shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday 7 September 2016

TANA TARE DANI...31--35

tana-tare-dani.jpg

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 31
BY MIEMIEBEE


“Am I clear?” Ya tambayeta.
   “Yes” tace murya chan ciki-ciki. “Good” daidai lokacin wayarsa ya soma ringing take ya d’aga “okay I’m on my way.” Ding! ya katse. Suit nasa ya jawo yasa yasake feffeshe turare jikinsa, Fannah duk tana tsaye ko kallon direction nasa batayi bale ya chakka mata magana. Wayoyinsa ya kwasa “follow me” yace da ita. A sanyaye tabi bayansa ganin ya nufa wajen personal elevator’n sa yasa ta juya dan bin na public kafin ya mata wani rashin mutuncin, duk abinda tasan ze jawo masu matsala k’ok’arin kiyaye sa take. Sanda ya bud’e yashiga elevator’n sannan yayi noticing Fannah bata biye dashi chan ya ganta tana nufan gun d’ayan elevator’n. “Miss Aleeyu!” ya kira sunanta a tsawace chak ta tsaya tare da juyawa. “Baki ji me nace bane? I said follow me.” Ya sake nanata kansa.

        “Sir-” bata k’are maganar ba ya katse ta “acikin rules d’ina na fad’a miki banasan muna musu.” Kanta sunkuye ta je ta samesa tana shiga ya rufe elevator’n, daidai nan wayarsa ya soma ringing daga side pocket na suit nasa, yana ciro wayar number ya bayyana kai bayan yayi nazarin wake kira ya d’aga danko baya saving number’n ‘yan mata a wayansa in bawai ta kama ba “hello Salmah?”
   “Cute eyes, ya kake?” tace dashi
   “Lafiya” ya amsa ta.
    “Cute eyes godiya nake son sake maka, dress daka kawo min ya had’u sosai, thank you.”
  “Don’t mention hun, zani meeting yanzu zan kiraki later.”
  “Okay cutie.” Nan yayi hanging. Fannah dake sauraransa kai kawai ta kad’a, dan aikinsa kenan a ‘yan satukan data masa aiki kwanaki bata san ‘yan mata nawa yayi dumping ba. Tsantsan so yake nuna masu na ‘yan kwanaki yana gaining trust nasu seyace suyi break up, ita ta rasa wani erin player ne Anas.

    Elevator’n na bud’uwa ya sa kai ya fita itama haka tana biye dashi. Wajen da ake ajiye masa key ya nufa chan yama driver’nsa magana dan yau baya jin driving. Bayan sun isa wajen motar nasa driver ya bud’e masa k’ofa “enter” yace da Fannah. Cike da mamaki take kallonsa kamar ya enter ina yakeson kaita?
    Katse mata tunani yayi, “incase kina wondering ko zan kaiki cin abinci ko shopping ne you are mistaking, you are my PA duk inda zanje dake zanje so get in.” Miyau ta had’iye ta shiga ta wuce can k’arhen gefen motan a yayinda shima ya shiga. Haka kawai taji zuciyarta na bugawa duk sanda ita da Anas suke kusa da juna se tana jin wani eri ba dad’i. Bayanin inda zasu yama driver’n a hankali ya soma tuk’i. Ita Fannah ta rasa wani erin san AC Anas yake, hijabi ne a jikinta amman sanyi takeji, hijabin nata ta duk’unk’une dan sanyi, ganin haka Anas ya saki murmushin mugunta ta gefen da dimple nasa yake. “Moosa ka k’ure AC’n zafi nakeji”
    “Okay Boss.” Nan ya k’ure tas! take motan ya d’au wani irin mahaukacin sanyi kallonsa Fannah ta tsaya yi, wato ya gane sanyi takeji shine dan mugunta ya k’ara, ita ba ma wannan ba, duk sanda tasha sanyi sosai pneumonia’n ta tashi yake tun lokacin da akayi raping nata a Bama ruwa ya mata duka take fama da pneumonia tashi tashi.

      “Don’t break my rules nace miki banasan kallo dayawa.” Bata ce masa komi ba ta kawar da kanta dakuma sake duk’unk’une kanta cikin hijabin. Kansa ya jingina jikin kujeran tare da rufe ido bada dad’ewa ba wayar Anas ya soma ruri ganin wa ke kira ya d'aga da sauri “hello an samun?”
   “Yes sir ga details d’in.” Cewar mutumin
    “Okay d’an tsaya please let me get a paper”  Juyowa yayi ya kalli Fannah, “ina jotter’nki?”
   “Jotter kuma?” Ta tambayesa cike da rashin fahimta.
         “Hold on please” yace da mutumin da suke waya sannan ya dawo kallon sa kan Fannah “yes you are my PA ya kamata duk inda zakije yazamto akoi paper da pen a tattare dake saboda kina jotting down abubuwan da nake buk’ata.”
    “I’m sorry” tace kanta a sunkuye.
    “Sorry? Meaning bakida ko paper knan?”
   “Yes” ta amsa sa.
     “Bakisan yau zaki fara min aiki bane da barakizo da shiri ba?”
   Farar jakarta side bag dake rataye kan shoulder’n ta Anas yasa hannu ya finciko, karap ta kama “Sir excuse me meh zaka min da jaka?”
    “Ki sake nace.” Yana ja tana ja “tunda bakida pape,  rubuta details d’in zanyi akan jakan naki gobe baraki manta ki taho da paper ko jotter ba.”
   “Haba Sir taya zaka min rubutu a jikin jaka?”
     “Haka kikace?” Wayar ya mak’ala a kunnensa tare da tarewa da kafad’arsa kafin ta fahimci me ya ke shirin yi kawai taji yaja hannunta ya bud’o tafin hannunta tare da ciro biro daga aljihun suit nasa. “Yes David ina jinka, tell me the details.”
 
    “Mr. Fauzi me haka? Ka sake min hannu!” K’ok’arin fisgan hannunta take amman takasa dan yadda ya rik’e gamgam kafin ta sake wata maganar har ya fara mata rubutu kan tafin hannu. Hawaye take taji yana ciko mata a ido da k’yar tasamu ta shanye kukan dan nasihan da Mami ta mata jiya na tadena yawan zubda hawayenta gabansa. Hannunta ya mayar kamar paper harda yin cancelation, kallonsa ta tsaya yi sanda ya gama sannan taja hannunta a hankali. “In kika kuskura kika bari ya goge you’ll answer to me.” Sanin santsin hannunta nan da ‘yan mintuna rubutun ze gushe tashiga damuwan Anas again kawai tafito da wayar ta daga jakarta tayi copying duka details d’in ciki. Yana kallonta bece mata komi ba can data gama yace, “Allah sa wannan abin da kike kira waya yayi saving details d’in da kyau in bahaka ba you’ll get it from me.” Bata tanka sa ba ta mayar da wayar cikin jaka ta sake duk’unk’una kanta cikin hijabinta dan sanyi tana kallon window.

