shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday 7 September 2016

TANA TARE DA NI...6---10

tana-tare-dani.jpg

 TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 06
BY MIEMIEBEE
       “Ni ba abinda nake nufi ba kenan, my point is adena kirar ‘yata kariya. Alhj Suleiman kai da d’anka zaku iya tafiya, abincin wani gub’an wani kamar yadda ka k’yamaci Fannah haka wani zeji kamar ya mutu mata. Ahmad Allah had’aka da rabonka, ka kasance masoyin Fannah na hak’ik’aamman there is nothing you can do now dole ka hak’ura kabi umarnin mahaifinka, in zakumin uzuri, I need to see my daughter.” Yana kaiwa nan ya shige d’akin Fannah.

       Idanun Ahmad take suka kad’a sukayi ja, koda wasa be tab’a tsammanin akoi abinda ze shiga tsakaninsa da Fannah ba, yana santa fiye da yadda yake san kansa. “Abba dan Allah kar muyi haka, wallahi nasan Fannah is innocent.”
      “Ahmad kaji na rantse maka kasake min maganan wannan kariyan zan tsine maka, ai saisa akace a bincike mutum shiru-shiru. Maza mu wuce gida, Alhj Khaleel nagode sosai Allah bar zumunci.”

      “Bakomai Alhj Suleiman, ita gaskiya haka take daga k’in jinta kuma se b’ata. Allah rufa mana asiri.” Da fad’in “ameen” Ahmad dake hawaye shida mahaifinsa suka bar asibitin. Suna ficewa ya Khaleel ya b’alle da dariyar mugunta. “Ai dama nace in shaa Allahu ‘yarka barata auri wani ba inba d’ana ba. Kyakkyawar mace me addinin muslinci Farouq ya cancanta kuma ba kowa bace illa Fannah saboda haka tana warkewa zanje in samu Baba (mahaifinsu) in masa magana.”

      Gida ya zarce yana isa ya soma k’olla ma d’ansa Farouq kira. “Farouq! Farouq! Zo nan” alokacin ya zauna kan wata tabarma bada jimawa ba Farouq d’in yafito da angansa an ga d’an iska wata shegiyar crazy wando ne a jikinsa da singlet. Ba laifi yanada kyau dadai dakuma tsawo. Bayan ya zauna yace, “gani Baba.” Ya Khaleel ya kallesa sannan yace, “d’ana ka kwantar da hankalinka Fannah ta kusan zama taka, Fannah taka ce! Yanzu ana sallamota daga asibiti zan wa kakanka magana.”

       “Baba dagaske!” Farouq ya tambayi mahaifinsa cike da jin dad’i. “Da dana ce maka seka auri Fannah ka d’au wasa nake maka ne? Ai Fannah taka ce.”  “Kai Baba na gode amman da akoi matsala Baba.”
      “Ina jinka Farouq mecece matsalar yanzu in warkar maka da ita?”
       “Fannah... Bata so na Baba ko kad’an zan iya irga sau nawa muka tab’a magana da ita, sam bata sona ta tsane ni.”
      “A da kenan...” Ya khaleel ya fad’a yana murmushin mugunta.
      “Ban gane a da ba kenan Baba.” Farouq ya fad’a a little bit confused.

      “A da datake da tabbacin cewa akoi masu santa amman banda yanzu data rasa budurcinta, kap ba na mijin da ze so ta yanzu, ta zamo tamkar k’azantar da akeson a yasar ne yanzu. Ko baka gane ba?”
      “Sosai na gane Baba na gode.”
   
    *
       Afrah ce tsaye kan Fannah tana kallonta hawaye suna gangara kan kumatunta a yayinda Baba da Mami suke zaune kan wata kujera, Aiman kuwa an mata shimfid’a a k’asa tana bacci. Hannu Afrah ta mik’a dan ruf’e Fannah mekyau da  bargo taga kamar Fannah tad’an motsa.

     “Barin je in kama ruwa” cewar Mami “ina zuwa yanzu.” Kai Fannah ta kad’a a hankali again. “Ya Fannah! Baba! Mami! Fannah tayi motsi.” Kafin su Mami su k’ariso Fannah ta soma bud’e ido a hankali tagama bud’e idanun nata ta sauk’esu kan family’nta dake tsaye a kanta suna murmushi da zubda hawaye a lokaci d’aya, murmushin tayi k’ok’arin mayar masu da k’yar.

     “Ya Fannah!” Cewar Afrah
     “Fannah! ‘yata” cewar Mami.
      “Mama na!” Cewar Baba.

      Kallonsu take a hankali cikin wata dashasshiyar murya tace, “Mami, Baba, Afrah.” Dad’a k’aruwa murmushin fuskarsu yayi Baba yace, “Afrah jeki kira nurse kice mata Fannah ta farfad’o.” Bayan minti d’aya Afrah dawata nurse suka shigo d’an dube-dube tayi wa Fannah sannan taceda su Mami “Alhamdulillah condition na ‘yarku is stable. Inda hali a had’a mata tea me kauri tasamu tasha se abata magunanta. Excuse me.”

     Hugging nata sukayi one-by-one kowa na muranan dawowarta. “Ina Aiman?” ta tambaya a wahalance kusan a tare suka amsata “gata can tana bacci.” “Fannah ya jikin naki?” cewar Mami
      “Da sau... Argh!” Tasaki k’ara.
     A rikice Mami tace. “ina ke maki zafi Fannah?” Take idanunta suka cike da hawaye, “k’asa na Mami, zafi.” “Malam ko zaka d’an bamu waje dan Allah” cewar Mami cike da tausaya wa ‘yarta. Bayan Baba yafita Mami ta umarci Afrah ma da tafita ba gardama ta fice.

       “Fannah kiyi hak’uri dole k’asarki ya miki zafi anji miki ciwo.”
     Tana kuka tace “Mami ya rabani da budurci na ko? Mami banida martaba yanzu.” Ta fashewa dawata erin matsanancin kuka.

     “Fannah ‘yata dan Allah kiyi hak’uri kukan nan k’ara miki rashin lafiya zeyi, kiyi hak’uri. Ki d’au wannan k’addara ce Allah ya turo miki.”

      Cikin kuka tace, “Mami yanzu akoi d’a na mijin da ze yarda ya aureni? Nasan ko Ya Ahmad ze gujeni.”
       Shiru Mami tai batace komai ba hakan ya sake tabbatar wa Fannah zancenta. “Yama riga ya tafi ko Mami?” Har yanzu Mami batace da ita komi ba se kuka ba sautin da takeyi. “Mami talk to me please, ki fad’a min gaskia.”

     “Fannah kiyi hak’uri wannan jarabawa ce Allah keson gwada ki, in baki rungumi k’addara ba seki fad’i. Ahmad be k’i ki ba mahaifinsa ne ya tilasta masa se ya rabu dake saboda Kawu Khaleel yace masa saurayin kine ya miki wannan abu.”
       “Mami amman ai k’arya ne, wallahi bansan shi ba acikin lungu kawai ya tsareni wallahi ban tab’a ganinsa ba inba ranan ba.”
      “Shhhh! Fannah basekin min bayani ba sanin kanki ne Kawu Khaleel tinba yau ba baya sanki, yayi hakan ne kawai dan ya shiga tsakaninki da Ahmad dan yaga Ahmad nasanki tsakani da Allah.”

       “Mami me na masa ya tsaneni haka? Mena ma wannan saurayin daya k’wace min martaba ta Mami? Shin na kasance mutumiyar banza ce da duk munanan abubuwa suke faruwa dani?” Hannu Mami tasa ta goge mata hawayen dake gangara kan kumatunta, “ko kad’an habibti, ita duniya haka take mutane masu kind heart su Allah yake jarabta saboda ya gwada nauyin imanin su. Wannan jarabawa ce Fannah you have to be strong.”

     *****
     *ANAS*

       D’aki ne babba da gadaje guda uku ciki, haka wardrobe ma, sannan da bathroom aciki. A d’aya daga cikin gadajen Anas ke kwance akai da earpiece a kunnensa wanda ke had’e da wata sabuwar Iphone 6s ajiye kan cikinsa. Sanye yake da ¾ wando da vest bak’a ya zura wa ceiling ido se tunani yake. Bada jimawa ba wasu samaruka guda biyu suka shigo wanda suke nan sa’anin Anas, da angansu anga ‘yan hutu. Gado d’add’aya suka d’auka suka kwanta kai har alokacin Anas besan da shigowarsu ba.

      Pillow d’ayan ya wulla masa a firgice ya mik’e ya zauna ganin su ne yasa ya sauk’e ajiyar zuciya. “Mehn! Yaushe kuka shigo bansani ba.”

      “Well kayi nisa a tunani taya zakayi noticing shigowarmu?” cewar na k’arshen. “Waima tunanin me kake haka? Kullum fa cikin tunani kake ko ka bar mata da ‘ya‘ya ne acan gda 9ja?”
   
     suka k’yalk’yale da dariya illa Anas daya tsaya yana kallonsu.
     “Musty waikam meke damun Anas ne?” cewar d’ayan.
     “Ji Abdul de da wata magana budurwarsa ce ni da zan sani?”
     “Oh oh no please banda maganan budurwa anan” Anas ya fad’a in an angry tone.
 
