TANA TARE DA NI...
TANA TARE DA NI... PAGE 61BY MIEMIEBEE
★‡★‡★‡
PRISON HOUSE MAIDUGURI, BORNO STATE.
K’aramin gate ne ya bud’u Ya Khaleel ya sa kai ciki, be tsaya ko ina ba se wajen da aka tanada dan masu visiting prisoners. Da zamansa befi minti biyu ba aka bud’o wa Farouq k’ofa sanye yake da orange T-shirt na ‘yan prison meh ‘32’ rubuce a ta bayan. Sosai ya rame yayi bak’i, ta gefen bakinsa yanka ne alaman fad’a dawani yayi har yasamu injurin. K’arisowa yayi a kasalance ya zauna a kujera opposite Ya Khaleel.
“Subhanallahi Farouq meya sameka anan?” Ya Khaleel ya tambaya cike da damuwa yana tab’a gefen bakin Farouq. Hannu yasa ya kawar da hannun mahaifin nasa “ba komai.”
“Kamar ya ba komai Farouq da wanne kakeson inji ne? Da rashin ka kokuwa da rashin jinka? Cikin nan d’in ma baraka bar fad’a ba?”
“Baba niba fad’a nayi ba” ya fad’i cikin murya cike da takaici.
“Allah shirya min kai Farouq” hannu yasa ya d’ago wata leda tare da azawa kan table d’in yana bud’ewa. Abinci ne mai rai da lafiya, ga kaji kota ina. Ba makawa Farouq yasoma chi dan ko rabuwansa da abinci me kyau about a week now tun komawar Babansa Bama. Seda yayi dam ya kora da cool malt drink sannan yajisa d’an dadai.
“Baba ya batun kud’in bailing nawan? Nagaji da zama anan.”
“Farouq kasan kud’in bailing nakan ba abu neba na wasa, gun aikinka nayi masu bayani ko zasu d’an ji k’anka, albashin ka suka yanke sunce ba ruwansu dakai. Banki kuma sunk’i bani loan saboda ba aiki nakeyi ba, bakuma wani abu nayi possessing ba.”
“Baba amman wannan abu is not fair, menayi da wannan Fauzin zesa a rufe ni?”
“Saboda kai talaka ne Farouq shikuma yanada kud’i. Kai baka gani bane? Ba lawyer’n dayakeson tsaya mana kan case d’innan da zaran sunji Mr. Fauzi ne opponent d’in se su soma mana wasa da hankali.”
“Bawani Mr. Fauzi dan ubansa, Fauzi kawai in bare amsa bakuma chan masa, uwarsa da Mr d’in. Wallahi na fito he must rule the day he was born.”
“Ai fitowanka ba nan kusa ba Farouq.” Cike da rashin fahimta Farouq yace, “what do you mean Baba? Ina dubu d’ari biyar da muke dashi a k’asa?” Kai kawai Ya Khaleel ke girgizawa. “Baba talk mana, ina yake?”
“Farouq a hanya na, na komawa Bama b’arayi suka tsare mana mota suka k’wace duka d’ari biyun danayi aiki na samu da k’yar sesa kajini shiru through out last week.”
“What?!” Ya fad’a a tsawace tare da zabura. “Farouq yi hak’uri ka zauna.”
“No! No! Baba this is unacceptable wallahi nagaji da zama anan. Nagaji, I can’t take it anymore. Yaushe ne zaka samu miliyan d’ayan da suke buk’ata ka cireni anan? Mschww!”
“Calm down Farouq-” katse Baban nasa yayi.
“No! I can’t calm down.” Mik’ewan shima Ya Khaleel yayi yace, “in har dan wannan baraka iya calming kanka ba then inaga there is no point ma in sanar dakai main abinda ya kawoni, ai wannan jaririn tashin hankali ne aganga da wancan.” Cike da rashin fahimta yace. “wanne kenan Baba?”
“A’a barin fad’a maka ba tunda wannan ma yayi freaking naka out there’s no need in sanar dakai wanchan.” Hannun Baban nasa ya rik’e suka zauna atare. “Mene Baba please tell me. Ba abinda ze tada min hankali se lafiyar Fannah. Baba ina ba wani abun bane ya sameta?” Shiru Ya Khaleel yayi hakan ya bawa Farouq daman sake magana, “Baba talk mana please.”
“Farouq inason ka kwantar da hankalinka ka sauraren da kyau.” Kai kawai ya gyad’a duk yakasa samun sukuni. “Jiya na je gidansu Fannah nake tambayan ‘yan gidansu ina take sabida ban ganta ba duk sukamin shiru ba wanda ya amsani I had to ask their neighbours nan ne suke sanar dani cewa Fannah tayi... Tayi...”
“Tayi meh Baba?? Tell me!” yayi demanding
“Farouq, Fannah tayi aure.”
“Tayi meh?” Ya tambaya disbelievingly.
“Tayi aure Farouq.”
“No... No” kai yake girgizawa ba makawa. “Baba halan baka gane bane, Fannah is mine, she belongs to me no one can take her away. Whats mine is MINE, FANNAH TAWA CE Baba.” T shirt nasa ya yaga daga gefe d’aya tattoo ne d’an babba ya bayyana a saman hannunsa anyi zanen heart ciki kuma an rubuta ‘F&F’ ma’ana ‘Farouq and Fannah.’ Cike da mamaki Ya Khaleel ke kallon hannun d’ansa totally speechless.
“Subhanallahi Farouq dan girman Allah me wannan? Tattoo ka zana a hannunka? Kana muslimi?”
“Eh Baba” ya amsa sa confidently “and I mean it I will never rest se ranan da Fannah tazamo TAWA sabida TAWA CE dama. Koma waye ya aureta seya sake ta inkuma hakan be yuwu ba, I don’t care koda zanyi spilting blood. Fannah tawa ce, ba mahaluk’in daya isa ya k’wace ta.”
Kai Ya Khaleel ya kad’a “koda kuwa mutumin Mr. Fauzi ne? Koda Mr. Fauzi ne mijin nata?”
“Mr. Fauzi? Kana nufin shine ya auri Fannah matata???”
“Shi ya aureta Farouq, Mr. Fauzi shine mijin Fannah, hak’uri ya zama 2 Farouq you can’t fight with Mr. Fauzi he is too powerful.”
“Baba abu d’aya nakeson kamin, kawai kasan ya za’ayi in fita daga god forsaken place d’innan. Wallahi kaji na rantse sena koya wa Mr. Fauzi @ whats mine is mine and mine alone!” ya buga kan table d’in.
★★★★★
MAIDUGURI INTERNATIONAL HOTEL LTD.
Kwance Fannah take bisa gado se kuka take duk tabi ta tadawa Anas hankali yarasa meke masa dad’i. “Fannah to muje asibiti mana” yace da ita cike da tausayi yana a zaune kan bediside drawer’n kanta.
Kai kawai ta girgiza masa “zuwa gobe ze dena we don’t have to.”
“Har se gobe? Tun safe ba abinda kikeyi banda kuka ko breakfast kink’i chi haka lunch ma. Ni ban zama care giver ba na gaji da kula dake, kimutu kika ga dama.”
“Ai banche ka kula dani ba nima, tun farko ma banche ka zauna nan ba, kaje office abinka.” Ta juya masa baya.
“Ai da kin fad’a hakan tun d’azu seda aka tashi a office d’in zaki wani cemin da ban zauna dake ba? Mschw!” Banza tayi dashi ta cigaba da kukan ta tana juye-juye. Ignoring nata yayi ya koma kan couch ya zauna tare da ciro wayarsa yana latsawa.
Chan da kwanciyan kan gadon ya gagareta ta sauk’o k’asa se juyi take tana kuka, sekuma ta basa tausayi shi aduk lokacin da baida lafiya zata bar duk wani abinda takeyi takula dashi, why can’t he do thesame? Ajiye wayar nasan yayi ya taso zuwa inda take a kwance ya tsuguna. “Fannah” ya kira sunanta. Baya ta juya masa. “Fannah okay I’m I’m...” sekuma yayi shiru bayajin ze iya ce mata sorry.
“Tashi kinji?” Nanma banza dashi tayi. “In had’a miki coffee?”
“Don’t bother, banaso.”
“Fannah bakici komai bafa since in the morning.” Shiru tayi bata ce komai ba. “Okay Fannah I’m sor-” be k’arasa fad’a ba yayi shiru. “Kinji?”
“Banji ba.”
“I just apologised to you, you have to accept it.”
“Ni haka nake baka hak’uri ne? ka rik’e hak’urinka banaso.”
“Okay I’m sorry kinji? Tashi ki koma kan gado.” Ba gardama ta mik’e ta koma gadon. Nan ya had’a mata yakai mata seda ya tabbata ta shanye yabarta ta koma ta kwanta.
**
Washegari Fannah ta tashi garau masha Allah taji sauk’i sosai. A farko ma cewa Anas yayi bare je office ba, Fannah ce tasa sa a gaba saboda tasan halinsa duk wani alkhairin daya ma mutum seya k’arisa da tsiya, dan haka kawai tasa sa a gaba seyaje, shikuma dan nuna mata be damu da ita ba ya shirya yayi tafiyarsa ko breakfast yak’iyi. Yana ji tana kirar sunansa ya dawo su karya yayi banza da ita.