    A haka har suka isa destination nasu, nan take tafito daga motar bayan driver ya bud’e wa Anas yafito shima tabi bayansa tafiya take kanta a k’asa duk inda suka shiga gaishe da Anas ake. Chan sama suka haura zuwa wani hall manyan mutane ne ciki tas kowa da suit. A kujerar tsakiya Anas ya zauna take kowa ya gaishesa ita haushi ma mutanen suke bata gashi de almost dukansu sun girme Anas amman wai suna gaishesa ai ba laifin sa bane baya mutunta d’an Adam jibi yadda ya mayar mata da hannu kamar takarda d’azu, tsuka taja wanda bata san sanda yafito fili ba aiko tuni hall d’in ya d’auka kowa ya juya yana kallonta cike da mamaki harda shi Anas d’in. “I’m sorry please” yace da mutanen wajen “excuse us please.” Nan ya mik’e kafin Fannah tayi tunanin wani abu kawai ya fisge hannun ta yaja be tsaya ko ina ba se a bakin k’ofa. “What ia your problem? Meke damunki da zaki ja tsaki haka? Kinsan ko suwaye wad’ancan mutanen kuwa dazaki ja tsaki gabansu?”

   “I’m sorry” tace kanta a k’asa.
   Kallo ya bita dashi sama zuwa k’asa. “You better be, maza mu koma ki basu hak’uri.” Neck tie nasa ya giara ya shige ciki tana biye dashi a baya. Bayan sun shiga tabawa mutanen hak’uri duk suka giad’a kai da nufin sun hak’ura. Daman tsaye take kusa da Anas gudun kar ta sake masa abin kunya ya nuna mata kujera chan k’arshen hall d’in taje ta zauna. Tayi zaman zama gashi ba abinyi, bacci kawai ta mik’e kan kujeran tanayi har aka k’are meeting d’in bata sani ba. Anas ne yazo k’arshen fita chan ya hangeta tana bacci tsuka yaja sannan ya nufa kanta ya tsaya chan ya tsuguna daidai fuskarta tare da k’ure mata ido bacci take a hankali ba alaman tashin hankali tattare da ita, tayi pillow da hannunta ta hanyan aza kanta kan hannayenta biyu. Kallonta yake kusan na minti biyu, chan kad’an daga cikin hijabinta ya fad’o kan fuskarta hannu ya mik’a ze giara aiko daidai lokacin ta tashi a razane taja da baya ganin Anas a gabanta meyake shirin mata? Ina sauran mutanen sukaje?

    Kunya sosai Anas yaji, yanzu setace kallon ta yake ta raina sa. Ni Miemie nace daman me kake?
     “Gomma da kika tashi, da nasa an kawo min ruwa na watsa miki. Ni bansan wace erin lazy PA ce keba, daga zuwa meeting se bacci. Bakisan ya kamata duk abinda akeyi kema kisa kunnen ki kina saurara ba? This should be the last time.”
     Sauraransa kawai take amman d’an baccin datayin nan ya mugun sa mata yunwa. “Lets go” yace da ita nan ta mik’e tare da bin bayan sa. Kamar d’azu haka driver ya bud’e mota bayan ta shiga shima ya shiga. Akan suyi hanyan office nasu seta ga driver yabi wani hanyan daban. Rabin zuciyarta tana ce mata ta tambayesa ina zasuje, rabin zuciyar kuwa na hanata dan ko ta tambayesa ba amsata zeyi ba, banda ya gasa mata magana. Shiru tayi tana ganin ikon Allah.

    Chan gaban wani makeken hotel taga driver yayi parking k’arfin bugun zuciyarta taji ya k’aru meze mata a hotel? Innalillahi nan tashiga tsoro kasa rik’ewa tayi ta tambayesa. “Sir please me zamuyi anan?”
   “Abinda zuciyarki ke saka miki.” ya bata takaicaccen amsa.
    Wani irin tsoro taji ya sake rufeta. “Sir dan Allah kayi hak’uri.”
    “What a dirty mind dake, me da kike tunani zamuyi anan? A tunanin ki d’aki zan kama mana? LOL inma zan kama d’aki nan bada yara kaman ki ba. Abinci nazo chi in kinajin yunwa kuma lets go.” Shiru tayi bata basa amsa ba, ji take kamar ta nitse k’asa dan kunya mesa hankalin ta yaje da nesa haka? Abinci yazo ci bawani abu ba ta tunatar da kanta.

    Tana kallonsa har ya fice daga motar zuwa hotel d’in. Yunwa takeji amman barata ci abinci dashi ba, amman kuma batasan k’arfe nawa ze turata gida ba shida bakinsa yace mata in aiki yayi yawa ze rik’eta fiye da k’arfe 4:00PM. Wayarta ta ciro dan duban time k’arfe 12:30AM taga wai lalle sun sha awowi suna meeting kam. A hankali tafito daga motar zuwa cikin hotel d’in. Ba kowa wajen cin abincin da alama yayi reserving ne. A kujeran dungu ta hangesa da wayansa a hannu da alama jiran order’n sa yake. Har yanzu beyi noticing nata ba se sanda wani security yashigo “Miss kiyi hak’uri please anyi reserving wajen nan, nanda ‘yan mintuna meshi ze tafi seki dawo.”