        “Wai Anas kai kullum haka kake ne? Ban tab’a ganin kayi dariya ba wallahi, whats wrong with you? And anytime aka kawo maganan girlfriend you seem so moody.” Cewar Abdoul.
 
    “Nima de, abin have been bothering me.” Hannu yasa yaja d’aya daga cikin bedside drawer’n gadonsa tare da ciro wani syrup ya wulla wa Anas karap ya cafke. “Meh wannan kuma?”

    “Wannan!” yad’an murmusa “lets say anti-problem kokuma problem reliever.” Shida Abdoul suka kwashe da dariya. Kallaon syrup d’in Anas yayi sannan ya ajiye kan bedside drawer’n nasa “no thanks barin sha ba.”

     “Chill bro!” cewar Musty. “It'll ease all your problems just give it a try.” Haka suka ta cika masa baki kan in yasha ze manta yanada problem ko d’aya akansa seya d’auka ze sha seya tuna wa’azin da Abuu yamasa amman kuma problems sun masa yawa right now gana Ummimi gakuma na yarinyar daya yi raping. Rufa ido kawai yayi daga k’arshe yasa kwalban syrup d’in a baki. “Dude (maza) karka shanye duk-” be k’are maganar ba Anas ya kauda kwalban syrup d’in daga bakinsa sanda ya kwankwad’e tas.

     Fuska ya yamutsa trying to adjust and in just 3 minutes Anas ya fad’a bacci, baccin daya jima beyi ba in a lifetime.

     _7 hours later_

     Daidai 8:30PM Anas ya tashi, ko sallan la’asar, maghrib da Isha beyi ba duk yini yayi yana bacci. “Holy shit!” Ya fad’i. Sede kuma kap ya nemi problems nasa ya rasa, da yayi niyan bare sake shan syrup d’inba amman dan yadda ya masa aiki he can’t resist it. Daidai ya mik’e ze shiga toilet Musty da Abdoul suka shigo da angansu anga wad’anda suka dawo daga party, dan aikinsu kenan. “Ya dude har ka tashi ne?” Musty ya tambayi Anas yana k’ok’arin zama.

         “How did you like the syrub? Your problems will all be gone for good two days and after that seka nema ka sake sha, continiously” Abdoul ya ma Anas bayani tare da fad’awa kan gadonsa da baya.

     “Great!” Anas ya ce, “I can’t remember any of my problems now saidai nata bacci ko sallan la’asar banyi ba.”
     Tsuka Abdoul yaja “yanzu dan kawai yau ka rasa sallolin nan shine wani abu? Kaifa Anas kanada case, wannan blue eyes naka basu taimake ba. Nifa the first time I saw you nad’au American ne kai to seme dan ka share sallolin yau?”

    “Tell him bro” cewar Musty. D’an murmushi Anas yayi lallai duk iskancin mutum dubu sun fisa, can a Bama sune ‘yan iskan gari nan kuwa a tafin hannun su Abdoul yake be sauraresu ba yashige toilet yayi alwala yafito ya rama sallolinsa.

  Da misalin k’arfe 11:30PM su Musty suka kuma yin wanka suka yi shiri tsaf a yayinda Anas keyin zanen project da aka basu a school. Da suka zo fitane suka juya suka kallesa tare da kad’a kai. “Anas wai kai ko kad’an baraka gwada zuwa clubbing d’innan bane? Wallahi its fun, more fun than wannan jakin project da kakeyi na 5 marks kacal.” Cewar Musty ransa a b’ace.

     “No kuje kawai, I have to get this done, maybe next time.” Anas ya sanar dasu yana d’an murmushi.
   “Dude listen to him, ko na yau ne kazo muje club d’innan.” Cewar Abdoul. Kai kawai ya kad’a masu bayan sun fice yayi rounding up abinda yakeyi ya kira Ummie bayan sun gaisa yasa ta mik’a ma Angel nasa suka ta hira abinsu. Anas na mutuwan san Amal badan komai ba dan abinda Ummimi ta mata.

     Ace yarinya kwanan ta d’aya a duniya amman dan rashin imani tasa a dawo da ita gida ko shayar da ita batayi ba.

 _2 days later_  

         Da misalin k’arfe 12:30PM Anas na kishingid’e kan wata couch (kujera me fad’i da akan iya bacci akai) yana bacci. Ya soma mafarki;
 
    _“Ummimi dan Allah karki tafi kiyi hak’uri indan plates dana fasa ne I promise baran sake ba. Ummimi I am sorry dan Allah karki tafi. Abuu ka hana Ummimi tafiya dan Allah kace mata I will be a good boy from now on.”_

       _“Yanzu Aysha bara kiji tausayin yaranki ki hak’ura ki zauna dasu ba. Kalli yadda suke kuka fa?_

    _“Mstww wannan kuma ku ya shafa nagaji da zama cikin talaucin nan, ace kullum se atashi ba’a san me za’a karya dashi ba gaskia nagaji daman tun farko sanda Abba na yace kar in aureka matsiyaci ne kai amman nak’i sauraronsa. Ga can miji Allah yamin har k’asar waje ze kaini saboda haka ban ga abinda zesa in cigaba da zama a wannan gidan ba.” Jakarta ta ja ta soma tafiya da sauri naje na kama k’afarta ina kuka ina rok’arta wani wawan ball tayi dani da k’afa sanda na ji ciwo a elbow na...”_

“UMMIMI!” Anas ya kira da k’arfi a yayinda ya farka daga baccin dayakeyi duk zufa yakeyi se nishi yake da k’arfi ganin mafarki yake yasa hankalinsa yad’an kwanta. Wani erin mahaukacin bacci yakeji saboda jiya kwana sukayi a studio amman saboda duk sanda ya rufe idansa mafarkin Ummimi yake yasa ya kasa baccin abu d’aya ne yasan inyasha ze gusar masa da problems nasa which is syrup na problem reliever (giya) da Abdoul ya basa ranan.

     Kash! Saidai basu gida sun fita yawo gashi bacci yakeji. Gwada jirarsu yayi na ‘yan mintuna ganin basu dawo ba yasa ya kira sa a waya kai tsaye ya tambayesa ina yake ajiye syrup daya basa ranan yana san sake sha. Dad’i sosai Abdoul yaji finally Anas is ready to change, bayanin ina yake ajiye wa ya masa yakuma tabbatar masa in zasu dawo gida ze sake siyowa tunda wanda ya rage kad’an ne.

       Exactly inda Abdoul yamasa kwatance yasamu syrup d’in bud’e sabon kwalb’a yayi yakafa a baki sanda yashanye tas, ko cikakken minti biyu beyi ba yasoma jin bacci me nauyin gaske tsalle kawai yayi ya fad’a kan gadonsa yasoma wani erin mahaukacin bacci me uban nauyin gaske

           *© miemiebee*

 TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 07
BY MIEMIEBEE


        FANNAH

      3 days later...
   
     Kwanan Fannah uku a asibiti tasamu k’arfin jiki aka sallamesu, ayau suke shirin dawowa gida, Alhamdulillah jikin nata da sauk’i sosai saboda anti-biotics datake sha masu k’arfi ne sosai. Baba ya sayarda shanunsa da shi ya samu ya biya kud’in asibitin ta da kuma na magunanta.

     Daidai sun sauk’o daga keke na pep kenan se ga irin almajiran unguwan nan sunzo sun tsaya gabansu.

         “Fannah! Dama ashe ke d’in kariya ce me bin maza, sekitayin abu kamar ‘yar malam saliha to Allah ya tona miki asiri tunda saurayi yayi miki ciki.” Hannu Mami ta d’aga ta wanke sa da mari. “In na sake jin wannan munanan kalamu daga bakinka kaji na rantse seka kwana a asibiti, bakai kad’ai ba dukanku nan. Fannah ba kariya bace abinda ya sametan nan k’addara ce. Maza ku fice min daga kallo.”

    Baya sukayi kad’an sannan suka soma wak’a “kariya! Kariya! Fannah kariya Fannah kariya!” Hannun Fannah kawai Mami taja suka shiga ciki a yayinda Baba ya koresu.
    Kuka Fannah keyi sosai. “Yanzu shikenan Mami kallon kariya za’a na mun? Shikenan rayuwata ta lalace Mami.”
        “Shhh karkiyi magana haka, karki saurare wad’ancan almajiran basu masan me suke fad’i ba.” Hugging nata tayi har sanda Fannah tayi shiru.

      Da yammacin ranar around k’arfe 4:45PM Ya Khaleel da d’ansa Farouq suka shigo gidansu Fannah. Mami da Afrah suna had’a girkin dare suka masu sannu da zuwa, ba abinda Afrah ke masu se harara. “Ke Afrah jeki kira min mahaifinku dakuma ‘yar ku kariyan can.” cewar Ya Khaleel.

