shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday 12 February 2022

GAREKI AMARYA - SIFFOFIN UWA TAGARI 14

GAREKI AMARYA - SIFFOFIN UWA TAGARI 14

Ki zama mai godiya ga Allah daya kawoki lokacin aurenki domin byyaiwa ce yayi miki wasu suna nan basu samu ba. 

Karki sabawa Allah a wajen sha'anin biki, abinda ya kyautu Shine kiyi godiya gareshi. 

Kiyi taka tsantsan da shawarar qawaye, kar su baki shawarar da za su burmaki domin da yawa akwai makiya wanda basu samu wannan ni'imar da kika samu ba.

Share:

Sunday 6 December 2020

Yadda Zaki Mallake Zuciyar Mijinki Ko Saurayin Ki Cikin Sauki!

Yadda Zaki Mallake Zuciyar Mijinki Ko Saurayin Ki Cikin Sauki!

Assalamu Alaikum barkanmu da warhaka barkanmu da sake saduwa daku a cikin sabon shirin namu wadda yake zuwa muku kai tsaye daga shafin “Abbagana Novels”, Kuna tare da jikan Marubuta Muhammad Abba Gana. Kuma insha Alllahu yau zamuyi jawabine akan yadda zaki mallake zuciyar mijinki cikin sauki.

Share:

Wednesday 20 February 2019

SHAWARWARI GUDA 7 DON INGANTA TARBIYYAR YARA - SIFFOFIN UWA TAGARI 12

SHAWARWARI GUDA 7 DON INGANTA TARBIYYAR YARA - SIFFOFIN UWA TAGARI 12

Tarbiya wata kalma ce da take nuni ga yadda ake kula da ‘ya’yanmu da kuma na kasa da mu. Hakika, girma da muhimmancin kalmar 'tarbiyya' sun wuce yadda muke anfani da ita a yau da kullun. Tarbiya ta banbanta da daga al’umma zuwa al’umma, ma'ana, abinda ke da kyau ga wasu mutanen ba lalai bane ya zama yana da kyau ga wasu. Amma a gani nan a kwai wasu abubuwa da za su da ce da kowa, kuma sune na kawo a nan zan yi dan sharhi a kansu, musamman hanyoyin da za’a bi don inganta tarbiya yara.

Share:

SHIN KO KUN SAN LADAN DA MACE KE SAMU A GIDAN MIJINTA? - SIFFOFIN UWA TAGARI 11

SHIN KO KUN SAN LADAN DA MACE KE SAMU A GIDAN MIJINTA? - SIFFOFIN UWA TAGARI 11

Albishirinku matan aure. Zaman gidan miji da kuke yi da yi wa mazajenku hidima, Allah ya tanada muku lada mai yawa. Ga kadan daga cikin irin garabasa dake tattare da aure ga mata.
*Daga lokacin da kikayi aure idan ki ka yi sallah, Allah zai baki lada dubu
*Idan kika kalli fuskar mijinki kika yi farinciki Allah zai baki ladan zikiri dubu
*Idan kika bashi ruwa ya sha Allah zai baki ladan azumin shekara daya
*Idan kika dafa masa abinci mai dadi duk girki daya Allah zai baki ladan hajji da umrah.
*Idan kin samu ciki kullum za'a rubuta miki ladan azumi shi kuma mijin a rubuta masa ladan kiyamul laili, har ki haihu
Share:

Friday 25 January 2019

SHAWARWARI 52 ZUWA GA MATAN AURE, ZAWARAWA DA 'YAN MATA - SIFFOFIN UWA TAGARI 10

SHAWARWARI 52 ZUWA GA MATAN AURE, ZAWARAWA DA 'YAN MATA - SIFFOFIN UWA TAGARI 10

Shakka babu, a wannan zamani 'yan mata da zawarawa kai harma da matan aure suna cikin zullumi da tsoro da rashin kwanciyar hankali, saboda yadda auren su yake yawan mutuwa, bayan kuma, an dauki dogon lokaci ana soyayya a tsakani, kafin a yi auren. Ga wasu shawarwari 40 wadanda idan matan suka yi la'akari da amfani da su da yardar ALLAH za'a samu kyautatuwar zaman aure.

