shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday 24 September 2016

TANA TARE DA NI... PAGE 82&83

tana-tare-dani.jpg

TANA TARE DA NI... PAGE 82 BY MIEMIEBEE Anas besan lokacinda ya fasa glass cup dake hannun saba daga riqo tsantsan wani irin baqin kishin daya tokaresa jin abinda Farouq yama Flowersa, kasancewar fatar jikinsa bame k’arfi bane take glass d’in yamasa kaca-kaca da hannu. K’ara Ummie da Amal suka sakar ayayinda Abuu da Shettima sukayi kansa suna tattara broken glasses d’in. Idanunsa take sukayi wani irin wawan jaaa a yayinda zuciyarsa ke wani erin tafasa. Amsar wayan Farouq yayi daga kunnen crying Fannah “Mr. Fauzi kaji ka gaskata zance na?” Cikin wani erin muryar da ban tab’a sanin Anas dashi ba yayi maganar “Farouq kaji na rantse I WILL KILL YOU WITH MY OWN BARE HANDS kawai kajira had’uwa na dakai.” “Hohoho!!! Kafin ka kasheni nikuma zana kashe maka Flower I have to go kasan akwai aikin abortion gabana” yana kaiwa nan ya katse wayar koda Anas ya gwada kiransa back cemasa ake the number does not exist kasancewar Farouq ya karya sim d’in yakuma kashe wayar gabad’aya ya cire battery bare sake amfani dashi ba gudun kar ayi tracking nasa down. Haka yayi da wayar Fannah ma ya cire sim nata ya karya yakuma kashe wayan. Wasu erin zafaffun hawaye ne suka soma sauk’o ma Anas akan kumatu. Waje Ummie tayi da Amal ganin Anas na kuka again. Daidai Abuu ya bud’e baki zeyi magana kenan wayar Anas ya soma ruri Abuu nakai dubansa yaga Mami. Kafin ya d’aga ya kalli Anas ganin ko kad’an hankalinsa bai jikinsa ya d’aga wayar kawai. “Hello Maman Fannah.” “Assalamu Alaikum” tace. “Wa’alaikis salam Abban Anas ne.” “Ayyah ina wuni?” Ta gaishesa. “Lafiya alhamdulillah” ya amsa. “Ya kowa da kowa?” “Duk k’alau.” “Masha Allah nace ko Anas na kusa inason muyi magana ne da Fannah nayita kirar wayarta bata d’agawa.” Zuciyarsa yaji yayi dum! Ya buga yama kasa magana. “Hello...?” “Maman Fannah inason ki saurareni dakyau dan Allah kuma kisani muna kan bakanmu na neman Fannah baramu tsaya ba semun sameta.” Gaban ta taji yayi mumunar fad’i. Bayan salatin data sakar cike da tashin hankali tayi k’arfin hali tace, “Abban Anas meya samu ‘yata dan Allah?” “Ki kwantar da hankalinki please, ‘yar ki Fannah ta na wajen Farouq yanzu haka as we speak...” Nan ya kwashe labarin komai yabata. Salati take alokaci guda idanunta suka ciko da hawaye. “Yaushe Farouq da mahaifinsa zasu fita harkar Fannah subarta taji dad’in rayuwa? Me tayi musu?” Hak’uri Abuu ya riga bata sannan daga bisani ya katse wayar. “Anas ka kwantar da hankalinka kaji?” “No Abuu I can’t.” Ya fad’a rai a b’ace. Hannunsa daya yayyanke Shettima yayi yunk’urin tab’awa “don’t touch me Shettima just leave please both of you dan Allah kufita min a d’aki am sorry please.” Kai kawai Abuu ya girgiza he understands exactly what his son is going through. “We will Babana zamu bar maka d’akin just behave yourelf, Shettima mu fita.” Nan suka fice, hankalain Shettima ya matuqar tashi kasancewar yasan halin wan nasa sam be iya rungumar k’addara ba tsoronsa kar Anas yakoma shaye shaye irin na da. Bayan ficewansu Shettima Anas ya miyar da kallonsa kan hannunsa me zuban jini alokaci d’aya ya miqe yashiga bathroom sabon spirit ya bud’e ya bulbula kan hannun nasa k’ara ya saki sosai dan sharp pain dayaji,gritting teeth nasa