shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Sunday 29 November 2015

KAUNA CE SILA***41---45

kauna-ce-sila.jpg

[8:55PM, 11/28/2015] Bana: KAUNA CE SILA 41

MUHD-ABBA~GANA


sai tace haba ke kuwa don Allah ki zo ko gaisawa ai ma yi nace mata to amma ba dan ina da shirin zuwa ba nasan ita kawar amaryace kusan yar uwa ne to ni kuma fa nan na ce dan ango zani shima ce min yake bai san ranar ba har ranar tazo na tashi zan yi alwalar salllar isha sai naji wayata na kara ina duba mai kira sai naga marwan abokin ya ahmad ina dagawa yace baza ki zo bane gamu an hadu za a tafi nace nifa ba zani ba yace amma da baki da kirki bikin yayan naki guda nace E ni ba zan iya zuwa ba yace don Allah ki zo akwai abin da yasa nake son kizo idan kina kaunar Allah da annabinsa ki fito yayi ta min magiya nace masa shikenan bara na tahoMUHD-ABBA~GANAwww.abbagana.pun.bz


KAUNA CE SILA 42
MUHD-ABBA~GANA
yace yawwa koke fa har na ji dadi gurin ya cika sosai lokacin dana isa gurin ango da amarya basu karaso ba amma naga kawaye na nan muka tsaya muna ta sururu muna dariya mu ce wanan muce wancan saboda yawan mutane ni bana iya hango kowa sai waka tana tashi sai kuma karar sifika muna nan din dai tsaye muka ji sanarwar ango da amarya zasu shigo kawai sai muka ji alamar bindiga kamar irin wadda akeyi wa sarki ai kuwa sai ga amar da ango hannun su rike da juna ango yayi kyau sosai ita ma haka ina ganin su naji wata muguwar faduwar gabaa kawai na fara innalillahi wa inna ilaihi rajiun har suka je suka zauna na daina ganinsu saboda mutane anan inda muke nan sauran kawaye na suka barni ni ba zan iya yawo a cikin gurin ba ina tsaye sai naji maganar marwan yace ana zuwa yin hoto da ango da amarya kizo mujeMUHD-ABBA~GANA
www.abbagana.pun.bz
[11:14AM, 11/29/2015] Bana: KAUNA CE SILA 43MUHD-ABBA~GANA


Nace wallahi ba zani ba ai ba abin da nazo yi kenan ba sai naga yayi dariya yace haba ke kuwa menene na saurin yanke hukunci kuma tare da rantsuwa nace ba zan dai je ba ban dade ba na fito na tafi gida shima marwan waya na masa nace nifa na wuce gida yace to bama yaji na saboda hayaniya ina zuwa gida nayi shirin kwanciyar bacci ina tsaka da bacci naji wayata na kara na rasa me ya mantar dani ban kashe ba na duba nan naga marwan na dauka da alamun bacci nace hello marwan sai yace au bacci kike yi nace wallahi na fara bacci yace ikon Allah dama zaki iya bacci sai na bude ido sosai nace ban gane me kake fada ba yace a'a ji nayi ana ta hirar ki wai yau an san ba zaki iya bacci ba yayanki yayi aure nace lallai to waye ya fada yace yanzu ake fada anan zoo road nace to gashi ina yi kuma komawa ma zanyi sai da safe yace Allah ya tashe mu lafiya nace ameen na kashe wayata ba sai na nemi bacci na rasa ba kawai na tsaya ina tunanin maganganun da muka yi da shi nace wai me mutane suke nufi da ni ne? ba komai Allah yana nan na juya nayi kwanciyata tun daya Ahmad yayi aure sai na daina kiran shi amma ban daina tunaninshi ba dan abune wanda ba zan iya hana kaina ba haka na ci gaba da gudanar da rayuwata yadda na saba a ban garena da salisu yanzu ya dan kara sakin jiki dani koh dan yaga ya ahmad yayi aure ne oho yaci gaba da zuwa gidanmu amma yanzu ba kamar da ba.MUHD-ABBA~GANA


www.abbagana.pun.bz


KAUNA CE SILA 44MUHD-ABBA~GANAZA ayi kamar wata biyu da bikin ya ahmad wata rana kamar misalin karfe daya saura ina zaune sai kawai na hangoshi yana kokarin rufe motarsa yana waya ina zaune ya shigo yana shigowa na gaisheshi ni dai naga ya kalkeni sai da ya dade yana kallona sannan ya amsa ashe gurin mai gidan mu ya zo a yi masa kida ina nan naji har an fara masa kidan akwai wata hauwa itama a gurin mu take tare da ita muke zaune lokacin daya shigo nace mata tashi muje kasa muyi alwala ta riga ni fitowa daga inda muka yi salla ina zuwa sai na tarar da su dukan su a zaune har da ya ahmad sai ya kalleni yace ina zan samu gurjiya? sai na kalli waje nace suna wucewa bara na duba ai kuwa sai na fita neman gurjiya dana samo sai naga shi ya koma inda ake masa kida kafin ya fito sai hauwa tace min waya fa aka masa sai naji yana cewa gurjiya to ko matar sa ce tace tana so nace mata oho yana fitowa sai naji yace a juye gabansu to ni dai anan naga yana ci dan su mai gurin ma duk sunci kamar biyu da minti goma ya sake fitowa yace min baki bani wake da shima fa tace bara a kawo maka yace to ya koma inda ake masa kida nan na gugice ina neman food flask jikina har rawa yake naje na wanke na cewa zainab dan Allah tazo ta rakani ai kuwa sai sa naje har dangi naje na siyo masa na kawo masa ya ci ranar ya dan dade a gurin mu dan sai da uku ta wuce sannan ya tafi yana tafiya hauwa ta sakani a gaba wai nice uwargida amarya tana gida tunda yace na bashi abinci nace a'a ai ni ba saurayi na bane yaya nane kuma ai ba wani abu bane dan yace na bashi ko sai kawai tayi dariya.
MUHD-ABBA~GANA


www.abbagana.pun.bz


KAUNA CE SILA 45MUHD-ABBA~GANA

Wata rana da safe na fito kamar sha daya da rabi dan a lokacin yajin aiki muke yi bamu ma da ranar komawa sai marwan ya kirani yace in gani a kasanku zanci waina kina sama ne nace eh bari na sauko bayan mun gaisa sai yace wannan yayan naki ne ya fito dani aiki nake so yayi min wallahi bara ma na kira shi sai ya fara neman layin shi daya dauka sai naji marwan nace masa ya jikinka Allah ya baka lafiya yanazu zaka fito? sai nace a'a gaskiya idan ba kudi zaka bashi ba ba zai fito ko bashi wahala ba sai naji narwam yana cewa kana jin kanwar kako ban san me yace masa ba har suka gama suna gamawa sai naji waya ta na kira ina dubawa naga sunan ya ahmad ina dagawa sai naji yace kuna zoo road ne sai na cemasa eh yace gani nan sai nace ya jiki yace da sauki sai na rasah me zance sai na kashe na cewa marwan bari na koma sama yace min to shikenan ina zama kawai na fara rubuta masa text kamar haka" SANNU ALLAH YA BAKA LAFIYA YASA KAFFARA CE YA KARA SAUKI
bai yi min reply ba amma dai nasan ya gani dama bai saba yi min reply ba saboda haka ban damu ba ranar nan mun sauka za muyi alwala sai kawai naji ina san kiran ya ahmad ina kira ya daga nace masa nifa bana ganinka sai yayi dariya ya ce ya gari ya kano? sai nace ya kano kuma? sai yace to ya vocal? nace vocal lafiya yace ya komai nace lafiya yace to yayi kyau by muhd abba gana

MUHD-ABBA~GANA
www.abbagana.pun.bz
Share:

Saturday 28 November 2015

KAUNA CE SILA***31----40

kauna-ce-sila.jpg

[8:50PM, 11/26/2015] Bana: KAUNA CE SILA 32MUHD-ABBA~GANAina hanya amma duk tunanin ya ahmad nake yi gaskiya ya ahmad yana da kyau kai anya akwai mai kyau shi kuwa a cikin mawaka anan namu gashi ya iya kwalliya dan Allah ji wata irin shiga da yayi ga wata rigar sanyi mai kyau akan kayan da ya saka da irin wadannan tunane tunane na karasa gida washe gari ya ahmad ya kira ni a waya bayan mun gaisa yace wai ni soyyya muke yine? nace a"a me ya faru yace yan nan gurin kowa sai cewa yake yi wai soyayya muke yi to ke kina sona? bude baki da zanyi sai nace masa ai kai ba saurayi na bane yaya nane yace haka ne nan muka yi sallama wata irin kauna nake yiwa ya ahmad wanda nake jin shi har cikin raina kuma ina ganin kamar gudan mu daya ko a ina na ganshi da gudu zan karasa na sameshi nayi ta masa surutu yana yawan zuwa gurinmu amma baya hawowa same sai dai ya tsaya kasa yace min cD yazo siya ya tafi wani lokacin ka sai yace min ruwa zan bashi ya sha ya tafi wani abin mamaki bana so naji ana fadin laifin ya ahmad bare kuma naji an zage shi duk yanda muke da kai naga kana bata shi to zaka ga bacin raina shi kuma kome ya ga nayi sai ya tambayi dalilin yi kamar yazo bai ganni ba ko takalmi ya gani a kafata to zai ce mai yasa kike son irin wannan takalmi bare kuma ya ga na dan rame hatta dan haske idan yaga nayi sai yace naga kinyi fari nakan ce masa ba komai wataran kuma idan yace yaga na rame sai nace masa aikai ne sai ya ce ni bani ba ne yayi dariya ya tafi wata rana fiddausi tace na raka ta wani biki a daula hotel an gayyaceta nace mata gaskiya sai naje na tambayo umma tunda kince da magariba ne tace idan kika fito sai muje nace mata bara na dawo


MUHD-ABBA~GANA


www.abbagana.pun.bz

KAUNA CE SILA 33
MUHD-ABBA~GANA

Lokaci da muka je gurin biki sai naga ashe mawaka ne da yawa dan akwai wata maryam a zaune ga wasu mawakan maza muna zaune ina daga idona sai naga shigowarsu ya ahmad kawai naji gabana ya fadi duk da naji na rikice yana zuwa kuwa sai naga ya zauna a kujerar da take kusa da ni ba dan gaisuwa ba abin da muka kara yi sai na juya muka cigaba da hira da fiddausi ina nuna mata wasu hotuna a waya ta sai naji yace bani wayarki na juya don naga me yake nuna min sai naga ashe hoton salisu ne akan waya ta ni na manta da shine ma akan wata ta naji ya kuma maimaita min tambaya da yayi min sai na hau kame kame nace ba saurayina bane shi ya bani wayar shi yasa kaga hotonsa sai yace hmmm ai nima ya taba cewa yana son budurwata nace wace yace oh yace daga yau ma itama ki dinga ce mata aunty tunda ai waccan maryam din ma aunty kice mata kuma ai duk sun girmeki nace to an gama munyi kamar sati daya bamu hadu da ya ahmad ba kuma bamuyi waya ba ranar ina idar da sallar magariba sai kawai naga missed calls dinshi ai kawai na fara neman layin shi tana fara ringing sai naji ya dauka yace ki kashe zamu kira ki kalmar dana ji ya fada ce ta karshe ta firgitani nan dai ina ta tunani sai da yayi kamar minti ashirin sai kiran shi ya sake shigowa dana dauka mamaki ne ya kamani muryar salisu naji a wayar bayan kuma layin ya ahmad ne yayi shuru na kasa magana sai naji yace mamaa gani da yayanki yace wai karna sake na yaudareki kafin nayi magana sai naji ya ahmad ya karba yana cewa na fada masa idan auranki zai yi to ya hanaki fitowa,


MUHD-ABBA~GANAwww.abbagana.pun.bz
[8:54PM, 11/26/2015] Bana: KAUNA CE SILA 34
MUHD-ABBA~GANA
idan kuma ba da da gaske yake ba to ya bar ki ki samu wani bawan Allah nace masa tam ni dai jikina duk ya mutu muna na rasa me yake min dadi na kuma rasa dalilin jin hakan wani canji dana fuskanta daga ya ahmad shine yanzu ya daina kira na a waya kamar da kuma ko da na kira shi ba ko yaushe yake dagawa ba idan na samu ya daga na fara masa korafi sai yace aiki ne ya masa yawa duk da nasan a yanzu aiki ya masa yawa dan kusan ya kara shahara kusan ko wanne film wakar shi zaka ji albumd na wakokin shi yana ta fitar da su daban daban amma a nawa tunanin wannan dalili bai isa ya hanashi kirana ba a matsayina na kawarshi da nake ji dashi ina tura masa sakon text a waya kusan ko wacce juma'a bai taba bani amsa ba dama kuma sakon baya wuce addu'a ana cikin haka wata rana yace na zo nayi masa aiki bayan naje sai ya tashi yasa wani yaro yayi recording din dan bama idan shi ne ya ce zaii yi recording din ba zan iya ba dana gama na fito sai na same shi zaune ban masa magana ba nazo zan wuce yace min zo nan sai na matsa kusa da shi ya kalli idona yace ina salisu? sai nace yana nan sai naji yace bara na kira shi ya zo nan muyi magana gani ga ki nace dan Allah ya ahmad ya kyaleshi wallahi duk mutane sai fada masa ake yi wai soyayya muke yi sai ya ce min to ai in na kira shi tun ma kina ciki gashi nan ma zuwa ina jin ya fadi haka na bar gurin ko shi bai san ta ina na bi na gudu ba ina hanya kiranshi ya shigo waya ta na dauka yace kina ina ki dawo nace wallahi naa kusa gida.