Share:

NASIHA ZUWA GA MATAN AURE - SIFFOFIN UWA TAGARI 9

NASIHA ZUWA GA MATAN AURE - SIFFOFIN UWA TAGARI 9


NASIHA ZUWA GA MATAN AURE
Ki kasance mai yi wa Allah biyayya a bayyane da boye, shi zai hana miki cutar da wadanda kike tare da su, mutane ne ko dabbobi, ki sanya wadannan sunaye hudu na Allah a tare dake koda yaushe, su ne kamar haka: “Assamii’u – Albasiiru – Al’aliimu – Alqadiiru”. Idan ki ka sa wadannan sunaye a gaba gare ki, to zaki rabauta a duniya da lahira, domin zaki bauta ma Allah kamar kina ganinsa.
Share:

SAKO ZUWA GAREKU MATAN AURE - SIFFOFIN UWA TAGARI 8

SAKO ZUWA GAREKU MATAN AURE - SIFFOFIN UWA TAGARI 8

Aure dai sunna ne na manzon Allah S.A.W, don haka a kowace sunna akwai lada matukar dai an yi ta kamar yadda manzon Allah S.A.W ya koyar. Don haka shi ma aure yana da nashi ladan idan aka yi shi kamar yadda Manzon Allah S.A.W ya koyar. Manzon Allah S.A.W ya yi bayanin irin ladan da ya kamata mace ta samu wajen biyayyan ta ga mijinta. Duk matar da take kyautata ma mijinta, tana faranta masa rai, tana kwantar masa da hankali, tana taya shi farin ciki a lokacin farin ciki, ta kuma taya shi bakin ciki a lokacin bakin ciki. To babu shakka itama xata ga farin ciki a duniya da lahira, Allah ya sa mu dace, amin.
Share:

Sunday 11 March 2018

SIFFOFIN UWA TAGARI 7

SIFFOFIN UWA TAGARI 7

KYAUTATA ZAMANTAKEWAR AURE BA TARE DA ZUWA WAJEN BOKA KO DAN DUBA BA.

Ki sani ya `yar uwata, akwai hanyoyi da dama da mace za ta bi, domin ta kyautata zamantakewarta ba tare da zuwa wajen boka ko dan duba ba. Ki sani yake `yar uwa, idan ki ka gyara zamantakewarki zaki samu rabon duniya da na lahira, shi ko boka ba shi da abin da zai qare ki da shi a gurin Allah, shin me ya sa ba za ki tsaya ki lura da kyau ba, ki san cewa boka babu abin da yake yi face ya yi sanadin da zai rarrabe kawunan mutane, babu abin da yake yi face ya shiga tsakanin mata da miji, boka babu abin da yake yi face ya raba ki da dukiyarki idan kin yi ganganci har da Imaninki, ya sa ki sami zunubi mai girma, shin, me ya sa ba zaki tsaya a tafarkin Allah ba, ki yi rayuwar aure mai kyau, wanda muka koya daga koyarwar Annabinmu Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) da sahabbansa, da muminai baki daya. Domin hadisin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana cewa: “Lalle Allah madaukakin sarki yana cewa ranar alqiyama, ina masu soyayya don neman yardata, a yau zan sanya su cikin inuwata, ranar da babu wata inuwa sai inuwata”. Shin `yar uwa ba za ki tsaya a tafarkin Allah ku yi soyayya don Allah ba? Kin je wurin boka idan da gangan ne, kin zama kafira, kin zama mushrika, kin zama `yar wuta, subhanallahi. Haqiqa `yar`uwa idan ki ka tsaya ki ka lura da kyau, zaki gane cewa boka da dan duba ba su amfana ma kowa da wani abu, face su raba mutane da dukiyarsu da imaninsu ga wanda ya yi ganganci, domin hadisin manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana cewa: “Duk wanda ya je gurin boka da dan duba ya gasgata abin da yake fada, haqiqa ya kafirce wa abin da Manzo ya zo da shi”. Boka ba ya iya cecen mutum a lahira, ba zai iya cecen ki ba, Idan ya ga za a sanya ki a wuta, ba shi da wani amfani a duniya da lahira, boka ya zama shahararren me hada fitina da husuma a tsakanin mutane, domin Alqur’ani mai girma yana fada mana cewa; “…shaidanu su ne kafirai, suna karantar da mutane sihiri… kuma ba su sanar da kowa ba, face su ce lalle mu fitina ne a gare ku, kada ku kafirta, suna neman ilimin abin da ke rarrabe tsakanin miji da matarsa…”. Saboda haka wannan ya sa mai sihiri ba shi da wani rabo a lahira alhali yana sane, kuma tir da abin da suka sayar da rayukansu da shi, alhali suna sane. Shaidan shi ne dukkan wanda ya san gaskiya kuma ya qi yin aiki da ita, mutum ne ko aljan. Haqiqa `yar uwa ki lura, ki fahimci abubuwan da za lissafa, zaki samu ki gyara zamantakewarki ba tare da zuwa wajen boka ko dan duba ba, domin ba zasu amfane ki da wani abu a wurin Allah ba.

