shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Sunday, 6 December 2020

Yadda Zaki Mallake Zuciyar Mijinki Ko Saurayin Ki Cikin Sauki!

Yadda Zaki Mallake Zuciyar Mijinki Ko Saurayin Ki Cikin Sauki!

Assalamu Alaikum barkanmu da warhaka barkanmu da sake saduwa daku a cikin sabon shirin namu wadda yake zuwa muku kai tsaye daga shafin “Abbagana Novels”, Kuna tare da jikan Marubuta Muhammad Abba Gana. Kuma insha Alllahu yau zamuyi jawabine akan yadda zaki mallake zuciyar mijinki cikin sauki.

Na samu sakonni bila adadin, korafe-korafe da mutane keyi na rashin jina na tsahon lokuta masa tsawo haka zalika naga wasu rubuce-rubuce da wasu keyi a dandalin sada zumunta na whatsapp da kuma facebook na cewar na mutu wasu kuma na cewar nayi aure ne sai sa na daina rubutu (Ko daya bai faruba).

To ina mai farin cikin sanar daku cewar ina nan klau kuma garau kawai de wasu sungulloline ke yawan rikemu amma akoda yaushe muna cikin hamdala tunda akwai lafiya. Ba tare da dogon surutu ba insha Allahu yau zamuyi bayani ne akan wasu matsaloli da ma’aurata ke fuskanta na rashin sannin yadda za’a mallake miji ba tare da boka ko magani ba.

Shakka babu, a wannan zamani 'yan mata da zawarawa kai harma da matan aure suna cikin zullumi da tsoro da rashin kwanciyar hankali, saboda yadda auren su yake yawan mutuwa, bayan kuma, an dauki dogon lokaci ana soyayya a tsakani, kafin a yi auren.

Baza’a iya jingina wannan matsalar ga jinsi guda ba domin kuwa hakan na faruwa ne daga dukka bangarorin wato bangaren miji da kuma mace, sai de a koda yaushe yana da kyau a matsayin ki na ya’ mace ki kasance kina da juriya da kuma hakuri koda kuwa laifin ba daga gareki bane; domin kedin uwace kuma mijinki shine aljannar ki hakan ya sanya yau na kawo miki wasu muhimman abubuwa da zaki dage da yi wadda hakan zai taimaka matuka wajen dauke zuciyar miji.

1.==> Ki dinga yawan sada zumunci ga mutanen gidansu (kamar ziyartarsu, kiransu a waya) hakan ba yana nufin cewar ki auri yawo da gulma ba.

2. ==> Ki zamo mai kirki, ladabi da biyayya ga Mahaifiyar mijinki kamar yadda zaki so shima ya zamo kamar haka ga mahaifiyarki.  

3. ==> Kada ki fara lissafowa mijinki matsalolinki ko na gida a lokacin da ya shigo, ki barshi ya huta tukuna ya samu nutsuwa.

4.==> Ki sanar masa a duk lokacin da wani abu ya kusan karewa misali abinci kada ki bari sai ya kare gaba daya.

5.==> Ki zamo mai iya kwalliya. Idan kin kasance mai zaman gida ce to kici ado ko da kuwa baza ki fita ko zuwa ko ina ba, hakan ba karamin faranta masa rai zakiyi ba.

6.==> Ki riqa yi masa halin mata, wato irinsu kisisina, shagwaba da dai sauransu, don namiji baya son mai halin maza ta zama matarsa.

7.==> Ki dinga bashi wani dan karamin aiki a gida; kuma idan yayi aikin sai ki gode masa. Hakan zai sa ya qara dagewa.

8.==> Ki dinga qarawa mijinki qarfin gwiwa akan abinda kika ga alamar yana nema ya karaya, hakan zai sa ya zamo gwarzo a cikin maza.

10.==> Ki tuna cewa mijinki ma yana da damuwa da farin ciki, saboda haka ki dinga tunawa dashi wajen yanke hukunci.

11.==> Idan mijinki ya nuna damuwa akan dan qaramin abu da kika yi masa to sai ki bashi haquri kuma ki dena.

12.==> Ki dinga fadawa mijinki cewa kina sonshi sau dayawa, dayawa dayawa, Aisha ­رضا عنها  tace Annabin tsira SAW ya kasance yana tambayarta qarfin soyayyarta a gareshi, sai tace mishi kamar ‘zarge’ (wato dauri ko kulli wanta bazai kwance ba), sai ya sake tambayarta ‘yaya zargen yake’? Kuma ya kasance yana cewa da ita Allah ya saka miki da alkhairi Aisha, ina farin ciki da jin dadi dake fiye da yadda kike farin ciki dani! Annabi yaji dadi ma waye kuma mijin naki?