MUHD-ABBA~GANAwww.abbagana.pun.bz
[8:59PM, 11/26/2015] Bana: KAUNA CE SILA 35
MUHD-ABBA~GANA

sai kawai ya kashe nayi kamar minti talatin ina shiga gida sai kiran salisu shima ya shigo ina dagawa naji yace yanzu ke ya kamata abin da kika yi kenan nace masa me nayi yace meye na fadawa ahmad cewa ana ce min soyyya kuke yi ban bashi amsa ba kawai ji yayi na sak iwani kuka mai karfi yace mamaa niya kamata nayi kuka ba ke ba nace to amma ai kasan me mutane suke cewa yace shi kenan kiyi hakuri zanzo da daddare daya zo gidan mu haka yayi ta min maganar shi fa baya son wata mu'amala tsakanina da ahmad dn shi kawai gani yake soyyaya muke yi nace masa ni fa yaya na ne kai kuma saurayi nane abinda kawai na sani kenan a wannan lokacin na fahimci wai abu ashe duk mutane sun san tsakanina da ya ahmad ashe har yi dani ake ana cewa idan ana so aga nayi fada to a taba shi wasu kuma sunce in dai kai maganarshi a gabanta to kuwa kamar yaji an gama ire iren wadannan surutan na mutane sune suke dagawa salisu hankali dan shi kanshi yasan ina bawa ya ahmad muhimmanci fiye da komai yana ganin idan har soyayya zata shiga tsakaninmu to yasan zan rabu dashi ana cikin wannan yanayine wataran salisu yazo gidan mu muna zaune sai nace bara na shigo gida ina zuwa ina fitowa naga salisu ranshi ya bace sosai ba kamar yanda na barshi ba nace masa ya ka tashi sai kawai naga ya miko min wayata yace tafiya xanyi yau ma kunyi waya da ahmad kuma me kika fada min bayan kiran ki yanzu amma gashi naga kin kirashi yau shima naga missed call dinshi a wayarki sai nace wallahi salisu aiki na masa amshi sai sa ya kirani.MUHD-ABBA~GANA


www.abbagana.pun.bz
[8:43PM, 11/27/2015] Bana: KAUNA CE SILA 36
MUHD-ABBA~GANA


nan dai salisu ya tafi ya barni da tunani a daran nayi ta kiran shi amma yaki dagawa daga karshe ma sai ya kashe wayar sa j kuma har safiya ban same ba haka naje makaranta ba wani kuzari a tattare dani husna ce ta shigo sai nake bata labarin abin da ya faru nace mata kinga husna ya ahmad ma yanzu kwata kwata bai da mu da ni ba ko waya baya min sosai tace bani number salisu naba ta shi bayan ya dauka naji tana bashi hakuri yace a wuce amma dole sai dai ta goge number ya ahmad daga wayata husta tace zatw goge yanzu nace gaskiya ba zan iya ba a zuciyata kuwa cewa nayi to ai kona goge ma ina da ita a kaina dan na haddace tare muka zo zoo road da ita wai dan ta bawa salisu hakuri yace mata ya hakura ba komai sannan ta tafi gida ni kuma na hau sauran benan mu wani abin haushi a wannan lokacin mutane sun sani a gaba sosai ko ina zan ce na ake yi cewa ina bala'in son ahmad cewa bana son laifinshi ba a taba shi kuma wai zan iya batawa da kowa a kanshi idan kuma a gabana sai kaji ana cewa ai ita mamaa ahmad ne yayanta sai nayi dariya nace na jini ma kuwa shi kuwa a bangarenshi yanzu ko ganinshi bana yi sosai kuma ya canja min sosai wannan ne yasa ko ganinshi nayi bana masa irin yanda na saba idan bamu hadu kusa da kusa ba bana bari ya ganni idan a nesa na ganshi sai nayi ta kallon shi har sai ya bar gurin yauma irin hakan ce ta faru yana kasan gurin mu suna magana da wani mai shirya film sai na labe a jikin kofar mu ina kallonsa ashe nura yana baya na yana gani na sai naji yace to ki sauka mana sai na juyo nace kai nura wallahi ba zan ma bari ya ganni ba.MUHD-ABBA~GANA
www.abbagana.pun.bz
[9:11PM, 11/27/2015] Bana: KAUNA CE SILA 37
MUHD-ABBA~GANAkawai sai na ji nura ya fara kiran sunanshi ni kuwa sai nayi dayan studio na kusa dan na shige ciki nayi kamar minti biyar sai kiran shi ya shigo wayata yace ina kika shiga fito gani a vocal ina zuwa sai ganinshi nayi a zaune a reception da wata mujalla a hannunshi na ce masa ina wuni sai naga ya kalleni kawai yace ance guduwa kika yi da kika ganni bakya son ganina? nace a'a yace to me nayi miki nace kai ne ka daina kulani sai yace to ai mamaa kin fi karfina kina da samari da yawa nace wallahi ni ban da samari yace salisu ba saurayinki ba ne har hotonku tare ya nuna min sai na ce rannan ne zamu je yin alwala ya ganni shine fa ya ce na tsaya a mana hoto yace shi kenan karki damu ya tafi ya barni a nan zaune yayi tafiyarshi muna zaune tare da su zainab ranar nan a reception sai ga ya ahmad kawai ganin shigowarshi nayi naji suna gaisawa da yan gurin sai na sunkuyar da kai kasa har zai shiga ciki sai ya dawo yace min keh sai na dago kai sai naji yace sai na yiwa salisu rashin mutunci ban ce komai ba sai naji mana jan mu yana dariya yana cewa mai yayi maka sai naji yana cewa wai yayi maka sai naji yana cewa wai cewa yake yi soyyaya nake yi da yarinyar nan ban san me manajan yace masa ba dan ciki suka shige saboda wata waka yazo dorawa mai gurinmu da aka yiwa matar da zai aura mawaka da yawa kowa baiti daya yake zuwa yana dorawa ina ganin fitowarshi na bi bayanshi nace masa ya ahmad sai ya juyo nace masa wadannan din da kake fadawa salisu yayi maka laifi sune masu fada masa cewa soyayya mukeyi.MUHD-ABBA~GANAwww.abbagana.pun.bz


KAUNA CE SILA 38
MUHD-ABBA~GANA
nace wai dama abin da ya maka kenan sai yace wai dan nace masa kuna kama da shi ne ni kuma yace min wai muna kama dariya ce ta subuce min sai naga ya sha kunu yace ba kina sonshi ba kawai kuje kuci gaba da soyyarku nace ni ba sonshi nake yi ba kawai dai yace yana sona nace masa to yayi tafiyarsa ya barni ban tsaye ban iya komawa studio ba har sai da naga ya shiga motarsa ya tafi wani abin takaici tun daga wannan lokacin ya ahmad ya daina shiga al amurana waya ko na kira sau nawa baya dagawa babban abin takaici ko gaisheshi nayi baya amsa min kamar da don idan yana cikin mutane ma ya ganni sai ya dauke kai idan kuwa muka hada ido sai dai naga ya harareni dana ga abin da gaske yake kawai sai na fara canja hanya idan na ganshi kiran nashi ma sai na daina duk da bana ji dadin hakan da muke yi haka na hakura na tattarashi na ajiye shi yau alhamis ina zaune a vocal sai kawai na tsinkayi muryar ya ahmad yana sallama ban san me yazo yi bs na dai ji yana gaisawa da mutane dana dago kaina sai kawai muka hada ido a take naji wata muguwar faduwar gaba wadda ban taba jin irinta ba tun da mahaifana suka kawo ni duniya ga wani yanayi dana tsinci kaina a ciki wanda ban taba jin irinshi ba wani abu ne naji yana fisgata tun daga tsakiyar kaina har kasa kafata numfashinta ne naji yana neman daukewa sai kawai na fita ban san iya tsawon lokacin daya diba ba na dawo daukar jakata na samu ya tafi dana je gida akasa komai nayi nayain da nake ciki daban ne ban taba shiga kwatankwacin shi ba bayan na idar da sallar magariba naje na samu uman mu nace mata umma yau daga ganin ya ahmad gabana yake ta faduwa har yanzu na ma rasa me yake damuna.MUHD-ABBA~GANA

www.abbagana.pun.bz
[9:12PM, 11/27/2015] Bana: KAUNA CE SILA 39

MUHD-ABBA~GANAumma tace ba komai ki dinga addu'a insha Allah babu komai na tashi na koma dakina kiral ayin shi sai yaki dagawa gannin bai daga ba sai kawai na kyaleshi a yan kwanaki nan na shiga wani mawuyancin hali ni kaina ban san haka na damu da ya ahmad ba dan ko yaushe tunaninsa ne abin yi nada shi nake tashi da shi nake kwana a raina har gizo yake min gashi kwata kwata na daina ganinshi wayarshi ma yanxu ban fiye jin ta a bude ba a hakan ne kuma na fara jin rade radin cewa wai ya ahmad aure zai yi ranar da naji ban iya hakuri ba sai da na kira shi dana kira naci sa'a ya daga bayan na gaishshi yace min kwana biyu nace ai ni na rasa in da kake buya yace ina nan aiki ne kawai ya boye ni sai nace ya ahmad wai aure zaka yi sai yace E kema kawai ki nemi miji kiyi aure ko kin fi so kiyi ta waka nace masa a'a zan yi sai yace yawwa na gode duk abubuwan da nake ji a zuciyata game da ahmad ban daina jiba kamar ma karuwa yake yi wata rana na sauko zan tafi gida sai na hango ya ahmad a xaune a kan motarshi shi da wani abonkinshi marwan yayi min kyau sosai dama ya ahmad karshe ne gurin kwalliya wata riga ya saka fara da bakin wando da farin takalmi banje gurin ba na tafi hanyar titi ina zuwa zan tsallaka titi sai na waiwayo don na kalleshi ga mamakina shi ma ni yake kallo har na tafi dana fito washe gari sai muka hadu da marwan wanda na gansu tare jiya yace jiya shine kika yi kamar baki ganmu ba koh?MUHD-ABBA~GANA


www.abbagana.pun.bz
KAUNA CE SILA 40


MUHD-ABBA~GANAnace ba haka bane naga kuna magana ne yace min yayanki fa auran shi ya zo nace masa eh na sani wai sauran kwana nawa ne yau yace bazai kai kwana ashirin ba nace Allah ya kaimu da daddare na kira layin ya ahmad na ce masa wai bikin ka saura kwana nawa sai naji yace wallahi ban san saura kwana nawa ba nace masa baka sani ba? yace da gaske ban sani ba nace to shikenan bikin ya ahmad ya zo duk inda naje zancen bikin ake yi na san hakak baya rasa nasa ba da tashi da yake yi a yanzu sannan bikin su biyu za a hada tare da abokan shi wanda shi kuma kida yake yi ina ji ana ta zancen wasu ma ni suke tambaya wai dame dame za a yi nace ina jin dinner ne kawai ranar ina tsaye sai ga salisu yana waya ban san da wa yake magana ba sai kawai naji yace nima ga matata zaku gaisa ashe ya ahmad ne kuma a ranar aka daura aure gobe dinner za a yi ina dora wayar a kunnena naji yace ina gajiya nace lafiya ban sake cewa komai ba naji yace ku yaushe ne bikin naku ina ji yana fadin haka kawai na mikawa salisu wayar shi na bar wajan nasan ya ahmad ya san nice ban yi niyyar zuwa gurin bikin ba har cikin zuciyata duk kuwa yanda muke da shi ina gida bayan magariba sai husna ta kirani tace gamu a gidansu amaryar ahmad muna shirin zuwa gurin biki sai nace nifa bana jin zanzo
MUHD-ABBA~GANAwww.abbagana.pun.bz
Share:

KAUNA CE SILA***26---30

kauna-ce-sila.jpg

[5:03PM, 11/25/2015] Bana: KAUNA CE SILA 27

MUHD-ABBA~GANA

a haka na kara kwarewa kuma na samu wayewa da abin haduwa ta da maryam yanzu tayi wahala tunda ni bana zama da ita ma ga makaranta sai dai mukan yi waya lokaci zuwa lokaci samari sun fara takura min da zummar suna sona wasu aiki zanje gurin sai kaji ance bani number ki ina sonki gaskiya ina fada musu cewa bana saurayi ina samun masu fahimta inda zaka ji sunce kila tana da mijin aure ne nakan yi murmushi wasu kuma sai kaga sunyi dariya wasu kuma suyi min kallan banza kawai su kyaleni ni dai abin dana sani ba soyayya naje yi ba a wannan yanayin ne da ake ciki wata rana mun sauko da zainab zamu tafi sai ga wani dan gurin mu mai suna rabiu yace min mamaa kizo in ji wancan sai na kalli inda yake nuna min ban san shi ba ko a fuska nan zainab tace masa meye yace taje mana taji na dan yi shuru kamar baxa ni ba sai kuma naje yace min ina gajiya nace lafiya yace sunana salisu nima dan vocal ne amma kwanan nan na koma kasuwa shi yasa baki sanni ba amma idan naxo ina ganinki bamu taba magana bane amma ni gaskiya ina sonki kawai sai na juya nace ina da miji baice komai ba dana sami zainab nafada mata sai tace rabu da shi dan Alhaji karki kula shi duk maza mayaudara ne{ amma wallhi bandani } nayi dariya nace to wa zai yaudari ai na fada mishi bana soyayya tun daga wannan ranar salisu ya takura rayuwata kuma abaya tashi zuwa sai ya fuskanci mun kusa tafiya gida kawai sai dai naga ya biyo bayanmu yana magiya

MUHD-ABBA~GANA
www.abbagana.pun.bz
[5:11PM, 11/25/2015] Bana: KAUNA CE SILA 28
MUHD-ABBA~GANA
wani lokaci ma a titi muke tarar da shi idan yana surutun shi bana ce masa komai kai rannan dai salisu har da hawaye kawai na tsaya ina kallon shi naji yana cewa wallahi ina sonki kuma dan Allah bazan cutar da ke ba ki bani dama ban san lokacin da bakina ya furta masa cewa nima ina sonka gaskiya yaji dadi dan fuskarshi ta nuna hakan anan ya karbi number ta dan dama yace shi baza zai karba a gurin kowa ba har sai na amince dashi da kaina an kafe mana sakamakon mu na jarabawa da muka yi yayi kyau ba laifi amma duk mu ukun muna da gyara wato reciting inji bature wanda sai mun gyara zamu tafi ajin gaba ni zan gyara maths and physics husna kuwa maths da chemistry in da ita kuma maryam zata gyara maths kawai mum yi recieting cikin sa'a da mun ci kuma har mun gama registration na shiga aji daya ND 1 mun fara lectures kamar darusan da aka yi mana an kara sosai haka lokaci tashi a yanxu muna tashi biyu na rana amma duk da haka ban daina zuwa studio ba soyyarmu da salisu a halina yanzu tayi nisa dan har gidan mu yana zuwa tun ina boyewa umman mu waye shi karshe dai dole na fada mata gaskiya al'amari dan a gaskiya bana so na dinga yi mata karya dan ta yarda dani kuma tafi so na dinga fada mata gaskiya a kan ko meye irin yanda salisu yake kula dani yasa na fada a soyyarsa kusan kullum ka'ida ne sai ya yi min waya sau uku a rana zai kira ni da safe kafin na tafi makaranta haka da rana haka da daddare koda kuwa yazo ya tafi ne yakan zo gidan mu sau uku a sati koh hudu tun da zuciyata ta amince da salisu sai na kara tsare kaina koda a wani gurin ne akace ana sona bana bada fuska.


MUHD-ABBA~GANA
www.abbagana.pun.bz
[8:41PM, 11/25/2015] Bana: KAUNA CE SILA 29

MUHD-ABBA~GANA

wata rana ina shirin tafiya gida da yamma sai fiddausi tace dan Allah na raka ta wani studio a kusa da gidan dan asabe nace mata muje mun shiga an bude kofar da take kallo inda nake ashe editing room ne nan naga mai fitowa wani shahararran mawaki ne da duniyar waka take yayin shi a wannan lokacin ya iya waka dan ko nima ina bala'in son wakokin shi amma ba abinda ya ba taba hadamu muna hada ido sai naji wata muguwar faduwar gaba nace masa ina wuni sai ya tsaya yace lafiya ya garin nace lafiya dama littafi ne a hannuna na hausa sai naga ya karba ya duba sunan sai ya miko min yayi ficewarsa yana fita sai naji wani dadi ya rufeni da fiddausi ta fito muka sauko tare nayi gida ita ma ta tafi bayan kamar kwana biyu da muka tashi daga makaranta sai na wuce kasuwar sabon gari dan ina so na siyo man shafawa da kuma takalmi dana gama siyayyata sai na nufi zoo road ina hanya sai naji ana kirana dana daga sai naji wani yace ina nan laila studio kizo kiyi min amshi sai nace ban gane me magana ba sai yace sunana umar a gurin nake sai nace to gani nan ina zuwa zan shiga sai muka yi kicibis da Ahmad shi kuma zai fito sai na dan kauce ya fara wucewa sai naga ya bude baki da alamun mamaki wanda nake tunani dan ya ganni da kaya ne niki niki a hannuna na gaishe shi ya amsa sai yace min zo nan na dan bishi sai yace min kina da number ta sai nace masa bani da ita sai yace to bani wayarki ina mika mishi ya saka min number ni kuwa nayi saving narubuta masa YAYA AHMAD.
MUHD-ABBA~GANA
www.abbagana.pun.bz
[8:47PM, 11/25/2015] Bana: KAUNA CE SILA 30

MUHD-ABBA~GANA
dana koma gida sai bayan sallar isha'i na kira number ya ahmad ta fara ringing kamar baza a daga ba can naji yayi magana sai nace hello yace ina ji wake magana nace nice mamaa sai yace ih mamaa vocal ko ya gida nace masa lafiya yace number ki kenan bara nayi saving nace to muka yi sallama ya kashe wayar shi ya barni ina kallon waya ta ina ta mamakin kaina wai ya ahmad ya sanni kai amma naji dadi wata rana ina zaune a vocal sai ga kiran ya ahmad bayan mun gaisa yace min dan Allah kzo studio da muka hadu ranar zakiyi wa wani yaro amshi dan unguwar mune yana so neya yi waka nace masa to sannan lokacin da naje gurin ban samu ya ahmad ba amma nayi aikin bayan na gama na fito na tafi tun daga wannan lokacin mutunci mai kyau ya shiga tsakaninmu da ya ahmad ina yawan kiran shi a waya mu gaisa mukan dan taba hira shima yana kirana amma yafi kirana da safe wanda yawanci ina makaranta ina matukar jin dadin mutunci da muke yi da ya ahmad dan gaskiya ina jin shi a cikin raina ina daukar shi kamar uwar mu daya uban mu data a wannan shekaranne aka yi hira da ni a gidajen radio har biyu gaskiya a halin yanzu na zama cikakkiyar mawakiya wadda nake alfahari da kaina salisu ma yana nan yana ta kokarin nuna min kulawa dan mutane da dama sun san mu tare duk da bana bashi fuskar muyi hira a gurin aiki ko da mun hadu sai dai mu gaisa yace in sai ya zo gida na ce masa toh.
MUHD-ABBA~GANAwww.abbagana.pun.bz
Share:

KAUNA CE SILA***21---25

kauna-ce-sila.jpg

[1:18PM, 11/24/2015] Bana: KAUNA CE SILA 21MUHD-ABBA~GANA


.