Abu na farko, shi ne girmama mai gida, haqiqa girmama mai gida yana da matuqar muhimmanci, ki yarda cewa mai gida yana da wani matsayin da zai sa ki abu, ki yi, kuma zaki girmama shi, ki dinga ba shi matsayi da girma a matsayin mijinki, amma yanzu wasu matan ba su gane ba, sun dauka cewa idan suka je wurin boka ya mallake masu mai gidan, ya zama na sai dai ta ba shi umarni, ya bi, shi ne matar, ba mijin ba, ya zama kamar yaronta, wai tana ganin kamar ta birge, ita ce wadda ta yi sa’a, to wallahi ba haka ba ne, Abu na biyu shi ne mace ta kasance mai lura da tarbiyyar `ya`ya lura da tarbiyyan yara, ya kan sa namiji ya qara son mace domin tana kula mashi da `ya`ya, yadda ya kamata, koda ba ita ta haife su ba, da sun wuce a dinga shi mata albarka, ana cewa kalli yarannan yadda aka yi tarbiyyarsu, kuma abin mamaki ba `ya`yan ta ba ne, riqo ta yi, amma ta ba su kulawa mai kyau, ki zama kowa na miki addu’a sabo da wannan, inko `ya`yanki ne, su zama abin kwatance a cikin al’umma, a dinga cewa kalli `ya`yannan ba ruwansu da shaye – shayen banza, da duk dabi’un banza, duk dabi’u na banza basa yi. Amma wannan ya gagara, kun kasa ganewa ku mata, haqiqa na miji ba ya so a ce `ya`yansa sun zama na banza koda shi din na banza ne, ya fi so a ce ga `ya`yansa sun samu tarbiyya mai kyau, iyaye mata da dama su suke koya ma `ya`yansu dabi’u na banza, misali sai ku ga ana fada da mahaifiya a cikin gida, sai ta je ta dauko `ya`yanta, wai su rama mata, ba za ta nuna wa `ya`yan cewa su ma mutanen gidan na da girma da daraja ba, koda an taba ta, sai ta yi haquri ta nuna wa `yarta, ta saba da haquri, amma a’a, ko da `yarta aka taba, sai ta yi ta masifa wai ita an taba mata yarinya, sai ku ga yara sun taso ba abin da suke yi sai rashin kunya, su taso cikin rashin kunya, su taso ciki rashin tarbiyya, su taso a wulaqance, babu mai cewa su bari, abin haushi abin takaici wai sai ku ga iyaye an taso sun zo gurin malamin Islamiyya, sun zo tambayan dalilin da ya doki yaro, kuma zaku ga yawancin masu yin haka iyaye mata ne, idan malami ya yi Magana su ce su sun san zafin haihuwa, shin wane irin wulaqanci ne wannan? Kuma idan kuka bibiya zaku ga yaran ne keda laifi, domin wasu yaran yadda suka taso cikin rashin kunya idan sun je makarnata haka suke yi, kuma iyaye sun fi yin haka a makarantun Islamiyya, basa zuwa makarantun boko idan an taba `ya`yansu, in banda rashin tunani, ta yaya wanda ya karantar da danki yadda zai bauta ma Allah, amma shi ne idan ya daki danki ko `yarki zaki sanyo hijabi ki taho wai kin zo ganin malamin da ya taba maki yaro, Wal’iyazu billah
Share:

Thursday 25 January 2018

SIFFOFIN UWA TAGARI 6


TAKA CECIYAR NASIHA

==> karki nemo kowa wurin warware matsala tsakaninki da mijinki, ku warware ku biyu ba tare da wadansu sunji ba, koda iyayen ku ne.

==> Karki sashi abinda bai da ikon yinsa.

==>Karki zauna a gidansa da kazanta.

==> Karki manta da bukatun mijinki.

==> Karki zagesa don yana da wani matsala.

==> Karki bari wani ko wata su shigo masa gida batare da izininsa ba.

==> Karkiyi masa gori akan taimakonsa da kike yi.

==>Karki ki yafe masa akan laifin da yayi miki.

==> Karki dauka fansa akan abinda yayi miki kice sai kin rama.

==> Karki tona masa asiri a wurin yan’uwansa da koma waye.

==> Karki ringa kawar dashi akan bin Allah da Mazonsa (S.A.W).

==> Karki dauki iyayensa a matsayin iyayen miji ki daukesu a matsayin kema iyayenki ne.

==> Karki dauki ‘yan uwansa a matsayin yan’uwan miji ki daukesu a matsayin kema yan’uwanki ne.


Da fatana Allah (S.W.T) ya bada zaman lafiya tsakaninku da mazajenku Ameen.
Share:

Monday 27 November 2017

SIFFOFIN UWA TAGARI 5


LALLE

Yar’uwata ki sani lalle kwalliyace ga duk ya mace kuma mace idan ta bar hannunta ko kafarta ba lalle to ba’a iya banbance ta da namiji. Kuma kowace irin kalan lalle da mata sukeyi kema kiyi da zaran ya goge sai ki biyoshi da wani kala domin cika siffarki ta ya mace.

BANGAREN ADO

Yar uwa ki sani kirkire kirkiren adon zamani wajibine akanki a gidan mijinki harma da irin naki salon adon, kuma duk wata dressing da mata sukeyi a duniya dolene ki rinka yiwa mijinki matukar bai sabawa addinin musulunci ba, sannan kiyi masa ado da duk irin kayan da kika mallaka.

KISISINA DA KARERAYA

Ya yar’uwata mace bata cika mace ba idan bata iya kisisina irin ta mata ba, kamar su kareraya, yanga da rigima. Kuma ki sani irin wadannan dabi’un su suke daukaka martabar mace a wurin mijinta acikin dukkan alamuran su, Magana ko tafiya ko kallo da makamantansu.

DAMUWA DA DAMUWARSA

Yar uwa wajibine ki karanci halin mijinki sosai kisan mijinki acikin halin farin ciki da kuma bakin ciki kuma ki lura da yanayin sa a lokuta kamar haka:
Ø     Lokacin fita nema
Ø     Lokacin dawowa daga nema
Ø     Lokacin gajiya
Ø     Lokacin farin ciki
Ø     Lokacin bakin ciki

Ø     LOKACIN FITA NEMA: A wannan lokaci yar’uwata ki sani dolene ki tabbata mijinki ya fita daga gida cikin kwanciyan hankali da natsuwa. Akwai wani dabi’a da matan magabata sukeyiwa mazajensu, su kan shirya bayan sunyi wanka da kwalliya sannan sai su raka mazan su har kofar gida ko kofar daki, sannan suna tafiya suna taku daddaya da rangwadi kuma su kan yimusu addu’a sannan su basu wasiyan cewa idan Allah yasa ka samu halal ka kawo mana, idan kuwa baka samu ba zamuyi hakuri da azabar yunwa akan azabar Allah. Bayan ya fita yayi nisa sai ki kirashi da wani sunan soyayya mai dadi sai kiyi masa Kiss da hannunki. Sai kice masa Allah ya bada sa’a. Allah ya sa mudace Ameen.