yake dan azaba idanunsa matse gagam. “Atleast I can feel kad’an daga cikin pain da kike feeling Flower, atleast you are not alone in this, atleast zan iya feeling koda half of your pain.” Fuskarsa ya d’ago yana kallon mirror instead yaga fuskarsa se fuskar Fannah kad’ai yake gani ciki, tunaninta duk yabi ya mamaye masa k’wak’walwa. Da tunanin abinda Farouq ya sake hitting masa k’wak’walwa kuwa besan a lokacin da ya shure kwalabai da robobin mayukan shafe-shafe da suke kan counter d’inba. “Fannah _TANA TARE DA SHI_ No! he can’t take away Fannah from me, Fannah is mine, Farouq I will hunt you down like an animal.” A fusace yabaro bayin besan a lokacin daya ciro wani dogon kara daga k’ark’ashin gadon sa ba yasoma fashe fashe daga kan TV, dressing mirror, hanged mirror ba abinda be fasa ba. Abuu dake parlour ne jikinsa yabasa ba lafiya ba agurguje ya bud’e k’ofar d’akin ya tarar da Anas d’auke da wuk’a yana kan tsaga tafin hannunsa se cize bottom lips nasa yake cike da azaba amman hakan be hanasa cigaba da gudanar da abinda yakeyin ba. “ANASSSS!!!!” ya kira sunansa diabelievingly a yayinda su Ummie ke bayansa suna sakar da salati kansa Abuu ya nufa ya tsinka masa mari tas kukeju take Amal ta b’uya bayan Ummie. “Bakada hankali ne iyyeh? Whats all this?” Yayi maganar yana k’are kallo wa mess da Anas yayi wa d’akin. “Ina ka kai hankalinka?” Hannu yasa ya k’wace wuk’an. Se anan Anas yayi magana; “Abuu give me back kabani please, be kamata inbar Fannah kad’ai tana shan wahala ba kabani wuk’an kaga se muna feeling pain d’in tare.” “Anas get your senses together kanajina koh?! What nonsense. Nasan wannan abu ne meh wuya amman hak’uri zakayi kamar yadda nayi nima da Ummiminku ta tafi ta barni, balle ma kai ba tafiya Fannah tayi ba kidnapping nata akayi kuma in shaa Allah zamu sameta meye amfanin wannan abubuwan da kakeyi iyyeh? It has to stop!” Ummie ce tasa baki; “A’a Ya Ibrahim kamishi uzuri, wannan tsaka che me wuya shi kad’ai yasan yadda yakeji kaima kasan how it feels like. In zaku bani dama kufita ku barni dashi” nan ta k’ariso cikin d’akin da Amal biye da ita batare da Abuu yace komai ba yafice haka Shettima ma. “Amal kema bisu.” “No Ummie please kibarni in zauna da Ya Anas” dagudu taje ta rungomoshi tana hawaye. “Ya Anas in shaa Allah zamu samu Fannah wannan mugun Farouq d’in bare mata komai ba, bare mana harming baby ba because we love our baby ba?” Sam be amsata ba kai kawai ya gyad’a mata daga baya a hankali nan da nan Ummie ta gyara masa kan gado suka hauro dashi ita da Amal. D’akin tashiga tattarawa ayayinda Amal ta aza kan Anas a cinyointa tana shafa gashin kansa a hankali bayan ta tare jinin dake d’iga daga hannunsa da tissue. Bayan Ummie tagama kimtsa d’akin ta taho da bowl d’auke da towel ciki d’an k’ananun yankan da Anas yajijji a jikinsa agarin fashe fahsen dayayi dakuma yankan dayaji wa kansa ta goggoge tayi treating masa cikin k’ank’anin lokaci ta kimtsa sa. “Zakaci abinci Babana?” Ta tambayesa shiru yayi be amsata ba hakan ya tabbatar mata baya jin yunwa. “Amal taso mu basa waje kinji?” Seda ya bari Amal ta mik’e sannan ya rik’e hannunta “ki zauna kinji Angel, don’t leave me too.” “Ya Anas I will never leave you _INA TARE DA KAI_ kamar yadda Ya Fannah ma take _TARE DA KAI”_ calming and soothing wors masu kwantar da hankalin d’an Adam