Isarsa office ya baje kan kujera nan Kacallah yashigo masa da files ba adadi yasoma bi one-by-one yana signing, by 10:00AM yafita meeting sede tunda aka soma yakasa gane me akeyi kwata kwata hankalinsa bayya jikinsa yana chan yana tunanin Fannah for sure yasan ta samu sauk’i but he can’t stop himself from being worried, ana fitowa daga meeting d’in ya kirata a waya a lokacin tana bayi tana wanka seda tafito taga missed call nasa k’waya d’ya. “Shegen girman kai, ko kiran mutum sau biyu ma be iya ba” nan ta kirasa back bada dad’ewa ba ya d’aga. Shiru tayi bata ce komai ba shima haka sun kusan minti biyu shiru sannan yakira sunanta “Fannah.”
“Na’am” ta amsa.
“Aww dama kina kai? Shine bakiyi magana ba tun d’azu?”
“Toh ai kai ka fara kira na.”
“Ya jikin naki?”
“Da sauk’i.”
“Okay...”
“Shikenan can I go ba k to what am doing?”
“Me kikeyi?” Ya tambaya haka kawai yaji yanason cigaba da sauraron muryarta.
“Yanzu nafito daga wanka zan shafa mai.”
“K’azama se kusan to twelve na rana zakiyi wanka.”
“Toh ai bacci nayi.”
“K’azama ba.”
“Niba k’azama ce ba, excuse me zan shafa mai nan ta katse.” Murmushi dukansu suka tsaya yi suna kallon wayoyinsu musamman ma Fannah. She can’t deny it anymore ta fad’a tarkon soyayyar Mr. Fauzi sede batason soyayyar yaje ko ina saboda batasan ayi hurting nata daga k’arshe ‘cause muddin Anas yasan sirrinta he will run away and leave her, aduk lokacin data tuna da wannan seta yayyafa wa zuciyarta ruwan sanyi dan huchar da zazzafan son Mr. Fauzi. Haka har tagama shirinta tana tuna jiya yadda Anas ya riga mata hidima ko da daddare da take kuka ya hana kansa bacci ya zauna da ita yana pompering nata, haka kawai taji tana murmusawa.
Shima Anas zaune yake cikin one of hotels daya saba chin abinci, ga abincin agabansa amman yakasa ci se murmusawa yake musamman ya tuna rananda take tsaye da towel a gabansa dakuma lokacinda cinyoyinta sukayi tsami yake shafa mata muscle pain reliever. Da k’yar ya iya ya kai spoons biyar yaji yama k’oshi tunanin Fannah kad’ai ya ciyar dashi. Be jira aka tashi ba yabar office ji yayai kawai Fannah yakeson sawa a idanunsa, it hasn’t been long amman seji yake like shekara da shekaru ne.
K’arfe 3:00PM
Tsaye Anas yake bakin hotel room nasu ya kasa shiga dan girman kai. “What if tace mena dawo yai since before lokacin tashi yayi, me zance mata? That I miss her I want to see her? No! No way ai seta raina ni ta d’au ko sonta nake.” Ya juya ze koma kuma yaji bare iya ba Fannah yakeson gani and no one else. Seya d’aga hannu zeyi knocking seya sake maida hannun nasa baya.
Fannah kuwa tayi waya da Afrah ta buga game, ta kalli pictures na bikinsu, tayi kallo, tagaji zaman shirun ya isheta. Sanin ba kowa a floor dasuke daga ita se Anas, Anas kuma baya nan ba wanda ze hauro ta d’au wayarta kad’ai. Atamfa ne d’inkin fitted riga da skirt ya mugun mata kyau a jikinta, kayan ya zauna tip tip. D’aurin ta ta daidaita sannan ta bud’e k’ofar, baki ta sake ganin Anas tsaye jikin k’ofar.
Mutuwan tsaye sukayi duk a wajen suna kallon juna sun kusan minti biyu suna abu d’aya sannan ta kawar da kanta zata rufe k’ofar dan komawa ta d’auko mayafinta kenan Anas ya rik’o hannunta. Be d’aga idanunsa daga kan k’irjinta ba har ayanzu se kallonta yake.
“Uhm Anas kasakeni in d’au mayafi na please.”
“Why?” Ya tambayeta se anan ya dawo da kallonsa kan kyakkyawar fuskarta data sha d’an light makeup.
“Anas hakan ba kyau-” katseta yayi.
“No I like it this way, kinfi kyau haka kar ki rufe jikin ki kinji?”
“But Anas-” katse ta ya kuma “Fannah I’m your husband nace nafison ganinki haka” se yanzu ya tuna da kalamun ta na ranan cewa batason tsinuwan mala’ikun rahma. “Ko ki zauna haka kokuma inyi fushi dake mala’ikun rahma suyita tsine miki.”
“A’a dan Allah don’t talk like that kaji karkayi fushi.”
“Zaki zauna hakan?” Kai ta gyad’a a hankali. “Good” ya saki brightest smile nasa.
“Da ina zakije ahakan?”
“Babu kawai nagaji da zaman cikin ne nace barin d’an lek’o waje.” Ta basa amsa tana k’oka’rin raba hannunta da nasa. “Shine zaki fito ahaka ba hijabi ba mayafi?” Ya fad’a a little bit pissed off, daga yadda yake magana za’a san kishi ya motsa.
“Toh Anas naga ba kowa a floor d’inmun, mu kad’ai ne.”
“I know what of room services? Insuka hauro alokacin da kike k’ok’arin fitowa ahaka fah? Se suganki?”
“Yanzu fa kace nafi kyau a haka kar insa mayafi.” Hannu yasa ya hargitsa gashinsa cike da haushi. “For goodness sake Fannah I’m your husband, taya zaki had’ani da room service? Nine kad’ai am aloud to stare at your body and not them.”
“I’m sorry” tace dashi tana kallon k’asa.
“No you are not Fannah, daga yau karki sake fitowa koda bud’e k’ofa ne ba hijabi ko mayafi do you get me? Banason mayafin ma hijabi constant kinji?”
“Haba mana Anas ai dan bud’e k’ofa kam mayafi ma yayi.”
“Ni bemin ba banaso, Fannah I’m serious.”
“Okay naji barin k’ara ba.”
“Better” yace yana hararta. “Matsa min in wuce.”
“Ka wuce ina? Anas lokacin tashi daga office fa beyi ba, meka dawo yi?”
“Me ruwanki? Ko kin d’au wai dawowa nayi saboda nayi missing naki? Hell No nadawo d’aukan wasu files ne, mema zan kalla a fuskarki ko jikin naki, excuse me?”
“Niba abinda nake nufi ba kenan” gefe ta matsa masa ya shiga tabi bayansa. Briefcase dayake adana files nasa ya ciro shi a dole yadawo ne dan d’auko abu tana tsaye akansa se dube-dube yake yakasa koda d’aukan d’aya ciki. Ganin har yaci minti biyar be samu ba Fannah tace, “Anas anya kuwa files d’in kazo d’auka ba wani abu daban ba?” Da biyu tamasa tambayan dan kuwa hankalinta ya bata ba file yazo d’auka ba wayasani ma ko missing nata yake dagaske tunda har ya bud’e baki yafad’a d’azu indirectly.
“Mind your business mana meh ruwanki da abinda nakeyi kin wani zo kin tsaya min akai sekace soldier (soja.)”
“Allah baka hak’uri niba abinda nake nufi ba kenan, I was thinking ko kanaso in tayaka nema ne.”
“Neman meh?”
“File da kake neman, koba file kace kana nema ba?” Shi se yanzu ma ya tuna eh file yazo nema.
“Toh banaso, zan nemi abu na dakaina.”
“Yi hak’uri in taya ka” tace dawani mocking smile tattare da fuskarta.
“Fannah yaushe na soma wasa dake? Mind your business.” Juya baya tayi tasoma tafiya zata kan couch ta zauna. “Mutum bare fito fili ya fad’a meya kawo sa ba se shegen zurfin ciki” tace chan k’asa k’asa almost kamar da kanta take maganar.
Bejita gabad’ai ba amman yaji some part. “Ke! Me kikace?” Take ta juyo dan bata tsamman yajita ba.
“Babu kawai cewa nayi Allah sa kasamu file d’in.” Harara ya galla mata tare da cigaba da nan file dayayi qarya yana nema. Chan ya d’ago kai yaga se lastse wayarta take, tsayuwa yayi yana kallonta ko kyafta ido baiyi data d’ago kai seya juya daga k’arshe ya ciro wani file yayi hanyan fita ai dagangan ya sakar da k’ara “awwchh! My ankle.” ya tsuguna yana rik’e k’afar. Da sauri ta nufa wajen “Anas meya faru?” Ta tambaya tana dubansa.
“My ankle nakega nayi spraining. Awcchh!”