           “Kawu Khaleel bamuda kariya a gidan nan.” Ta fad’a stubbornly.
          “Ke ni keke gaya wa magana? Iyye?”
     “Kawu kayi hak’uri Afrah kibasa hak’uri kije ki ma Babanku da Fannah magana.” A sanyaye ta mik’e taje ta kira Baba sannan takira Fannah a tare suka fito. Fuskar Baba a tamk’e ya zauna kan tabarman da Ya Khaleel da d’ansa ke kai ba tare da ya musu magana ba.

       “Ina wuni kawu?” Gaisuwar Fannah.
        “Yawwa sannu an sallamoki kenan. Se a kiyaye aukuwan na gaba kafin wani saurayin yasake fiad’e ki.”

     Har tsakiyan kanta tajiyo wannan kalamai ba ita kad’ai harsu Baba da Mami da Afrah. “Ya Khaleel in kasan batun daya kawo ka gidana dan kaci zarafin ‘yata ne dan Allah kayi hak’uri na had’aka da Allah ku tashi ku tafi.”

       “Ba seka koremu ba yanzu zamu tafi. Magana d’aya biyu na zoyi nan saboda haka nakeson ku bud’e kunnuwanku ku saurareni. Kunfi kowa sanin yadda ake k’yamatan kariya a gari, ba uban da ze so d’ansa ya auri macen da batada budurci. Fannah kuwa ‘yata ce dukda abin kunyan da ta mana ina san ta saboda haka zan bata wa d’a na Farouq.”

     “What!?” Baba yayi exclaiming.

     “Bari na gama mana k’ani na. Na riga nayi wa Baba magana kuma ya goyi bayan zancen d’ari bisa d’ari bawai nazo nan bane in baku choices saboda bakuda choice inbanda ku yarda mu rufa wa kariyarku asiri dan na tabbata kap garin nan bame san aurenta. Kinji ai Fannah? Ga Farouq nan mijinki, kina k’are secondary ze rufa miki asiri ya aureki zaki iya gode masa saboda wannan jahadi yayi. Auren kariya ba wasa bane.”

     D’ago jajyen idanunta tayi ta azasu kan Farouq dake ta mata murmushi. Hawaye se gangara suke kan kumatunta, kuke take sosai. Tasani a yanzu kam kamar yadda Kawu ya fad’i ba na mijin da zeso aurenta saboda ta rasa budurcinta martabatar ta, amman duk da haka gomma ta mutu batai aure ba data auri Farouq. Farouq baida tarbiyya ko kad’an d’an iska ne ba aikinsa se bin mata Allah kad’ai yasani ko baida cutar k’anjamau ma. Ba yadda za’ayi ta auresa.

       “Kawu dan Allah kayi hak’uri ni baran auri Ya Farouq ba, dan Allah ka rufa min asiri.”

        “Ji shashasha dabadan Farouq nada imani bama jinki ze yarda ya aureki ne? Ajinki a kariyan da kike yanzu zaki samu na miji kamar Farouq yace ze aureki ne? Inba mahaukaci ba wallahi ba na mijin de so ya aureki gara ma tun wuri kinsan ina ke miki ciwo”

      “Enough Ya Khaleel!” Cewar Baba a fusace. “ ‘yata barata auri wannan d’an iskan ba. Mungode da alfarman da kuka bamu amman bamuso da in aura wa ‘yata d’an iska kaman Farouq na gommaci kartayi aure a duniya. Yaro ko gaishe dana gaba dashi be iya ba. Ku tashi kubarmin gida zanje in samu Baba in masa magana yaja da baya da wannan zance. Fannah bata san Farouq saboda haka barin tilasta mata ba.”

      “Aww haka kace kenan? Yanzu har zaka bud’e baki ka kira d’a na Farouq d’an iska? Kariyarka kuma fa? ai nakega sede ace mata ‘yar guguwa, aure tsakanin Fannah da Farouq kuma consider it done bari ta k’are shirmen secondaryn nan kuga ikon Allah. Wawiya ana taimaka miki kina wawanci mschww Farouq tashi mu tafi da Allah.” Suna ficewa Fannah ta ruga d’aki da gudu ta baje kan katifar ta tana kukan cire rai. Afrah ce tabiyo bayanta itama kukan take tabbas Fannah tana cikin tsaka me wuya duk wanda ya aikata mata ta’addancin can ya cuce rayuwarta har a bada.

       Tun ba yau ba Fannah ta tsani Farouq taya za’ace shi zata aura? Kasheta akeson yayi?

     “Yi hak’uri Ya Fannah dan Allah kibar kukan nan in shaa Allah baraki auri Ya Farouq ba.” D’ago jajayen idanunta tayi “Afrah shikenan ni haka rayuwata zata k’are cikin k’unci da bak’in ciki? Mesa se ni Afrah? Mena tab’ayi da ba kyau to deserve all this? Duk abinda addini na yace inyi inayi wanda kuwa ya haramta ina k’ok’arin nisantar kaina daga aikatasu. Mesa seni wancan saurayin zeyi raping? Mena masa Afrah? Mesa seni za’a ce zan auri Ya Farouq kinfi kowa sanin halinsa. Kullum yana nan a bayan gari yana kwanciya da mata, Afrah dan Allah ki taimaka min.” Ta kuma fashewa cikin matsanancin kuka.

     Itama Afrar kuka take ta rungumi yarta tana bata hak’uri.

     ****

        “Malam dan Allah kayi wani abu karka bari Kawu ya cimma burinsa na aura wa Fannah aure da Farouq kafi kowa sanin halin Farouq so nawa ake kamasa a bayan gari? Dan Allah kaji k’an ‘yarmu Fannah. Ko kad’an she’s not to blame for what happened to her fiad’e aka mata munyi iya binciken da zamu iya mun kasa samun waye ya mata wannan d’anyen aikin.” Ta fashe da kuka.

      “Maman Aiman in shaa Allah barin bar Fannah ta auri Farouq ba. Yanzun nan zanje in samu Baba in masa magana kishiga ciki kibata hak’uri ki kwantar mata da hankali dan Allah. Ni na wuce...”

**

     “Ina wuni Baba?” Gaisuwar Malam Aliyu Babansu Fannah ga mahaifinsa da Ya Khaleel.
       “Lafya Aliyu, ya jikin Fannan?”
      “Da sauk’i Baba.” Ya amsa yana kallon wansa Khaleel da d’ansa dasuke zaune a gefen mahaifin nasu.
       “Nasan maganan daya kawo ka Aliyu saboda wan ka Khaleel yamin bayanin komi yanzu. Kasani wan ka bare tab’a maka abinda ze cutar dakai ko iyalinka ba. Kafi kowa sanin halin da ‘yarka tashiga kallon kariya ake mata agari me bin maza-”

      Malam Aliyu katse mahaifin nasu “amman Baba ai duk munsan ba haka asalin abar take ba, fiad’e aka mata.”

      “It still will not change anything Aliyu, in mu mun yarda da hakan mutane fa? Baramu iya fahimtar dasu ba. Kap garin nan ba mahaifin da ze b’ar d’ansa ya auri wacce batada budurcinta tattare da ita kasani Aliyu. Allah ya kawo mana sauk’i gida ga wan ka nan Khaleel he is ready ya rufa wa ‘yarka asiri ya d’au d’ansa ya aura ma ‘yarka dukda ba cikakkiyar mace take ba yanzu amman har ka bud’a baki kace bakaso? Ina zaka zo ka kai ‘yar taka?”

    “Baba in shaa Allah, Allah ze kawo mata miji wanda ze sota a yadda take.”

     “Har tsawon yaushe kuma zaka tsaya kana jiran wannan rana da bakasan ranan zuwanta ba? Iyye Aliyu? Bana sake jin wani zance, Fannah zata auri Farouq wannan shine san da muke mata bamusan tak’are rayuwarta batayi aure ba.”

      “Baba dan Allah kayi hak-”

   Baba ya katse sa. “Aliyu wannan shine karo na farko da kake k’ok’arin bijire min, kar muyi haka da kai. Farouq.” ya waiwayo da kallonsa kan Farouq

    “Na’am Baba.” cewar  farouq.

    “Kanason Fannah zaka aureta koda bata da budurcinta a tattare da ita?”

        “Eh Baba ina santa k’anwa tace koda duniya sun k’ita ni baran k’ita ba.”

    “Masha Allah” Baba yace. “Kaikuma fa Khaleel ka yarda d’anka ya auri macen da tarasa budurcinta?”
   
      “Na yarda Baba” cewar ya Khaleel. “Fannah ‘yata ce matuk’an ina raye zanyi duk iya abinda zan iya dan in kula da ita in rufa mata asiri.”

   “Toh masha Allah kadeji Aliyu. In nine kai godiya zanyi wa Khaleel da Farouq.”

    “Baba amman Fannah batasan Farouq, bata tab’a sansa ba, taya zamu tilasta mata auren wanda bata so.” Cewar Malam Aliyu.

      “Wannan kuma ba me wuya bane, in suka soma ganin junansu a hankali zasu shak’u. Allah dad’a had’a kawukan ku.”
    “Ameen” Ya Khaleel ya amsa banda Malam Aliyu dake ji kamar yayi kuka.

**

     “Sannu da dawowa Malam” cewar Mami tana k’ok’arin shimfid’a masu tabarma. Bayan sun zauna take tambayarsa ya had’uwan nasu ya gudana. Kai ya kad’a a hankali take jikinta yayi sanyi.