      “I’m sorry” tace masa, a sanyaye ta juya zata koma cikin mota Anas ya danna mata kira “Miss Aleeyu.” Chak ta tsaya ba tare da ta juyo ba “security let her in.”   “Miss Aleeyu Mr. Fauzi yace a barki ki shiga yana kiran ki.” Idanunta gam ta rufe rabin zuciyarta na ce mata tace wa security’n zata tafi rabi nace mata taje kiran Mr. Fauzi chan tabi zuciyar data ce mata ta koma cikin motan. Taku d’aya ta k’ara ya sake kiran sunanta “Miss Aleeyu!” wannan karan a tsawace b’ari ta soma wai mesa bare na kiran ta da sunanta ba se dana Babanta. A hankali ta juya k’afafunta suna rawa kanta sunkuye a k’asa, sejin idanunsa take a kanta, ignoring kawai tayi ta k’ariso gaban sa. Bata ce komi ba “sit” yace mata.
  Baki na b’ari tace, “Ss... Sir zan koma mota.”
    “I said sit!” Ya daka mata tsawa. Bata san sanda taja kujerar dake kallonsa ba ta zauna hannu ya d’aga waiter’n ya iso “make the plates two.” yace masa.
   “Okay Sir!”
    Tun bayan tafiyan waiter’n suka soma zaman kurame Anas kam se faman latse latse yake a waya. Bayan kamar minti uku abincinsu ya iso aka ajiye wa Anas nasa sannan itama aka ajiye mata nata. Ita kajin kai ne ma yamugun tsorata ta, batada kud’in biyan wannan plate dududu da dubu d’aya ta fito da, gashi already ta kashe d’ari biyu a zuwa kamar yadda zata kashe d’ari biyu a komawa d’ari shida ne kawai ze rage mata wanda tasan ba siya mata plate na gabantan zeyi ba.

    “Uhm please plate d’innan nawa?” Ta tambayi waiter’n. “N1,500 ne Miss.” Ya amsata a takaice yana murmushi. Miyau ta had’iye tare da waro idanunta dariya sosai tabawa Anas wanda da k’yar ya danne tare da yin tarin k’arya sarai ta gane da ita yake. Tace a mayar da plate d’in kuma tsoro take ji chan ta tuna zata je ta tambayi driver’n Mr. Fauzi cikon kud’in yaso ko gobe seta maido masa. Bayan waiter’n ya tafi ta mik’e tare da d’aga plate nata da nufin zuwa wani table.

    Blue eyes nasa ya d’ago yana kallonta. “Ina kuma zakije?”
   Kanta a sunkuye tace, “d’aya daga cikin tables d’in.”
   “Wannan kuma meya samesa?”
  “Babu kawai nag-” bata k’are maganar ba ya katse ta “sit.”
   “But Sir-” nan ma ya kuma katse ta “I said sit!” yafad’a a tsawace. Carap ta zauna tama kasa ko kallon abincin nata se yatsun ta da take murzawa wanda suka had’a gumi. Bayan yaja plate nasa gabansa ya d’au spoon “eat!” yace mata.
   Kai ta d’ago a hankali tana kallonsa shima kallon nata yake “ko cin abincin ne baki iya ba in kira d’aya daga cikin waitresses su baki?”
    “A’a na iya” tace tare da sunkiyar da kanta tana kallon abincin dakuma kajin da suke mata salamu alaikum!
   “Good, then eat nanda 20 minutes zanbar nan kuma ba jiranki zanba” yana kaiwa nan ya ajiye wayarsa yasoma cin abincinsa hankali kwance yakai kusan spoons biyar Fannah bata ko tab’a plate nata ba. Gugugur! Cikinta yayi k’ara sakamakon hakan yasa Anas dariya sosai amman seya danne yayi tari kad’an. Kunya taji sosai kamar ta nitse k’asa. A hankali ta d’au spoon d’in duk Anas na kallonta ta gefen ido.

       Da k’yar ta iya takai spoon d’aya baki sosai abincin ya mata dad’i, da kad’an kad’an tasamu tana cin abincin saboda yadda Anas yayi kamar besan tana zaune ba, abincinsa yake taci be sake kallon ta ba. Ko daya gama be motsa ba, bakinsa ya goge ya d’au wayarsa yana latsawa da wayo yake satan kallonta. Fannah kam ta baje se cin abincinta take, dam ta cika bakinta da fried rice d’in guda gudan salad cream d’in yamata staining baki kunya sosai taji da suka had’a ido da Anas. Take ta ajiye spoon d’in da k’yar ta had’iye abincin bakin nata sannan ta kora da ruwa ta goge bakinta bece mata komi ba yakira waiter’n, ganin haka Fannah tace, “sir excuse me please.”

      Har ta tashi Anas yace, “ba se kinje aran kud’i wajen driver ba I’ll pay for it” kunya sosai taji wai ya ma akayi yasan abinda takeson yi kenan? Wannan Mr. Fauzi se Allah. Cike da kunya da k’yar tace, “thank you.”

   *© miemiebee*

TANA TARS DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 32
BY MIEMIEBEE



Bece da ita komai ba yabiya masu kud’in abincin, ahaka suka dawo cikin motar suka koma office, a lokacin azahar yayi. “Sir excuse me zanje inyi sallah.” Ba tare da ya kalle taba yace, “you have 5 minutes to do so, in kuma kika tsaya hira da Yusuf kikayi delaying d’ina you’ll answer to me.” Kai ta giad’a a hankali ta ajiye jakarta ta fice bayan ta idda sallah suka had’u da Yusuf hira yakeson janta dashi amman sauri take kar ta makara Mr. Fauzi ya samu abin magana kai. “Yusuf kayi hak’uri please, minti biyar Mr. Fauzi yabani ko second na k’ara ze ci mutunci na kabari in aka tashi zanzo musha labari har se sanda ka gaji.”
    “Toh Allah taimaka aiki as PA wa Mr. Fauzi kam seda hak’uri.” yace da ita yana tausaya mata, a haka ta koma office nasa,yana zaune kan kujera yayi focussing kan laptop dayake aiki akai kafin ta zauna yace taje ta had’a masa coffee bayan ta had’a tazo ta ajiye masa. “Kinga flasks biyu da suke can?” Ya nuna da yatsa. “Eh nagani” ta amsa a hankali.
   “Good ki cika min su da coffee.” Ido ta bud’e tana kallon ikon Allah yanzu dan tsiya har flask biyu? Ya kai ina?