Ø     LOKACIN DAWOWA DAGA NEMA: Ki sani yar’uwata miji yana dawowa gida a halin gajiya kafin ya dawo kin shirya ma dawowarsa.

Ø     LOKACIN GAJIYA: A wanna lokaci ki sani zaki nemi ruwa mai dumi a lokacin sanyi idan kuma lokacin zafine, sai kinemo ruwan sanyi ki kai masa wurin wanka bayan ya gama wankan ya dawo daki ki bashi abinci

Ø     LOKACIN FARIN CIKI: Yar’uwata a wannan lokacine zaki baje kolin shagwabar ki da rungumarsa

Ø     LOKACIN BAKINCIKI: Yar’uwata a wannan hali babu wasa babu tsokana a tsakaninku har sai kinji mai ya bata masa rai, idan ya fita bai samo bane sai ki kwantar masa da hankali, sai ki nuna masa kullum Allah yana basa sai kawai don yau baka samo ba sai muyi hakuri mu godewa Allah. Idan kuwa wani ne ya bata masa rai, sai ki bashi hakuri da kuma kwantar masa da hankali, sannan idan ya dawo miki cikin tashin hankali sai ki warware masa bayan kinji mai ya faru dashi. Idan ba zaki iya warware masa ba sai ki kaishi inda za’a warware masa damuwarsa.

1. MACE TAGARI ITACE WACCE IDAN MIJINTA YAYI RANTSUWA AKANTA ZATA BARRANTAR DASHI: Yar’uwata ki sani wajibine idan mijinki yayi miki rantsuwa sai ki barrantar dashi misali idan yace wallahi yau sai kin yafe min laifin da nayi miki, kawai sai ki yafe masa don ki barrantar dashi.

2. MACE TAGARI ITACE WACCE IDAN MIJINTA BAYANAN KOKUMA YAYI TAFIYA SAI TA KIYAYE KANTA KUMA TA KIYAYE DUKIYARSA: Yar’uwata ki sani idan mijinki bayanan dolene ki kiyaye kanki da dukiyarsa, kuma karki yarda ki nuna adonki ko kwalliyarki ma wani kuma karkiyi almubazarranci da dukiyarsa. To yar’uwata idan kika cika wadannan sharuda wallahi kin zama mace ta gari injin Manzon Allah (S.A.W). da fatan Allah (S.W.T) ya baki ikon cika wadannan sharuda Ameen.
Share:

Saturday 18 November 2017

SIFFOFIN UWA TAGARI 4SIFFOFIN MACE TA GARI

Yar uwa mai karatu ga kadan daga cikin siffofin mace ta gari, idan kuwa baki da wadannan siffofin, to sai ki rungumi wannan su zamo dabi’unki. Allah yasa mu dace Ameen
1.                       Itace idan mijinta yayi mata umurni zatayi masa biyayya.
2.                       Itace idan mijinta ya kalleta zata farantamasa rai.
3.                       Itace idan mijinta yayi rantsuwa akanta zata barrantar dashi.
4.                       Itace idan mijinta yayi tafiya zata kiyaye kanta da dukiyarsa

1.                       MACE TAGARI ITACE WACCE IDAN MIJINTA YAYI MATA UMURNI ZATA YI MASA BIYAYYA: Yake yar’uwata ki sani duk irin umurnin da mijinki yayi miki to wajibine kiyi masa biyayya matukar bai sabawa Allah ba. Kuma acikin kowani hali kika samu kanki ba tare da yamutsa fuska ba. Balle jan aji, kuma yar’uwa ki sani jan aji haramunne idan mijinki yayi miki umurni, wajibine ki zamo mai bin umurninsa. Allah ya baku ikon bin umurninsa Ameen.