Amal ta riga furtawa yayanta tana sake tabbatar masa dacewa Fannah tasa ce kuma zasu same ta, shi ya jasu sallan isha sam yak’i barinta ta fita daga d’akin cemata yayi a d’akin yakeson ta kwana ita akan gado shi kan couch*** Baa tare da b’ata lokaci ba Mami tasamu Baba ta gaya masa halin da ake ciki hankalinsa yayi matuk’ar tashi tuni Afrah da Aiman suka soma kuka Mami na mara masu baya. Ya Khaleel Baba ya kira sam munafikin Allah ya nuna masa besan halin da ake ciki ba ce musu ma yayi rabonsa da Farouq sati d’aya kenan yanzu. Suna gama wayar ya kira Farouq ya sanar dashi. Dariyan bosawa Farouq ya sakar “barsu Baba basuda hankali ne karka damu inada miliyan 2 yanzu sauran miliyan uku daga nan se muyi proceeding plans namu” “Kayi daidai Farouq danko Fannah taka ce tun kana d’an yaro kake santa.” “Maganar ka dutse Baba will get back to you later” nan ya katse. Maido da kallonsa yayi kan crying Fannah cike da azaba ya d’agota daga saman hannunta, mijinki is trying my patience you will have to bear the burden janta yayi zuwa d’akin d’azu tana had’asa da Allah amman ko sauraronta beyi ba d’aureta ya kuma yi sede wannan karan be toshe mata baki ba. Wani samsung S5 yaciro ya d’auketa hoto sannan yabi ta whatsapp yayi sending takan Anas yasan sarai Anas ba shiga whatsapp zeyi ba dan haka yamasa sending SMS Hurry! Smart guy and check in your whatsapp Amal ce ke kusa da wayar alokacin da saqon ya shigo. “Ya Anas you have a new message.” “Barshi Angel am not in the mood.” “Ya Anas inkuma ya shafi Ya Fannah fah?” jin ba k’arya a magananta ya miqe tare da amsar wayar bayan ya karanta hankalinsa ya sake tashi fiye dana da ba tare da b’ata lokaci ba yayi enabling cellular connection first message da yayi popping up ya bud’e ganin pictures na Flowersa hannaye da k’afafunta a d’aure kansa yayi wani erin mumunar bugawa, hannu yasa ya dafe kan nasa ta gefen migraine d’in. Cike da tashin hankali Amal ta matso kusa da shi tana dafe sa, “Ya Anas mene ne? Meya faru?” Kasa koda furta mata ‘A ’ yayi. Ba tare da b’ata lokaci ba yakira layin karap Farouq ya d’aga. “Hello smart guy now what? Zakayi as I say kokuwa I need to let her suffer some more?” “Farouq please let her go ka saketa dan Allah kai bakasan darajan ‘ya mace bane? Musamman ma me d’auke da juna biyu?” “Bansani ba kuma banason sani do as I say and I will let her go.” “You filthy son of a b*tch what the f*ck do you want? Meh kakeso?! ” Amal dake a gefensa seda taja da baya tsabagen firgita datayi dan kalan tsawan da Anas ya daka. “Zamuyi magana if you are ready, I’m hanging up.” “Kafad’a min meh kakeso and let her go.” “Miliyan uku nakeso... For now.” “Are you crazy Farouq?” “Yes I am, zakayi transferring kud’in kokuwa haka kakeson Fannah ta kwana?” “I will zanyi please ka saketa please.” “Ka turon kud’in first.” “Nace zan maka sending ka sake ta please.” “Senaga alert” nan ya juyo yana kallon Fannah dake ta kuka ba sauti. Fuskarta ya shafa “Farouq please kadena tab’ani banaso.” Maganarta har kunnen Anas. “Farouq me kake mata? Kadena tab’a ta please.” “Meh aciki dan na tab’a wifey na?” “Kai wai bakasan tab’a macen da muharramarka haramun bane?” “Bansani ba kuma banason sani send me my 3 mil and I will let go your wife.” “Son of a b*tch” cewar Anas sannan ya katse wayar nan da nan yama Kacallah magana aka mai