shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday 20 February 2019

SHAWARWARI GUDA 7 DON INGANTA TARBIYYAR YARA - SIFFOFIN UWA TAGARI 12

SHAWARWARI GUDA 7 DON INGANTA TARBIYYAR YARA - SIFFOFIN UWA TAGARI 12

Tarbiya wata kalma ce da take nuni ga yadda ake kula da ‘ya’yanmu da kuma na kasa da mu. Hakika, girma da muhimmancin kalmar 'tarbiyya' sun wuce yadda muke anfani da ita a yau da kullun. Tarbiya ta banbanta da daga al’umma zuwa al’umma, ma'ana, abinda ke da kyau ga wasu mutanen ba lalai bane ya zama yana da kyau ga wasu. Amma a gani nan a kwai wasu abubuwa da za su da ce da kowa, kuma sune na kawo a nan zan yi dan sharhi a kansu, musamman hanyoyin da za’a bi don inganta tarbiya yara.

1. Abu na farko shine cusa wa yaro tsoron Allah. Hanyar cusa wa yaro tsoron Allah kuwa shine shine sanar da shi Allah din da abinda Ya yi umarni da abinda Ya yi hani. A duk lokacin da yaro ya zama mai tsoron Allah da kokarin yin abinda Allah Ya yi umurni, da barin abinda Ya yi hani, tarbiyarsa zai zamo mai sauki a wurin iyayensa, ko yaro na tare da su ko ba ya tare da su.

2. Cusawa yara son ilimi. Kasancewar ilimi shine ginshikin rayuwa, to hakkin iyaye ne su muhimmantar da ilimi wajen tarbiyar ‘ya’yan su. Su yi wannan ta hanyar maida hankali da ilmantar da ‘ya’yan nasu da kuma su kansu iyayen. Ya kamata su dauki ilimi a matsayin haske mai haskaka rayuwa ta ko wani fanni ba wai kawai don neman aikin abin duniya ba.

3. Dole iyaye su kasan ce abin koyi ga ‘ya’yansu. Ma’ana a nan duk wani abinda iyaye za suyi, ya kasan ce irin abinda suke son ‘ya’yansu suyi ne, domin shi yaro yafi koyon abu a aikace fiye da abinda za’a gaya masa. Misali in har uwa bata son yaran ta su koyi zagi da tsinuwa to ta kiyaye zage-zage.

4. Yawan kula da abinda yaro ke yi. A matsayin mu na masu kula da ‘ya’yanmu ya zama lallai mu kula da duk wani abinda suke yi. Na san yana da wahala amma wajibi ne in har ana son a yi tarbiya ta kwarai. Kula ba yana nufi hana su sakewa, sai dai yana nufin kasancewa kana/kina sane da inda suke ko abinda suke aikatawa dai dai gwargwadon iyawa a kowani lokaci. Wannan zai ba da ikon sanin halin da yaro ke ciki, sannan in yayi ba daidai ba za a gyara masa.

5. Iyaye su guji yin munanan kalamai a kan yara. Kowa ya sani a addini mugun baki bai da kyau ga ‘ya’ya. Yaro idan ya sosa wa wasu iyayen rai, musamman iyaye mata, sai ka ji ana “Allah wadaran ka wane” ko “la’a nanne,” da dai sauran munanan kalamai, wanda suna iya binshi, sai ka ga yaro ya shiga yin taurin kai ba zai saurara wa kowa ba, ya zamanto bai da muntunci bai gani wani da mutunci, kuma daga karshe a rasa yadda za’ayi da shi. Allah ya sauwake.

6. Koya wa yaro girmama na gaba da shi. In ka ga yaro na girmama na gaba dashi to ya gani a na yi ne. Iyaye dole su nuna wa ‘ya’yan su muhimmanci girmama babba ko da daga ina mutuminnnan yake, daga kauye ne, birni ne, talakane shi, mai dukiya ne, addinku daya ko ba daya ba. Idan iyaye suka yi haka a aikace to yaro shima zai yi.

7. Koyawa yara kyauta ta hanyar aikatawa. Tarbiya ta kunshi rayuwa ce gurungundumarta, sabo da haka komai ya kamata yana ciki. Kyauta aba ce mai kyau da yara ya kamata su fahimci cewar mutun ya zamanto mai yawan bayarwa ba wai mai yawan tsammaniba. Iyaye su kasance masu kyauta don nuna wa yara mahimmancin kyautar, misali ta hanyar aikensu su kai kyauta gidan dangi ko makota ko dai abokan arziki. Kuma kar a yarda a rika yin gori idan ambayar, sabo da yara suna jin duk abinda iyaye su ke fada, kuma su ma in sun tashi haka za su yi.

Allah Ya ba ku ikon tarbiyartar da 'ya'yanku ta hanya madaidaiciya.
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).