2.                       MACE TAGARI ITACE IDAN MIJINTA YA KALLETA ZATA FARANTA MASA RAI: Ya yar’uwata mijinki ba zai taba kallonki har ki faranta masa rai ba, face kin dauwama a siffarki ta ya mace.
GA WASU DAGA CIKIN SIFFOFIN KAMAR HAKA KWALLIYA DA GAYE: Yar’uwata ki sani yana daga cikin asalin hallitar mace akai shine kwalliya, don haka ba’a son mace cikin sahun mata idan batayin kwalliya, anan wajibine ki kasance zinariya a gidan mijinki ko wani lokaci da irin salon kwalliyan da zaki yiwa mijinki acikin lokuta guda hudu kamar haka:
i-                        LOKACIN SAFIYA: Yar’uwata bayan kinyi Sallah wajibine kiyi wanka kiyi kwalliya irin kwalliyar Amarci.

ii-                     BAYAN BREAK FAST: Idan kin gama wanke kwanukan da aka ci abinci kinyi shara sai kiyi wanka kiyi kwalliya, yar’uwata kar ki yarda mijinki ya dawo ya sameki a hargitse, kamar yadda wasu mata sukeyi, abin kunya wai suna da zanin zaman gida kuma suna da zanin fita anguwa, wallahi wannan mummunar dabiane a dena.

iii-                   BAYAN ABINCIN DARE: Yake yar’uwata anan ma ya zama dole ne kiyi masa kwalliya irinta zamani wadda zaki kayatar dashi.
iv-                   LOKACIN BARCI: Yar’uwata anan kuma wajibine zaki yiwa mijin ki kwalliya da shara sharan kaya wadda zasu rikita mijinki.


do you want to learn how to blog and also make money online check this site
Share:

Saturday 11 November 2017

SIFFOFIN UWA TAGARI 3


MACE TAGARI

Mace ta gari za a same ta da:
1.                       KAMEWA: Daga duk wani abu da zai sosa wa maigidan ta rai, a kanta ne ko gidansa ko abincinsa da sauransu.

2.                        GASKIYA: In za ta yi magana ba ta qarya, domin samun riqe gidan gaba daya.

3.                       AMINCEWA: Duk abin da yake so ta yi ta amince, don yarda da cewa ba zai halakar da ita ba, tana qaunarsa.

4.                       TAWALU'U: Ta qanqar da kai gare shi koda kuwa tana da ilimi, arziqi da shekaru sama da shi, kamar dai Khadeejah R.A da Annabi (S.A.W)

5.                        NATSUWA: Kar ta riqa tuno abubuwan da suka gabata, kuma ta dena tsoron masu zuwa.

6.                        KUNYA: Ta riqa jin kunya, wannan ado ne gare ta, masamman in tana tare da mijinta a cikin jama'a, wannan zai qara masa kaunarta.

7.                        KWANCIYAR HANKALI: Mantawa da matsalolin rayuwa da qoqarin tura farin ciki ga mai gida koda suna cikin matsala.

8.                        GODIYA: Duk abin da ya zo da shi a nuna masa jin dadin zuwa da shi komai girmansa komai qanqantarsa.

9.                       HAQURI: A kan duk abin da zai bayyana daga miji (wannan ne kawai muka dauka alhali suna da yawa)

10.                  TSAYUWA QYAM: A wajen bauta da qarfafa mijin da 'yayan su.

11.                  AMANA: Ta zama mai amana, kar ta yarda maigidan ta ya ga ha'incinta koda kuwa sau Daya ne, ta riqa gaya masa abin da za ta yi domin maganin shedan. ‎
Wadannan abubuwa guda 11 su suke nuna mace nagari, dan uwana kada ka riqa binciken qyalqyal banza, ke ma yar uwa ki dai na kallon kudi ki duba rayuwarki idan kin shiga gidansa, komai kudinsa in ba kwanciyar hankali ba za ki ji dadinsu ba. Biyayya ga miji ba mai iya wa sai mace ta tagari, da yawa mata suna so a ce su ne wadan da Annabi (S.A.W) ya sifanta dinnan da (Nagari) sai dai biyayyar ce ta yi qaranci, ko za’a yi sai dai a gabansa in ya matsa an watsar kenan.