Ga kuma computer da speakers a gabanshi idan yake kall kuma a nan nake yin wakar shima kamar daki amma an raba shi da glass idan kika shige to kofa kika rufe za a dinga kallonki ta glass din nan a ciki dai akwai micro phone da kuma earpeace da shi zaki wakakarki ina nan ina ta dube dube sai naji ifan yana cewa wai shima dan kamfanin ne to yanzu zata fara ne? kafin ya bada amsa naji gabana ya fadi yace E mana tunda dama ita take jira ifan yace min shiga ciki na dan zunguri maryam sai tace haba kawai ki shiga kawai na mike na mika mata jakata da wayata na shiga ina shiga ifan yace ki saka abin a kunnenki zakiji abin da za a saka miki nace to duk da gabana yana faduwa amma sai na dake sai naji nura yace min kina jin kida a kunnenko nace masa E H yace to idan kika ji ta fara duk abinda ta fada shi zaki maimaita nace to yace zan nuna miki hannu nace masa to ai kuwa haka akayi sai gashi ko bata ban yi ba ina gamawa sai naga su nata tafawa har da maryam ina fitowa sai naji nura yace ai wallahi kamar ma murjace don gaskiya kin yi kokari nan naji wani farin ciki ya rufeni sai ya kunna kawai sai naji muryata tayi min dadi nacewa maryam kinji muryata tace ai tayi gaskiya murya ki da dadi muna cikin ji sai mama tayo waya gata a kasa sai ifan yace dama ai sai gobe za a cire mana tunda suna da aiki yau da yawa.MUHD-ABBA~GANA
www.abbagana.pun.bz
[1:23PM, 11/24/2015] Bana: KAUNA CE SILA 22MUHD-ABBA~GANA
muka sauko tare muka tafi gida muna ta bawa mama labari ni kuwa baki ya ki rufuwa don kamar mafarki nake jin abina ban shiga gidan su ba dan kawai sauri nake yi naje gida na kai labari ina zuwa kuwa n farw bawa umma labari nan tace ikon Allah lallai to Allah ya taimaka ya sanya alkairi a ciki washegari ni kadai naje a can na same su shi da oga yace naji wakarki tayi dadi ifan ya yi min bayanin komai keta gida ce bana bukatar sai nace zan gana da iyayenki saboda haka kin zama yar kamfaninmu kuma mawakiyarmu ina so ki nutsu ba ruwanki da kowa kuma ki sa a ranki aiki kika zo nace masa na gode da magariba na dawo gida dan dama banje gurin ba saboda go slow har da cd plate dina na waka ta na dawo ina zuwa na hau jona socket ina gwadawa umma shiru tayi ta kasa magana da taji muryata ta cemin yanzu mamaa kece wannan nace wallahi umma nice sai naga umma ta daga hannu sama tace Allah mun gode maka kuma na fuskanci itama tana cikin farin ciki matsananci yau tace ai kuwa babanki yana zuwa zan saka masa ke kuma sai kiyi masa bayani nace to na tashi don yin sallah ina zaune ina cin abinci kiran baba ya same ni na tashi a tsorace naje gaban baba na tsugunna yace min zauna sosai na zauna yace da gaske ke kikayi wannan wakar nace masa E nice yace min ke meyasa kike so kiyi waka nace masa tun ina makaranta nake so kuma baba ana fadakarwa ta hanyar waka ga mamakina sai naji yayi dariya yace shi kenan Allah ya shige mana gaba
MUHD-ABBA~GANAwww.abbagana.pun.bz
[8:00PM, 11/24/2015] Bana: KAUNA CE SILA 23MUHD-ABBA~GANA
amma ina so ki sani zan bar kikiyi waka ne idan har baxa ki bar karatunki ba kuma ko daza ki karatu to ya zama bakya wasa nace insha Allah sai baba yace shikenan ki kula da kanki sosai bana so abinda zai ja mana abin magana sannan ki sani ina da wannan da nake mu amala dasu da yawa wadanda aikinsu ya shafi kamar irin wannan sannan kain san harka irin wannan da ake kira industry basu da sirri duk abin da suke ciki mutan gida suna sani a wani lokacin ana hada musu da sharri saboda haka kiji tsoron Allah kuma ki kama kanki tace masa in Allah ya yarda yace tashi kije nace na gode baba da safe muna karyawa umma tace min mamaa nace ma'an tace bani hankalinki na kalli inda take zauna tace min dan Allah kar ki bani kunya wallahi na yarda da ke fiye da zatonki na san mun yi miki tarbiyya daidai gwargwado amma a hakikanin gaskiya nutsuwarki daga Allah ne ina yi masa godiya ki kula da kanki kar ki sake hali ba ruwanki da samari iri na gurin dan nasan baza ki iya fada ba dama ba abin so bane kin san yanda muke jin labari mata suna fada akan samari nace mata insha Allahu umma ba zan yi saurayi ba har in bar waka (hmmm ashe zaki tsufa a gidan ubanki) tace to kiji tsoron Allah ki bawa duk wanda ya girmeki girma ki zauna da kowa lafiya nace zan kiyaye tace Allah yayi miki albarka ya tsareki ya sa ki fara a sa'a nace amin ina murmushi har wannan satin ya kare ban koma zoo road ba amma kullum sai na ji waka a kuma duk wanda ya zo gidanmu dan unguwa
ko dan uwa sai na saka masa yaji ranar litinin da misalin karfe tara na safe na shiga makaranta ina shiga na hadu da wani dan unguwar mu jamilu yace min kin gama komaine nace masa eh amma ban saan department din printing ba yace nan aka kaiki nace masa E yace zo muje ai kin fita daga gate din nan su anex suke lectures nace muje dan Allah ka nuna min ajin yace to tafiyar ba wata mai nisa bace tsakanin gate din biyu titi ne dai ya rabasu muna zuwa ya nuna min kofar aji yace nan ne nace masa na gode ya juya ni kuma na shiga aji ina dan dari dari dan ban san kowa ba ina karasawa wajen zama sai na zauna a layi na biyu a kan wata kujera ina zama naga wata tazo ta zauna a kusa dani da alamar tashi tayi ta dawo sai tace min sannu nayi mata murmushi nace yauwa tace kema nan aka kawo ki nace E tace sunanki fa nace mata mamaa tace ni sunana husba ismail muhammad nace mata anan zamu dinga daukan lectures ne sai tayi dariya tace baki taba zuwa ba koh? tace ai har an fara ga time table ma ta nuna min nan tayi min bayanin abin da ban gane ba muna cikin haka sai ga wata itama ta shigo amma da alamar sun san juna don naji tace maryam har kin dawo tace na dawo

MUHD-ABBA~GANA
www.abbagana.pun.bz
[8:02PM, 11/24/2015] Bana: KAUNA CE SILA 24MUHD-ABBA~GANAsai naji tana gabatar mata da ni cewa yau na fara zuwa aji ta miko min hannu tace welcome nace mats tank u ina jinsu suna ta hira sauran yan aji ma kowa yana ta hada hadarsa sai dai na lura duk yan ajinmu maza ne mu matan bamu fi biyar ba bayan mu na hango wata a bayanmu tana karatu a gabanmu kuma da daya wadda daga gani ba musulms bace kuma zata girme mu ina ganin wannan dalilin ne ma yasa banga alamar wasa a tattare da ita ba sha biyu da rabi muka tashi daga makaranta tare da husna muka fito wani abin mamaki kusan tsayinmu daya da ita haka yanayin jikinmu har kusan kamanni ni dai ban ce mata komai ba har ta hau mashin tayi gida ni kuma na hau nace a kaini zoo road a daidai kasan vocal na sauka na hau sama ina shiga nayi sallama ban dade da zama ba sai ga wata mawakiya mai suna hasiya yanda naji yan gurin suna mata magana nasan ba bakuwa bace na bude baki zan mata magana sai naga ta harareni duk da haka na gaisheta ta amsa da kyar ina ji an fara kiran sallah azahar na cewa ifan zan tafi gida tace tun yanxu nace daga makaranta nake kawai biyowa nayi yace min to ya rakani har ya tsallakar dani sai da yaga na hau mashin sannan ya juya dana koma gida ban bawa umma labari abin da a kai a zoo road ba amma nace mata na biya, washegari tun takwas saura na bar gida ban wuce makaranta ba har sai da takwas ta wuce da minti goma ina zuwa kuwa na tarar da malami a aji ana lecture yana koyar da chemistry na shiga na samu guri na zauna dan ko motsi baka ji a ajin ina zama na bude jakata na dauko dan memo na fara jotin abin da yake cewa sai na fahimci kusan duka abin da muka yi a farkone sai de kamar wannan a bude shi sosai.


MUHD-ABBA~GANAwww.abbagana.pun.bz
[9:41PM, 11/24/2015] Bana: KAUNA CE SILA 25


MUHD-ABBA~GANAmalamin da ya shigo na karshe ne har zai fita sai ya ce to tunda an baku time table kuma kowa ya san numbern shi da ajin shi gashi har an fara lectures sosai daga yau ko wanne dalibi takwas ta zama kana aji don idan mallami ya riga ka zuwa ba zaka shiga aji ba sannan attendance yana da matukar amfani kuma muyi karatu yan ajin suka amsa da cewa to muna fitowa bakin aji wayata ta fara kara ina dubawa naga ifan yace kina ina ne? nace ina makaranta amma mun tashi yace yaywa zo kiyi wa wani amshi nace masa to gani nan mun rabu yau mada husna a bakin gate kamar jiya dan ita maryam ba da ita muka fito ba wai tana jiran wata yar uwarta yanda husna ta fada min
dana shiga sai na tarar da mutumin yana ciki yana wakar gaskiya ban sanshi bada alama dai bako ne yazo yin waka dan wakar siyasa ce da ya fito sai na shiga aka saka min na fara bin yanda yayi da farko banyi daidai ba sai aka kara saka min a nan buyun sai nayi daidai dana gama na fito na zauna nan aka fara gyara masa dan a daidai ta masa da kida muna zaune sai wata ta shigo ita ma daga gani anan take sun gaigaisa ita ma dai naga ko kallo ban isheta ba mai wakar ne naji yana magana da ifan wai ashe tam baya yake wa zai bawa kudin aikin ni ko shi sai naji yace mamaa karbi kudin hannunshi dana fito zan tafi sai na cewa ifan ba ka karbi kudin ba sai yace ai nakine nace to ka raba mana yace a'a kar kiji komai dana je gida yau ma duk abin da ya faru sai dana kai labari tun daga wannan
rana dai kusan kullum sai naje studio don ina barin makaranta nake wucewa wata rana naxo kamar daya saura na rana ban dade da zama ba aka kira sallar azahar sai nace wa ifan ina zanyi salla sai yace na shiga daya shagon wanda daga vocal sai shi ina shiga naga wata tana zaune a kujera na gausheta ta amsa nace Dan Allah sallah zanyi tace zoki shiga nan ta bude bandaki na shiga nayi alwala sai naji tana cewa idan kin fito ga sallaya nan kiyi a nan ina fitowa naga har ta shimfida bayan na idar sai naga ta shigo tace min ashe ke ce sabuwar mawakiyar vocal koh? nace mata E tace ni sunana zainab barkanki da zuwa nace na gode tace min bara nayi salla sai muje mu ci abinci
nace mata to bayan ta idar ta re muka jera har gurin abinchi wani restaurant da yake kallon benen da muke wato shab'an bayan mun fito muka koma nan muka hau hira har da su kwatancen gidajen juna ashe ita ma waka take yi amma ba guri daya muke ba zan iya cewa duk matan dana fara haduwa da su ita kadai ce ta karbe ni hannu biyu a farkon ganintada ni xan iya cewa a wata daya zuwa biyu na gama gane industry dan na fuskanci ita ma kamar makaranta ce daan akwai bangare bangare kuma ko ina da mawaka maza da mata haka duk studio akwai makada ko makidi haka kawai yaran studio masu kuma aiki daban daban zainab tana daya daga cikin wa yanda suka nuna min gurare don a mafiya lokuta muna zaune idan aka kira ta aka ce to zo tayi amshi sai tace dan Allah naxo na rakata to kusan a haka nasan wasu guraren da studios din.MUHD-ABBA~GANA
www.abbagana.pun.bz
Share:

Monday 23 November 2015

KAUNA CE SILA***16----20

kauna-ce-sila.jpg

[11/22, 2:34 PM] Ábbä~Gåñā: KAUNA CE SILA 16


MUHD-ABBA~GANA

da muka saba sai naje gurin ummanmu na zauna nace umma kin san meye? tace sai kin fada sai kuma na kwashe da dariya sai tace amma kin fiye shirme to ki fada min mana meye sai nace mata ina zuwa sai na nufi daki ba dan nayi komai a daki ba sai akuma na fito nace mata hmm! umma waka zan fara tace ban gane ba nace mata waka dai irin wadda kike ji a radio sai tace haba mamaa sai kace wasan yara kin san kuwa me kike cewa? nace Allah umma ba wasa nake ba nan dai na bata labarin komai tun daga ranar dana fara fadawa maryam har zuwa yau tace to ni dai ba abinda zance sai nace Allah ya zaba abinda yafi alkairi Allah shi kadai yasan dai dai.naji dadin bayanin umma kuma gaskiya ta kara min karfin gwiwa sosai hudu da minti goma daidai ina gidan su maryam muna ta hira ina ta duba lokaci dan a kule nake da doki biyar daidai ifan ya kira maryam gashi a kofar gida tace to tare muka fita muka gaisheshi ya amsa maryam ta kawo kujeru muka zauna aka kawo wa ifan lemwo sai yace min da gaske kike kina so kiyi waka sai nace dashi eh har zuciyata ina so sai yace amna fa kin san waka dalilin yinta suna da yawa zaki iya fada min daya daga ciki sai nace masa ra'ayi sai yayi dariya yace har da wannan ma amma kara tuno wani nayi shuru alamar tunani can nace masa eh fadakarwa sai yace yawwa kinga yanzu kika dauki hanya to amma kina ganin zaki iya fadakar da mutane ta hanyar waka"


