakafi kowa
arziqi cikin mutane.
3. "Ka kyautatawa maqobcin ka, zaka zamo
(cikakken) Mumini.
4. "Kasowa mutane abinda kake sowa kanka, zaka
kasance (cikakken) Musulmi.
5. "Kada ka yawaita dariya, domin yawan Dariya na
kashe zuciya.
SILSILATUL AHAADIISUS SAHIHA 930.
MANZON ALLAH (S.A.W) YACE KA RIQESU KOKA
SANAR DA WANDA ZAIYI AMFANI DA SU.
IDAN KA TURAWA YAN'UWA MUSULMAI BAKASAN
WA ZAI YI AMFANI DA SU BA, KAGA KASAMU
LADAN MUTANE MASU TARIN YAWA.
Allah bamu ikon anfani dashi
ReplyDelete