   “Bakiji bane?”
   “Naji” ta amsa a takaice. “Good off you go.” Bayan ta isa wajen ta juyo tana kallonsa, shan coffeensa yake hankali kwance yana duban laptop tare da yin wasu ‘yan rubuce rubuce time to time “Sir ba d’an wani babban roba ko kwanon da zan had’a ciki se injuye cikin flasks d’in tunda dayawa zan had’a coffeen?” Ta tambayesa a nitse.
    “Babu kuma koda akoi ma ba barin ki zanyi kiyi amfani dashi ba ga cups nan kina had’awa ciki kina juye har ki cika.” Wannan wace erin mugunta ne kwata kwata cup d’in fa k’ananu ne erin teacups d’innan yaushe har zata cika wannan manyan flasks.
    “Sir hakan ze d’au lokaci ba gara naje kitchen na ari bowl ba.”
    “Bara kiyi ba, kinga banasan musu na fad’a miki stop breaking my rules in zaki had’a good in barakiyi ba kuma in kira Mami in sanar da ita kina min rashin kunya.”
   Chan k’asa k’asa tace, “ba se kanada lambarta ba.” Murmushi kad’an yayi, “haka kikace?” Wayarsa ya d’aga ya kai kan contact na Mami da yayi saving just d’azu data ajiye jakarta zuwa yin sallah. “Zo kiga” bayan ta k’ariso taga eh fah lambar Maminta ne to ya akayi ya samu? Ba tare da tace masa komi ba ta koma ta fara had’a coffeen cikin teacup d’in tana juyewa cikin babban flask d’in. Tayi hakan kusan sau goma amman data gwada jijjiga flask d’in taji har yanzu da saura cikansa ko rabi, gashi ko soma cika d’ayan ma batai ba haka kamar tayi kuka ta samu ta cike d’ayan da k’yar ta zauna dan ta huta.

      “Kin gama ne?” Ya tambayeta
   Kamar wacce bara tayi magana ba tace, “da saura d’ayan.”
   “Well? Me kike jira toh?”
   “Sir hannu na yagaji barin d’an huta please.”
    “Hutu?” Ya tambayeta yana murmushi. “Kin tab’a ganin inda aka huta a office? Get up ki cigaba we have thousand of things to attend to.” Haka kamar ta kashe kanta ta tashi ta soma cika d’ayan har tsayawa take tana mik’a hannunta Anas kuwa ganin haka dad’i yake masa nan gaba zata sake barin masa aiki ba tare da ta sanar dashi ba seya biya duka coffeen dayayi missing time da ta tafi. Tana gamawa ta koma zata zauna, kafin ta zaunan ya kirata fuskarta ta yamutsa kan kashi sannan ta nufa table nasa.

         “Ina details dana rubuta a hannun ki d’azu?” Jakarta ta koma ta ciro wayarta takai kan inda tayi saving sannan ta tura masa gabansa “gashi.” Kallon wayar nata ya tsaya yi sekace bashi ya d’auka ya copy number ciki d’azu ba. “Wannan shi kike kira da waya?” ya tambayeta. Sosai tambayarsa ya bata mamaki haka kuma ya bata haushi taga de wayarta bara a zagesa ba, tecno ce D7 ba abinda bayayi, duk abinda iphone 6s nasa da samsung galaxy 6 edge nasa dayake tak’ama dashi taga nata ma yanayi kawai de d’an cracks ne wanda basu fi uku akai ba. Amsa daidansa ta basa “shine, kuma naga ga details da kake buk’ata a kai.”

    Biro da paper ya mik’a mata “ungo copy it down for me banasan wannan fashasshen screen nakin ya tsaga min hannu.” Kallonsa tayi tare da kad’a kai kamin ta amsa ta yi copying masa neatly bayan data gama ta mik’a masa d’aga wa yayi yana kallo ya d’au batada clear and neat handwriting ne da seya samu abin magana kai se yaga kamar tafi sa iya rubutu ma dan haka ya gwada yin shiru amman shegen neman maganansa bare barsa ba. “I don’t think wannan wayan kin zena recieving calls da emails me kyau yakamata asan nayi.”
  “Sir nifa waya na ba abinda ba yayi, kuma naga ta nan nake answering calls naka da.”
   “Da kikace, ada dakike as my coffee maker yanzu kuma you are my PA abin kunya ne ma in shiga dake cikin jama’a da wannan abin da kike kira da waya.”
      Kasa rik’e bak’ak’en maganganunsa tayi yanzu kam, abin nasa yayi yawa. “Excuse me Mr. Fauzi just because ina aiki k’ark’ashin ka be baka izinin looking down on me ba, I’m not ashamed ko ina zan shiga da waya na tunda ba wani ne yasaya min ba ni na saya da kud’i na.”

      “Wannan kuma ke ya dama na fad’a miki cikin rules naki banasan ina fad’an abu kina fad’a kema ba, I’m your Boss duk abinda na fada koda ba haka bane dolen ki  kiyarda in baki san me kalman respect ba kisani yau.” Telephone nakan table nasa ya ja tare da danna ‘yan lambobi akai “hello? Akoi iphone 6 gold ne a shop naku?”
    On the other side matar tace, “yes Sir akoi.”
  “Good akawo min guda d’aya yanzu the money will be delivered very soon.”
  “Okay Sir thank you.” Kallon sa Fannah ta tsaya yi iphone 6 ma waye? Inma wa ita ne toh ya kwantar da bokatin hankalinsa ba amsa zatayi ba, tecnon ta ya isheta.
    “Stop starring at me” yace da ita yana me cigaba da abinda yakeyi cikin laptop d’in. Bata ce masa komi ba takoma ta zauna shiru tana mamakin hali irin na Anas. Bayan kamar minti goma knock ya shigo daga k’ofar office nasan. “Get the door” yace da ita hankalinsa kan abinda yakeyi. A sanyaye ta mik’e ta bud’e mace tagani sanye da uniform da k'aramar shopping bag na tambarin AA communications a hannunta. Bayan ta gaishe da Fannah ta mik’a mata leather’n, amsa Fannah tayi ta kai wa Anas tare da ajiye masa kan table wani card ya ciro ya mik’a mata da nufin takai wa matar tana kai mata, ta amsa tayi godiya sannan ta fice, ciki Fannah ta dawo kafin ta zauna Anas ya kirata. A gaban table nasa ta tsaya a yayinda ya mik’o hannunsa da nufin ta ajiye masa abu kai. Itako bata gane me yakeso ba dan haka ta tambayesa “excuse me?”

      “Bani wayarki” ya fad’a a nitse. Zatayi magana ya tsawa ta mata “nace bani wayarki! Don’t let me repeat myself.” Tsabagen tsoro bata san sanda ta ajiye masa wayar a tafin hannu ba. Bayan wayar ya bud’e tare da ciro sim nata “Sir meh zaka min da sim card?” Ta tambayesa ko d’aga kansa beyi ya kalleta ba bale ya amsa ta, daman micro sim cikin wayar tatan, nan ya bud’e leather'n ya ciro sabuwar iphone 6 pil daga ciki ya sa sim d’in ciki wayarta kuwa ya jefa a dustbin kusa da shi.