MUHD-ABBA~GANA


www.abbagana.pun.bz
[11/22, 7:43 PM] Ábbä~Gåñā: KAUNA CE SILA 17


MUHD-ABBA~GANAsai nace masa eh zan iya sai yace to shikenan yanzu bani number ki sannan kiyi min kwatancen gidan ku nace masa toh yace yanzu yamma tayi amma zan kira ki na zo gidanku kamar jibi haka nace masa na gode ina jira dana koma gida sai na bawa umma labarin duk abin da ya faru yau sai naga kawai ta yid ariya da alamun dai umma bata gamsu ba tana ganin kawai shirme nakeyi bayan kwana uku da rabuwar mu da ifan sai ga kiranshi bayan magariba wai aina fita na tarar dashi har ya samarwa kanshi gurin zama a dakalin makwabtanmu nayi sallama sai ya amsa tare da fara'a yace yauwaa yau fa zaki fara daukan karatu nace masa kai yace da fatan kin shirya nace masa eh sai naga ya zaro farar takarda da biro daga aljuhunsa ni abin ma sai ya bani dariya sai kawai na basar kar ya gane nace masa lallai kuwa kamar karatu yace aike wasa kika dauka nace a'a ni din wa ai kuwa kamar karatu haka muke yi ni da ifan don yana biyawa ina yi nima har yaji na rike yace kin yi kokari ya kuma ce kin san sunar wakan nace a'a yace sunansa (langar fasi) sai nace me kenan ban taba jiba sai yace yana nufin langar da ake yayi nace oh na nage sai naga ya mike yace bara na tashi na tafi sai da safe ki tafi da takardar nan kiyi tayi kafin na dawo ki iya sosai nace masa toh Insha Allah dana shiga na bawa umma labari na kuma nuna mata sai naga ta kalleni....
MUHD-ABBA~GANA
www.abbagana.pun.bz
[11/23, 8:09 AM]abbä~Gåñā: KAUNA CE SILA 18MUHD-ABBA~GANA
kawai da alamu dai har yanzu umma bata gamsu da abin da nake yi ba ta dauki abun wasa ko yaushe ka gannni da takarda a hannu na ni a dole na samu abun yi in har ba aiki nake yi ba to kuwa zaka ganni da takarda ta a hannu ko idan zan yi sallah,dan abinci ma baya hanani nazarin waka ta kuma wani ikon Allah sai gashi na iya sosai har na rike ko ba takar da zan iya yi maka bayan kamar sati daya ifan ya dawo gidan mu ya tambayeni na iya nace masa eh yace to na rerra masa yaji nnan na hau rere waka kamar karatu yace excellent gaskiya kin yi kokkari amma yanzu tunda a n rubuta ta gaba daya zan je studio ayi kidan ta sai nayi tare da wata mawakiya idan muka yi sai na kawo miki kiyi taji idan kika iya sai muje kiyi irin yanda tayi nace masa toh yace dan kar ki sha wahala ne nace masa to na gode yace ba dammuwa a wannan watan ne kumma aka kafe sunayen mu nasamu amisssion a makaranta zamu fara registration na gama cikin sauki aka bani printing technologgy zan fara daga pre nd na yiwa Allah godiya duk da ban san cos din ba sai da naga an kafe ni a can amma nace zan yi don ina zaton hakan shine alkahairi da nake roko na samu rabuwar mu da ifan zai yi kamar sati daya sai gashi a gidanmu da wata yamma duk da garin ana zafi amma garin ba kowa ba kuma hayaniya a yanzu ifan ya zama dan gida dan har ciki yake shiga ya zama kamar dan uwan mu na jini bayan an gaigaisa ne sai ya ce min ga CD plate din wakar ki mun rera tare da murja baba sai nace au waka tace ma? sai yace r
eh mana na karba ina ta murna sai yace shi zakiyi taji har sai kin iya duk yanda tayi"MUHD-ABBA~GANA
www.abbagana.pun.bz
[11/23, 8:17 AM] Ábbä~Gåñā: KAUNA CE SILA 19

MUHD-ABBA~GANA

nace masa toh da zai tafine naji umma nace masa abin nan kuwa da gaske ne yaushe mamaa zata iya waka yace umma zata iya dan gaskiya tana da kokari da sa kai kiyi mata addu a kawai tace to mun gode washegari na nufi gidan su maryam ina ta murna na nuna matw CD tace ai kuwa yanzu zamu ji muka kunna cd muka fara ji nan na nutsu burina kawai naji duk yanda take karyar da muryar ta nima na yi irin haka sai dab da magariba na baro gidan su maryam haka dai na ci gaba da jin wakar nan dan kullum ina aiki ma aina ji har na haddace bayan kamar sati guda na kira ifan nace to na haddace yace to shi kenan yau wace rana nace masa yau litinin
yace to ranar laraba da yamma ki zo tare da maryam sai ki doro wakarki ki fadawa umma sai ku zo zoo road idan ku kazo sai kiyi kuna fitowa zaku yi min waya ina wani studio local sound studio yana kallon junction din cort road nace masa kace naxo nayi waka cikin wata irin rudewa yace eh nan na daka wani tsalle na ce masa Allah ya kaimu na fadawa umma sannan na kira maryam na fada mata. 27/02/.... wannan ranar ta laraba ta kasance mai dinbin tarihi a tattare da ni domin a ranar ne na fara waka kuma tana daga cikin ranakun da bazan taba mantawa ba har abada.
MUHD-ABBA~GANA
www.abbagana.pun.bz
[11/23, 8:18 AM] Ábbä~Gåñā KAUNA CE SILA 20

MUHD-ABBA~GANA

karfe hudu na shiga gudan su maryam na same ta har ta shirya nace mata to taho mu tafi sai tace min mama zata je sharada tace zata ajiye mu a zoo road din idain ta dawo sai ta dauko mu nace kai amma naji dadi muna haka sai naji muryar mama tana kwalawa maryam kira na bita nima dan na gaisheta ta amsa tace a'a mawaka har kin kararo nace eh tace to zo muje muka fito ina rike da jakar mama,maryam ta shiga gaba na zauna a baya mama tace min mamaa ta ya zance karatunki fah sai nace sai wani sati zan fara zuwa na gama komai tace to ai yafi kar kice kuma karatun ba za ki ba shi mahimmanci ba nace tab! ai ba zan soma ba mama muna hawa kan titi zok road nayi wa ifan waya yace bara ya fito bakin gurin a daidai gurin mama ta ajiye mu amma ba ta tafi basai da ta ga ifan ya sauko daga beben har suka gaisa sannan ta tafi da muka shiga studio sai ya fara nuna mana yan gurin inda ya fara nuna mana mai gurin sunansa muhammad bello muka gaishe shi yace ku kannen ifan ne kuma ifan dan uwana ne shi yasa ba zan matsa da bincike ba nan dai yayi ta nuna mu yana gabatar da mu har muka isa dakin da ake wakar annan na sha kallo na kuma zama yar kauye dan ban taba zata haka zanga abin ba gaskiya da mutum ya ga irin kayan aikin su yasan abin ba na wasa bane banda inda muka fara zama nan ma da wani studio na farko kuma duk iri daya ne amma muna biyun muka wuce fasalin dakin ne kamar ciki da falo anan na farko wato engineering room akwai kujera kamar uku har da ta wanda zaka zauna a kan computer wanda shine zai dauki recording.
MUHD-ABBA~GANAwww.abbagana.pun.bz
Share:

Sunday 22 November 2015

KAUNA CE SILA***12---15

kauna-ce-sila.jpg

[9:36AM, 11/22/2015] Bana: KAUNA CE SILA 12MUHD-ABBA~GANA

dan shiga gida na rasa me yake min dadi gashi dai ba son jibrin nake ba amma a hakikanin gaskiya ban ji dadin irin sallamar daya zo ya min ba duk da nasan ba laifinsa bane mahaifina ne bai amince dashi ba ina kwance har aka kira sallan magariba ina ta tunani iri iri na tashi nayi alwala dan yin sallah ina idar da salla sai na tsinci kaina da addu'ar Allah yasa haka shine mafi alhairi kuma wai sai gani ina hawaye ina addu'a a ban san kukan me nakeyi ba abin dai dana sani ko bana son jibrin mun saba dan shi kuma yana nuna kulawarsa a kaina wani ikon Allah tun daga wannan ranar na manta da al'amarin jibrin na ci gaba da harkar gabana duk da nakan ji abin da yake ciki kamar ranar daya kai kudi da ranar da aka sa masa rana da sauransu MAMAA nidai sunana sa'adatu i muhammad an haifnine a tarauni kkuma nayi primary school dina a nan tarauni na fara karatuna na secondary a unity college kachako bayan nayi shekara uku na zana jarabawar science na tafi girks science college garko na karasa inda na gama a can matan mahaifina biyu ummanmu ce ta farko sai antinmmu amma ba gida daya suke ba( dan gudun barna) ummanmu tana tarauni kishiyar ta kuma tana kundila mahaifiyata mu biyu ta haifa daga ni sai kanina abubakar sadiq ita kuma kishiyar ummmanmu tana da yar uku salima,salim da salis anfi sanina da mamaa dan da shi ake kirana saboda sunan mahaifiyar babbanmu aka saka min niba baka bace ba zan kuma saka kaina a layin farare ba amma ni nasan kala ta tana da kyau dan gaskiya irin chocolate colour din nan ce dukk man da na shafa sai dai yasa na yi kyau dan bana amfani da mayukan kara fari don bana son abinda zai bata min fiska balle ma rayuwata.MUHD-ABBA~GANAwww.abbagana.pun.bzKAUNA CE SILA 13


MUHD-ABBA~GANAdan bani da kuraje ko kadan a fuskata baza a kira ni kyakkyawa ba amma ina da shi daidai nawa ina da diri bani da tsayi amma ina da jiki ba can ba na iya kwalliya dan duk kayan da na saka sai ance nayi kyau ina da fara'a da yawan wasa da dariya ina da idanu masu kyau da daukar hankali dan na sha jin mutane suna fadin cewa irin idanuna ne ake cewa sexy eyes wasu kuma sunce na iya kallo na sanya nutsuwa to ni dai abin da na sani nima na yarda idanu na suna da kyau, ina da matukar hakuri amma ina da saurin fushi da kuma saurin sauka don ana yi min abu zan nuna bacin raina amma dana nuna ya wuce don bani da riko ba kuma na iya boye abu a zuciyata ba kuma ni da rufi ina kuma da saurin sabo da saurin yarda da mutum wannan kenan.


haka muka cigaba da rayuwa cikin farin ciki da nishadi har sakamakon mu ya fito yayi kyau ba laifi anabln muka siyi forms maryam ta sayi legal ni kuma babanmu ya kawi min na kano state polytechnic haka muka cike muka mayar muka zauna jiran admissiion a haka dai kusan kullum muna tare da maryam ko dai a gidani su ko a gidanmu maryam tana da samari sosai amma tafi son wani dan film din hausa mai suna sani tana matukar sonshi shima yana nuna mata kauna don kusan kullum in dai yana gari to sai yazo wani lokaci tare suke zuwa gidanmu muyi hira tare nima samari su kan ce suna sona amma tunda na rabu da jibrin hankalina duk ya bar zauce su yanzu nafi tunanin karatu dan shine a gabana wata rana muna zaune a dakin maryam muna ta hira sai nace mata kin san meye? tace a'a nace nifa waka nake so na fara tace kamar ya? nace waka dai ta film da kika sani.MUHD-ABBA~GANAwww.abbagana.pun.bz


KAUNA CE SILA 14

MUHD-ABBA~GANAtace ke mamaa dan kina dan yin waka a makaranta shine kike ganin zaki iya to wai ma yaza kiyi da karatun naki baba ma zai barki ne nace mata ai addu a nake kuma duk hadawa zan yi tace lallai abin naki babba ne nace mata ni dai malama idan zaki hadani da sani yayi min hanya to tace ba damuwa idan yazo zamuyi magana nace da kin kyauta muka yi dariya na tashi na ce mata zan tafi tace to ta rakani na hau mashin na nufi gida a wannan ranar da daddare bayan sallar isha i muna zaune a tsakar gida sai naji sallamar maryam ta shigo suka gaisa da ummanmu sai naja ta daki nace ya aka yine? tace uhum kya sani dai yana mota yana jiranki kije yayi miki interview nace kai na zaro idanu sai naga tana dariya tace au kin fasa zama mawakiyanne? nace to shi ne har da wani interview kamar wani akin gwamnati ko aikin kudi tace lallai yarinya wasa kikeyi nace mata ni dai gaskiya ba zanje ba tace ke wasa nake mamaa Allah na fada masa shine yace muje ya ji dai daga bakinki nace to muje amma fa gabana faduwa yake kuma maryam ta gane duk da ban fada mata ba a mota muka same shi yana ta danna waya yana ganinmu ya ajiye nace masa ina wuni yace lafiya hajiya mamaa ya hutu nace hutu sai ku.MUHD-ABBA~GANA


www.abbagana.pun.bz
[9:41AM, 11/22/2015] Bana: KAUNA CE SILA 15


MUHD-ABBA~GANAyayi yar dariya yace to mun gode Allah kawarki tace min kina so ki fara waka haka ne? nayi shuru maryam tace shiru ko ba haka bane? nace haka ne cikin wata murya mai nuna akwai tsoro a tare da ni yace toke me yasa kike so ki fara waka? nace kawai ina so don ni mawaka suna burgeni ina so naji ina son wakokin su yace to shikenan niba harka taba ce duk da kusan duk daya ne amma kanina yana yi sosai xan hada ku zakiyi insha Allah komai zai zo miki da sauki nace masa to na gode yace ba damuwa ai ke babbar kawarmuce ya kalli maryam da yana yin tsokananta maryam tace bara mu tafi za ki ji ni a waya nace mata sai da safe ki gaida mama tace zataji suka juya suka tafi duk abin nan da ake ciki ba wanda ya san halin da nake ciki daga ni sai maryam munyi kamar kwana biyu bamu hadu ba kuma ba muyi waya ba ranar wata juma'a sai ta kirani a waya tace to ki shirya dan ifan yace yaushe kike da lokaci da zai fara koya miki waka sai nace ni ai ko yaushe sai tace to shikenan tunda gobe asabar ba aiki zance masa ku hadu a gidan mu da yamma amma fa ki zo da wuri kar ya riga ki zuwa nace mata to ina kashe wayar sai naji wani nishadi da karfi yazo min kawai sai nake ganin ai kamar ma na riga na iya.da safe na tashi naji ni ina ta jin dadi bayan mun gama komai na al'adar gida da......
MUHD-ABBA~GANA


www.abbagana.pun.bz
Share:

KAUNA CE SILA***8---11

kauna-ce-sila.jpg

[9:33PM, 11/21/2015] Bana: KAUNA CE SILA 8
MUHD-ABBA~GANAyace wayyo baba ya rigani Allah ya sani abin da nake ta shirin hada miki kenan amma ba komai Allah ya biya baba nace ameen muka dan taba hira ya tambayeni yaushe zan dawo nace ba zan wuce sati daya ba yace min to bara ya tafi dama da zanyi tafiyane yau ya zo ya mikomin wani abu kamar wasika a envelope ya bani kudi ne shiyasa ma ban karba ba nace wallahi ba zan karba ba ka kuma san muhimmancin rantsuwa yace shi kenan amma ranshi baiso ba ban samu damar zuwa yiwa maryam sallama ba dan abubuwa da dama ne suka sha mim kai ranar lahadi baba na ya daukeni zuwa tashar unguwa uku don sakani motar jos muna isa babanmu ya nemi motar jos aka ce masa saura mutum uku ya ce a'a yarinyace ita kadai zata hau naga dai yaron motar yana yiwa babana bayani ban san ya sukayi ba sai ganinsa nayi ya kinkimi jakata ya saka a bayan mota baba yace to mamaa shiga Allah ya tsare nace ameen kujera tsakiya na nufa amma ina jikin window ina shiga wani matashi ya shigo ya zauna a kusa da ni ina yan addu'oi na sai naji mota na kokarin tashi nan na zaro wayata na kira maryam nace afuwan kawa wallahi gani a tasha har mota zata tashi tace lallai! mamaa sallamar kenan to Allah ya tsare zan kira ki idan kuna hanya nace mata ameen sai kin kira kamar jira yake shima jibrin ina aje wayar maryam kiranshi yana shigowa muka dan taba hira nace mun fara tafiya ya ce Allah ya kiyaye bara ya bari sai mun sauka nace to tafiyace mai nisa tsakanin kano da jos ni dai tun ina ganin dajuka da bishiyu da kayuka masu abin sha'awa har bacci ya kwasheni.


MUHD-ABBA~GANAwww.abbagana.pun.bz
[9:42PM, 11/21/2015] Bana: KAUNA CE SILA 9
MUHD-ABBA~GANA

kawai na kifa kaina a cinya ta na fara bacci ban tashi farkawa ba sai dai naji magana a sauting windon da nake ina dasowa sai naga soja gabana ya fadi naji yana cewa driver go ashe wai dajin falgore muka zo sai kuma na nemo wayata don duba lokaci nan naga missed call shuda biyu na maryam ne daya kuma na baba na sauran ukun na umma na yayar ummanmu da zan je wajenta na fara kiranta nace bacci nake yi kuma wayar a silent take tace to sai munkaraso haka na kira baba na shima dai hakan nace masa maryam ce ban kira ba nace idan na sauka na kirata kawai,mun shiga garin jos wajen misalin biyu na rana gaskiya tsari da baiwa da ni ima da Allah ya bawa garin jos ta birge ni matuka don muna shiga na fara karantar garin kamar ba musu rana ko ina lumshe alamar koyaushe ruwa zai iya zuba a rashar ba wani park aka sauke mu gaba dayanmu ina sauka na fara neman layin yayar ummanmu nace mata hajiya mun sauka tace toh bara na aiko a xoba tafi dake nace la hajiya barna na nemi mashin ya kaini tunda ina da kwatancen tace zaki iya kuwa nace ba damuwa hajiya ina so na kalli garine tace to Allah ya kiyaye nan na nemi mai mashin nace masa dan Allah mallam babban masallacin juma'a zaka kaini wajen yan dankali yace ba damuwa hau muje ya dora jakata a gaban mashin din muka dauki hanya mun kusa karasawa yace min wane layi zakije nace masa yan dankali muna zuwa ya ajiye ni na bashi kudinsa nace masa na gode.

MUHD-ABBA~GANA


www.abbagana.pun.bz
[9:54PM, 11/21/2015] Bana: KAUNA CE SILA 10


MUHD-ABBA~GANA


ya juya na fara turo jakata sai naga wani dan saurayi nace masa sannu don Allah buzu street nake nema yace min ai gaki a ciki nace gidan su wani wai mustafa yace yan kano ko nace E yace gidan can no 4&10 nan ne gidan nace masa na gode ya wuce ya barni ina jan jakata har gate din gidan yayar ummanmu ina tura gate din gidan muka hada ido da hajiya tana zaune a kan kujera tana daddana waya tace min ke nake shirin kira nayi murnushi nace mata ai ba wahala tace to mu karasa sannun ki kinsha hanya masha Allah sannu sannu ta nuna min dakin anty ummalkhairi tace shiga nan dakin ina umma ki watsa ruwa kiyi salla ga abincinki can nace mata to na shiga bandaki dan watsa ruwa da alwala tunda naje garin jos kusan kullum kuma koyaushe sai jibrin ya kirani a waya mukan dade muna hira kuma yana kara jaddadamin niyyarshi da nuna min shifa ya shirya so yake kawai ya fito neman aurena idan ya fada na kan ce masa to kawai don gaskiya dai ba zan ce bana sonshi ba amma bana jin abin a raina gaakiya naji dadin zaman garin jos mun zaga gurare da dama na shakata mun sha yawo har da kasuwanninsu munje mun je one life parki refil resorced a mixeed park kullum idan muka je tun hudu sai da magariba muke dawowa dani da aunty ummulkahiri muka fi fita wani lokacin kuma daya mustafa.


MUHD-ABBA~GANA

www.abbagana.pun.bz
[9:12AM, 11/22/2015] Bana: KAUNA CE SILA 11


MUHD-ABBA~GANA

sati na biyu na dawo kano tare da kewar su tsarahata ta abin da yafi burgeni a garin kusan kullum sai anyi ruwa kuma dan yayyafi baya hana mutane yin hada hadarsu tayau da kullum tunda na dawo kusan kullum sai naje gidan su maryam idan na gama duk aikin gidanmu sai kawai na tafi gidan su muyi ta hira a wanan lokacin ne kuma jibril ya matsa min da maganar shifa fitowa zai yi nace masa to amma kabari na fadawa umman mu ni dai bazan ce ga abinda ya faru ba sai jin zuwan yan gidan su jibrin nayi wai sun zo ana tambayan babanmu shiko babanmu yace bai san da zancen ba dan shi gaskiya ba aure zaiyi min yanxu ba har sai yaga na fara karatu yan gidansu sukace to shikenan bayan kwana biyu sai nafara ji a unguwa ana cewa wai mahaifiyar jibrin ta ce aini ba yar gwal bace saboda haka ya nemi wata,ita dama baso take ba ni dai bai fada min ba amma ya rage zuwa nima kuma ban damu ba.
ranar wata lahadi da misalin karfe biyu na yamma yai min waya wai dan Allah yana son ganina gashi a kofar gidanmu nace to ganni zuwa na nemi hijabina na saka na fita na sameshi bayan mun gaisa sai na fuskanci kamar ranshi a bace yake nace masa lafiya yace dama zuwa nayi na miki sallama na samu wata yarinya a kofar nassarawa zan aura dan gaskiya ni aurre nake son yi nace masa toh Allah yasa haka shine mafi alhairi yace amin amma ki sani ban taba son wata ya mace kamar ke ba kuma na san har na koma ga Allah bazan samu ba nace masa na sani bara na shiga gida' yace min sai anjima nace to,


MUHD-ABBA~GANAwww.abbagana.pun.bz
Share:

KAUNA CE SILA***6--7

kauna-ce-sila.jpg

KAUNA CE SILA 6


MUHD-ABBA~GANA
yafa mayafi purple na sake bakin takalmi dama ni bana saka plat sai mai tudu ko don bani da tsayi ne sosai amma dai irin takalma na kenan dana fito nacewa umma ni zan tafi tace to ki gaida mama marayam da maryam din amma kar ki kai magariba don Allah gidan su maryam na nufa na shiga da sallama na ganta a tsakar gida tana karatun littafin hausa nace mata har an fara ta tareni da dariya muka shiga falon su muka zauna t kawo min ruwa na sha muka fara hira tace bari ta zubo min abinci nace mata ai a koshe nake don yau ko abincin dare ma bana jin zanci tayi dariya nace mata yana ji gidan shiru tace min duk sun tafi kamu wata yar uwarmu ni suka bari da girkin dare nace ai gara da na sameki na mika mata wayata ta fara daddannawa tana murna tace yauwa ai yanzu kin zama babba ta dauko wayarta ta saka number ta ta kira naga tana yin sarving anan ne nake bata labarin yanda muka yi da jibrin tace toko shi ya sai miki nace a'a ubana ne tayi dariya tace iyye ashe mun kusa shan biki nace dawa din? nifa bana sonshi tace meyasa? nace nifa kinsan nafi son dan gayu kuma mai ilimi tace au shi ba gaye bane? nace gaskiya ba sosai ba muka tafa tare muna dariya munyi hira sosai da maryam wadda rabi ta samarice har take cemin ina fa wallahi duk tafi son wanda yake wasan hausa nace mata to Allah ya taimaka


MUHD-ABBA~GANA

09039016969

www.abbagana.pun.bz

KAUNA CE SILA 7

MUHD-ABBA~GANA
bayan ta rako min nake fada mata cewa zanje jos gurin yayar ummanmu amma kafin na tafi zanzo muyi sallama tace to zata kira nima nace mata to tace dan Allah ki gaida min umma sosai kafin nazo tace to ranar ne da daddare ummi take fada min babnmu yace na shirya ranar lahadi na tafi jos din nace mata to ina murna,bayan sallar ishai yaro ya shigo yace wai jibrin yana kirana haka naje kmar yanda na saba fuska taba yabo ba fallasa na zauna tare da sallama bayan mun gaisa na dan daure fuska nace jibrin ashe dama kaya ka kawo min har kala uku to gaskiya ni bna so kawai sai ka hau kawo min kayan sakawa yayi yan dariya yace haba mamaa nifa nake fatan zama mijinki idan nayi miki ai kaina nayiwa ko? nace masa eh duk da haka dai yace tro amma fa a min afuwa nace shikenan washegari na fito zanje wanki kawai sai muka hadu da jibrin sai na dan sunkuyar da kai na kasa nace masa ina wuni yace lafiya ina zak haka nace saloon yace muje na rakaki nace a'a ka barshi na gode yace shikenan har ya dan yi gaba sai nace masa au gobe zanyi tafiya zan je jos gurin yayar mamanmu yace amma shine ba ki fada min ba nace kayi hakuri na manta yace ba komai sai nazo da daddare nace to da daddare yazo kamar yanda ya saba haka na karasa na zauna muka gaisa nace masa ga number ta.