“Ya Salam! But how?” Ta tambaya.
“Nima bansani ba, argh!!” Hannunta ta zagaye ta bayansa tayi assisting nasa ta kwantar dashi kan gado. Se faman “awch!” na k’arya yake, sam yaji bayason rabuwa da ita koda na second ne shiyasa yayi coming up da wannan plan na spraining ankle nasa.
Takalmasa ta cire masa da socks d’in, da ta tab’a k’afan hagun nasa seya sa ihu. ”Sorry, d’an tsaya in gani.”
“A’a barshi.”
“Anas kasan fa bareyi abar k’afar haka ba, nida cinya na sukayi tsami kwanaki ba haka kasani a gaba ka riga shafa min man zafi ba? Ka tsaya inga.”
K’afan nasa ta aza kan cinyarta tana d’an mammatsa wajen ankle nasan. Sekuma abin yasoma masa cakulkuli, dariya yakeson yi amman ya matse se faking “awch!” Yake tayi.
“Amma Anas banga alaman koda b’ullowan muscle bafa, kuma kace kayi spraining.”
“Aww maqaryaci kikeson cemin komeh?”
“A’a kawai de da abun ban mamaki ne.”
“Sakemin k’afa ba sekin zagen ba.” Nan ya d’aga k’afarsa daga kan cinyar tatan.
“Anas ba abinda nake nufi ba kenan I’m sorry.”
“Banaso, tashi kibani waje.” K’afar nasan ta mayar kan cinyarta. “I’m sorry kaji?”
“Naji” yace ba tare da ya kalleta ba. “In shafa maka magani awajen?”
“No you don’t have to.”
“Anas in ba’a shafa ba baraka iya taka k’afan bafah.”
“Don’t worry just come lets sleep.”
“Sede inkai ni banjima da tashi daga bacci ba.” Nan ta mik’e ta rage masa kayan jikinsa ta juya kenan ya rik’o hannunta “lets sleep kinji?” Be jira amsarta ba ya jata ta fad’a jikinsa.
“Anas me haka?” Ta fad’a a lokacinda take k’ok’arin tashi.
“Lets sleep.” ya sake matseta jikinsa.
“Ahaka? Ai namaka nauyi barin kwanta a gefe kaji?”
“No I want it this way.” Bata sake cewa komai ba sede sam ta kasa samun sukuni, wani erin baqon yanayi ta tsinci kanta ciki.
20 minutes later...
“Anas” ta gwada kiran sunansa jin yayi shiru, ta d’aga hannunsa daya zagaya akan bayanta a hankali sannan ta taso daga jikinsa ta yadda bata tadashi daga baccin nasa ba.
*© miemiebee*
TANA TARE DA NI...
TANA TARE DA NI... PAGE 62BY MIEMIEBEE
Suit da shirt nasa data cire d’azu ta d’au tasa a laundry basket. Bayan ta dawo tana tsaye akansa ta gwada tab’a k’afar sa dayace yayi spraining to her suprise taga beko motsa ba, sake tab’awa tayi da d’an k’arfi nanma be motsa ba se baccinsa yake. Mamaki ne ya rufeta mutumin dayace yayi spraining k’afar ne ana tab’awa amman baiko jin zafi? Lallai kam! Komawa kan side drawer’n gefensa tayi ta zauna tana k’ure masa kallo daga gashin girarsa, idanunsa hanci dakuma lips nasa, batasan seda takai hannunta kan lips nasa ba haka kawai taji tanason ta tab’a, taji tanason tab’a lips nasa masu uban fidda bak’ak’en kalamu ganin yad’an motsa ta miyar da hannun nata baya haka tata kallonsa har seda La’asar prayer yashiga.
“Anas!” takira sunansa a hankali. “Anas katashi lokacin Sallah yayi.” Nanma shiru seda tasa hannu ta tab’a sa ya bud’e ido ya azasu kanta. “Lokacin Sallah yayi” tace tare da kawar da kanta.
“Kefa barakiyi ba?” Ya tambayeta dan kwata kwata ya manta batayi. Yi tayi kamar bata jisa ba ta mik’e.
“Yes?” Cewar Anas.
“Anas banayi ka manta ne.” Ba tare da yace da ita komai ba ya mik’e kan gadon kwata kwata ya manta da k’aryan spraining ankle nasa daya mata, garau ya mik’e yana tafiya. Baki ta sake tana kallon ikon Allah.
“Anas har k’afan ya warke ne?” Se a yanzu ya tuna ya mata k’arya kuma tariga ta gano gaskiyar.
“Da sauk’i be warke ba” yace da ita yana basarwa tare da d’an karkata tafiyar tasa. Daga yadda take kallonsa yasan tagano gaskiyar no point ya cigaba da k’aryan. “Okay, okay naji you caught me lying actually ba spraining ankle d’ina danayi I just faked it are you okay?” Dariya sosai ta b’arke da, Anas be tab’a ganinta tana irin wannan dariya ba se yau and he find her cute, admiring nata ya tsaya yi se dariya take harda ‘yar hawaye se chan tad’anyi shiru. “I’m sorry” tace tana girgiza kai hannunta na akan cikinta.
“Kin gama?” Yace da ita.
“I’m sorry but Anas why do you have to lie?”
“Nima bansani ba, meh ruwanki?”
“Anas daga tambaya.”
“I miss you thats it” yace da ita sincerely dan dama haka yake he is straight forward. Wani irin yanayi ta tsinci kanta ciki a yayinda bugun zuciyarta ya k’aru. She couldn’t help it batasan seda ta soma blushing ba. ‘yar k’aramar tsuka yaja;
“Mschw! you can stop blushing, not anymore I don’t miss you again” daga nan ya shige bayi tana zaune kan gado har ya idar da Sallah. Abinci yamusu ordering bayan da suka gama ci ta d’au towel nata da hijabi ta nufa bayi dan sake watsa ruwa tad’an kwanta kafin Maghrib.
A yayinda ya cigaba da gudanar harkar gabansa a laptop shikuwa, bayan like 2 minutes ya tashi ya fice bada dad’ewa ba ya dawo yatsansa na yoyon jini da alama yankewa yayi. A gurguje yashigo d’akin, bayi ya nufa ya bud’e kasancewar Fannah batasa lock ba. Idanunsa basu sauk’a a ko ina ba sekan Fannah dake wanka, kwata kwata ta rasa me ya hanata sa lock bakin k’ofar a tunaninta wai ai Anas yasan tana ciki bare bud’e taba shiko yankan da yayi yasa ya mance da tana cikin bayin. Seda ya k’are mata kallo sama da k’asa sannan tasa wani irin masifaffen ihun da bata tab’ayin irinsa ba. Hannu yasa yakai baki kan wanda zeyi amai sannan da wurwuri ya rufe k’ofar. Both of them were speechless for the mean time, Fannah can’t believe Anas yaganta a haka kamar yadda shima yakasa believing yaga Fannah ba komai a jiki.
Kuka tasa a bayin wanda har shi Anas d’in ya jiyota, tissue yaja ya tare zubar jinin sannan ya dawo kusa da k’ofan ya tsaya yana sauraron sautin kukanta, yarasa nayi ganin bata da niyyan barin kukan yakira sunanta “Fannah.”
K’arfin kukan nata ta k’ara. “OMG! Fannah kukan me kuma? Stop crying please.” Banza tayi dashi takoma cikin jacuzzi ta zauna se kuka take. “Fannah stop crying na manta kina ciki ne, kinji?” Nanma bata ce komai ba.
“Kema mesa baki rufe k’ofar ba?” Cikin sautin kukan tace, “toh ai naga kasan da shiga na, kawai kawani kama ka bud’e mutum...” ta fashe da kuka.
“Fannah ai ba da gangan na bud’e miki ba na manta ne.”
“Bawani mantuwa wallahi...” ta k’are maganar cikin kuka.
“Toh acewarki zan bud’e ki ne da gangan? Mezan kalla a jikin naki? Mschw!” ya fad’a a tsawace. K’arfin kukanta ta dad’a.
“Okay, okay I’m sorry I should have knock still, bar kukan kinji?” Batace dashi komai ba tacigaba da rera kukarta.
“I said I’m sorry, kinji?” Nanma shiru.
“Ko sena shigo zakiyi shirun?” Still batace komai ba. Handle na bayin ya waina.
“A’a dan Allah karka shigo” ta fad’a cike da tashin hankali, k’ok’arin jawo towel nata take amman takasa.
Murmushi kad’an ya saki, ,“zakiyi shirun?”
“Eh zanyi, nama nayi, nayi dan Allah karka shigo.” Daga nan ya koma kan gado ya zauna yana jiran fitowarta se canza tissue yake jinin bebar zuba ba har yanzu. Tuntuni Fannah ta gama wankan amman tak’i fitowa batasan dawani idon zata sake kallon Anas ba. Har yanzu takasa believing abinda ya faru d’azu. Ganin about 10 minutes har yanzu tak’i fitowa Anas yace, “Fannah wai haihuwa kike cikin barhroom d’inne?” Chan k’asa k’asa tace, “bansani ba wallahi da kallon tsireci ba haramun bane dana rama nima, nasan dagangan ka bud’eni.”
