shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Sunday, 17 January 2016

NA DAINA SO!! 43 & 44

na-daina-so.jpg

NA DAINA SO! 43Muhd-Abba~Gana


duk irin kokarin da mairamu keyi don ganin ta kawar da tunanin yusuf abu ya faskara tunaninsa ne abu na farko da take yi idan ta farka daga bacci kuma tunaninsa ne abu na karshe da take yi kafin bacci yaci nasarar sure ta ita da kanta ta gamsu cewar tana bukatar taimakon gaggawa tun kafin al,amarin ya kai ga wargaza kwakwalwa. by muhd abba gana

** ** **

a wani yammaci kabir ne da mairamu zaune a gefen kogi kan wasu duwatsu mairamu ina mai ba ki hakuri hakurin me? hakuri bisa laifin da nayi wanne laifi kayi? da tun da farko na goyi baya har yusuf ya zama mijinki wannan ai ba laifi kayi ba taimako na kayi na samu abin da nakeso laifi nayi mana tun da na san cewa yusuf ba mutumin kirki bane mai kake son cewa? sannin kanki ne cewa tare muka yi karatu da yusuf abin da kusan duk mutanen kauyen nan basu sani ba shine bai kammala karatun jami'a ba korarsa akayi....... saboda me? saboda wani laifi da yayi wanne laifi? sai da ya dan yi jim kafin ya bata amsa "wata budurwa ya yiwa ciki"


Muhd-Abba~Gana


NA DAINA SO! 44


Muhd-Abba~Gana


duk shiru sukayi kamar ruwa ya cinye su mairamu ce ta katse shirun ba kayi laifi ba yaya kabir don a lokacin ko da ace ka yi min wannan bayanin ba zan fasa aurar yusuf ba watakila ma naji haushinka mai yiwuwa nayi tunanin cewa ko bakin ciki kakeyi min saboda makahon so nakeyi wa yusuf kuma ba zan iya .....kasa karasa maganar tayi ina son ki saurari wata magana wacce magana? ki shirya gobe da safe muje kotu ayi me? a raba auren ki da yusuf raba aurena da yusuf zai dawo min da shekarun dana salwantar? raba aure na da yusuf zai kankare bakin cikin da ya kunsa min raba aure na da tusuf zai dawo min da farin cikin dana rasa a rayuwata? mene ne amfanin raba auren? saboda ki fuskanci sabuwar rayuwa ta hanyar sake yin wani aure? kwarai kuwa wallahii wallahi ba zan kara yin wani aure a rayuwata ba ki daina fadin haka to ai gaskiya ce wannan ba gaskiya bace to wane ne zai yarda ya aure ni? nine kai?? shakka-babu ko kina shakka a bisa irin so da nake yii miki?Muhd-Abba~Gana


www.abbagana.pun.bz
Share:

1 comment:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).