      “Maman Aiman Ya Khaleel ya riga ya saye Baba nuna masa yayi intensions nasa are clean tsakani da Allah yakeson ya aura wa Fannah Farouq saboda tsantsan tausayi.”

    “Malam amman ai duk munsan badan haka bane.” Mami ta katse Baba. “Tun ba yau ba idanun Kawu suke kan Fannah shikansa yasan tana da tarbiyya mekyau da hankali so yake ya aura wa Farouq Fannah saboda ta giara masa d’a ita kuma tasha wahala in the process.”

        “Ba k’arya cikin magananki Maman Aiman ni kaina abin nan ya dameni bansan ya zanyi ba, tausayi Fannah take ban matuk’a yarinya me hankali ace arasa ma wa za’a d’aura wa k’addara erin wannan se Fannah.” yaja numfashi.

   “Uhn uhn Malam kayi istigifaar kar kayi sab’o. Wannan Allah kad’ai yasan mesa ya d’aura wannan mumunar k’addara kan Fannah bekamata muyi ma Allah shisshigi ba.”

     “Hakane Maman Aiman Astaghfurullah.”

     “Yanzu Malam shikenan sede mu zuba ido muna ganin ‘yarmu zata auri wannan d’an iska? Ba abinda zamu iya mata? Innalillahi!”

     “Da akoi abinda zan iya da nayi Maman Aiman banasan Fannah ta auri Farouq ko kad’an. Ran Baba ya b’aci ya dage se Fannah ta auri Farouq inhar na hana aikuwan wannan aure, zamu iya samun sab’ani da mahaifina.”

       Fannah dake lab’e ajikin bango tana sauraronsu ba abinda takeyi se hawaye. Daidai lokacin wani yaro yashigo gidan bayan ya gaisheda Mami da Baba yace “wai Fannah tafito inji Farouq.”  “Barata fito ba” cewar Baba a fusace. “Kace masa barata fito ba inji mahaifinta.” Nan Fannah dake lab’e tafito “kace masa ina zuwa.”  “Fannah!” Mami da Baba suka kira a lokaci d’aya.

         Tana kuka tana maganar, “Baba naji duk abinda kuka fad’a barinso saboda ni kasamu matsala da Baba ba. Muyi hak’uri mu rungumi k’addara fatarmu Allah sa hakan shi yafi alkheri, Allah sa auren Farouq ba sharri bane a gareni, addu’an da nake so kumin kenan. Barinje kirarsa kar yaje yasamu Baba ya fad’a masa wani abu daban yajawo maka matsala.” Tana kaiwa nan ta fice.

     Kuka me k’arfi Mami ta fashe da shikansa Baba sanda ya zubda hawaye, babu kamar Fannah, yarinya me hak’uri da hankali dole yasan abinda zeyi ya hana aukuwan wannan aure.

     Tana fitowa taga Farouq zaune kan benchin da take zama kullum da Ahmad nata take hawaye ya ciko mata a ido. “To ke kuwa Fannah haka ake hira? Haka kika sabayi ne in samarukan ki sunzo wajen ki? Taho nan mu zauna mana.”
       Kafin tace meh Farouq ya taso ya cafke hannunta da sauri ta waske hannun nata daga rik’onsa. Tana kallonsa da jajayen idanunta.

    “Meh haka kuma? Yau na miji ya soma rik’e hannunki ne? Kinga nifa ki sake jikinki dani tunda nasan ciki nasan waje ba sekin tsaya kina proving min innocence ba.” Hannun nata yasake rikowa da k’arfi sannan ya aza d’ayan hannun sa kan fuskarta yana shafawa. “Ji laushin jiki wai a haka ma kinbar samaruka suna tab’awa kenan.”

       K’ok’arin k’watan kanta take amman ta kasa se hawaye take yi “Farouq kasake ni bana so, kadena tab’ani.” K’in saketa yayi “meh aciki dan na tab’a mata ta ko kin manta a matsayin mijinki nake yanzu.” Matso da fuskarsa yayi sosai kusa da nata. Numfashinsu yana had’uwa. Kafin ya hankara Fannah ta tsinke sa da mari wanda besan sanda ya saketa ba.
 
     Hawaye take sosai “karka kuskura ka sake tab’ani in kai d’an iska ne toh ni ba ‘yar iska bace, in ka saba tab’a mata anyhow ni ba d’aya daga cikin ‘yan matan da kasaba tab’awa bane.”

   “Dallah can kariya kawai, keda kike bin maza kowa ya sani, zaki wani zo kina min zak’in baki. Kuma barikiji in fad’a miki duk sanda kika kuskura kika sake marina wallahi kinji na rantse sekin sake kwana a asibiti. Humm!” ya sakar da wata shu’umar murmushi “bari a aura min ke zaki yaba wa aya zak’inta. Se gobe ko baby, ki kula min da kanki please karki sake bin wani har abu yakuma shiga tsakaninku nasan you are itching to be with a guy.”

© miemiebee

 TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 08
BY MIEMIEBEE


Kasa cemasa komai tayi, kallonsa kawai take hawaye na gangarowa kan kumatunta, kuka ne yafi k’arfinta juyawa tayi tashiga gida da gudu ta tsaya daga wata lungu ta share hawayerta sannan ta k’arasa ciki. Mami da Baba ta tarar zaune yadda ta barosu. Basu ce da ita komai ba dan haka tashige d’akinsu da Afrah ta fashe da kuka bata san da wanne zata ji ba da rabata da akayi da budurcinta martabarta na k’arfi da yaji ne kokuma da auren wannan monster me suna Farouq tun be aureta ba ma yasoma mata rashin mutunci yana zaginta bale ace in sunyi aure, kwata kwata baida slightest regard mata.

     Bada jimawa ba Mami ta aike Afrah shago siyo man giad’a tun kafin Maghrib yayi gudun kar abinda ya faru da Fannah yakuma samun Afrah. Afrah ne tashigo d’aukan hijabi a d’akinsu, Fannah dake kwance a kan katifa da Qur’ani tana karatu ta d’aga kai tare da tambayarta. “Ina zakije haka?”
      “Shago fa Mami ce ta aikeni siyo man giad’a.”
      “Okay, jirani muje tare nagaji da zama nan shiru ni kad’ai.”
     “Toh sanya hijabinki muje Ya Fannah.” Nan Fannah tasa hijabi suka fito tare, “ya haka ina zaki Fannah?”  tambayar Mami ga Fannah.
      “Zan bi Afrah ne Mami nagaji dazaman cikin.”
     “Toh Allah kare dan Allah in har babu anan shagon Ya Wakil dana mak’otansa karkuyi nisa ku dawo gida kawai, kunji?”
     “In shaa Allah Mami” cewar Fannah sannan suka fice. A shagon Ya Wakil suka samu man giad’an sun jiyo zasu fice sega yaran unguwa sun taru suka soma wak’a

        “Fannah kariya me bin maza Fannah kariya me bin maza.”

         Hawaye tasoma yi bata tab’a tsammanin zatayi witnessing rana kamar ta yau ba, ranan da za’a ce tafita waje ana binta ana zaginta me bin maza.

          “Ku wai bakuda hankali ne?” cewar Afrah “wanj irin ‘yan iska ne ku? Wallahi in baku bar nan ba zan jefe wannan munanan bak’ak’en kankun da dutse, jahilai kawai. Bara ku matsa bane?”

        Ko ajikinsu ma magana ake masu  wak’an su suka cigaba dayi. Mari wani ya sake ma babban cikin nasu Tasss! Kukeji a fuska take ya soma kuka saurayin na juyawa suka had’a ido hud’u da Fannah take ta kau da kanta. Kolar rigarsa Ahmad ya rik’e da hannu d’aya “kanajina in sake jin ka kira Fannah ko wata mace a garin nan da kariya kaga abinda zan maka ba kai kad’ai ba dukanku nan” ya nunasu da yatsa. “Kunjini ko bakuji ba?”

     Baki na rawa babban yace, “munji dan Allah kayi hak’uri.” Ahmad na sakesa suka kwasa da gudu suka bar wajen. K’arisowa gabansu Ahmad yayi “Fannah kiyi hak’uri kibar kuka dan Allah, karki bari maganan yaran nan to get to you.”
 
         “Ya Ahmad dan Allah kayi hak’uri” Fannah tace tana hawaye hannu kawai tasa ta rufe bakinta ta ruga a guje se kiran sunanta Ahmad yake ko sauraransa batayi ba. Juyawa yayi ya kalli Afrah da itama idanta suka cike da hawaye. “Afrah kiyi sauri ki bita kar wani abu ya sameta. Tell her tayi hak’uri ta rungumi k’addara in shaa Allah, Allah ze sak’a mata kuma kice mata I will never stop loving her koda ban aureta ba, da santa zan mutu kice mata tayi hak’uri, ina kan mata addu’a.” Kai kawai ta giad’a masa tabi bayan Fannah da gudu.