“Fannah I will open the door in baki fito ba.” Ya fad’a a lokacin dayake takowa zuwa bakin k’ofar. “I have a cut on my finger I need to wash it ki bud’e.” Tana jinsa tak’i koda motsawa, tsaye take sanye da hijabinta gaban mirror.
“I’m couting to three in baki bud’e ba I will saboda nasan kin gama wankan tun d’azu. One... Two...” Duk tana tsaye tana jinsa “Three!” Karap ya bud’e k’ofar tsaye yaganta gaban mirror “awww kinaji na dama?”
A ranta tace kad’au yanzun ma ba kaya zaka ganni ko? Seka koma.
“Fannah I’m talking to you.” Ko d’ago kai ta kallesa batai ba dan batason sake had’a ido dashi gefensa tabi ta fice nan yayi treating ciwon nasa yafito shima.
Bayan fitowarsa ya tarar da ita zaune kan gado tayi jugum ga d’an hawayen dake forming cikin idanunta. A farko yayi niyyan ignoring nata sekuma ta basa tausayi, itan da ko cinyar ta batason agani bale ache duka aka ganta. Takowa yayi zuwa gabata batako noticing nasa ba saboda yadda tayi zurfi cikin tunani. “Fannah” ya kira sunanta a nitse, nanne hankalinta ya dawo jikinta kai ta d’ago, idanunsu na had’uwa tayi saurin kawar da kanta tare da sa hannu tana share hawayenta. Mik’ewa tayi dan ciro mai nata ta shafa tazo bin gefensa kenan ya rik’o hannunta tare da dawo da ita baya. Kukan da take k’ok’arin had’iyewa ta soma, kallonta ya tsaya yi be hanata yiba seda tayi me isarta sannan yasa hannu yana share mata hawayen. “I said I’m sorry I didn’t mean for it.” yace cikin wani irin salo. Kai kawai ta gyad’a masa tana k’ok’arin karb’an hannunta.
“Baki hak’ura ba?”
“Na hak’ura” tace ba tare da ta d’ago kai sun had’a ido ba. Hannu yasa k’ark’ashin hab’anta tare da d’ago ‘yar fuskarta yana kallo har a yanzu tak’i barin su had’a ido.
“Fannah you’re not, look at me” k’in kallonsa tayi. “Please...” anan ne ta d’ago idanunta ta azasu kan fuskarsa “I’ve looked at you, shikenan?” Tasa hannu ta sauk’e hannunsa daga fuskarta. Gefensa tabi ta d’au mai nata zata shiga toilet dan shafawa ya dakatar da ita ta hanyan kiran sunanta. Chak ta tsaya “I’ll excuse you kinji? You don’t have to go in there.” Be jira jin me zatace ba ya fice, ajiyar zuciya ta sauk’e. A nitse tasamu ta shafa manta tasa wani sabon atamfa d’inkin riga da skirt tagama shirinta tsaf sannan ta mik’e a kan gado. Har ayanzu Anas be dawo ba, da kwanciyarta bekai da minti biyu ba akayi knocking bisa k’ofar. Tashi tayi dan bud’ewa seta tuna da dokar da Anas ya kafa mata seda tasanya hijabi sannan taje ta bud’e.
Tsaye ta tarar da Anas, “can I come in?” Ya tambayeta. Kai ta gyad’a masa tare da matsa masa. Bayan ya shiga ta rufo k’ofar tare da ajiye hijabin a gefe, tayi miqarta kan gado. “kishirya Amal said she wants to see you.” Dama zaman nan d’in ya isheta ba musu ta mik’e ta soma shiri shima haka. Mayafi kalan atamfarta ta yafa duk Anas na kallonta seda ta gama shirin sannan yace, “ina zakije ahaka?”
“Kamar ya ina kuma? Kaifa kace Amal wants to see me.”
“I know I mean da wannan shirin.” Ya nuna ta da hannu.
Kallon kanta tayi up to down bataga wani abin aibantawa ba. “Anas wani abu ne?”
“Yes kisa hijabi baraki fita da wannan gyalen ba.”
“Anas gidanku fa kace zamuje ba wani wajen ba”
“Nasani nide ki cire kisa hijabi.”
“Haba mana Anas nan da gidan kun ma sena sa hijabi ai naga bawani gun zamuje ba gidanku fa zamuje, waze kalleni achan?”
“Shettima da me gadi zasu kalleki nikuma banaso.”
“Yanzu Anas kishin Shettima kakeyi?” Ignoring nata yayi ya nufa wajen akwatunanta, medium red d’in ya bud’e sannan ya d’ago kai yaga kalar atamfar tata yaciro color’n hijab daze shiga dashi. Daga nan ya nufa wajenta mutuwan tsaye tayi takasa koda motsawa se binsa da kallo kawai take. Gyalen nata ya cire ya ajiye a gefe “gashi sa wannan lets go.” Se ayanzu hankalinta ya dawo jikinta “but An-”
“Fannah banason surutu just wear it” ta gefen idanunta ta watsa masa harara sannan ta cire d’an kwalin nata ta b’urma hijabin.
“Perfect!” yace a lokacin dayake kallon ta. “Lets go” ba abinda Fannah ke banda bin Anas da harara ahaka har suka isa zuwa wajen motarsu ya bud’e mata tashiga sannan ya rufe.
★‡★‡★‡
Haka de rayuwa tacigaba da kasance ma Anas da Fannah. Anas yana tsantsan kishin Fannah, ko kad’an bayason wani d’a na miji yagane mata jiki musamman inya tuna ranan da ya ganta a bathroom. Shi karan kansa yasan yasoma sonta yanzu saide bayya tsammanin ze tab’a fad’a mata ‘cause har a yanzun bawai yayi accepting bane yasan sarai da ze samu wani yayi mai bayanin how he feels towards Fannah cemasa za’ayi yana sonta, abinda bayya son ji kenan. Sesa har ayau yak’i yarda wai sonta yake. Ko zaune yake a office muddin da pen a hannunsa bai sanin seda yake soma rubuta sunanta akan paper, a kullum burrinsa yadawo hotel nasu ya samu Fannah.
Ta b’angaren Fannah ma duk kanwan ja che, sede ita tayi accepting son da take masa amman kuma barata bari son yaje ko ina ba saboda rashin martabar ta, she don’t want to be broken.
Ba laifi Fannah da Anas suna shiri yanzu danko se su d’au kwana biyu basuyi fad’a ba amman gasa bak’ak’en kalamu kam na nan, da abun ya tab’o Mr. Fauzi kuwa se yayi dalilin dazesa zasuyi fad’a at the end kuma yazo yana bata hak’uri.
***
Da bikin auren Anas da Fannah wata d’aya cus kenan, cikin wattani shida dasukayi agreeing akai. Anas ya biya Fannah first salary nata wanda yake N500,000 duka ta d’au ta dank’ala wa Mami akan sukai Baba National Hospital Abuja a dubasa dakyau amasa duk wani abinda ya kamata. Koda da Mami ta tambayeta a ina tasamu uban kud’i haka ce mata tayi Anas ne ya bata shiko koda da Mami takira sa dan masa godiya be nuna mata wani abu ba.
Alhamdulillah! Su Mami sunje sun dawo lafiya qalau da zaran Baba ya shanye magunansa ana fatan masa waraka.
**
Yanzu Fannah take gama had’a musu kayakinsu ansamu an gama masu sabon gidansu, she is super excited taga gidan musamman ma dataji Anas ne ya zana da hannunsa. Bayan ta gama had’a musu kayakinsu duka yasa aka sauk’o masu dashi aka kai mota wajen biyan bills ya nufa yayi settling. Fannah na zaune a mota tana jiransa. “Lets go?” Yace da ita alokacin daya kunna motar. Kai ta gyad’a masa cike da jin dad’i “yes.”
Unguwar Giwa Barack yajasu chan inda sabon gidansu yake, daidai gabar wani mansion Anas yasa kai, gate d‘in na identifying plate number’n motar nasa seya bud’u da kansa. Baki Fannah ta sake cike da mamaki, kasa b’oye mamakin nata m tayi ta tambayesa. “Anas dakansa yake bud’uwa?” Be amsata ba seda yayi parking a lot sannan yace, “yes ‘yar k’auye dakanshi yake bud’uwa dakuma kulluwa muddin anyi registering plate number’n.”