           Mace ta gari takan yi qoqarin ta zama wa mijinta aljannarsa ce, ba ta son ta ga gazawarta a idanunsa, don haka takan yi farin ciki in taga murmushinsa, takan damu matuqa in ta ga fushinsa ko da ba da ita yake ba, ba ta jinkiri a wajen abinci, kuma ta iya dafawa ba tare da almubazzaranci ba, ita ce amin taccen abokin shawararsa, mai iya riqe masa sirri, ba ta yarda wani ya sani ko waye kuwa, sannan ga taimako.

do you want to learn how to blog and also make money online check this site
Share:

Thursday 2 November 2017

SIFFOFIN UWA TAGARI 2

SIFFOFIN UWA TAGARI

Kalmar macce abu ne mai matukar girma sabida daraja da kuma kima da Allah ya bata, Yaku mata kada ku shagala da jin dadin rayuwar duniya kuyi biris da baiwar da Allah ya yi muku kusani cewa duk wata jin dadin matukar baki kame kanki daga aikata fasadi ba yazama na banza kuduba kugani yanxu Rayuwar da muke ciki a bin haushi matan aure basa fita irin wadda Addini ya umurcesu dasuyi wa'iyazu billah haba mata, Ina kuka baro Hijabinku suturar ku wadda Allah ya ce ku lulluba da ita...??? Wai ace matar aure zata fita unguwa saita kashe makeup tamkar zataje gasar sarauniyar kyau amma abin haushi In ka tarar da ita A cikin gidanta tamkar yar aiki, Wai bazatayi wanka da tsaf ta ba sai in zata gidan biki ko asibiti ko wani abin to wallahi kisani duk wanda zaiga adonki ya yaba matukar ba mijinki bane kinyi a banxa. Wani abin haushi abin takaici Wai yanxu mata basu sallah cikin lokaci sabida an miki kwalliya karkije alwala ta goge Innalillahi wa'innah illaihirraju'un kenan kin xabi duniyarki a bisa lahira ko....?? wace riba gareki idan Allah ya dauki ranki kina cikin irin wannan halin...?? mezaki ce da mahaliccinki..?? kokinsan cewa mutuwa kowane lokaci zata iya yi miki bazata gaskiya mata a gyara yakamata ace duk wani abu komai mahimmancinsa ki hakura dashi har sai kin gana da mahaliccinki (SALLAH) , Adaure ayita cikin lokaci kuma bada garaje ba dan naga wasu ma sallar basusan yanda zasuyita cikin nutsuwa sabida kawai dadin duniya ya shagaltar Dasu. Allah ya sawwake. Ameen!!
Da farko yake yar’uwa ki sani aure bautan ubangiji ne. To amma mai yasa ku mata kuke banbanta yanayin zaman aurenku bayan Annabinmu dayane, domin da yawa daga cikin yan uwa mata basu dauki aure a matsayin bautaba wallahi. Bayan aure itace babban hanyar shigarki Al-jannah idan kikayi hakan kuma kika yarda da hakan to kinci riban duniya da kuma lahira. Allah yasa haka Ameen. Sannan ki sani yar’uwa duk wata ibada tana tareda jarrabawa musamman ma aure, domin zamane da ya kunshi farin ciki da bakin ciki, dadi. da mara dadi, hakuri da rashin hakuri, da sauran wasu abubuwan da basai na ambacesu ba, Yake yar’uwa ki sani aure anayinsa saboda wasu abubuwa da dama amma babban su shine natsuwa. Kuma natsuwa baya samuwa sai idan mace ta zama tagari shiyasa da yawa daga cikin maza basuda natsuwa saboda matansu ba nagari bane. Manzon Allah (S.A.W) yace duniya abin jin dadi ne, amma mafi alkhairin jin dadin duniya shine mace tagari, don haka ya yar’uwata idan harke ba mace tagari bace to ki sani baki da amfani a zaman gidan aurenki da mijinki idan kika sake baki gyara zamanki da mijinki ba, to wallahi zaki samu mummunana sakamako a wurin Allah. Allah ya karemu Ameen.