transferring kud’in. Kacallah na sanar da Anas yayi transfer d’in yakira Farouq back sede sam layin yak’i shiga kodaya gwada trying na Fannah ma haka, hankalin Anas in yayi dubu be tashi ba he can’t wait gobe a fara investigating, fatan ranan had’uwansa da Farouq kawai yake. ** “Mijinki d’an Amanah Fannah har ya turo kud’in” cewar Farouq alokacinda yake since mata hannu. “Muje muci dinner.” “No way! Ya Farouq I have to pray first.” “Ba matsala zaki iya yin duk wani abinda kikeso tunda mijinki ya cika min buri.” “Burin meh?” Ta tambayesa tana shafa hannunta daidai wajen daya d’aure har seda yayi pink.” “Karki damu sooner zan sanar dake shiga kiyi alwalan ina jiranki.” Tsuka taja sannan ta shige bayan tafito ta had’a Maghrib da Isha yana zaune yana jirarta ko ajikinsa ma beyi Sallah ba, bayan ta idar yajata da hannu zuwa dining room nasu achan sukayi having dinner. “So wifey time to sleep koh?” “Kamar ya time to sleep?” “Ya kike kwana da Anas?” “Ya Farouq shin wai bakasan Anas miji na bane? Kaikuma ba muharrami na bane saboda haka barin had’a kwanciya dakai ba.” “Kinsan me nafiso? Nafison kina fighting d’ina haka ‘cause it gives me more and more reasons to fight you down, dani zaki kwana ko kinaso ko bakiso.” A fusace ya miqe ya doso gabanta tare da miqar da ita da hannunta. Hannun nasa ta hau bigewa “ka sakeni Ya Farouq let me go.” Ko saurarenta beyi ba haka yajata sama zuwa d’akin daya tanadar masu akan gado yayi wurgi da ita. Kuka take sosai. Kayan jikinsa ya hau cirewa boxers zallah yabari. “Ya Farouq dan Allah na had’aka da Allah kayi hak’uri ka kaini wani d’akin in kwana dan darajan manzon Allah.” “Zaki ajiye wannan mayafin agefe ne kokuwa?” Sake matse gyalen tayi ajikinta ganin batada niyyan cirewa ya nufeta tare da jan gyalen seda ya rabata dashi ihu tahau yi tana kiran sunan Anas. Dukiyar fulaninta ya cafko wani irin k’ara ta saki sannan daga bisani ta tsinke sa da marin da bai expecting ba. Cikin kuka take maganar “bakada hankali ne Farouq?” Yau ko yayan ma babu. “Wallahi the next time ka gwada yunk’urin tab’ani I wont hesitate to kill you mugu, azzalimi maras imani kawai wanda besan darajar mace ba Alla-” bata k’are maganar ba ya kawar da ita da mari. “Ni kika d’aga hannu kika mara dan fitsara? Sa’arki ne ni? You are asking for it.” Hannunta ya ja be tsaya ako ina ba se wani d’akin da ba komaj ciki banda uban duhu da poles guda uku ciki. “Ya Farouq ka sakeni mugu, azzalimi kawai ka sake min hannu” wani marin ya sake kai mata anan seda gefen bakinta ya fashe. A k’asa kusa da d’ayan pole d’in ya yasar da ita sannan ya d’ago wani thick igiya ya d’aure mata hannayenta duka biyu daga baya ihu sosai ta rigayi dan yadda ya matse mata hannayenta bibbiyu a bayan pole d’in sannan ya k’ulle da k’arfi gabanta ya sha ya k’ulle k’afafun ma sannan ya matso da fuskarsa gab da nata bata bar kukan ba har yanzu “Ya Farouq dan Allah kayi hak’uri ka sakeni please.” “Mu kwana lafiya kikace min a’a ba? Haka anan zakiyi spending night naki alone in this room.” Nan zuciyarta yawani buga tunda take bata tab’a kwana ita kad’ai ba se yau ita ina ma d’aki ne me fasali da dasauki. “Ya Farouq dan Allah kayi hak’uri.” Fuskarta ya riqo sannan yasoma laluban lips nata dawuri ta maqesu chiki haka yatayi amman tak’i barinsa yayi kissing nata, daya gaji ya d’auko cellotape