“Owwww!” tayi exclaiming tana gyad’a kai. “In d’an wannan kina sake baki nakega by the time muka shiga ciki zakimin littering marble floor na miyau.” Harara ta galla masa ta gefen ido. “Lets go in” yace da ita. Atare suka fito ta tsaya k’are wa gidan kalloi, flat mansion ne me penti fari daga sama se divider milk k’asan kuma brown, tunda Fannah take bata tab’a ganin gida katafare me kyau ba kamar wannan ba sede a TV show. Juyowa yayi ya kalleta seyayi murmushi ganin yadda ta kasa rufe baki, hannunta ya fisga “lets go” wajen garden yasoma kaita gabad’ai wajen green carpet ne seda coloured flowers wanda suka sake k’ayata wajen, a gefe guda kuwa bishiyoyi ne da dama kamarsu guava, mango, banana, dates (dabino) da sauransu. Gaba da wajen kad’an aka yi wani ‘yar runfa me kyan gaske, cikinsa tables ne guda biyu da kujeru hud’u-hud’u a kowanne. Daga gun garden ya wuce da ita swimming pool an k’ayata sa sosai, daga chan suka sake dawowa gaban gidan inda yake ajiye motocinsa da ko plate number ba’a sa musu ba alaman na kwalya ne bawai na hawa ba. Sabin motoci ne pil sauran ma ko b’are ledojin jikin ba’ayi ba, irgawa ta soma da Anas ya gano haka seyace “ba sekin b’ata lokacin ki ba guda 7 ne kacal lets go in.” Haka yajata zuwa main door d’in. K’ofar kad’ai ma abar kallo ce. Irin manyan security doors d’innan ne. Password d’in yasa anan k’ofar tayi kukan “welcome home Mr. Fauzi and unknown.” Nanma seda Anas ya rufa ma Fannah baki yau tana ganin ikon Allah k’ofa na magana. ‘Yan danne danne yayi jikin k’ofar se ya sake managa “Mrs. Fauzi added to family list, welcome home.” A hankali ya bud’u suka shiga ya sake rufe kansa.
Kaftareren parlour ne da had’ad’d’un frames, wallpaper da verses, cushions na cikin farare swal seda colourful throw pillows jere akai. Rug d’in dake parlour’n na nan colourful shima. Cinema (babban TV) ne manne jikin bangon kai tsayuwa dan bayanin had’ewan gidan youngest billonaire b’ata lokaci ne ayita imagining kawai nagaji(LOL) Haka yabi ko ina cikin gidan ya nunnuna mata Fannah de takasa magana har a yanzu inbanda wow datakeyi ba abinda ta iya tace, jacuzzi ko ina cikin bathrooms banda d’akin Anas dake nan harda Live CNN connected ciki.
Bayan da suka gama biye ko ina cikin gidan suka sake dawowa parlour, daba dan Anas ba da Fannah ta b’ace cikin gidan danko ta manta hanyan da suka bi. “So kinga d’akin ki ba? The purple one, nikuma nawa ne farin, we will no more be sharing a room.” Cewar Anas, da biyu yayi maganan danko yasan sarai Fannah da uwar tsoro barata iya kwana ita kad’ai a d’aki ba. Idanun ta ta d’aga ta aza akansa. “Eh nagani this is a wonderful house, kudos to you. Amman Anas nikad’ai zanna kwana cikin makeken d’akin chan??” Ta tambaya tana zaro idanunta.
“Yes ke kad’anki-” katsesa tayi.
A’a dan Allah Anas wallahi barin iya kwana ni kad’ai ba kayi hak’uri please, ko a k’asa ne a d’akin ka zan na kwana.”
“Why?” Ya tambayeta yana me jin dad’i amman se nuna ma ta yake kamar bayyaso.
“Anas a list na contract namu ai bakace za’a na raba kwanciya ba, kuma kafa san mutumin, wallahi ze dawo dan Allah karka min haka.” Cruel smile ya saki, “I will think about it.”
“Anas please...” Ta rok’esa.
“Okay naji” yace ganin zata soma masa kuka. Dad’i taji sosai wanda ta kasa b’oyewa.
“Ermmm... Anas nace d’akuna nawane a gidan duka?”
“Ke wani irin brain ne dake daman ba k’irgawa naga kinayi ba d’azu?”
“Nafara irgawa sena rikice.” Kallonta yayi ta gefen ido, “fish head” yace a hankali. Sarai tajisa amman tayi shiru. “Guda 7 ne including guest room seda parlour biyu dakuma toilets 7 se kitchen d’aya da store room biyu. Clear?” Kai ta gyad’a a hankali tare da had’iye miyau. Sede daya kalli fuskarta ya gane tanada tambaya.
“Say it out”,yace da ita.
“Ermm. Anas duka d’akuna 7 d’in zanna sharewa ni kad’ai?”
“Eh da meh aikin ki? Aure fa kikazo yi ba hutu ba Fannah.”
“Anas nasani amman...” se kuma tayi shiru “kad’an taimaka please ga shara ga mopping gakuma girki yi hak’uri.” Murmushi ya saki wanda fararen hak’waransa na sama kad’ai suka bayyana.
“Karki damu akwai masu aiki zasu na zuwa morning and evening suna duk wani aike-aiken, abinda zakina yi kawai cooking ne dan ba daga hannun kowa nakecin abinci ba, kema se kinyi sanitizing hannunki tukuna, clear?”
*© miemiebee*
TANA TARE DA NI...
TANA TARE DA NI... PAGE 63BY MIEMIEBEE
Assalam, as I promised zan bud’e new blog address, I did and its beeenovels.blogspot.co.ke *so to my blog readers lets hit! Thanks for the love and support and also for the warm prayers, love you all!*
*Also masu cewa nayi repeating page 62 twice a’a ku gane mutane ke yi ba ni ba, ina miyar da hankalina sosai wajen numbering pages so take note bana mistake anan. Masu editing min pages nasan kwad’ayin son next page ke saku yi amman kuyi hak’uri ku dena please kuna janyo confussion*
Kallonsa ta tsaya yi danko be isheta da kallo ba wai har setayi sanitizing hannu tukuna ta masa girki, shima kallon nata yake da gira d’aya a d’age. “Baki jini bane? Nace you need to sanitize those hands” ya kalli hannun nata “before cooking for me” Kallonta ta kawar daga garesa ba tare da tace komai ba. Taku d’aya ya k’ara kusa da ita tare da rufe gab dake tsakaninsu da sauri tayi taking step backward, ganin haka ya k’ara 1 step forward haka suka tayi seda yakaita jikin bango, wani irin kallon tsiya yake mata da tuni yasa zuciyarta bugawa fat-fat.
“Kinji ni?” Yasake cewa da ita alokacin dayake kallon lips nata. Kai ta gyad’a cike da tsoro “nn... Na... Naji.” bending wuyansa yayi ta hanyar matso da fuskarsa kusa-kusa da nata dududu ratan dake tsakaninsu befi inchi d’aya ba. K’ara dad’uwa bugun zuciyarta yayi a yayinda k’arfin numfashinta ya dad’u. “Anas pl-” bata k’are maganar ba ta matse idanunta gam ganin Anas yasake matso da fuskarsa kusa da nata, har had’ewa numfashinsu yake.
Juyawa tayi zata bi gefen damanta dan guduwa, karap ya aza hannnsa jikin bangon ya dakatar da ita, haka ma yayi a gefen damanta “Anas please ka ba-” bata k’are maganar ba taji ya kunna switch d’in wuta daga jikin bango tare da matsawa baya. Shu’umin murmushi ne fal d’auke a fuskarsa “Da me kika d’au zan miki? LOL such a negative thinker. You thought I’ll kiss you right?” Wani irin kunya taji ya rufeta ji take kamar ta tone k’asa ta b’oye kanta, gabad’ai ta gama tsorata ta d’au kissing natan zeyi, amman dan iskanci ze kunna wuta shine seyayi kalan abinda ya mata? Mschww.
“Ni ba abinda nake nufi ba kenan” ta fad’a dan kare kanta tana kallon k’asa.
“Whatever ba sekin min k’arya ba.” ya fad’i da wani murmushin tsiya fal a fuskarsa. Ganin batada abinda zata ce masa kawai ta fara tafiya dan barin parlour’n although batasan ina take dosa ba. Kallonta yake ganin ta d’au hanyan store room ya tsayar da ita ta hanyan kiran sunanta, “Fannah!” Banza dashi tayi tana me cigaba da tafiyarta. “In d’akin ki kike nema that is not the way, you go right” ya nuna mata da yatsa. Bata ko tanka sa ba tabi right d’in ta fice. Achan ta samu d’akinta.
Akan gado ta zauna se kai take girgizawa ta matse idanunta gam har a yanzu kunyan abinda ya faru tsakaninta da Anas d’azu take. Tsuka taja a fili “mscwh! Ai seya d’au dama tunba yau ba ina expecting kiss daga garesa, Ya Salam!”
Knock ne yashigo daga k’ofarta. Kafin tace zata bud’e tajiyo muryan Anas “ga luggages naki and ba zama zakiyi cikin d’akin ba am hungry kifito ki dafa min dinner, kinji?”
“Naji” tace chan k’asa k’asa. Seda ta tabbata yabar wajen ta bud’o k’ofar tashigo da akwatunan nata tare da ajiyesu wajen ‘yan uwansu. Hijabin jikinta tacire had’e da kayan ta, sannan ta ciro wani silky white fitted doguwar riga me spaghetti hands tasa tare da sake maida hijabin nata. Anan ne ta fito, seda ta tabbata ta rufe kusan rabin fuskarta da hulan hijabin nata sannan ta fara neman hanyan kitchen se addu’a take Allah sa kar su had’u da Anas aiko tana leqa parlour ta gansa zaune kan one seater, vest ne da shorts a jikinsa kad’ai yayi cross legging k’afa. Kafin ta koma baya yaganta “come back” ya fad’i a lokacin da yake ajiye newspaper’n hannunsa a kan side table. Numfashi ta saki sannan ta tako parlourn idanunta matse gam.