13. ==> Kada ki rokeshi kudi ko kuma wani abu na hannu, yin hakan na zubar da mutunci sannan kuma yawan roko yana cire kaunar mutum daga zuciya.

14.==> Kada ki kawo gulman wani ko wata ba tare da izininsa ba. Abinda nake nufi anan shine kada ki ringa kawo wasu gulma ko labarin wani abun daya faru da wani ko wata face ya tambayeki.

15.==> Hajiya abinci shine komai a rayuwa. Sanin dabarun iya griki mai dadi shine babban sirri na farko da mace zatayi amfani dashi wajen sace zuciyar mijinta.

16.==> Ki kyautata kwanciyarsa, gamsasshen jima’i shine gishirin aure. Idan mijinki yanajin dadin saduwa dake to, babu macen data fiki a wajensa.

17.==> Ki zama kin iya barkwancin magana wajen baiwa mijinki dariya.

18. ==> Kada ki zama mai rainuwa a cikin duk abinda mijinki ya baki.

19.==> Ki dinga yawan neman shawarar mijinki akan duk wani al'amari da zaki yi.

20.==> Lallai ki yi kokarin gama aikace-aikacenki kafin dawowar mijinki.

21.==> Kada ki ce mijinki sai ya saya miki abinda ba shida ikon saye.

22.==> Ki kula da tarbiyar yaransa, ehh; ya kamata nace yaranku ko? To yaransa ne. idan Allah ya baku haihuwa tare dashi, kiyi qoqarin ganin sun tashi da tarbiya mai kyau.

23.==> Ki kasance mai tunatar dashi haqin Allah. Hakan kuma baya nufin komai zaki gaya masa son ranki ba yana da kyau idan zaki masa Magana ta wannan bangaren kiyi shi cikin kulawa domin ana samun matsaloli bila adadin ta wannan bangaren.

24.==> Ki yawaita masa kyauta. Babu zuciyar da bata son kyauta yana da kyau a duk lokacin da kika sami wani dama ki siya abu komin kankantarsa ki bashi a matsayin kyauta hakan zai faranta masa rai kuma ciwon kaunarki zai kara wanzuwa cikin zuciyarsa.    

25. Ki yawaita yabonsa da kuma ambatonsa da sunaye masu dadi. Mafi yawancin akasarin matan mu na gida basu dauki wannan a matsayin komai ba, wasu suna masa kallon kauyanci, na fi karfin nayi ko kuma baka kai nayi maka ba. 

Sau dayawa zakaji mata na kiran mijinta da sunansa, wadda abonkansa suke kiransa dashi ko kuma wani suna wadda ba wando misali “Babban ayman”, “Baban Musa”, “Dan tsiri”, “kai” da dai makamantansu.

Wadda bai kamata kinayi ba akwai jerin sunaye da kalamai masu yawan gaske da zaki iya amfani dasu wadda zai sanya kaunarki ya narke chan karkashin zuciyansa har wasu lokutan ma yayi miki kyauta ba tare da sani ba. Yana da kyau ki yawaita chanza masa sunaye bayan ko wani mako ko rana wasu daga cikin jerin sunaye masu dadi sun hada da:

  • Darling
  • Sweetheart
  • Rabin Zuciya
  • Hasken Idanuna
  • NurulKalbee
  • Habibina
  • Farin Cikina
  • Abin Alfaharina
  • Jarumina
  • Taurarona
  • Mahadin rayuwata
  • Abar Sona
  • Abar Alfaharina
  • Sahibina
  • Aminina

     Da dai sauransu. Akwai littafi dana rubuta na mussaman mai suna “Siffofin Uwa Ta Gari” wadda na tattauna ire-iren abubuwan nan bila adadin wadda zai taimka matuka, za’a iya samun littafin ta hanyar saukarwa anan è SIFFOFIN UWA TA GARI haka zalika za’a iya samun sa a cikin kasuwanni a duk fadin kasar nan.

A karshe nake cewa, wannan shi ne abinda Allah ya hore min in rubuta a kan wannan matashiya mai matukar mahimmanci, kuma na yi kokarin ambaton manya-manyan  abubuwan da zaki iya yi wajen samun zuciyar mijiki.  

Amma ba ina nufin iyakar su kenan ba, a’a, na yi ne a takaice, don haka kofar kari a bude take. Allah Madaukakin Sarki ya sa mu dace, ya kuma gafarta mana kurakuranmu. (Ameen).

Yawwa yan mata kuma hajiyarmu a duk lokacin da kika sami damar mallakar zuciyarsa zaki iya miko min domin yin tsire dashi. Allah shi sa mu dace. Ameen!

Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).