      Tana isa gida ta tarar da Mami a tsakar gida se safa da marwah take.    “Mami ga man giad’an.”
        “Afrah meya samu Fannah tashigo tana kuka ta rufe k’ofar d’akinku nayi nayi da ita ta bud’e tak’i wani abu ne?”
        “Mami wallahi Ya Afrah tausayi take bani, yanzu fitan mu almajirai suka taru suna mata wak’a suna kiranta da munanan suna Mami.” Ta k’are maganar tana hawaye.

     “Allah sarki Fannah” cewar Mami itama tana hawayen, “Afrah inda zan iya karb’e pain da Fannah ke feeling danayi wallahi, it hurts me seeing my daughter in a horrible situation like this kuma ba abinda zan iya mata.” Hannu tasa ta share hawayerta addu’a zamu mata Afrah ko a islamiya ki fad’awa Malamanku su sata cikin add’ua kinji?”
          “In shaa Allah Mami barinje in sameta.” Tana tashi taje ta k’ofar d’akinsu tun daga bakin k’ofar take jin sautin kukan Fannah. “Ya Fannah dan Allah kibar kukan nan batada amfani, addu’a zamu dage dayi, bud’e k’ofar kinji? Ya Ahmad yabani sak’o in isar miki, yi hak’uri ki bud’e.”

    Fannah na jin Ya Ahmad ta tsananta kukanta haka ta tayi kusan na minti ashirin sannan ta tashi ta bud’e ma Afrah k’ofar bayan sun zauna Afrah ta isar mata da sak’on Ya Ahmad, se kuka Fannah ke Afrah na bata hak’uri. Comb ta d’auko da mai ta shafa ma Fannah a gashi sannan ta taje ta kama mata da k’yar, rabuwan gashin Fannah da giara tun kwanciyar ta a asibiti.

      Haka fa rayuwa ta cigaba da kasance wa Fannah, bak’in cikin yau daban na gobe daban, sam bata fita daga gida yanzu saboda duk sanda ta fita se yaran unguwa sun taru suna mata wak’a. K’arshen yawonta bakin k’ofar gidansu ne in Farouq matsiyacin yazo. Makaranta ma ko ina tashiga nuna ta akeyi da yatsa haka suka gama exams nasu batasan me take rubutawa ba.

       Kwata kwata ta fita daga kamanninta tayi duhu ta sake rama. Abinci ma ba kullum take ci ba rayuwa de takoma upside down wa Fannah baiwar Allah ba abinda ke mata dad’i ciki, Allah sarki!

     _One year later..._

       Alhamdulillah Fannah is trying to move on from her past. Hasken ta ya d’an dawo, ta rage tunani yanzu addu’a sosai ita da iyayenta suka dage dayi. Abun da yaran unguwa suke mata kuwa yanzu da sauk’i sosai seta fita kusan sau uku-hud’u ba’a samu matsala ba. Watanni uku da suka wuce akace su Ahmad sun bar garin Bama, koda yazo mata sallama k’in fita tayi badan komai ba wai dan ita a ganinta she don’t deserve him anymore bata san ma ya sake ganinta bale yaji yana santa. Shekarunta goma sha shida yanzu this year ta gama secondary school.

        Baba kam sanda ya kamu da ciwon zuciya saboda erin wahalar da suka sha wancan shekarar, sak abinda ake ma Fannah haka ake masa in ya shiga cikin jama'a shima, ga bin abu a zuciya haka sanda ya kamu da ciwom zuciyan. Yanzu haka gasu nan ne kawai d’an aikin kanikancin dayake d’an yin ma yadena banda ciwon zuciyan dayake damunsa ga hypertension da ciwon sugar sam da angansa za’a tausayawa masa gashi ba kud’in kaisa asibiti a masa aiki.

        Bakuma komai bane ya haifo masa da hypertension d’innan banda halin wansa Ya Khaleel, sam ya dage seya aura wa Fannah Farouq, abinda Baba bayaso kenan ita Fannan da za’a mata auren ma ta hak’ura ta rungumi k’addara yanzu tunda duk saurayin da ya soma zuwa wajenta tun gama makarantar ta se ‘yan unguwa sun korasa, daga yazo yau gobe bara a sake ganinsa ba.

     Farouq kuwa ba kalan walak’ancin da baya wa Fannah musamman ma dayaga yanzu Baba bayida lafiya ko magana be cika san yi ba. Fannah kuwa dama ba mutumiya ce me hayaniya ba haka zezo ya zageta yazagi Babanta ba abinda zata ce masa illa tayi kuka, maganan aurensu kuwa Ya Khaleel ya dage se shiri yakeyi.

        Yau ranar ta kasance Asabar, Mami, Afrah da Aiman sun je gidan suna a unguwar noma Fannah kuwa tana zaune a gida saboda bata san shiga cikin mutane gudun kar a fara nuna ta da yatsa ana kiranta da sunan data tsana wato kariya. Wanke wanke take tajiyo knocking bam bam bam a bakin k’ofa kafin ta wanke hannu tasa hijabi ta duba ko wayene already meshi ya shigo Farouq taga tsaye da alama ya bugu baya cikin hankalinsa.

          “Ya Farouq me kakeyi anan a buge? Dan Allah ka tafi gida” Cewar Fannah murya na rawa.

    Bece komai ba sanda ya iso inda take, atake ta soma b’ari incident daya faru da ita shekara d’aya daya wuce ya soma yawo a kanta shima wancan mutumin daya rabata da martabatan ta a buge ya zo mata, gashi ko hijabi batada. Baya baya take Farouq na matsowa kusa da ita sanda suka kai bango. Hawaye ke tsiyaya daga cikin idanunta “Ya Farouq dan Allah kayi hak’uri kabari.”

      “In bari ko in fara? Ai kinsha yi da samarukan ki se me dan nayi dake yau? After all ni zan aureki.”
      “Ya Farouq dan Allah kayi hak’uri kabari.” Hannu ya aza kan gashinta me uban yawa yana shafawa. “Baba dan Allah kazo ka taimakeni Ya Farouq dan Allah kabari.” Kuka take tana had’asa da Allah. Finciko gashinta yayi da k’arfi “kice kina sona!” Ya daka mata tsawa.

        “Ya Farouq dan Allah kayi hak’uri ka sake min gashi da zafi.”
      “Who cares? Tell me you love me!” Yayi demanding.
      Bakinta b’ari yake se hawaye take zubarwa. Gashin nata yakuma ja fiye da yadda yayi d’azu, k’ara ta sakar. “Nace tell me you love me and you'll marry me ko in miki kaca kaca anan anyways dama ni zan aureki.”

     Baba dake kwance a d’aki jikin sa yatashi sosai ko motsi dak’yar  yake yajiyo muryan Farouq. Ja da ciki yayi yafito zuwa bakin k’ofar ya d’aga labile. “Farouq... Dan Allah kayi hak’uri kabar ta.” Cewar Baba a wahalance.

     “Nak’i hak’urin Baba, seta ce tana sona kuma zata aureni wacce erin uselsess budurwa take ‘yan matan waje na ma suna cemin suna so na se ita wannan kariya me bin mazan.” Gashin nata ya sake ja “tell me you love me and you’ll marry me for the last time.”

      “Farouq yanzu magana nake maka baraka jini ba?”
      “Da Allah Baba ka rufa min baki da mata ta nake magana bada ubanta ba.”
 
     “Farouq ina sanka zan aureka dan Allah kayi hak’uri ka sake min gashi” Fannah ta fad’i tana kukan azaba.
       “Banji ba sake fad’a min.” Shiru tayi tana jan hanci se b’ari take ga shi yak’i sakar mata gashi. “Farouq dan Allah ka sake ta, mesa baka ji ne?”
       “Baba nace kamin shiru ko? Kai bakasan addini bane? Ana shiga tsakanin mata da miji ne?” Yadawo da kallonsa kan Fannah “nace tell me you love and you’ll marry me ko sena rage miki kayan jikin kine?”

     “A’a dan Allah karka min haka, kayi hak’uri.”
     “Ke kariya kike kome baraki fad’a min abinda nakesan ji bane?”
     “Ya Farouq ina sanka zan aureka, Ina sanka zan aureka dan Allah kayi hak’uri ka sake min gashi.” Murmushi yayi sannan ya sake ta tare da cusa ta jikinsa k’ok’arin k’watan kanta take amman takasa ga jikinsa duk warin giya. “Yawwa my beautiful Fannah I love you too, karki damu nan da ‘yan watanni za’a mana aure.” Kuka take sosai “Ya Farouq dan Allah ka sakeni.” Yasar da ita yayi a k’asa sannan ya juya yana tafiya nan da can ya fice.

     Kuka sosai Fannah keyi so helplessly shi kansa Baba kuka yakeyi bare iya barin Fannah ta auri Farouq ba there has to be a way. Farouq besan darajar Fannah ba be kamata ace an barsa ya aureta ba inbanda wahala ba abinda zata sha a gidansa. “Fannah mama na dan Allah kiyi hak’uri in shaa Allah baraki auri Farouq ba, kiyi hak’uri barin iya tashi in taimakeki ba.”
 
       Hannu tasa ta share hawayenta “karka damu dani Baba kabar kuka kar jikinka ya k’ara tsananta.” A sanyaye ta mik’e zuwa d’akinsu ta baje kan gado tana kuka kamar zata cire ranta.
 