“Gyara hijabin naki.” Banza dashi tayi, “don’t let me repeat myself.” A hankali ta miyar baya idanunta na a k’asa har yanzu. “Good, so me zaki dafa mana.”
“Nima bansani, tell me what you want.”
“Just cook anything yummy good. I hope kin iya girki banason jagwal-gwale.” lallai ma tace a ranta. “Yes...? Kin iya?” Kai kawai ta gyad’a masa seda ta juya ta soma tafiya yasake kiran sunan ta kamar wacce zatayi kuka ta juyo.
“Cire hijabin, ko bakisan ba’a shiga kitchen da hijabi ba? Ba fata ba what if mistakenly hijabin naki yakama da wuta fah? Kicire.” Ba k’arya a maganansa dankuwa ko Mami ta hanata shiga kitchen da hijabi hannu tasa zata cire sekuma ta tuna kayan dake jikinta ai seta miyar da hannun nata baya.
“Cire hijabin ne baki iya ba?”
“Na iya excuse me inje d’aki incire.” nan ta juya.
“Not excused, dawo kicire anan Fannah banason surutu.”
“But Anas-”
“But Anas what?” Ya katse ta. “Mene a jikin naki ban gani ba” se yad’an tsaya ya murmusa, baki ta murgud’a masa ganin bai kallonta. The moment ya sake d’ago idanunsa ya aza akanta kuwa seta kawar da kanta “just take it off before I lose my temper.”
“Anas ai zan cire amman ka bari inje d’aki mana ko anan zan ajiye?”
“Eh anan zaki cire kuma ki ajiye, I’m hungry kina b’ata min kokaci.” Zata sake magana ya daka mata tsawa “Now!!” Bata san seda ta cire ba se b’ari take. Mak’ale hijabin tayi a k’irjinta da hannayenta bibbiyu akai se kallon gefe da gefe take tana b’ari.
Wai ita da ace atamfa ne a jikinta da barata damu ba amman wannan shegen kayan datasa dan shan iskan ne ke damunta.
“Oya ajiye ki bani waje.” Fuska ta maraice “Anas kayan jikin nawa ne... Erm... Erm...” Yi yayi kamar ze nufi wajenta atake ta ajiye hijabin kan kujera. Murmushi ya saki tare da sake daidaita zamansa cikin kujeran. Kallo ya k’are mata up-to-down anan ne ya gano dalilin da batason cire hijabin.
Hannu tasa ta soma kare k’irjinta ganin haka ya mata nuni da hannu da nufin ta basa waje “go am not interested” yace da ita chan k’asa k’asa kuwa ba abinda yakeso kaman kallon jikin Fannah. Juyawa tayi ta soma tafiya. Bin bayan ta yake da kallo yana murmusawa abinsa. Se anan ta tuna kayan jikinta silky ne showing komai yake gashi batasa underwear skirt ta ciki ba, kayan nata ta soma ja tana kare bayanta, ahaka harta fice daga ganinsa. Murmushi kawai yake, leb’b’an k’asan sa ya cize tare da d’ago newspaper’n dan cigaba da karantawa sede sam yakasa dena tunanin Fannah.
50 minutes later...
Rik’e Fannah ke da wani had’ad’d’en food warmer a hannunta ta lab’e jikin k’ofar kitchen d’in tarasa ya zata k’ariso gaban dining table ta ajiye, ganin ba Ubangiji se Allah kawai tasa kai ta ajiye idanun Anas na akanta. Bayan ‘yan mintuna ta gama jera kan dining d’in tare da d’iba macaroni da co-slow data girka musu a plate nata. Parlour’n ta k’ariso har a yanzu Anas bebar kallonta ba ignoring nasa kawai tayi. Seda ta d’aga hijabinta da d’ayan hannun ta tace, “dinner is ready.” Daidai ta juya kenan Anas yayi tsalle daga kan kujerar dayake zaune akai se gabanta har tsorata tayi. Plate na hannuntan ya soma amsa, “Anas my plate gachan naka a flask a dining.”
“I know” yace da ita tare da amshe hijabin d’ayan hannun nata ya miyar kan kujerar. “Anas hijabi na.” ganin ta mik’a hannu zata d’aga yayi saurin d’agawa yayi wulli dashi achan k’asa yayi decending. Kafin tayi magana ya rik’o hannunta har gaban dining table ya jata.
D’aya daga cikin kujerun yaja mata kallonsa ta tsaya yi. Abincin ya ajiye a gabanta sannan yace, “sit.”
“But-”
“Anan zakici so sit banason surutu.” Badan tanaso ba ta zauna yaja mata kujerar ciki. Opposite da ita ya zauna shima. “Serve me.” Kai ta d’ago tana kallonsa lallai ma Anas, ayi masa girki akawo masa, zubawa ma yace se anyi masa? Sauran chi ma kace ni zanbaka. Katse mata tunani yayi “well? I’m hungry.”
“Toh Anas barin d’auko hijabi na please.”
“Fannah I like you this way, the only time zakisa hijabi is in zamu fita ko munyi bak’i but in ni da ke ne banaso, kinji?”
“Naji amma-”
“Chapter closed” ya katse ta. “Now serve me dinner.” Mik’ewa tayi duk she is feeling uncomfortable ta bud’e flask d’in ta zuba masa abincin da co-slow se binta da kallo yake adaidai gabansa ta ajiye tare da tsiyaye masa exoctic juice cikin cup sannan ta koma ta zauna. Spoon d’aya yakai ciki har ya bud’e baki ze fara mata masifa seyaji girkin yayi dad’i komai is perfect, be tab’a cin macaronin daya mai dad’i kamar wannan ba no offense amman Fannah tama fi Ummie iya girki. Wasu biyun ya k’ara kaiwa cikinsa itade Fannah kallonsa kawai take. “Anas bakace komai ba” ta fad’a kanta a sunkuye.
“Me kikeson inche? Maggi yayi yawa kokuma gishiri?” Gira ta had’e takai spoon d’aya baki itama sekuma taji komai yafita daidai. “Amman Anas ba abinda yayi yawa fa, zak’in is okay.”
“Toh ni bemin dad’i ba, ahaka ne kin iya girkin? Dan de inajin yunwa ne kawai zanchi mschw!” yaja ‘yar k’aramar tsuka. Haka yata loda abincin ita de Fannah na ta ido ne. Mutumin dayace abinci beyi dad’i ba amman yafita chi. Bayan daya k’are plate nasa ya sake dad’awa. Baki tabud’e sosai tana kallonsa.
“I thought kace beyi dad’i ba kuma nga harda k’ari kayi.”
“Nayi ina ruwanki? Yunwa nakeji is not as if kin iya girki.” Murmushi kad’an ta saki danko tasan he don’t mean what he said. Bayan da suka gama chi ta kimtsa wajen. Sallan isha ya jasu.
Bayan nan takoma d’aki tasoma tsefe kitson da Afrah ta mata last 2 weeks. Guda uku kacal tayi tasoma jin tsoron zama a d’akin ita kad’ai, ina ma ace gidan da hayaniya amman sekace mak’abarta shiru. Fitowa parlour tayi ta tsinci Anas zaune kan kujera yana kallon football. Kamar ance Anas juyo ya juya idanunsa basu sauk’a a ko ina ba sekan Fannah dake tsaye da kayan jikinta na d’azu. Kai ta kawar ta tako a hankali ta zauna kan d’aya daga cikin kujerun ta cigaba da tsifarta. Bayan daya k’are mata kallo ya miyar da kallonsa kan TV’n lokaci zuwa lokaci yake satan kallon Fannah, da ta tsefe biyu se ta tsaya taja hannunta normally agida daman ko Mami ko Afrah ke taya ta, dama dama ache kalaba ne takan iyawa da kanta. “Come let me help you” yace da ita. Kai ta d’ago cike da mamaki tana kallonsa. “Eh?” Ta tambayesa fuskarta cike da neman k’arin bayani.
Hannu ya nuna mata “come.”
“Erm Anas don’t worry thanks zan iya da kaija.”
“Baraki iya ba wannan uban gashin kin just come.” Tunanin taje ko a’a karta je take ganin haka ya taso daga mazauninsa ya dawo kan kujerarta. Baya ta matsa da wuri sede kafin tayi hakan ya cafko hannunta tare da karb’e kibiyan. Ta bud’e baki zatayi magana ya kwantar da kanta kan cinyarsa. Wani irin baqon yanayi ta tsinci kanta ciki. “Anas zan zauna a k’asa kar cinyoyonka su maka tsami.”