      “Excuse me! Mr. Fauzi taya zaka jefar min da waya a dustbin da kud’i fa na saya in kai bakasan almubazaranci ba kyau ba toh ni nasani” wajen dustbin d’in ta nufa da nufin zaro wayarta karap ya d’aga ya kai d’ayn gefen. “Sir ka bani wayata.” Drawer’n dayake ajiye kad’an daga kud’ad’ensa ya bud’o tare da ciro bandir na naira d’ari ya ajiye kan table d’in “I’m sure wannan yayi kud’in wayarki. Take ita tare da sabon wayanki.” Bandir na d’arin ta d’aga “zanje in sake siyan sabon waya kalan nawa in chenji ya rage zan dawo maka dashi amman ni barin karb’i iphone naka ba bana buk’ata.”

     “Miss Aleeyu!” Ya kira sunanta a tsawace. “Kap building d’innan bame gaya min magana, bame crossing d’ina se ke. Ko a gida in nayi magana ba’a objecting d’ina saboda haka ki mayar da hankalin ki, I’m your Boss not your friend.” Yayi lecturing nata cikin tattausar murya. “Wannan yazama karo na farko nakuma k’arshe da zan miki magana ko in saki yin abu kimin musu. Ki d’au iphone d’in, I don’t care ko kin koma kin sake siyan kalan wancan abinda kike kira  waya dashi all I know is da wannan wayar zamuna business dake, now take it.”
    Shiru tayi chan ta mik’a hannu ta d’aga da kwalin duka. “Good” yace tare da mik’ewa “follow me.” Ba musu ta mara bayansa still a floor na saman yakaita zuwa wata office a saman aka rubuta MISS ALEEYU ajikin kuwa aka rubuta PERSONAL ASSISTANT bayan ya bud’e k’ofar ya shiga still tana biye dashi office ne babba me kyan gaske da table na katakon zamani da kuma kujerun office guda biyu, kan table d’in laptop ne seda telephone, dasu fax and printing machine da cup cike da pencils da biro da sauran office equipments irinsu stepler, pin, glue, dade sauransu. Gefe guda kujerar cushion ne 3 seater dogo me kuma fad’in da za’a iya kwanciya akai se ‘yar k’aramar fridge dakuma dispenser se kuma split AC dakuma toilet a ciki. Sosai office d’in ya had’u ya kuma yima Fannah kyau dan se kallace-kallace take kamar zata karya wuyar ta.

     “Kallon ya isa haka ba sekin karya wuyarki ba” yace da ita cike da kunya ta daidaita kallonta gu d’aya. “Kin iya karatu ba sena fad’a miki ba, nan office naki ne as my personal assistant kamar yadda kika karanta rubuce a bakin k’ofar. Duk wani abinda zaki buk’ata akoi anan, ba kuma na baki office bane dan kisamu wajen yin bacci da hira da saurayin ki aiki ne yakwo ki nan, wancan telephone should stay on always, karki kuskura koda wasa kiyi disconnecting daga jikin plug na bangon saboda dashi zan na miki magana as well as other staffs, clear?”

    Kai ta giad’a “yes.”
    “Good saboda haka yanzu ba ruwanki da office d’ina fashe ni na kiraki, nima zan huta da kallo, for now ki biyo ni akwai aikin da zan baki ki fara dan nasan na barki anan ba abinda zaki amfana se bacci.” Ita tama soma sabuwa da bak’ak’en kalamunsa. Jakarta ta ajiye ta juya tabi bayansa bayan sun isa office nasa ya zauna ya d’ago blue eyes nasa yana kallonta “ina jotter’n ki?”
   “Yana d’ayan office d’in” ta amsa sa a takaice.
    “Okay office d’inne zena d’auka miki record d’in kokuma so kike kicemin ilimi yamiki yawa da duk abinda na fad’a miki zaki iya d’auka akai ba mistake.”
  Share abinda ya fad’a mata tayi tace, “barin je in d’auko”
    “Make it quick” ya amsata yana duban rolex agogon hannunsa bayan minti d’ai Fannah tadawo rik’e da biro da jotter.
 
        Tun kafin ta bud’o biron ya soma bata aiki  “Kije file room acikin first cabinet akoi stack papers type A-D  kiyi printing sekimin e-mailing, bayan haka ina buk’atar neat handwritten version nasu, avoid any mistake. Sekije 5th floor ki karb’a wasu papers a wajen Miss Suleiman kiyi typing nasu a computer kimin e-mailing, take note kowani paper seprate document ne, bayan kin gama typing nasu print them out ki mayar filing cabinet kiyi arranging. You can go now.” Hannun Fannah har b’ari yake dan yadda take rubutun da sauri duk wannan uban bayani da numfashi d’aya Anas yayi dan mugunta, magana yake sauri sauri saboda tayi missing wani abu dan ta buk’ace sa ya koma baya seya samu ya zageta yanzu.

    A sanyaye ta juya ta fice file room 3rd floor ta nufa kamar yadda ya mata kwatance taga a rubuce a sama 1st cabinet papers d’in ta tsakuro sunyi kusan d’ari har yaushe zatayi typing nasu har tayi e-mailing sannan ta zauna ta k’ara rubuta su da hannu? ai aiki ne babba why not kawai in tayi typing tayi printing ai duk d’aya ne. Bayan ta tattara  papers d’in ta haura 5th floor ta amshi papers wajen Miss Suleiman ta haura sama inda office nata dana Mr. Fauzi suke. Office nasa ta soma wucewa dan masa bayani bayan tayi knocking yace, “come in” tana bud’e k’ofar yaga itane sarai yasan meya dawo da ita, so take ta nemi alfarman printing stack papers d’in ba seta rubuta su ba, da gangan dan mugunta daman ya buk’aci ta rubutan dan kawai yayi punishing nata.