**
      Da dare around k’arfe 8:30PM.
    “Abinda d’an mayen yazo yayi ma Fannah kenan Malam? Wallahi abun nasa yayi yawa gaskia k’ara zan kai wajen me gari.” Cewar Mami cikin tashin hankali. Bata tsaya jin me Baba ze fad’a ba ta fire zuwa d’akinsu Fannah a kwance ta sameta tana bacci a wahale numfashinta se sama sama yake dan yadda tasha kuka. Take idanunta suka cike da hawaye tayi kan ‘yarta tare da zura mata ido. “Fannah dan Allah kiyi hak’uri wallahi in shaa Allah baraki auri Farouq ba, zanyi duk abinda nasan zan iya in hana aukuwan wannan aure.”

     _“Bawan Allah dan Allah karka lalata min rayuwa kayi hak’uri ka rufa min asiri I'm just 15.”  “Nak’i baran hak’ura ba. Ita da ta tafi taji tausayin mu ne? se na k’wace abin yau yaso seki je ki fad’a mata, banga abinda ze hanani miki wannan abu ba yau.”  “Dan Allah kayi hak’uri. Wayyo Allah Mami na ze kasheni...!!”_

     Firgit! Fannah ta farka daga baccin da takeyi se nishi takeyi me nauyi, zuciyar ta na bugawa da k’arfin gakse jikinta duk yayi zufa se b’ari take. Mami na tab’a ta, ta k’urma wata erin ihu. Daga nan Mami tagane mafarkin incident na ranan tayi dama haka yake mata duk sanda tayi mafarkin seta tashi tana b’ari tana kuka da an tab’ata kuma seta tsala ihu. Yau k’imanin shekara kenan kusan kullum se Fannah tayi mafarkin daren da aka rabata da budurcinta martabarta.

      “Fannah Mami ce ba abinda zan miki, Mami ce” a hankali ta sake gwada tab’a Fannah wani ihun ta kuma b’urmawa. “Mami ce Fannah, Maminki” a hankali ta tab'a hannunta sekuma batayi ihun ba hugging nata Mami tayi a hankali tana shafa kanta.

      “Mami mutumin... Dan Allah kice karya dawo.”
    “Shhhh! Mafarki ne Habibti mutumin yatafi bare sake dawowa ba. Mafarki ne kinji? In kawo miki ruwa?” Kai Fannah ta giad’a a tsorace Mami na mik’ewa taja zaninta “Mami dan Allah karki tafi, ze dawo. Ki zauna dani dan Allah.” Zama Mami tayi Fannah ta rungumeta gamgam wane za’a k’wace mata ita tana hawaye.

© miemiebee

 TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 09
BY MIEMIEBEE


United Kingdom, London
ANAS


                 _shima bayan shekara d’aya..._
   

             Acikin babban Beach dake waje da London, Anas ne mik’e kan wata doguwar kujera da blue sunglasses a fuskarsa kwata kwata short nicker ne kad’ai ajikinsa seda headphone dake kansa wanda ya had’a da wayarsa yana nin cool music. Kallon sama yake yayi nisa cikin tunani.

       Bottled wata aka wulla masa a firgice ya mik’e ganin Musty ne yasa yayi murmushi wanda ya bayyano da fararen hak’waransa. “Kai! Abdoul where are you? Yau Anas yayi murmushi harda ciro hak’wara. Tell me why do you seem so happy?”

     Murmushin ya sake, “my dreams are coming true one-by-one.” cewar Anas.
      “Wani dream kenan Anas?” Musty ya tambaya.
     “Humm!” yakuma murmusawa ta gefen da dimple nasa yake. “Ni dreams d’ina guda uku ne kacal a duniyan nan.”
     Musty ya giara zama “ina jinka!”
     “Kaga na farko to be a billonaire not a millonaire but a billonaire. After that kaga in nayi kud’i I can toy with women hearts, saboda one thing I've learnt in life is ba abinda mata sukeso fiye da kud’i a duniya, zanyi amfani da wannan damar in saye zuk’atarsu dashi, akan kud’i they are ready to sacrifice everything I mean everything harta family'nsu, kaga ko in nayi kud’i nasan ba macen da zata k’i ni ko akoi?” Ya tsaya ya tambayi Musty.

     Musty dake jin dad’in wannan labari yace, “ai ko a yanzun ka ma ba macen da zata k’ika Anas you've got the looks and the blue eyes also.” Murmushi sukayi dukansu “ehemm. Ina jinka...”
 
      “Yess! As I was telling you, inason inyi wasa da zuqatan ‘yan mata a k’alla 100-200. So nake na karya musu zuqatansu ta yadda barasu sake san kawo na miji cikin rayuwarsu ba, so nake su d’and’ana how it feels to be left alone.”

     Kai Musty giad’a a hankali alaman yana gane abinda Anas ke nufi “so in ka karya masu zuqatan nasu what will you benefit from it?” Daidai lokacin Abdoul yazo ya zauna dawata American babe kan cinyarsa tasha bikini (pant and bra) “Hi Fauzy!” Tace da Anas sunan da ake kiransa dashi a can London kenan kasancewar su turawa sun saba da kiran mutum da family name nasa (ANAS IBRAHIM FAUZY)

          Ba tare da ya kalleta ba yace “hey.” Abdoul ya d’ibi k’asa me laushi dake beach d’in ya watsa wa Anas. “Budurwar tawa ma seka ja mata aji ne? Kaifa Anas daban kake I keep on telling you.”
      “Abdoul kaga magana muke da mazan nan kuma kallon wannan me farin gashin kusa dani amai yake sani so please ka koreta kokuma ku tafi tare.” Cewar Anas batare da ya nuna damuwa ba.
 
    “Allah...!” Abdoul ya fad’i cike da mamaki wai ace baturiya ma bata burge Anas ba to wace zata burge sa!? Dariya sosai Musty ya fashe da ba k’arya maganan Anas ya sasa dariya. Baturiyar ce ta tsargu danko ba jin yarensu take ba. “Hey Auwal (family name na Musty) whats funny why you laughing?”
    Dariyan yake har yanzu “ohh Emily its nothing don’t worry.” Bayanta Abdoul ya shafa “excuse us babe I'll be right back.” Kiss ta manna masa a cheek sannan ta tashi ta fice.

     Fuska Anas ya yamutsa a k’yamance yana mamakin Abdoul wai har baturiya yake bari tana masa kiss. “Seka sake fuskarka ai tunda na miji da na miji kaga suna kiss ba.” Cewar Abdoul a little bit pissed off. Murmushi kad’an Anas yayi “LOL mamaki kawai kuke bani, I can’t waste my time on girls. They aiint worth it”

         “Aini Anas da ban sanka ba senace gay ne kai.” Cewar Abdoul “anyways what are you two discussing about da kuka sa na kora Emily.”
       “Labari Anas ke bani” cewar Musty yana jin dad’i. “Ehem ina jinka continue.”

      Komawa yayi ya jinginu jikin kujerar sa yana kallon sama sannan ya cigaba “kace what will I benefit in nayi breaking hearts na mata?” Musty ya giad’a kai dukda ba kallonsa Anas yake ba. “I will benfit everything, zan ramawa Abuu abinda Ummimi ta masa, dukda ba direct kan Ummimin zan d’au revenge d’inba atleast ‘yan uwan ta mata zasuji jiki tunda ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ce.”

     Cikin rashin fahimta Abdoul yace, “wait wait nade san waye Abuu mahaifinka ba? what of Ummimi? Wace ita? As far as am concerned Ummie nasani mamanka har kana bamu waya muna gaisawa.”

     Numfashi Anas yaja “well apart from my family you guys are the first people da zan bawa wannan labari so listen closely after na baku labarin seku fad’a min ko inada laifi in nace mata are evil creatures da be kamata a tausaya masu ba.”

      _[Abuu kamar yadda kuka sani mahaifi na ne kanurin Bama ne dake jihar Borno. Ummimi kuwa mahaifiya tace unfortunately, asalin shuwa arab ce daga Maiduguri. Mu uku ne gun iyayenmu nine babba I'm 19 years old, followed by my brother Shettima shikuma he is 17½(sha bakwai da rabi) yanzu. Shekara 1½ (d’aya da rabi) ne tsakanin mu sekuma little sister’nmu my angel Amal she's just 9 years old.]_

     _[Base on yadda Abuu yabani labari auren soyayya shida Ummimi sukayi. As you guys know scholarship nasamu nazo nan school d’in not like you guys da iyayenku suke biya muku da kansu. Abuu bashida wani arzikin azo agani, yanada arziki ne dadai na rufin asiri a yanzu haka in za’a kira masu arzikin garinmu Bama nasan definately za’a sa Abuu amman dekam bade da kafin sui aure da Ummimi ba. Shi da kansa yake bamu labarin irin rayuwar talaucin da sukayi shida Ummimi kafin a haifemu harkuma da aka haifemu so dayawa ana tashi a gidanmu ba’a sanin me za’a ci.]_

    “You guys must be wondering ya akayi Ummimi shuwa arab da uban san kud’insu ta auri talaka kamar Abuu na ko?” Ya juya ya kalli abokansa. Kai suka giad’a a tare murmushi ya saki kad’an “well you don’t have to.”

