shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Thursday 28 January 2016

BANA KAUNARKA!!! 10

bana-kaunarkajpg.jpg

BANA KAUNAR KA!!!





10





MUHD-ABBA~GANA


bayan kwana biyu da yin maganar ina zaune dainmu ina karatun wani littafin addu'o'i ya shahid yai sallama na amsa ciki-ciki'domin yanzu haushi yake bani ya zauna kusa dani bai magana ba sai da ya shafe kusan minti goma sannan ya kalle ni 'ba ki iya gaisuwa ba ne ?na dago " sorry na manta ka tafi lafiya? gani nan lafiya ba lafiya ba lafiya nan da sauki wahida ina son muyi wata muhimmiyar magana okey ina jinka wahida kin san ina sonki ko? what nikake so? wahida me yasa kike son wahalar da dan uwanki...? ban gane nufin ka ba kin san mahida ta zabi dan uwana a matsayin abokin rayuwarta ina so kema ki sauke ra,ayin son karatu ki amince min billahillazi nayi alkawarin barin ki ki ci gaba da karatunki nai murmushi shahid kenan na fada maka bani da lokacin soyayya kwata-kwata ba zan iya hada karatu da soyayya ba shikenan zan iya jiranki ko nan da shekara goma ne no ka nemi wata kawai wahida kin san kuwa irin azabar da nake ji? oho kai kaso ka don haka bbu abinda ya demeni domin na fada maka gaskiya wahida nifa dan uwankine wahida me yasa ba kya sona in wani hali nake dashi wanda ba kya so dan girman Allah ki fito ki fada min kaga na farko bbu abin dana tsana irin shan taba kai kuma kana shan taba,maganar gaskiya ina zarginka da abubuwa da dama shahid ko ba haka ba dama ance sojoji suna shaye shaye kuma suna neman mata wa'iyazu billahi yace tare da mikewa ya cillo min kati gashi nan na baki cikakken sati kiyi bincike a kaina bayan taba me take sha tabar ma koki ka sank sha amma insha Allahu daga yau na barta har abada yana gama maganar ya fice jiki babu kwari.tunda wannan lokacin na shiga bincike kan bom boy har har sati biyu amma ban ga wani aibunsa ba in ban da da yake samu gun jama,a da dama sai dai wani abu ko kadan bana jin sonsa sai ma hausinsa da nake kara jiba kamar in na tuna shi soja ne kuma mugu ne na karshe domin bana mantawa ina karama mugun tsoransa nake innai abu aka ce za a fada wa shahid na kanyi kuku domin ban bashi da wasa gashi da girman kai rashin son magana yanzu ne fa da yake sona yake sakar min iska ni na san yana aurata zai daina sakar min fuska koda dama ance matar soja sai hakuri.kamar kullum ina zaune ya shigo da sallama tun kan ya karaso kamshin turaransa ya cika dakin kai gaskiya ina son turaransa haka nan kamshin kan sani farin ciki ko da kuwa ina cikin bacin rai gashin ban san sunan turaran ba bare in siyo gashi ina ganin kamar zubda ajine in tambaye shi sunan turaransa,kamar kar in amsa sallamar sai kuma na tuna girman sallama da darajarta sai na amsa ciki ciki na janyo remote na kunna T.V domin ta taya shi hira na mike domin in bar masa dakin suyi hirar da T.V caraf ya kamo hannuna sai naji hannunsa dumi ga wani irin taushin ji nai kamar in kwace hannun don wani irin sanyi dadi naji yana ratsa zuciyata na daddage na tofa masa yau a hannu ya daga hannun a tunanina mariina zai ko ya goge min yawun a jikina amma sai naga akasin haka domin ganina yasa harshe ya lashe yau din yace baki san yawunki yafi ice cream ba a gurina na yamutsa fuska ashe kai kazami ne??


MUHD-ABBA~GANA

www.abbagana.pun.bz
Share:

1 comment:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).