    Bayan ta k’arisa gabansa ta daidaita muryarta ko ze d’an tausaya mata ya yarda da k’udurinta. “Sir naje na d’ibo stack papers d’in nace ko ze yuwu kawai nayi printing nasu bayan nayi typing d’in? Ma’ana ba sena rubuta ba.”
        “Miss Aleeyu nan office ne ba gidan hutu ba, yadda nace sekin rubuta sekin rubuta off you go.”
       “Sir but plea-” bata k’are maganar ba ya dakatar da ita “banasan musu just go nima in huta.” Daman tasan ba yarda zeyi ba juyawa tayi ta nufa office nata. Chan ta soma da typing stack papers d’in bayan tagama ta masa e-mailing duka sannan tayi printing papers data amso wajen Miss Suleiman ta sauk’a taje ta jerasu a filing cabinet sannan ta sake haurowa ta koma office nata batasan a wani shekara zata gama rubuta wannan uban papers da suka kai kusan d’ari ba.

      Guda 20 ta rubuta amman wani erin zogi hannun ta yake mata, kuka ne kawai batayi ba haka da k’yar tayi ta huta ta rubuta hamsin saura hamsin. Telephone dake kan table nata ne yasoma ruri tana kai dubanta taga CEO rubuce akai kamar barata d’aga ba kawai ta sa hannu tayi picking. “Yes Sir” tace masa.
    “Kin gama?” ya tambayeta
    “A’a Sir da saura papers d’in fa har d’ari ne.”
   “Good kicigaba da yi in kin gama seki kawo min akoi aiken da zakije min.”
   Kamar wacce zatayi kuka tace, “Sir please kabar aiken gobe wallahi nagaji please.”
    Murmushi yayi cike da mugunta “kin gaji? Ai bakiyi komi ba tukun hurry up nan da one hour ki tabbata kin gama.” Ding! Ya katse. Tsuka taja “mugu kawai.”

    © miemiebee

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 33
BY MIEMIEBEE


Haka har k’arfe 4:00PM lokacin tashi yayi Fannah bata gama rubutun ba acikin d’ari tayi 77, daga k’arshe ma da gajiyan ya mata yawa bata san sanda  bacci ya sace ta a wahalince ba. Anas kuwa tun 3:50PM awa d’ayan daya bata yayi ya kirata ba iyaka a telephone nata haka har call d’in ya tsinke bata d’agawa se baccinta takeyi daga k’arshe kam ma Fannah unplugging wayar tayi daga jikin bango dan distracting nata da yake, sannan takoma kan table d’in tare da aza kanta ta cigaba da bacci. Haushi ne ya cika Anas dam wato bayan yace mata kar tayi disconnecting wayan shine tayi ko? da kyau. A fusace ya mik’e daga office nasa ya nufa nata, yana isa yayi banging k’ofar bacci sosai Fannah take cike da gajiya ko noticing abinda yayi ma batayi ba.

    Mamaki ne ya cikasa daya ga yadda ta bararraje tana bacci kan table lallai ma! Bece da ita komi ba, bayi ya nufa tare da d’ibo ruwa cikin mod’a yafito dashi sannan yayi kanta sanda ya k’are mata kallo sannan ya sa hannunsa cikin mod’an ya d’iba ruwan cikin hannunsa sanda ya tabbata ya matsar da papers d’in gefe guda sannan ya watsa mata a fuska a birkice ta tashi tana nishi da k’arfi razana tayi ganinsa a gabanta yaushe ya shigo? Yaushe ma tayi nisa a baccin? Na ‘yan mintuna fa tace zata d’an huta.
   
    “Sannu da hutawa ko Fannah Aleeyu? Kin gama aikin dana saki kenan har kike bacci. Bayan haka kuma kikayi unplugging wayar daga jikin bango saboda kar a tada ke daga beautiful sleep naki koh? dukda kinsan na hanaki.” Se yanzu ta tuna lokacin data zare wayar daga bango ma, ita ta d’au duk a mafarki ne. Kasa fad’in komi tayi har yanzu mamakin ya akayi ta fad’a bacci take. “Baki amsani ba har yanzu, kin gama abinda na saki kokuwa in sake watsa miki ruwan ki gama tashi?”
   “Ban gama ba da saura” ta basa amsa kanta sunkuye tana tsiyaye ruwan daya fesa mata a fuska da cikin hijabin ta.
    “Sauran guda nawa?” Ya tambayeta.
   “Saura 23.” Papers d’in ya tattaro gabanta “oya finish them.” Hijabin ta tasa ta sake share ragowan ruwan fuskartan sannan ta soma rubutun bayan ta gama d’aya ya amshi ya rik’e. Tambayar sa tayi “Sir k’arfe nawa ne please? Kar la’asar ya wuce ni.”
       “Nima bansani ba da kika kwanta kina bacci ai baki tambayeni k’arfe nawa ba” yabata amsa takaicacce. A daidai lokacin ta d’aga kai ta sauk’e idanunta kan wall clock aiko taga 4:07PM “nashiga uku! banyi sallah ba” tana gwada yunk’urin tashi Anas ya zaunar da ita “sit! Ai ba inda zaki sekin gama sauran 22 d’in nan gaba in na saki aiki zakiyi bacci.”

    “Sir Sallah fa na gaba da komai, 5 minutes kad’ai ya isheni in na idar se na cigaba.”
         “Wa’azi zaki min? Toh banasan ji. Damuwanki ne dan bakiyi sallah on time ba da waya ce ki baje kiyi bacci?” zama yayi kan table d’in “get on with it, in kin ga kin tashi yin sallah toh se in kin gama rubuta sauran” Zata sake magana yace, “now!” A tsawace. A ranta tace ai wallahi zunubin na kanka. Haka yana zaune akanta har ta gama rubutawa tas sannan ya mik’e tare da tattara sauran ya had’a gu d’aya. “Kin gama aikin ki na yau zaki iya tafiya.” Dad’i sosai taji a cewarta ya manta da aiken dayace ze mata. “Gobe first thing in the morning zaki aiken da nayi niyan miki yau, karki zata ko na manta ne dan kar Mami tayi tunanin na rik’e ki a ranar farko ne yasa nayi hakan.” Yana kaiwa nan ya fice. “Allah raka taki gona” ta fad’i bayan da ta tabbata ya fice “mugu kawai, kuma Allah ze sak’a min” mik’ewa tayi ta shiga bayi chan tayi alwala tayi amfani da mirron ta giara fuskarta bayan tafito ta idda sallah nan ta tattara kayakinta ta fice, koda ta sauk’o bata ga Yusuf ba dad’i sosai taji dan gida takeson zuwa yanzu ba sauraron labaransa ba.