    _[Alokacin da Abuu yaje Maiduguri yin diploma ne ya had’u da Ummimi tana sayar da abinci a school nasu a lokacin iyayenta sun kasance talaka sosai amman kunsan shuwa arabs koda su talaka ne se masu kud’i sukeso unlike Ummimi back then, dukda tasan Abuu baida kud’i makaranta yake hakan be hanata falling masa ba kamar yadda shima ya juma da falling mata dan kyan ta dakuma hali, sosai Ummimi kyakkyawa ce kap mu yaranta kamanninta muka dauka sede nafi kama da ita fiye da Shettima da Amal wanda har yau in na tuna da haka se inji kamar inje inyi plastic surgery in canza kamanni na sam banasan abinda ze sa ina tunawa da ita but anytime I look at myself in the mirror ita kawai nake gani...]_

    Musty da Abdoul da suke duhu sukace “ban gane ba” a tare. “Mesa ka tsani mahaifiyarka haka Anas?” Cewar Musty.  “Shin yanzu bata gidanku ne?” Abdoul ya tambaya.

         “Zakaji reason dayasa na tsaneta Musty, bata gidanmu Abdoul Allah kad’ai yasan ko tana nan aduniya ko  lahira.”
     “Babbar magana!” cewar Abdoul “kanada picture’nta inasan ganin ta.” Hannu Anas ya mik’a ya d’aga wallet nasa daga kan wata ‘yar table ya bud’o sannan ya ciro wata hoto “wannan family picture’nmu ne Abuu, Ummimi se nida Shettima time d’in ba m’a haifi Angel ba. Sede bara ku gane fuakarta sosai ba saboda na dirje da biro.” Nan ya mik’a wa Abdoul sosai kam ya dirje fuskar Ummimi a hoton se ansa ido sosai za’a d’an ga kutsirin fuskarta amman ko a hakan ma za’a gano kamanninta da yaranta musamman ma da Anas kamar yadda ya fad’i bayan Abdoul yagama gani ya mik’a wa Musty, shima daya gani yayi returning wa Anas, amsa yayi tare da mayar wa cikin wallet nasa sannan ya cigaba;

   
_[Sun yi shekaru biyu suna soyayya batare da sanin iyayensu ba lokacin da Abuu yagama polythecnic ne ya sanarda da iyayensa kan yasamu mata kuma yanasan ya aura dukda cewar ba aiki yake dashi ba. Kowa murna ya tayasa seda akaji batun Shuwa Arab ze aura ne hankalin kowa ya tashi gudun heartbreak da suke masa dan sunsan for sure in iyayen Ummimi sukayi learning truth about status na Abuu barasu yarda suba d’ansu wa talaka ba sunfi san wanda ze kawo masu gwala gwale yakai su Hajji da umara.]_

       _[As expected da Ummimi tayi introducing Abuu wa iyayenta sam sukace ‘yarsu barta auri talaka ba suka masa kaca-kaca sannan suka koresa. Amman dan erin soyayyan da Ummimi kema Abuu yasa ta bijirewa iyayenta tace ita sam inba Abuu ba zata kashe kanta kuma she was serious duk suka tsorata ba yadda suka iya dolensu suka yarda mata saboda ita kad’ai ce ‘ya a garesu. A munafirce mahaifinta ya tura ‘yan uwansa suka tsare Abuu a hanya suka masa tsinannen dukar mutuwa basu barsa ba sanda suka ga baya numfashi jinyan wata d’aya Abuu yayi kafin ya samu sauk’i alokacin Ummimi ta tada borin inba a aura mata Abuu ba zata fad’a rijiya dole aka musu aure iyayenta wane bak’in ciki ya kashe su]_

     _[Bama ta biyo Abuu aka basu BQ a family house nasu Abuu. Aiki Abuu yashiga nema dan earning living and to make his beautiful wife happy but  kunsan yadda k’asarmu take sam be samu aiki ba haka ya soma noma, safe, rana, yamma, dare. Duk sanda yayi harvesting shuk’ansa once in a year yakan kai maiduguri ya siyar a wannan lokacin ne yake samun kud’i ya ma Ummimi siyayya and duk abinda ya kawo mata tana appreciating. Bayan shekara d’aya da aurensu aka haifeni Abuu yace ni ko ragon suna ba’a min ba sanda nayi wata uku tukuna. Sam basu ji dad’in haifan Shettima da akayi bayan shekara d’aya da rabi da haifa na ba dukda cewar kowani d’a da arzikinsa amman talaucin nasu yayi over. So dayawa ana wayen gari ba’a san me zamuci ba. Mahaifin Abuu ke turo mana abincin dazamu ciki.]_

      _[Daga bayan Shettima kuwa Ummimi bata sake samun ciki ba. Shekarana goma a duniya lokacin Ummimi tasoma staying late at night seta fita tun safe bata dawowa se dare abin ba k’aramin damun Abuu yake ba. Da ya d’anyi bincike kuwa se aka gano wani Alhaji ne daga Yola take had’uwa dashi. Attajiri ne sosai yanada kud’i Abuu yace kullum cikin canza mota yake. Yana ganin Ummimi kuwa ta masa kyau ya fara nemanta ita kuma  saboda cin amana tak’i fad’a masa tanada aure. Soyayya sosai suka fara sam Ummimi tadena kula damu kullum cikin dukan mu take kamar ba yaran cikin data haifa ba.]_

     _[Koba abin duka ba seta bugemu musamman ma a weekends lokacin da wannan Alhajin nata ya koma Yola ba me bata kud’i. Ranar lahadi da sassafe baran tab’a mantawa da wannan rana ba. Da misalin k’arfe 8:00AM Ummimi ta tashi se had’a akwati take sam nida Shettima bamu damu ba acewarmu ko tafiya zamui duka sede naga kayakinta kad’ai take ta had’awa dana tambayeta in zataje kuwa ba kunya ba tsoron Allah ba tausayi ta kalli cikin idanuna tace min *talaucin mahaifinku ya isheni tattara kayakina nake saurayi na zezo ya d’auke ni in tafi inbar nan* atake kaina naji ya soma juyawa wace erin magana Ummimi take dama mata masu aure sunayin saurayi ne? Danni ban tab’a jin malamin islamiyan mu ya fad’a mana ba. Sema na d’au wasa take na shareta mukaje muna ta wasa nida Shettima. Abuu na zaune a Parlour ya tambayeni. Anas Baba na ina mamarku? Ko yau d’inma ta fita ne? A’a Abuu tana d’aki tana shirya kayakinta tace min wai saurayinta ze zo ya d’auketa. Take Abuu ya mik’e what!? Niko na sake nanata masa. Bada dad’ewa ba sega Ummimi tafito tana jan akwatinta.]_

       _[Aysha ina zakije haka?_
     _Aww d’an naka bai fad’a maka bane? Tafiya zan saurayi na na jira na._
    Haba! Aysha wace erin magana kike? Wani erin saurayi kuma? Cewar Abuu]
     _[Ai kasan sa Alhajin Yola, shi nake nufi, rayuwar talaucin nan ya isheni ni tafiya zan inje inji dad’in rayuwa na nima.” For the first time naga idan Abuu yacike da hawaye kafin in hankara naga yana kuka take nima na fara same goes to my brother. Rok’arta na soma haka Shettima ma banda Abuu dayayi mutuwan tsaye.]_

     “Huhhh!!! Nagaji I'll continue some other day.”
     “Haba! mana maza da Allah k’arasa mana.” Cewar Musty.

    “Nace maku I'll continue tomorrow or later I promise, baki na yagaji da surutu kunfi kowa sanin ban cika magana ba ai nayi k’ok’ari ko?”

    “Sosai kayi Anas namu me blue shining eyes. Yi hak’uri ka gama mana amma” Abdoul ya fad’i yana masa zak’in bak’i.

    “Okay toh siyo min soda sena cigaba ishi nake ji.” Ba musu Abdoul ya tashi ya siyo masa ya dawo da sauri. “Gashi toh cigaba muna jinka please.” Bayan ya bud’e sodan ya kwankwad’e tas sannan ya cigaba kamar haka;

©miemiebee

 TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 10
BY MIEMIEBEE         “Last words da mukayi exchanging da ita are forever stuck up in my head.”

_[“Ummimi dan Allah karki tafi kiyi hak’uri indan plates dana fasa ne I promise baran sake ba. Ummimi I am sorry dan Allah karki tafi. Abuu ka hana Ummimi tafiya dan Allah kace mata I will be a good boy from now on.”]_  “Haka nata had’ata da Allah ko saurarena batayi ba”

       _[“Yanzu Aysha bara kiji tausayin yaranki ki hak’ura ki zauna dasu ba? Kalli yadda suke kuka fa?”]_ cewar Abuu

    _[“Mstww wannan kuma ku ya shafa nagaji da zama cikin talaucin nan, ace kullum se atashi ba’a san me za’a karya dashi ba gaskia nagaji daman tun farko sanda Abba na yace kar in aureka matsiyaci ne kai amman nak’i sauraronsa. Ga can miji Allah yamin har k’asar waje ze kaini saboda haka ban ga abinda zesa in cigaba da zama a wannan gidan ba.” Jakarta ta ja ta soma tafiya da sauri naje na kama k’afarta ina kuka ina rok’arta. “Ummimi please don’t leave us we love you dan Allah karki tafi, Abuu will find a better job dan Allah karki tafi...” wani wawan ball tayi dani da k’afa nafad’i na ji ciwo a elbow na har d’inki sanda aka min wajen...”]_
 
        “Kun ga ci won?” Ya mik’o hannunsa ya nuna masu Musty. Ciwo ne babba sosai ace yau shekaru kusan goma amman hakan besa ciwon ya rage girma ba. Komawa yayi yasake kishingid’a.