“Dake ance miki rago ne ni ai.” Shiru tayi bata ce komai ba a hankali taji yasoma tsefe mata kitson. Sake jikinta tayi sannan tace, “thank you.” Yi yayi kamar be jita ba, ”Anas I said thank you.”
“No big deal.” Haka yata tsefe mata kitson har yayi rabi saura rabi wanda seta juya tana fuskantanshi ze iya tsefe mata. “Fannah turn around.” Shiru beji amsar taba. “Ke Fannah!” Fuskarta ya leqa yaga bacci ma take mekyau, lallai ma yace a ransa yana murmushi wato dan dad’in tsifar har tayi bacci. Juyo da ita yayi gabad’ai sannan ya cigaba da mata tsifan. Yanayi yana kallon fuskarta cikin baccin tace, “taya ka iya tsifa haka? Kafi Afrah ma iyawa.” Murmushi kad’an ya saki be amsata ba chan ta sake cewa “haka kitso ma ka iya, god bless you Mr. Fauzi.”
Dariya kad’an yasaki wanda ya k’ara masa kyau seda ya gama ya kama mata gashin gu d’aya tare da d’aga ta ya kaita d’akinta ya kwantar da ita ya rufeta da bargo sannan ya kashe wutar d’akin ya rufo mata k’ofar. D’akinsa ya nufa ya kwanta shima.
_2 hours later..._
Firgit Fannah ta tashi daga bacci around 11:30PM ganin ta soma mafarke mafarken nata, hamdala ta saki ganin mafarkin beyi nisa ba. Gefenta ta tab’a taji wayam ba Anas. “Anas!” Ta kira sunansa, a 360 ta janyo pillonta da bargo tabar d’akin. Ta bud’e nan ta bud’e chan har ta isa d’akin Anas gwada bud’ewa tayi taji a rufe. Knocking take bam-bam. Cikin bacci yace, “who is it?”
Hamdala ta saki jin muryarsa. “Anas please let me in Fannah ce.”
“Bakiyi bacci ba dama?”
“Anas dan Allah ka bud’e.” A kasalnce ya mik’e ya bud’e mata, kallonta ya tsaya yi “what now?”
“Anas mutumin” ta sanar dashi a kidime
“Muje in rakaki ki kwanta toh.” Kai ta kad’a “please lets sleep together.” Abinda yakeson ji kenan dama. “Kaifa kace d’azu ka yarda zamuna kwana tare.”
“Noo Fannah ba abinda nace ba kenan ce miki nayi naji I’ll think about it.”
“Eh toh ni whatever please let me in.” Kafad’a ya buga mata. “Anas please...” Ta maraice fuska tana k’ok’arin k’irk’iro hawaye. “Okay naji shigo” ya matsa mata. Cike da murna tashiga kan gadonsa ta haye.
“No! No! No! No way sauk’a min akan gado, ke baki iya bak’wanta bane? Kin wani zo kin hayemin kan gado, off my bed.” Cike da kunya ta sauk’o tana tattara pillonta da bargo. “Kin manta me kikace d’azu? Cemin kikayi ko a k’asa ne zaki kwana ko ba haka ba?”
“Eh Anas but-” nan ya katse ta ta hanyan aza yatsansa bisa lips nasa. “Shh! so a k’asan zaki kwana.”
“Ayyah Anas mana...”
“Oya zo ki koma d’akin ki.” Da wurwuri tace, “a’a na yarda zan kwanta a k’asan.”
“Good” yace yana murmusawa. Wani babban bargo ya ciro ya mik’a mata “gashi shimfid’a achan” yamata nuni da hannu “ki kwanta in kin gama ki kashe min wuta” yana kaiwa nan ya haye gado. D’agawa tayi ta shimfid’a kusa da gefen gadonsa dan tsoro. A hankali ya bud’e idansa daya rufe “Fannah bafa anan nace ba, achan” ya sake nuna mata da hannu. “Anas I know please let me sleep here chan d’in ina tsoro.”
“Whatever” ya miyar mata. Bayan data gama komai ta kashe wuta ta dawo ta kwanta har a yanzun tsoro takeji, be isheta ba seda tajawo kad’an daga bargon da Anas ya ruhu dashi ta rik’e se b’ari take ta kasa komawa bacci. Shima kasa baccin yayi hankalinsa duk na a wajenta.
“Fannah” ya kira sunanta a hankali.
© MIEMIEBEE
TANA TARE DA NI...
TANA TARE DA NI... PAGE 64BY MIEMIEBEE
Cikin murya me rawa cike da tsoro ta amasa , “na’am.”
“Are you still afraid?” Kai ta gyad’a wane yana kallonta jin shiru ya juyo ya kalleta, ganin hannunta rik’e da blanket nasa ya tabbatar masa tsoro takeji har yanzu. “Come” yace da ita. Abinda take jira dama kenan ba tare da b’ata lokaci ba ta d’ago pillonta ta haye gadon daga chan k’arshe. Matso da pillow nasa yayi kusa da nata. “I’m here kinji?” Yace da ita a lokacin daya aza kanta bisa k’irjnsa. Kai ta gyad’a a hankali tare da zagaye hannunta kan cikinsa, yana shafa bayanta a hankali har tasamu ta koma bacci.
7:00AM
Yanzu take gama had’a dining table, jin shiru Anas be fito daga d’aki ba har yanzu yasa ta mik’e dan duba ko lafiya, tana bud’e k’ofar Anas na bud’e towel nasa dan gyarawa tun d’azu yak’i shiga wanka se a yanzu ya ke fitowa. Ido wuru-wuru Fannah ta zaro tare da sako baki in shock, sandarewa Anas yayi ya kasa rufe towel nasan. Daga bisani taja k’ofar ta rufe alokacin hankalinsa ya dawo jikinsa ya d’aure towel d’in gam bakamar yadda ya saba yiba sakwa-sakwa. “What just happened?” Ya tambayi kansa disbelievingly. “Did Fannah.... Did Fannah? Oh God! No!” Hannu yasa yana hargitsa gashin kansa tare da jan wani doooogon tsuka.
Fannah data sandare har yanzu a bakin k’ofa ta rasa gane ma ko a duniya take ko lahira, kallon k’ofar take har a yanzu baki wangalau har d’igan miyau take. Daga bisani ta kad’a kanta “La ilahi! Ya Salam! Astaghfitullah, Astaghfirullah, Astaghfirullah...” Sede har yanzu bata bar tunanin abinda ta gani ba. “Ya Salam ina Qur’ani inje in karanra.” Daidai zata juya kenan Anas ya bud’o k’ofar d’akinsa kamar ance su kalli juna suka d’ago kai suna kallon juna sun kusan minti suna a haka sannan daga bisani ya kawar da kansa besan meba seya soma jin kunyarta.
“Uhm uhm” tayi gyaran murya. “Anas I’m sorry bansan... Bansan” ta tsaya sosa kai. “Is okay kema kin rama now we are even” ya galla mata harara. Tafiya ya soma ya na nufan dining area binsa ta soma tana fad‘in “Anas ba fa ramawa nayi ba, bansan ka bud’e towel naka ba, da ban shi-” bata k’are maganan ba ya juyo yana mata wani irin kallon dayasa hanjin cikinta d’aurewa. Kanta ta sada k’asa tana murza yatsunta “me kika ce?”
“Babu nace I’m sorry.” ‘Yar tsuka yaja ya k’arisa kan dining d’in bayansa tabi tayi serving nasa, nan ta d’ibi nata itama ta zauna ganin haka ya mik’e. “Anas ina zakaje?” Be kalleta ba yace, “d’aki.” Hannunsa ta rik’o ta dakatar dashi “wait, mesa?”
Idanunsu na had’uwa ya kawar da kansa “sake min hannu unless you want me to be late for work.”
“Anas I said I’m sorry nid’in baka kalleni bane...” Sekuma tayi shiru “sit kaji? Lets just assume ban gankan ba, lets all say it never happened okay?”
Kai ya gyad’a mata ya nisanta “but the picture of me... Erm it is still stocked in your head, right?”
“No nayi deleting babu bangani ba, sit kaji?” Hannun nasa ta sake a hankali ya zauna bayan sun gama ya koma d’aki ya sako suit nasa tare da saqalo jakar laptop nasa, wanka da turare yayi as always sannan yafito alokacin ta koma d’akinta ita kuwa.
Har yakai bakin k’ofa sekuma ya dawo ya nufa d’akinta, knocking yayi ta taso ta bud’e masa. Besan me ba seyaji yanason sanar da ita ze fita, “I’ll be going” yace da ita yana kallon k’asa.
“Okay Allah ya kare, what will you like for lunch? Oh sorry jiya kace girkin beyi dad’i ba just buy something and eat.” K’ofar ta miyar zata rufe yasa hannu chak ta tsaya. Hannunsa yasa k’ark’ashin hab’anta “Fannah I don’t mean any of those words, I was joking actually you’re the best cook.” Ya k’are maganar yana mata murmushi.
Sosai taji dad’i “do you really mean what you said now?” Kai ya gyad’a mata “yes Fannah I do, you are best at cooking.”