     Kallo d’aya za’a mata asan tasha aiki yau ta kuma gaji. Mami ta soma tararwa a tsakar gida tana sirfen wake. “Sannu dazuwa Habibti.”
“Yawwa sannu Mami” ta k’irk’iro murmushi. “Ya aikin? Yau da alama agaje kike wuce ciki ki watsa ruwa ki kwanta kafin nan mun gama alalen.”
     “A’a Mami zan tayaki sirfen.”
    “A’a Fannah wannan aiki na da Afrah ne itan ma tashiga bayi ne yanzu zata fito karki damu.”
   “Toh Mami sannu da aiki” tana kaiwa nan ta wuce d’akinsu, sosai taga d’akin ya canza kamanni duk an sake cikasa da kayakin da Mr. Fauzi ya kawo musu jiya tsuka taja wanda yasa Afrah fitowa daga bayan wardrobe inda ta lab’e tana chatting. “‘yar munafukai kinzo kina chatting kinbar Mami na aiki ita kad’ai ko?” Cewar Fannah ba alaman wasa tattare da ita.
   
       “Ya Fannah dan Allah kiyi shiru kar Mami ta jiyoki bayi nace mata zan shiga.”
     “Ai wallahi sena fad’a mata gaskia a mayi seizing wayar taki ai nima haka kika sa baki jiya nakoma wa Mr. Fauzi aiki.”
    “Yi hak’uri Ya Fannah dan Allah ya office d’in?”
   Baki Fannah ta murgud’a mata “bansani k’anwar shed’an kawai jibi yadda hannu na ya kumbura shafin paper guda d’ari na kwafe masa ai wallahi Allah ya isa kuma duk laifin ki ne. Mami! Mami!”
    “Na’am Fannah wani abu ne?” cewar Mami da k’arfi yadda Fannah zata jiyota.
    “Ya Fannah dan Allah karki fad’a mata.” Afrah tace k’asa k’asa.
   “Ai wallahi se na fad’a.” nan ta d’aga muryarta “Mami ga Afrah nan ta mak’ale tana chatting ba bayin da ta shiga.”
   “Mami wallahi k’arya take yanzu fitowa na” wayarta ta mayar cikin wardrobe d’in.
   “Fito nan Afrah kinsan zan karb’e wayarki ko?” Gwalo Fannah tamata a yayinda Afrah tafice zuwa samin Mami tana bata hak’uri. Kayan jikinta ta rage ta fad’a bayi dan watsa ruwa.

  **

       “Oyoyo Ya Anas!” Amal tayi hugging Anas a wajen parking lot. “Oyoyo Angel.” Flasks biyun yaciro daga motarsa ya mik’a mata empty’n “ungo wannan rik’emin.” Bayan ta amshi tace, “Ya Anas me acikin na hannunka?”
   “Coffee ne” ya amsata a takaice yana murmushi. “Toh shine har flask biyu.”
    “A’a d’aya ne na riga na shanye d’ayan.” Ido wuru wuru ta zaro “ka shanye?? Duka wannan na hannun nawa?”
    “Eh Amal yunwa a office.”
   “Ayyah Ya Anas to ko zaka soma tafiya da lunch box ne?” Dariya ya d’anyi kad’an “karki damu I can take care of myself mu shiga daga ciki.”
   “Toh Ya Anas.” A parlour suka tarar da Abuu da Ummie suna zauna se tattaunawa suke sannu da zuwa suka masa a yayinda ya mik’awa Amal flask na hannunsa me coffeen kan takai masa d’aki. Shettima kuwa na dining space yana d’iban abinci shima da alama yanzu ya dawo daga school. “Sannu dazuwa Ya Anas.”
     “Sannu maza” ya amsa sa. “Abuu, Ummie sannunku da hutawa.”
    “Yawwa Anas ga abinci can seka d’iba kaci ko akai maka d’aki ne?”
   Shi da yakeda coffeen sa yau har cikin flask me zeyi da abinci? “A’a Ummie don’t worry bana jin yunwa munje meeting naci abinci a hotel d’azu.”
 
       “Ai dama kullum haka kake cewa toh a huta gajiya.”
   “Yawwa Ummie” ya juya ze nufa d’akinsa kenan Abuu ya kira sunan sa “Anas!” chak ya tsaya tare da juyowa “na’am” Abuu ya amsa cike da girmamawa. “D’an zo ka zauna magana nakeson muyi.”
    Ba musu ya k’ariso cikin parlour’n tare da zama kan rug d’in.
Giaran murya Abuu yayi, “ni Anas shin baka da tsarin aure ne a rayuwar ka?”
      Blue eyes nasa ya zaro tare da sake baki wangalau cike da mamaki. Bambarak’wai yajiyo maganar, dududu shekarunsa nawa ne? 24 nede da ‘yan wattani akai shine za’a masa maganar aure? Cikin mates nasa gabad’aya ba wanda yaji ance yayi aure ko Baana me san mata ma beyi ba se shi ne za’a ce yayi aure? Lallai kuwa! ai da fili kawai Abuu yafito yace masa ya gaji da basa abinci ya tattara kayakin sa yabar masa gida, da yafi mai akan yace wani baida tsarin aurene a rayuwarsa.
 
    “kayi shiru Anas.” Abuu yasake tambayar sa.
    Juyi kansa yaji yana masa da k’yar ya iya fad’in, “aure kuma Abuu?”
       “Eh Anas aure” Abuu yasake jaddada masa.
     “Abuu aure fa kace? Ko ka manta shekaruna ne? I’m just 24 fa, Ummie ki tuna masa mana.” Yadawo da kallonsa kan Ummie. Shiru Ummie tayi dan itama sanda ta fad’a wa yayan nata kan kar ya tinkari Anas da wannan zance na aure yayi yaro he is just 24 amman Abuu yak’i sauraranta saboda wasu k’wararun dalilun dayake dashi.
 


        “Ya Ibrahim nakega abar maganan nan, Anas yaro ne” ta fad’a tana b’ari gudun kar wan nata ya masifeta. “Nafeesa munyi maganan nan dake d’azu inhar kinsan baraki bani goyin baya ba to kiyi shiru.” Kum taja bakinta tayi shiru, dawo da kallonsa yayi kan Anas da ransa ke tafasa, blue eyes nasa sun sake shiga jin an ambato masa kalman ‘aure’ abinda ya tsana fiye da komai. Haka kawai yau yana jin dad’insa Fannah ta dawo masa aiki za’a tinkare sa da zancen aure. Mschww!