   _[ko waiwayo wa ta dubani batayi ba jakarta taja ta fice, asibiti Abuu yayi rushing d’ina. Tun daga ranan Abuu ya rasa walwala, Abuu da mukasani da fara’a da murmushi ya koma wani abu daban. Kullum cikin tunani, nida Shettima tun tafiyar Ummimi muka rasa gatanmu, kakarmu bata raye bale ace ita zata kula damu, abinci ma waninsa’in mancewa ake damu haka zamu kwana da yunwa Ummie sister’n Abuu ce data dawo daga Maiduguri tayi alk’awarin zama damu. A lokacin ina primary 5 zamuyi common entrance, ikon Allah ne kawai yasa nayi passing exams d’in saboda tafiyan Ummimi yayi affecting d’ina psychologically, mentally and socially.]_

     _Tun daga lokacin na canza, na dena dariya, nadena wasa koda da Shettima ne kullum cikin tunani nake har wani psysho psycho na soma zama. Ganin haka Kaka yabawa Baba shawara akaini Maiduguri Boarding school a tunaninsa in ina cikin yara zan sake, unfortunately koda aka kaini can abun nawa be ragu ba sede worse da yayi ma, bana cin abinci bana magana da kowa karatu na kawai nakeyi saboda blue eyes d’ina yasa yara dayawa suna san zama friends dani ace warsu ma ni bature ne sam bana basu chance guda biyu ne sukaci galaba a kaina Baana da Kashim, su biyu kawai suka samu na sake dasu muka zama friends.]_
 
    _[A lokacin da mukayi second term hutu bayan na dawo gida na tarar da Ummie da jaririya kuma a iya sani na Ummie bata da aure. Tambayarta nayi ko ‘yar wace me kama dani haka amsar data bani ne ya mugun sake tada min hankali.]_
      _[“k’anwarka ce Anas, uwar ku d’aya uban ku d’aya. Shekranjiya Ummimi tasa wani almajiri ya turo ta cikin wata basket da wasik’a.” Zafaffun hawaye ne suka soma gangarowa kan kumatu na. “Mesa Ummimi zatayi haka Ummie? Mesa barata tausayawa wa baby’n nan ba? Me tamata itakuma da zata rabata da d’umin jikinta? Mesa Ummimi ta tsane mu haka Ummie?”]

    _[“Anas nima bansani ba hak’uri zakayi, I'm here for you guys, bar kuka Baba na.” “Ina wasik’ar Ummie?”_  Na tambayeta. Acikin wata drawer ta d’auko ta mik’a min na karanta kamar haka...]_

   [_ Ibrahim ‘yar da ke cikin wannan basket, ‘yarka ce da cikinta nabar gidanka. Allah ya taimakeni nasamu na haifeta ga abinka nan na kawo maka, banasan abinda ze sake had’ani da kai ko da ‘ya‘yanka..._]

         [Hawaye ne suka soma sauk’owa kan kumatu na hannu na mik’a na amshi sister na da ko suna Abuu be sa mata ba dan tashin hankali. Hawayen idanuna na d’iga kan fuakarta ta bud’e idanunta a hankali tana kallo na se kamar Ummimi nake gani, Amal na kirata dashi ina hawaye. Daidai lokacin Abuu yashigo. “Amal kasa mata Anas?” Alokacin ban fahimce abinda yake nufi ba sanda na tambayesa yake fad’a mun yak’i sa mata suna ne saboda ni yake jira nayi naming nata tunda nace mata Amal sunan ta Amal kenan. Tun daga ranan na d’au alk’awari zanyi protecting Amal da raina, zan zame mata uwa.]_

        _[Ban tab’a jin inason d’an Adam kamar Amal ba, simply because of tausayin da take bani har yau bata san tanada wata mahaifiya bayan Ummie ba, rok’ar Abuu nayi kar a fad’a mata gaskia banasan rayuwarta ta tab’arb’are kamar yadda nawa yayi. Komai ni nake wa Amal har noma nafarayi tun ina d’an yaro in nayi harvesting se in siya wa Amal kaya da kauan abinci as Abuu har a lokacin be samu aiki ba. Tun tana k’arama take sona ko kuka takeyi ina amsarta zatayi shiru kwana ma tare mukeyi da ita, ko yawo zanje da ita nake zuwa. Sam banso komawa makaranta ba da hutun mu yak’are gudun kar nayi missing nata. Ba yadda na iya haka na koma amman kullum da tunaninta nake kwana in tashi.]_

_[Ina jss 3 aka sa Shettima a school namu, jiki na jasa sosai ko kad’an bana barin school bullies su tab’a sa. Abokai na abokansa ne. Alokacin Abuu ya samu aiki rayuwar mu yasoma canzawa a hankali ya gina mana gida Amal kuwa se girma takeyi a lokacin tana da shekaru biyu da abu akai. Amal completes me, kullum tare muke da ita duk sanda nazo komawa school setayi kuka tace seta bini. Har dan haka nad’au alk’awarin barin sake dawowa gida ba se nagama school d’in gabad’aya bana san ganin kukan Amal. 3 years later nagama secondary school I was 16 years then Shettima kuwa yana ss1 time d’in. I can’t believe Amal dana ganta she was 5 years then, ta girma sosai in na ganta kaina kawai nake tunawa da muguwar Ummimi.]_

     “Tun daga lokacin na cigaba da kula da sister na har ila yau. Ummimi kuwa bamu sake jin labarinta ba tunda ta bar gidanmu yau about 10 years kenan.” Numfashi ya saki tare da tasowa daga kan kujerar ya mik’e tare dayin mik’a “kunji labarina you guys are the first to know. Kunji dalilin dayasa na rasa happiness d’ina, dalilin dayasa na tsani Ummimi da kowace mace banda mata guda ukun nan; Amal, Ummie seda yarinyar danayi blaming nata akan laifin Ummimi har nayi raping nata wanda har yau ban san ya take ba, bansan kona kasheta ba bansan irin ciwon dana ji mata ba. I can’t ever forgive myself for what I did to her har se ranan dana ganta na nemi gafararta ta yafemin. She was just 15”

             “Anas stop blaming yourself, ba’a cikin hankalinka kayi mata abinda ka mata ba in shaa Allah bata mutu ba someday in the future zaku had’u kuma zata yafe maka inhar ka bata labarin ka. Gaskia Anas kasha gwagwarmaya a rayuwarka, kayi witnessing bak’in cikin rayuwa at a very tender age. Ummininku sam bata kyauta muku ba.” Cewar Abdoul cike da tausayawa wa Anas ashe saisa kullum yake cikin tunani baya dariya, he has been through so much ba laifinsa bane because of how he is now.

          “Anas if only zan iya taimaka maka da nayi, you've had such a horrible past just know that when ever you need a shoulder to cry on we are here for you.” Musty yayi assuring  nasa.
 
     Kallonsu Anas yayi tare da ciri sunglasses nasa rana ya haska blue eyes nasa da skin nasa yayi kyau sosai. Murmushi ya saki kad’an wanda ya bayyano da fararen hak’waransa “thank you guys, so now what? Kun ga laifi na saboda nace na tsani mata barin yi aure ba?”

     Kai duk suka kad’a “wallahi ko k’adan Anas you have every single right ka tsani mata fiye da komai sede inda zaka yayyafa wa zuciyarka ruwan sanyi you can find love in your own way I'm sure Allah ze sak’a maku abinda Ummimi ta muku by kawo maku matan da zasu kula daku su soku tsakani da Allah badan kyanku ko kud’inku ba but tsakani da Allah and barasu tab’a barinku ba kai da wanka Shettima se mutuwa.” Cewar Musty. “Sosai dude Musty is absolutely right.” Abdoul ya mara wa Musty baya.

         “Ofcourse you guys are right, but niko kad’an I don’t have faith in love to talk more of marriage, I wish to finish my life single ba senayi aure ba. Dama ai ana aure ne dan a haifafa I have Amal, she is like a daughter to me.” Musty ze sake magana Anas ya katsesa by changing topic of discussion d’in. “Yau da kuka sani na tono past d’ina dole se na sha 2 bottle na syrup d’incan if not barin iya bacci ba and also I
Share:

3 comments:

  1. Da kyau Allah kara basira

    ReplyDelete
  2. Allah kara basira bro

    ReplyDelete
  3. Ubangiji Allah ya kara barira da hazaka

    ReplyDelete

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).