Ya kamata duk matar da ta tsinci kanta adakin aure, a wannan zamanin da muke ciki, ta gode ma Allah. Ba don komai ba, idan ta duba zata ga wasu 'yan-mata irinta, sunfi ta kyawun halitta da iya ado, amma har yanzu basu samu mijin aure ba. Don haka zai fi alkhairi agareki ki Qudurce acikin zuciyarki cewa GIDAN MIJINKI NAN NE WAJEN NEMAN ALJANNARKI Ki rike mijinki hannu bibbiyu, ki kula da tsaftar jikinki da tsaftar Muhallinku. Ki kiyaye MUGAYEN QAWAYE... Ba zasu rasa yi miki hassada ba. Tunda ke kin samu miji, su kuwa basu samu ba... Dole suyi miki hassada. Ki kiyaye sirrin mijinki, kar ki gaya ma kowa. Musamman ma kawayenki zasu so suji abinda yake faruwa. Don haka kar ki gaya musu Idan kuna da 'ya'ya to ki kula dasu, ki kula da tsaftarsu. in ma 'ya'yan kishiyarki ne, to ki kula dasu kamar yadda zaki kula da 'ya'yanki. Ki kiyaye dukkan amanonin mijinki. musamman ma iyayensa da 'yan uwansa da dukiyarsa. Allah Ya bamu ikon kiyaye Hakkin iyalan mu.
Share:

SIFFOFIN UWA TA GARI


SIFFOFIN UWA   TA GARI


NA

MUHAMMAD ABBA GANA
(09039016969)


GODIYA

Dukkan godiya su tabbata ga Allah (S.W.T) Ubangijin Talikai bisa ni’imominsa bayyanannu da boyayyu, wanda da ikonsa ne da yardarsa na rubuta muku wannan littafin, Allah nagode maka.

GAISUWA A GAREKU DA JINJINA

Dukkan gaisuwa ga yan uwa musulmai maza da mata Allah ya hada mu a Aljannah. Baran manta Daku ba:
Hajiya Saratu (Maman Abdallah)
Hajiya Fatsuma (Maman Iklass)
Hajiaya Fatima (maman salihu)
Hajiya Rukayya (Maman munir)
Hajiya Maryam (Maman dada)
Hajiya Fatima (Maman Shafiu)
Shamsiya aminu umar (maman usaimin)
Shamsiya shuaibu (maman islam)
Sakina umar (Maman Habibullah)

                                            INA KAUNARKU

ina kaunarku ‘yan uwana da masoyana, nagode da soyayyarku a gareni.


                                                     SADAUKARWA

Na sadaukar da wannan littafin ga kannena da ‘yan uwana da iyayena da masoya, Allah ya bar zumunci.

YA ZA’AYI IN MANTA DA KU?

Iyayena abin alfaharina a kullum addu’ata Allah yaja da ranku ya baku tsawon rai mai amfani. Hadiza Wahira da Mallam Abba Gana Kolo, Allah yasa Aljanna ce Makomarku, Ameen.

GABATARWA

Ina gabatar da wannan littafi wanda ya kunshi takaitaccen bayani akan iyaye mata. Domin a hakikanin gaskiya iyaye mata sun bambanta, Allah yasa mu dace, Ameen. Wannan wata fadakarwace ga yan’uwa mata zalla, ko zasu fadaka daga gurbatattun dabi’un da sukeyi a gidan aurensu. Muna rokon Allah ya daidaitamu bisa bin hanya madaidaiciya kuma ya shiryemu ya sanya mu cikin bayinsa salihai Ameen.

---------------------------------------------------------------------------------------------
do you want to learn how to blog and also make money online check this site
Share:

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).