ya manna mata a bakin “sleep tight wifey” yace mata tare da kashe wutan d’akin wani erin baqin duhu ne ya ratsa cikin d’akin alokacinda ya bankad’e k’ofar. Kuka take sosai tana ta murza hannayenta ko zata iya sinche igiyiyin amman takasa haka yadda taga rana taga dare seda gari ya soma wayewa ne tasamu wani wahalallen baci yayi awon gaba da ita. Shegen se 9:30AM ya tashi ko Sallah baiyi ba, bashin da ake binsa jiya ya sauk’e Asuba da Azahar kad’ai sauran se anjima in ya samu time. Bayan yayi wanka ya shirya cikin black top da jean trousers sannan ya nufa d’akin Fannah har a lokacin bacci take, tsugunawa yayi a gabanta fuskarsa d’auke dawani murmushin tsiya. Ba abinda yake kalla a fuskarta banda lips nata tsabagen k’azanta ko brushing Fannah batayi ba amman ahakan yakeson yayi kissing nata. Fuskarta ya shafo a hankali ganin batako motsa ba ya sake matsoda fuskarsa gab da nata ta yadda nishinsu ki tinkling. Abu k’iris ya rage yayi owning lips nata ta bud’e idanunta lokaci guda. Wani irin nishi taja tare da warwaro idanunta, baya yayi kad’an alokacin dayaga ta maqe lips nata. “Good morning wifey da alama you had a wonerful night” ya k’are maganar yana since mata igiyoyin. Ganin batada niyyan masa managa ya cigaba “muje kiyi wanka ina neman shawararki.” “Kayi duk abinda kakeso daman ka tab’a neman shawara na game da abu?” “Wifey mesa kike min haka ne? Kullum bakida abinyi banda fad’a dani mijinki?!” “Niba matarka bace kamar yadda kaima kake ba mijina ba.” “Nasani ai shiyasa nakeson muyi aure, auren sunnah.” K’irji ta dafe “aure? Ya Farouq dan Allah ka rufa min asiri taya zaka aureni bayan inada igiyan aure akaina??” “Wannan duk ba komai bane, zamu bar Nigeria zamu koma ko Ukraine ko Ghana seki zab’i k’asan da kika fiso.” Hawaye ne suka soma ambaliya kan fuskarta... durk’ushewa tayi har k’asa a gabansa jin ya ambaci barin k’asa gabad’aya. Rok’ansa ta soma “Ya Farouq dan girman Allah kayi hak’uri dan soyayyar da kake ma manzon Allah kayi hak’uri kaji k’aina karka kaini wani k’asa daban karka rabani da iyayena dan Allah Ya Farouq...” Ta k’are maganar cikin sautin kuka. Ina me baku hak’uri da posting da bana samunyi kwana biyu my phone is having a problem, ku k’ara hak’uri I love you guys so much © MIEMIEBEE

TANA TARE DA NI... PAGE 83 BY MIEMIEBEE “Haba! wifey me yayi zafi haka? Tashi please I’m trying to change your future.” “Ya Farouq dan Allah karka gudu dani zuwa wani k’asa daban please.” “Kinsan me wifey? Wannan had’ani da Allahn da kike ba tasiri zeyi akaina ba ki tashi kiyi Sallah muyi breakfast inkuma se anjima zakiyi sallahn then muje mu karya.” “No Ya Farouq! Allah yafika mugu, azzalimi maras imani kawai wallahi baraka gama da duniya lafiya ba, you are going straight to hell such a demon.” “Ki kirani da duk wani sunan daya miki abu d’ayan da nakeson kisani shine ke TAWA CE! YOU ARE MINE!” bejira ta sake magana ba ya finciko ta da hannunta ta sama be direta a ko ina ba se abayin d’akinsu “na baki minti goma kuma” yana kaiwa nan ya ja k’ofar ya rufe. Kuka me tsuma rai takeyi tafi minti biyar tsugune a bayin sannan daga bisani ta miqe tayi brushing sannan tayi wanka da alwala, kayan jikin nata ta miyar sannan cike da tsoro ta fito mayafinta na jiya ta gani a k’asa dashi tayi Sallah tariga roqan Allah daya kareta daga sharrin Farouq. Bada jimawa