         “Aure Anas nakeson kayi, kai kanka kasan kalan kud’in da kake dashi, kalan arzikin da Babanka ya bar maka yaro ne kai har yanzu baka gama mallakan hankalin ka ba hanya d’aya ce kuma zata sa ka mallaki hankalin shine ta hanyan yin aure, yazamto kanada mace a gefenka wanda zata tayaka shawarwari da sauransu. Kuma ko ba dan haka bama kai bakasan ace d’an daka haifa ko ‘ya suyi gadon wannan company naka me albaraka? Sanin kanka ne kap a ‘yan gidan nan bame iya kula maka da wannan babban company koda ace yau kafad’i ka mutu, ga kuma yadda ake mutuwa, iyye Anas?” Shettima dake sauraronsu kai kawai yake kad’awa, ma’ana maganganun Abuu na shiga ta nan na fita tacan ne kawai dan ko za’a had’a sama da k’asa Anas bareyi aure ba inama ace yasamu yarinyan dayake neman ne, wacce ya amshi martabarta da se ace da sauk’i halan ya yarda yayi auren.

    Ganin Anas baida niyan magana Abuu yace, “kayi shiru Anas ko bakada abin cewa ne?”
     Giyansa kawai yakeson sha yanzu shi kad’ai ne ze daidaita masa tunaninsa gashi dama ya d’an kwan biyu be tab’a ba. “Abuu aure? Ni nayi aure? Ai in neman me shawara nake ga Ummie gaka ga Shettima. Ko Amal ma zata iya bani shawara gaskia Abuu ni banasan wannan shawara.”

         “Kinji irin rashin hankalin danake fad’a mikin ba Nafeesa?” Abuu yafad’i yana kishingid’a bayansa jikin kujerar dayake zaune kai. “Anas yaro ne kai har yanzu bakasan ciwon kanka ba aure ne kawai zesa ka mallaki hankali, kasan ko kap Nigeria kaine youngest billonaire? Taya kakeson ka rik’e sunan nan in bawai kanada wanda zata na baka shawara ba? A yanzu a hakan ka tsab abokan banza zasu iya juya maka hankali kayi messing up rayuwar campany’n ka amman in kanada mata fah? Barata tab’a barin hakan ya faru ba. Kai yanzu tsakanin ka da Allah komi da kake ciki ne kake sanar dani ko Ummie’nku?”
    Kai Anas ya kad’a a hankali. “Toh! Amman in mata kake dashi komi zakaji kanasan sanar da ita, in kuwa me hankali da tunani ne duk abinda kakeyi ba daidai ba zata jawo hankalinka, ko baka gane ba?” Ko giad’a kan da Abuu ke jiran Anas yayi beyi ba shifa bega abinda zesa yayi aure ba, shida aure sun raba hanun riga.

      “Baraka fahimce abinda yasa nace kayi aure a yanzu ba se a nan gaba, se anan gaba zaka gano so ne yasa na keson kayi aure.”
    “Abuu wai wani irin aure? Ni ban tab’a jin inda me shekaru 24 yayi aure yayi aure a wannan zamani ba, ko kaifa 27 kayi aure Abuu, a da ma kenan”
        “Nonsense, taya zaka had’a kaina da kai? Kuma ai dama baraka ji ba Anas saboda yawancin masu irin shekarunka basuda aikinyi wasu yanzu suke kammala makarantar wasu kuwa sun kammala ba aiki har yanzu to taya zasuyi aure ba aikin yi? A da ne ko ba aiki mata suke yarda su auri maza amman banda yanzu da ‘yan mata suka sa kwad’ayin abin hannun mutum. Kaga ko dole kace baka tab’a jin me shekaru irin naka yayi aure ba. Amman kuwa in kayi la’akari kai naka case d’in daban ne kap cikin mates naka akoi wanda yakaika samu ne? Mu ajiye samu a gefe ma akoi wanda yake da aiki me kyau kamar naka ne? Ai dama abinda yasa ake delaying aure kenan, rashin samu da abinyi. Kaida Allah ya riga ya baka fa? Seka tsaya yin meh? Jira zakayi se sanda mates naka suka soma aure kaima kayi?”

       “Eh Abuu” ya amsa ransa a b’ace.
    “Toh Anas kayi k’arya dolenka kayi aure kodan mutuncin company’nka kai bakasan in kanada aure mutanen da kake alak’a dasu a sauran k’asashen duniya zasu fi baka mutunci da girmamawa bane? Sabida shi aure hankali yake k’arawa dakuma daraja a idan mutane. Ka ajiye k’ank’antan shekarunka a gefe kayi facing reality Anas, aure ne ya kamance ka kodan kare martaban company’n da Babanka yabar maka.”

       “Abuu gaskia ni barin yi aure ba, my company is doing perfectly fine duk abinda nasan ya kamata inayi ba abinda muke lacking, aure ba abinda zemin inbanda raba min hankali.”

     “Anas yau da ni kake yin che in che? Aure zakayi ko kanaso ko baka so, abinda babba ya hango yaro ko ya hau kan tudu bare gani ba wannan kenan.”
 
   Kamar wanda zeyi kuka yace, “Abuu dan Allah karka min haka please, karka sani yin abinda banaso banida interest akan aure I’m not ready, wallahi kabi duk sauran investments da companies da muke aiki dasu kaji, komi ina kiyayewa ina running business d’ina perfectly, na yarda duk sanda kaji ance maka nayi wani abun da be kamata ba ka sani auren, in fact ka nemo min matar da zan auran ma da kanka amman banda yanzu please. Please Abu.”

          “Anas taimakon,ka nakeson yi, trust me barakayi regretting wannan shawara na yin aure ba.”
      “Abuu please fa nace dan Allah-”
   Katse sa Abuu yayi “a’a ya isa Anas,  na d’aga wannan shawara ya zamto umarni yanzu wanda dolenka ka amince ko kanaso ko bakaso, dolenka zakayi aure ko kanaso ko bakaso ni na fad’a maka.”
    “Ya Ibrahim dan Allah kayi hak’uri take it easy on him, yaro ne.”
   “Dakata Nafeesa wannan uban san da kike ma yaran nan ze zamo musu illa wataran, in gaskia tazo dole a fad’eta, ehe!”

   
   *© miemiebee*
Share:

1 comment:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).