“Thank you so what will you like to eat today?”
“Anything I trust you, I’m going now.”
“Okay Allah ya kare.” Har ya juya se ya dawo ya rik’e kanta da hannayensa biyu tare da aza mata hot peck a goshi, wani irin nishi ta saki ta d’ago kai tana kallonsa cike da mamaki, kashe mata ido d’aya yayi (wink) sannan ya sakar mata dawani murmushin daya sosa mata zuciya d’aki ta koma da gudu tare da rufo k’ofar. Kan gado ta fad’a takasa dena murmusawa. “He pecked me! He pecked me! Omg! This can’t be happening” wajen mirror ta nufa tana kallon goshinta daidai inda Anas yayi kissing wani sanyi taji ya ratsa ta se murmusawa take. Kasa riqeta k’afafun nata sukayi ta sulale k’asa sewani blushing take tafi 30minutes ahaka sannan ta tattara kanta tashiga bayi tayi wanka.
Shima Anas yana zaune a office amman hankalinsa na akan Fannah he can’t hide it anymore. “Yes I’m in love!” ya fad’a a fili dawani murmushi ta gefe guda a fuskarsa. “Theres no denying again I love Fannah, I’ve said it, I love her and I have to let her know. I don’t know how it all happened but I don’t want her out of my life, zan sameta in mata magana muyi canceling contract marriage d’in I’ve got to tell her I love her.” Daidai nan knock yashigo “come” yace. Kacallah ne ya k’ariso “good morning Sir.”
“Morning” yayi greeting nasa back. “Any papers to sign?”
“Oh yes, yes Sir” ya amsa tare da gabatar masa da papers d’in bayan da Anas ya gama signin yace;
“Erm.. Sir ansamu matsala da wiring na 2nd and 3rd floor electrician namun yakasa gyarawa.” Jira kawai Kacallah yake Anas yace masa ‘kaje kace masa he is fired and find someone better kayi replacing nashi’ to his suprise Anas yace, “kaje kace masa ya sake gwadawa inya kasa anemo external electrician yatayasa su gyara okay?”
Baki Kacallah ya bud’e yana ganin ikon Allah, anya kuwa Boss ne?
“Kacallah kajini kuwa?”
“Yy.. Yes Sir naji, thank you.”
“You’re welcome.”
“Wow Sir you seem in a good mood today.” Seda yasaki brightest smile nasa sannan yace, “yes I’m happy today Kacallah, kaje kayi ordering friedrice and chiceken from Int’l Hotel for free ma kowani staff anan harda cleaners.”
“Wow... Wow thank you so much Sir.”
“You’re welcome.” Bayan Kacallah ya fice Anas yayi grabbing pen da paper ya fara had’a name nasa dana Fannah. Sunan Enterprise nasa yakeson canzawa. Yayi ya goge yayi ya goge haka yatayi...
3:40PM
Aiki sosai Fannah keyi a kitchen yanzu tagama had’a kidney sauce, stew nata ma nan a ajiye ta riga ta gama coconut rice d’in take jira ya nuna ta sauk’e. D’inkin lace ne red and black, riga da skirt sanye ajikinta ya mugun amsar jikinta. Sab’anin kullum yau tad’anyi applying makeup tayi lining tasa mascara ta taje dogayen lashes nata kamar yadda Afrah ta koya mata. Jan janbaki ne mekyau a bakinta sosai tayi kyau, tad’an kitsa calaba k’ananu guda uku tacirosu tagaba wanda tsayinsu ya sauk’a a kasan k’’irjinta da kad’an.
Parlour tafito dan shan iska kafin shinkafan ya nuna rurin wayarta yasa ta mik’a hannu ta d’ago daga kan centre table ‘Anas’ taga ke kira. Take taji wani erin farin ciki ya rufeta wanda sakamakon haka yasata murmusawa sosai a nitse ta d’aga tare da komawa kan kujera ta zauna.
“Hello...” Tace
“Hey Fannah” yace da ita batasan meba amman seji tayi kamar yau ta fara sauraron muryan Anas danko be tab’a mata dad’i haka ba.
“Na’am, Anas.”
“So what are you doing?”
“Nothing just cooking.”
“Yummm thats why nakejin k’amshin spices naki har anan.” Dad’i sosai taji se blushing take.
“Awwn! Anas don’t flatter me.”
“Am serious, yestarday’s dinner was great.”
“I hope you enjoy today’s also.”
“Ofcourse I will tunda hannayenki ne suka girka.” Kallon hannun nata tayi setaji wani sonsu ya shigeta.
“So me kika girka mana?”
“Its a suprise, ya office?” Ta canza musu topic d’in.
“Boring I miss seeing you over that cushion.” Dariya kad’an tasaki cike da k’asaita. “I miss you shouting at me too, I miss you making me correct 500 papers.”
“Oh common Fannah, barin k’ara ba unless ke kikeson kiyi, which I won't let you.”
“Mesa?”
“Saboda your hand will ache nikuma banaso.”
“Ohh really? Ada da kake sani bakasan ze samin ciwon hannu ba kenan.”
“Yanzu da da aiba d’aya bane Fannah you know that.”
“No I don’t, tell me” ta fad’i tana murmusawa tare da ciza yatsan ta d’aya a hankali.
“You used to be my PA but now you’re my wife I... I care about you... Like alot.” Wani irin dad’i taji, ji take kamar an tsunduma ta cikun Al~Jannah. Shiru tayi ta kasa mayar masa da amsa.
“Hello Fannah, you there?”
“Uhm yes” ta amsa chan k’asa k’asa. “I said I care about you.” So take tace masa she cares about him too amman kunya bare barta ba. “Fannah don’t you care about me too?” Shiru tayi takasa cewa komai. “Toh shikenan am hanging up.”
“No don’t” ta hanasa. “I care about you also.” Take ta kashe wayar tare da rungumesa a yayinda shikuma yashiga photos yana viewing pics nata yabi ya k’osa 4:00PM ya buga yaje ya kalli FLOWER nsa danko haka yayi re-saving numbanta a wayarsa yanzu.
4:10PM
Password ya danna k’ofar yayi welcoming nasa. Fannah najin Mr. Fauzi tasoma cin faracunta. “What do I do now?” Ta tambayi kanta. Kwata kwata ta mance ta bar abu kan wuta taje chan tanata waya da Anas ga shinkafan ya k’one yanzu. Daidai ta aza new pot kan tukunya kenan Anas ya dawo. Kafin ta sauk’e pot d’in daga kan gas ta b’oye inaa Anas ya riga yasa kai cikin kitchen d’in.
“Hi” ya ce da ita. A kidime ta juyo ta kallesa wani kyau taga ya k’ara mata kamar yadda shima yake kallonta tayi bala’in masa kyau. A hankali ya tako izuwa gabanta. “Oh hi welcome back.”
“Thank you, is lunch ready? I’m starving-” ya tsaya yad’an shinshine kitchen d’in “is something burning?”
A rikice tace, “no, nothing ka koma parlour and wait for me, lunch will be ready in the next 30 minutes.” Daya karanci fuskarta seya ga kamar tana b’oye masa wani abu. “Fannah are you hiding something?” Ya tambayeta tare da rik’o hannunta yana murzawa a hankali. So take ta masa k’arya amman sam takasa jin hannunsa akan nata. Sad face take wearing. “Anas I’m sorry shinkafan ya k’one, I’m sorry please kabani 30 more minutes zan sake dafa wani.”
“Is that why you’re sad?” Kai ta gyad’a a hankali, “I’m sorry.”
“Mugani” yace da ita yana k’ok’arin bud’e pot data b’oye a bayanta.
“A’a’ah Anas please don’t kaj-” bata k’are maganar ba ya matsar da ita gefe guda kamar doll baby tare da bud’e pot d’in. Murmushi yayi kad’an “wannan ne ya k’onen?” Kai ta gyad’a a hankali nan ma.
“We can eat it kinji?”
“Anas we can’t ya k’one zan dafa sabo.”
“NoFannah karki tak’ura wa kanki kinji? Ina food warmer’n injuye a ciki.”
“Anas...” Ta kira sunansa kan wacce zatayi kuka
“Trust me, you wasted your time kika dafa I don’t want your sweat to go in vein. So karki damu kinji?”
“Thank you” nan ta mik’o masa flask d’in tana ganinsa ya juye ciki ashe ma k’asa k’asan ne ka
bantabajin book Din dakesani Nishadi irin wannan ba Allah Kara basira
ReplyDeleteD most sweatest buk i ever read in my lyf.allah kara basira miemie
ReplyDeleteagaskiya littafin yaburgeni sosai
ReplyDeleteyayi did sosai
ReplyDeleteShukran
ReplyDeleteGaskia book dinnan yayi dadi allah ya kara basira
ReplyDeleteagaskiya Littafin nan yahadu bantaba karanta littafi maidadi irin wanan ba,Allah yakara karfin ido da laushin hannu ,Allah yakara basira
ReplyDeleteJazakallahu khairan
ReplyDeleteAllah yakara basira da kuma ilimi mai amfani
ReplyDelete