ba Farouq ya dawo d’akin zaune yasameta ta d’aga hannu sama tana addu’a, waje yanema ya zauna tare da zura mata ido har seda ta tofe. “Excellent ina fatan kinyi addu’an Allah sa d’an cikin kin me cetoh ne.” Cikin dashasshiyar muryar tace, “me kake nufi Ya Farouq?” “Zubar da cikin zanyi bazeyi mu tafi dashi Ukraine ba chan inda na yanke hukuncin zamu, I want us to start a new life.” “Nasan ba point rok’anka amman dan Allah ka rufa min asiri karka min haka Ya Farouq na rok’eka please kamin rai.” “Wifey fa ba ke nace zan kashe ba shegen abinda ke cikin ki nace zan kashe” ya nuna cikin nata da yatsa. “Before then muje mu karya inajin yunwa.” “Banaji kaje ka karya kai kad’anka” ta k’are maganar hawaye na ciko mata a ido. “Wifey kinga banason taurin kai nace muje mu karya” bejira ta amsa shiba ya fisga hannunta be direta a ko ina ba se akan dining chair nata “eat wallahi ko kici ko in zubar da cikin nan at this instant.” Shiru tayi bata amsashi ba, bara kichi bane sena zubar da cikin komeh??” “Meh amfanin chin abincin? Ko nachi ko banchi ba bashi ze hanaka aiwatar da abinda kayi niyyah ba.” “No wifey” ya shafo fuskarta wanda tuni ta bige hannun nasa. “Kichi barin zubar ba.” Idanunta ta d’ago tana kallonsa da nufin bata yarda ba. “I swear wifey, kichi barin zubar ba, ki k’i chi in zubar.” “Kabani reason d’aya da zaisa in yarda dakai.” “Because I’m Farouq, now eat.” Fork d’in ta d’aga tasoma ci bayan tayo bismillah se anan ya koma nasa b’angaren dining table d’in shima yasoma chin nasa kamar jiya yau ma fargaba ya hanata chin abincin sosai kad’an tachi taji ta k’oshi. Bayan da yagama chi ya sake janta zuwa d’akin nasu tare dayin wurgi da ita a k’asa, wardrobe ya bud’e tare da ciro wani powdered substance fari k’ulle cikin leather. Tana gani jikinta yabata abin zubda cikin ne kuka ta soma papawa. “Ya haka sekace kinga mala’ikan mutuwa?” Kai kawai take kad’awa tana baya-baya. “Ya Farouq dan Allah kayi hak’uri.” Hannunta ya cafko “kinga karma kibani wahala ki bud’e bakinki kisha wannan dakanki if not zan d’ura miki na k’arfi da yaji.” “Ya Farouq I beg you dan girman Allah.” Ledar ya bud’e “ungo gashi” sam tak’i karba. Kad’an daga cikin maganin yasa a hannunsa tare da maquro fuskarta “bud’e bakin bud’e nace!” gamme bakin nata tayi se buginsa take a k’irji haka seda ta zubar da maganin hannunsa dana ledar duka a k’asa dan shuresan data tayi. “Ke?! Bakida hankali ne? Maganin kika zubar?” Wani wawan mari ya kai mata “tunda kince bara abi hanya me sauk’i ba by the time na miki fyad’e anan shegen cikin naki ze zube.” Bugata yayi da jikin bango yasoma sunsunar wuyanta yana bin jikinta da filthy harshensa k’afanta ta saita takai masa bugi a daidai manly place nasa fiye da na jiya. “Arrgghhh!!” Ya sakar da wani irin wahalallen k’ara tare da durk’ushewa da gudu ta bi ta gefensa mayafinta daya riqo tasa hanu ta fisge da sauri tasa gudu se k’olla mata kira yake amman sam tak’i juyawa a gurguje tafito daga d’akin ta inda taga staircase tabi wajen. Har a yanzu hannunsa na a rik’e a wajen nasa jikin bango yake dafawa har yafito daga d’akin. “Guards! Securities! restrain her!!” yayi maganar da ihu, k’ara gudun ta tayi bayan ta sauk’o last floor d’in ta dosa babban k’ofan data gani, chan tayi kicib’is dawani giant mutumi bak’i k’irin wane an pentasa, baya tayi da wuri ayayinda yake takowa gabanta. “Bawan Allah dan Alkah kayi hak’uri ka rufa min asiri kabarni in gudu dan Allah...” tana maganan tana ja da baya gum! Taji jikinta ya had’e dana mutum a hankali cike da tsoro ta juya fuskar Farouq tagani nan tashiga wani sabon b’arin. “You can never escape from me you stupid” yakaura mata mari. “Take her Joseph kaje ka k’ulla min ita da chains ka kuma rufe min bakinta.” “Ya Farouq dan Allah kay-” bata k’are maganar ba Joseph ya sab’ata a kafad’arsa achan yaje ya k’uk’k’ulleta**** ANAS 10:45AM Amal ce tsaye akansa yana zaune bisa Sallaya se kuka yake ba makawa, “Ya Anas dan Allah kukan nan ya isa bayida amfani ko bacci fa bakayi ba through out jiya da daddare nafilfili ka rigayi da garin Alkah ya waye yanzu kuma barakayi bacci ba? Please is okay in shaa Allah zamu sami Fannah kabar kukan please.” “Angel how?” Abinda bakinsa ya iya furtawa kenan, “taya zamu sameta bayan bamu ma iya reaching nata duk layin da nasan zan iya samun Farouq na kira basu shiga and I have no idea ina zan sameta bansan wani hali take ciki ba Amal.” Bayansa tahau bubbugawa “is okay Ya Anas zamu sameta in shaa Allah.” Daidai nan Ummie tashigo ma Anas da breakfast haka sam yak’i chi danko bayida appetite ko kad’an, inbega Fannah ba bai tunanin ze iya sake chin abinchi da k’ak’ani k’ak’a Ummmie tasamu yaci kad’an bayan yayi wanka suka fita police station dan fara investigating al’amarin. Daga gidansu Fannah suka fara inda akyi ma su Mami da Baba tambayoyi da dama cikin wuni d’aya Mami ta fita hayyacinta ta canza kamanni gabad’aya. Waya akasa Baba yayi wa Ya Khaleel bayan ya d’aga aka had’asa da police fitsari ne kawai beyi ba daga jin muryan police. Minti goma kacal aka basa da yazo sa gidansu Fannah if not za’a iya using rashin zuwansa against him ayi arresting nasa. 8 minutes later... Daidai nan shigowar Ya Khaleel sekace salihin asali sewani behaving innocent yakeyi tambayoyi da dama aka masa wanda duk ciki be bada amsa d’ayan daya kasance gaskia ciki ba, “ya akayi Farouq yafito daga gidan yari?” “Bansani ba wallahi ranka shi dad’e.” “When last rabuwanka dashi?” “Sati uku da suka shud’e kenan yanzu, tun daga ranan dana kai masa visit dana sake komawa washegari akace min anyi bailing nasa nata gwada layinsa bana iya samunsa, ku tayani nemo d’a na please.” “Are you sure Mr. Khaleel danko kamana k’arya zamuje mu duba record.” “Www... Wallahi Ba k’arya nake ba” ya k’are maganar yana had’a gumi. Ko da aka buk’acesa da ya kawo wayarsa aduba aga, ba fargaba ya bada saboda Farouq ya fad’a mai aduk lokacinda sukayi waya yana deleting logs nasa dan haka ba’a samu aka gano wani abu ba. “Abuu wallahi he is lying he is definately lying yasan duk wani whereabouts na Farouq b’oyewa yake munafikin Allah kawai.” “Haba Anas d’ana-” katsesa Anas yayi “shut the f*ck karka sake misantani da d’anka criminal ass kaji na rantse Ya Khaleel kome kake wallahi in na gano you also have something to do with the disappearance of my wife I won’t hesitate to kill you da hannu na zan kashe ka irresponsible father kawai.” “Nasan da ky-” be k’are maganar ba Anas ya mik’e a fusace tare da shak’uresa jikin bango “ina Farouq yakaimin Fannah?! Tell me! Ina yakaita?!” Abuu ne dasauran police d’in suka yi sauri suka k’wato Ya Khaleel kafin Anas yayi masa illa, d’an banza tuni nishinsa ya canza idanunsa suka wani fito waje dan azaba. FANNAH 1:50PM A hankali aka bud’e d’akin da aka rufeta ciki, a firgice ta maida kallonta wajen idanunta suna tsiyayar hawaye. Bak’in fuska taga d’auke da abinci da ruwa a hannayensa nan tashiga rawa daidai gabanta mutumin ya ajiye abincin tare da since mata bakinta da hannu d’aya yace “ga abincinki inji Boss kichi.” Seda ta bari yakai bakin k’ofa sannan takirasa da “bawan Allah” chak ya tsaya. “Wani abu ne?” Ya tambayeta tare da kewayo wa. “Bawan Allah muslimi ne kai?” “Eh me kika ga?” ya bata takiacaccen amsa. “Masha Allah k’arfe nawa ne dan Allah?” Bayan ya duba agogon hannunsa yace, “1:52PM” numfashi ta saki “dan Allah ka sinceni inyi Sallah banyi Sallan Azahar ba.” “Boss bece in sinche ki kiyi Sallah ba so eat insamu inbar nan.” “Be fad’a ba amman ai kai kasan haqqin Sallah dan Allah ka sincheni.” Wayarsa yaciro ya kira Ya Farouq alokacin yana a airport yana proceeding abubuwan tafiyansa Ukraine da Fannah dakuma Ya Khaleel kasancewar yasamu passport nata acikin jakarta. “Hello Boss gata nan na kawo mata abincin amman tace setayi Sallah.” “Karka damu kabarta tayi amman ka tabbata kana tsaye a kanta har tagama okay?” “Okay Boss” “Good bayan ta gama kuma ka kuma d’aureta karku bari tayi escaping.” “Angama Boss” yana gama wayar ya maidashi cikin aljuhunsa sannan ya nufo gabanta ya sinche mata chain d’in da kwad’on da aka datse. Kamar wanda k’wai ya fashe ma aciki ta shiga bayi tayi alwala sannan tayi Sallah duk mutumin na kallonta, jira yake taci abincin yayi tafiyarsa amman tak’i koda bud’ewa. “Hey Miss kiyi ki ci abincin mana banason wasan cha-chan nan ya wuceni fah.” “Kayi tafiyar ni barin chi ba.” “Suits you right” nan ya mik’e ya kamata ya k’uk’k’uleta again hawaye take sosai “bawan Allah nasan da akoi ragowar imani a tattare dakai dan Allah ka taimaka min nakoma gun mijina dan Allah nace.” “Allah sarki kyakkyawar hallita sede yadda kika gannin nan barin iya cin amanan Boss d’ina ba” yana kaiwa nan ya fice haka tata kuka gawani erin bak’in yunwan da takeji. Har Sallan Maghrib Farouq be dawo ba kamar d’azu ya tura MB daya kawo wa Fannah dinner anan ne daya sinche ta tayi alwala ta had’a La’asar da Maghrib sede yunwa takeji sosai yanzu dan dole tad’an tab’a abincin. Tana cikin chi wayar MB yasoma ruri a hanzarce ya d’aga “hello Mazzaaa yaneh?” On the otherisde aka amsa “gani nan fah ina cikin gari wallahi harka ya taso kana ina?” “Ohh boi! Ina nan bayan gari ta wajen gidan man Mobil.” Gidan man Mobil? Fannah ta nanata a ranta dad’a kasa kunnenta tayi tana sauraronsa. “Mobil wanne d’aya kenan Mazzaa?” cewar abokin nasa. “Mobil daya d’auki hanyar barin Maiduguri mana ta Yobe.” “Oh okay toh zan iso semu had’u.” “Okay toh ina jiranka” nan ya katse wayar tare da kewayo da kallonsa kan Fannah, yi tayi kamar bata masan yana kallontaba se chin abincinta take a hankali. “Hey Miss ko Mrs kike kiyi sauri kina b’ata min lokaci.” “Nagama tace dashi ba imani kaman d’azu ya sake k’uk’k’ulleta sannan yayi tafiyarsa. Tunanin ya zatayi tasamu waya tayi texting wa Anas location da take yanzu take tunda tagano location d’in, sede sam takasa batasan ina zata samu waya ba duk masu ma Farouq aiki zuciyarsu a karye suke kamar nasa. © MIEMIEBEE

Share:

4 comments:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).