MUHD-ABBA~GANA

09039016969


www.abbagana.pun.bz
Share:

Friday 20 November 2015

KAUNA CE SILA*** 4---5

kauna-ce-sila.jpg

[8:26AM, 11/21/2015] Bana: KAUNA CE SILA 4
MUHD-ABBA~GANAbayan taci abinci tayi sallah na fada mata ina so don Allah naje gidan yayarta nayi kamar sati daya Zan gaishesu na kuma fada musu na gama lafiya tace to bakomai bayan kwana biyu da dawowar mu mahaifinmu ya dawo ya sauka a gidan mun yi murna sosai daganina sannnan shima yayi min nasiha mai ratsa jini.lokacin ne ma yake fadamin cewa dama y ahanani sauraran samari ce don ban kammala karatuna ba amma yanzu ina da dama kula duk wanda nake so amma ba hakan yana nufin na kawo masa kare da doki gida ba na kula sosai don nasan halin shi ya kuma cewa sakamakon ku yana fitowa zan nemar miki gurbin karatu sai ki zama cikin shiri nace to na gode har na tashi zan tafi sai yace ga wannnan naki ne na karba ina godiya ina shiga daki na bude sai naga wani kwali mai kyau karami ashe waya ce mai kyau kirar panasonic gaskiya wayar tana da kyau sannnan da layi n glo na bude ina ta murna umma tace lalle to an gode sai ayi mata caji tukunna koh nace to bakina yaki rufuwa dan murna wai nice da waya yau a wannnan ranar ne mauna zaune nida umma a tsakar gida muna hira naji sallamar wani yaro dan makotanmu yana cewa wai ana sallama da mamaa nace inji ea kuma sai yace jibirne nace wa umma kai da alamar ban ji dadin kirana ba sai umma tace tashi kije ai gaisawa zaku yi na tashi don nemo mayafin kayan jikina jibrin wani dan layinmune daya dade yana cewa yana sona tun ina makaranata na sha ji ana fada idan nazo hutu a bacin yan unguwa wai yana cewa ni zai aura ni dai sai dai nayi murmushi yau ya kai yi min kwanta idan yaga ina siyen abu a...
MUHD-ABBA~GANA


www.abbagana.pun.bz
[8:31AM, 11/21/2015] Bana: KAUNA CE SILA 5
MUHD-ABBA~GANA

Waje ko shago haka bana kawo komai idan nayi la akari da yanda yan layin mu muke zaune kamar uwa daya uba daya na fito na sameshi a kan dakalin makwaftanmu nayi masa sallama ya amsa da fara a yace min mamaa ina wuni nace lafiya daga haka ban sake cewa komai ba yayi dan jan numfashi kadan yace mamaa kamar bakiji dadin zuwana ba ko nace a'a me ka gani yace najiki shiru ne nace to mai zance yayi dariya yace dama nazone na miki murna sannnan na kara jaddada miki ra ayina akan ki gaskiya ina sonki kuma in Allah ya yarda aurenki nake so nayi a take naji gabana ya fadi ba tare da nasan daliliba amma ban bari ya gane ba nace Allah ya mana zabi mafi alhairi yace ameen nace masa kaga hadan kamar ruwan za a fara bara na shiga gida yace min to ga wannnan ya miko min leda nace ka barshi na gode yace wallahi sai kin karba na karba ina masa godiya ina shiga na tarar da umma tana t tattare kaya don har an fara iska da alamu yayyafi na shiga na ajiye na fito ina tayata da safe da muka tashi ranar juma'a ne t fito zata tafi nace mata ga abin da ya bani jiya tace me yasa kika karba? nace wallahi rantsewa yayi tace shi kenan amma gaskiya bana so ki saba da karbar abin samari dan haka hatsair ne babba nace mata to zan kiyaye da yamma nayi wanka nayi kwalliyar juma'a nayi kyau gaskiya sosai don wata atamfa na saka mai ratsin purple a jikina


MUHD-ABBA~GANA


09039016969www.abbagana.pun.bz
Share:

KAUNA CE SILA 1--2--3

kauna-ce-sila.jpg

[10/11, 2:39 PM] Ábbä~Gåñā: KAUNA CE SILA 1

**********NA************MUHD-ABBA~GANA
garin ya kasan ce mai dadi saboda yanayin damuna da muke ciki garin ya yi luf-luf da alamar hadari ga wata iska mai sanyi da take kaduwa ranar laraba ne shida ga watan goma shekara ta dubu biyu da sha biyar wannan ranar ta kasance ranar farin ciki ga daliban mkaaran tar kwana ta kimiyya wato garko don a ranar ne suka kammala karatunsu na secondry wato candy idan ka duba harabar makarantar dalibai ne ko ina sanye da fararen uniform mai ratsin kore suna ta musayar adireshkn gidajensu ne wasu kuma suna tsattsaye yayin da suke jiran a zo a dauke su don zuwa gidajensu a gefe wasu aminnan juna ne a zaune a gindin bishiya darbejiya wato mama da kawarta maryam maryam ta kalli mama tace mamaa nace mata na'amm tace tunda har yanxu mama bata karaso ba rakani shagon hanyar hostel na siyo bread yunwa nake ji nace mata to tare da mikewa mun tashi kenna tana zaro kudi a jakarta na hango motar mama nace mata maryam ga mama nna sai ta juyo da sauri ai kuwa mama ce nna muka karasa cikin sauri da murmushi dauke a fuskarta ta tare mu tace a'a yan mata yan garko to congratulations muka hada baki muka ce mata thank you sanan muka gaishe ta mama ta bude mana boat muka fara zuba kayan mu sanan muka bita ta karbo mana pass a ofisin shugabn makaranta bayan mun fito muka dauki hanyar fita maryam ta shiga gaba nikuma na zauna a baya fitowar mu kennan mun dan hau titi mama ta dan rage tafiya ta fara magana kamar haka:
MUHD-ABBA~GANA
www.abbagana.pun.bz
[10/11, 2:57 PM] Ábbä~Gåña: KAUNA CE SILA 2


MUHD-ABBA~GANATo alhamdullilahi yau kun gama makaranta Allah ya gani mun baku tarbiya daidai gwargwado ina kara jan hankalin ku da ku nutsu ku sanya tsoron Allah a ranku domin yanzu ne zaku fara rayuwa kuma zaku fuskanci kalubale iri iri sannan zaku hadu da kawaye daban daban masu kuma tarbiya daban daban ku kula sosai dan irin mutanen da zakuyi mu'amala Allah ya yi muku albarka mukace ameen a tare nida maryam mama tana kai aya ta karo sautin radio ta mike hanyar kano.tafiya muke tayi cikin nutsuwa da kwarewa amma a hakikanin gaskiya hankalina baya tare dasu ina ta tunanin gaskiyar hankalina baya tare dasu ina ta tunanin maganganun mamaa suna ta min kuwwa a kunne in ta jujjuya su to wani iri kalubale mama take nufi zamu fuskanta kalubale hum a hakan ne ta lura da maryam har bacci ya dauketa mun iso kano misali 1pm daidai mun isa tarauni layin uba yan katsere daura da gidan shakatawa na tarauni wato garden a kofar gidan mama ta ajiye ni yayin da suka wuce gidan su wanda yake a kano bus stop ina shiga gida na tarar da ummanmu ta fito daga bandaki ita da buta a hannunta zatayi alwala sai kawai ta ajiye butar ta taro nida fara arta tace oyoyo yan garko yau dai kukan komawa ya kare sai nayi dariya na bude baki da zummar gaisheta sai kawai naji hawaye wanda bansan dalilin zubowar suba ta kalle ni tace ikon Allah to meye haka? shi kenan to shiga ki cire kayan kizo kici abinci dana shiga daki saina saka daya daga cikin kayan da muka dinka na fitar mu doguwar rigar shadda mai ruwan jinin kare na fito don yin alwala ina idar da sallah na zauna kenan zan fara cin abinci nace wa umma wai ina baba ban kuma ga sadiq ba.


MUHD-ABBA~GANA

09039016969

www.abbagana.pun.bz
[10/13, 7:58 AM] Ábbä~Gåñā: KAUNA CE SILA 3
MUHD-ABBA~GANA

TAce min bababku yayi tafiya muna sa ran shi jibi shi kuwa sadiq yana makaranta an jima kadan zaki ganshi ina cin abinci amma ina hammma don baccine a idanu na saboda gajiya da muka sha ga hayaniya da koke koke kowa dai yasan yanda yan makarantar kwana suke yi a lkkacin da ake ce musu zasu fita ina gama cim abinci na fara bacci ban tashi farkawa ba sai hudu da mintina kamar goma shima umma ce ta tasheni da kyar dai nayi sallar la a sar ina tashi naga safiq kanina yana cin abinci ya kalleni da murmushi yacemin yyaa mamaa congrats! nace masa tnx you bayan na idar da sallar la'asar ne nayi azkar na shiga bandaki na watso ruwa na canja kaya nazo na zauna a tsakiyar su muka fara hira nna na dinga jin labaran abubuwa da suka faru da bana nan wani nayi dariya wani naji tausayi har da labaran wa'yanda suka riga mu gidan gaskiya duk nace Allah ya jikansu ya kyauta namu karshe haka muka kai har dare muna shan hira dan sallah ce kawai take tashar damu har lokaci kwanciyar bacci yayi muka kwanta tun asuba muka tashi abinka da gidan da kowa aiki yake tafiya umma ta riga mu karyawa da misalin bkawai ta tafi aiki don tana koyarwa ne a makaranatar primary ta gwammaja dake kano atare da sadiq muka karya shima muna gamawa ya tafi mkaranta sai suka barni ni kadai a gida bayan na gama sauran aiyukan gida da suka rage sai nayi wanka na saka wani dinki riga da wando kamar fakistan amma da material aka dinka mai launin shudi mai duhu da misalin karfe daya saura na rana umma tashigo tare da sallama nayi mata sannu d zuwa ta shiga dan rage kayan jikinta
MUHD-ABBA~GANA
09039016969

www.abbagana.pun.bz
Share:

YA FURTA SAKI, AMMA MATARSA BA TA JI BA, YA MATSAYIN AURENSU ???

garin-ciki.jpg

YA FURTA SAKI, AMMA MATARSA BA TA JI BA, YA
MATSAYIN AURENSU ???
Ass. Malam mutum ne ya furta saki ga matarsa
amma bata jiba, shin ta saku ???
AMSA:
=====
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.
To dan uwa matar tasaku, saboda sanin tasan an
saketa bashi daga cikin sharudan saki.
Mutukar miji ya furta saki, mace tasaku koda bata
jiba, yana daga cikin ka'idoji awajen malaman
fiqhun musulunci:
Duk wanda ba'a damu da yardarsa ba wajan
tabbatuwar abu, ba'a damuwa da saninsa.
Saboda haka yardar mace ba sharadi bace wajen
zartuwar saki, haka ma saninta.
Dafatan Ma'aurata za'a dinga kiyayewa ana kai
zuciya nesa.
Allah yayi mana mai kyau.
Share:

NI DA MATATA

sabo.jpg

Assalamu.alaikum malam wata matane take
kuntata ma mijinta amma iyayensa suna ganin
kamar laifin sane suna fushi dashi ganin haka
sai ya kirata ya sanarda ita idan tabar wannan
hali ya yafe mata amma taki bari saboda da
taga mahaifansa na fushi dashi shin fushin
nasu zai samu wannan mai gida?


walaikummussalam godiya ta tabbata ga ubangijin talikai,
Inhar bashida laifi babu abunda zesameshi da izin Allah
Share:

UMMULKULTUM***54--57 (karshe)

img-20151113-173905.jpg

UMMUKULTHUM
By Adermerh_MD

54yana zuwa dakinshi yah fada akan gadonshi yana tunani har bacci barawo yh dauke shi sea around 6am yatashi yayi sallan asuba daga nan kuma yah kara komawa yh kwanta sai 11am yh tashi yayi wanka yah shiga cikin gida yasamu hajiya da kaltume ah falo dasu aunty murja yh dauki nana yah zauna gefen aunty murja bayan an gaisa neh hajiya tace yau kuma sea ynxu kah tashi yace wlhy hajiya kaina neh kemun ciwo dazu tace eyyh har umar yazo ae yace bazea tashe kah baa asannan neh maa uthman yatuno baiga kaltume baa cikin sauri yace hajiya ina ummukulthm hajiya yace wlhy kaikam dazun nan da umar yazo inason aikan ummukulthm gdn kawata hajiya maryam sea yace mun zai kaita tow yanzu kam ma inaga suna hanyan dawowa azuciyanshi yace kaii amma gsky wannan abokin nawa idan nayi da wasa zai kwace mun ummukulthm gsky sea nayi wanda nayi narabasu insha Allahu ahaka yayi tah maganan zucii........UMMUKULTHUM
By Adermerh_MD

55lumar kam tun fitan su daga gd yake tah yiwa kaltume surutu ita kuma tayi masa shuru wai ita ah dole batason surutu shikuma yace wananna yace wancan haka dai harsuka isa gdn bayan tah kai aikan neh taadawo suna hanyan dawowa yake cemata tabashii nmbr tah taso tahana shi amma yanda taga yana zakewa neh tabashi dasuka dawo yace tah gaida hajiya shikam zai wuce gd anjima zea shigo wajan uthman tace towh ngd har cikin zuciyanshi yaji dadin godiyan data masa tashiga cikin falon da sallaman tah tah fado kan hajiya tace wayyo hajiyana yah gaji wlhy hajiya tace sannu ainima nasan dole kigaji dan tun jiya kk zirga zirgan aika uthman kam haushinta yakeji gani yakeyi kaman sun fara soyayya da umar anata tadi amman banda shi murja tace yadea uncle uthman anata tadi amma kayi shuru kaltume tace yana tunanin faridanshi neh akayi dariya nikam baice musu komea bah can sea yayi dariya komea yah tuno ohon masa yah tashi yaje dakinshi yah chanja kaya yasa kayan hauwasa yayi kyau kaman ah daukeshi ah gudu yazo falon hajiya yace hajiya barin fita tace tow adawo lpy aunty murja maa tace saika dawo kaltume kuma cikin shekiyanci tace ah gaida aunty farida yayi murmushi baice mata komea bah yayi tafiyarsa kow ina zaije oho nima ah dunno
UMMUKULTHUM
By Adermerh_MD

56yau bikin uthman da farida saura kwanan uku amarya tana tah shirin yin events dinta ango kam cewa yayi tahada komea yah kaimata kudi itada kawarta fadila suna tah shirye shirye bbu zama uthman kuma duk yh cire damuwan kaltume aranshi hajiya ma taga yafita daga damuwan dataga yana yi kwana 2 da suka wuce kaman bashi bah kuma tayi farin ciki da hakan nikuma nayi mamakin hakan kodea yah daina son kaltus din nawa neh.....

Yau neh amarya tayi kamunta tayi kyau sosea abun sai wanda yagani dan an cancara mata makeup kam ango maa yayi kyau kafun su kaltume sutafi neh umar yazo har gd yace wa kaltume tah shirya su tafi tare itakam bataso hakam bah amma haka tah shirya batayi wani makeup bah itakam amma ahakan ma tayi kyau tun tana fitowa daga gd umar yake kallonta har ta iso gun tace tafito muje yace ohhh tow inh su aunty murja da nana tace sukam ae tareda yaya majid zasutafi yace ohk muje suna cikin tafiya neh uthman yah kira umar ah waya yace ina kk neh inata neman kah yace wlhy ganinan ah kan hanya kana ina neh kaidin yace kazo kadauken inah gd yace towh haka yah koma gd uthman yana fitowa yagansu tare da kaltume baice mata komea ba yah bude gdn baya yah shiga yacewa umar muje gdnsu farida mu dauko tah yace haka zaayi abokina suna tafiya suna tadi kaltume kam tayi tsit kaman kurma dan taga hararan da uthman yake mata aranta tana cewa ran auren naka ma sea kanunamun halin naka tana cikin wannan tunanin neh har suka isa gdnsu amarya dama suna nan suna jiran ango yazo ya dauki amarya sungama shirinsu suna zuwa aka shigarda amarya sea kawarta fadila tazo tah bude gaban motan wea kaltume tah fito tah shiga wai ae itane babbar kawar amarya tare zasu tafi itakam koh kalloma fadilan bata isheta baa bare ma tayi mata mgn umar yace bakiga tare mukazo baneh kk cewa haka uthman yace fadila kiyi hqry ki nemi wani motan plx kinji kawar amarya da kyar tah yadda tah nemi wani motan fareeda kam tah tsume wea anyiwa kawarta haka uthman yh kalleta yace matata meye kuma nah bata rai tana jin yace matata tah manta da fushi datakeyi maa tayi ta washe hakora kaman mai tallen closeup......

UMMUKULTHUM
By Adermerh_MD


57anyi biki anyi bidiri buredede yau eh ranar saturday aka daura auren fareeda da uthman da daddare kuma akayi dinner washe gari aka watse aka bar ango da amaryansa .......

Ankai amarya gdnta wanda yake chan cikin new GRA gd yayi kyau kam dan itama kanta amaryan tah yaba da kyan gdn part 2 neh ah gdn acikin cikin part din farida babban falo neh sea kuma akwea daki biyu ah ciki kowanne da falo da uwar daki sea kuma bandaki ah ciki dayan dakin kuma dakin uthman neh shima da falo ah ciki da bandaki sea kuma kicin ah chan gefe acikin babban falon gidan dai dan dagwas dashi......Alhmadullilah mu hadi a kashina na biyu

Adermerh_MD
Share:

UMMULKULTUM**51---53

img-20151113-173905.jpg

UMMUKULTHUM
By Adermerh_MD

51da dare yayi majid yazo daukansu hajiya tace abar mata ummukulthm su kwana tunda gobema murja zata dawo sukace towh sukayi sallama da hajiya ah waje neh suka hadu da uthman da umar suna zauna akan plastic chiar suna tadi suka gaisa da majid sukayi musu sallama suna isa bakin motan kaltume ta bude ta ajiyewa murja hangbag dinta tace seada safe tayi kissinn din nana ta kalli majid tace sai da safe yace Allah yh kaimu uthman yace maman nana yau kuma anan kukabar mai renon naku murja tayi dariya tace nabarwa hajiya itane ita kuma kaltus sea murgude murguden baki takeyi wai ance mata mai reno tayi cikin gd tana gunguni majid yayi dariya yace kaida kanwar takan nan ae sea Allah sukayi dariya duka harda umar....


UMMUKULTHUM
By Adermerh_MD

52 bayan tafiyansu neh umar yah kalli uthman yace dan Allah uthman waye wanann ummukulthum din gsky yarinyar tamun ni bantaba ganin yarinyar data dauke mun hankali bah kaman wannan gsky tamun am in love with her yah za'ayi dan Allah uthman yaji gabanshi yafadi anan yaringa jin wani iri kaman zai susuce yarinyar daya dade yanaso neh yau amininshi yake soo yana wannan tunanin neh abokinshi yakatse shi yace kayi mgn mana kayi shuru baza ta yarda dani bane kokuma tanada wanda take so?? Uthman kam atunaninsa bbu abunda zai iya hana umar arayuwansa amma bazea iya barmishi ummukulthm bah saboda tun tana yarinya yake sonta yah raini soyayyanta umar yace haba bruh kayi magana mana kayi shuru.........


UMMUKULTHUM
By Adermerh_MD

53yayi murmushi yace haba malam daga ganin yarinya kabi kah susuce kaman bbu enmata ah duniya inah muneeran taka neh umar yace haba uthaman nikam kadaina mun mgn nn muneera plz becuz nah riga nasamu wata anan uthman yah kalleshi sosea yace ae wannan kam anbaada ita sea kayi hqry yace koma wa aka bawa nidea ISA seana auri UMMUKULTHUM uthamn kam kaman yah hau umar da duka yakeji sea umar yace nikam baka fada mun yar waye bane maa uthman yace kanwar aunty murja neh matan yaya mijid umar yayi murmushi yace tazo gdn sauki maa ai abokina tunda naa gdn neh
Yace bari maa natafi gd gobe zamu karisa hiran nan kar mama taga shuru har yanzu sukayi sallama umar yatafi uthman kam Allah neh kadea yah kaishi dakinshi dan idonshi yagama rufewa baya ma kallon gabanshi.........

Adermerh_MD


www.abbagana.pun.bz
Share:

UMMULKULTUM***45---50

img-20151113-173905.jpg

[8:14AM, 11/20/2015] Bana: UMMUKULTHUM
By Adermerh_MD

45farida yanzu jin zuciyarta takeyi fes tunda hajiyan uthman tah warware mata komea tace mata bbu abunda yake tsakanin uthman da ummukulthm sea yan uwantaka .......

Da kyar hajiya ta shawo kan uthman akan yaje yadubo farida sea datayi da gsk tukun yace zaije nan da yamma hajiya da murja da majid sea kaltume suna zaune ah falo suna hira sea ga uthman nan yayi kwalliya kamn ango yah shigo cikin falo kaltume tace yaya uthman sai inaa haka yace bansaniba din tace Allah yh baka hqry nikam
Yace aamin majid yace kukam dea kuncika fda wlhy yace hajiya barinje dubu faridan tace yawwa agaisheta da jiki yace tow har zaifita yadawo yace ummukulthm zoki rakani mana kafun yagama mgn tace bbu inda zani yace aikuwa dolenki kije hajiya tace banson takura yi tafiyarka murja tace haba hajiya meye ah rayakiya ta kalli kaltume tace ki tashi kuje tana tura baki taje ta dauko gyalen ta ta fito suka tafi.......


UMMUKULTHUM
By Adermerh_MD

46mommy kam fushi takeyi da kowa ah gdn har yar gaban goshin nata farida Idan tahau dakinta ah sama bata saukowa......
Uthman da ummuklthm suna isa suka shiga falonsu uthman dinne ah gaba tana biyedashi sunsami zainab da fareeda ah falon suka zauna farida kam kaman ta rungumeshi takeji dan dadi kaltume ta gaida zainab amma ko kallon farida batayi baa faridan bataji haushin hakan bah tunda dea taji bata soyayya da uthman kam ae shyknn komiye zata mata bazataji haushi bah bayn sun gaisa da uthman neh ta kalli kaltume tace ummukulthm dan Allah kiyi hqry akan abunda namiki kaltume tace bbu komea tace ywh yar gari ngd miki zainab kam dayake sun dan saba da kaltume gunta taje suna ta tadi abunsu sun bar uthman da faridansa

Adermerh_MD
[8:17AM, 11/20/2015] Bana: UMMUKULTHUM
By Adermerh_MD

47farida tayi rau rau da ido tace uthman kamun alkawari idan munyi aure bazakamun kishiya bah uthman yah kalleta kaman ya mareta sea dea kuma yana tausaya mata saboda dalilinsa ta samu ciwon zuciya harta gama surutunta baice mata komea bah yah kalleta yace farida ki kiramun ummukulthum mutafi tace haba swtat tun yanzu yace ehh inada wani aikin da zanyiwa abba neh tace tow ba matsala ta tashi tayi dakinsu wajen kaltume da zainab tashiga da far'an ta tace ummukulthum swata dina yana jiranki wea zaku tafi kaltume kam cikin zare ido da shakiyanci tace waye kuma swtat din farida tace uthman dina kaltume da zainab sukayita mata dariyan shakiyanci har cikin zuciyanta taji haushi amma haka ta matse ita aganinta tunda dai uthman zai aureta bata da wata damuwa dawani ta fita ta barsu ta koma gun rabin ranta zainab ta kalli kaltume tace wlhy ummukulthm kema kin iya iskanci kaltume tayi murmushi tace tow adda zainab zamu tafi sea wataran kuma zainab ta dauko turare tabawa kaltume tah karba tayi mata godiya take cewa adda zeee nikam banga mommynku bah zainab tace hmm kekam kyale mommyn nan tana fushi da kowa ah gdn kaltume tace ohhhh ah waje suka hadu da su faridan ita da uthman dinta injita da fada sukayi sallama da zainab takariso gunsu tah bude mota tashiga abunta ta zauna sea daddanna wayanta takeyi shima uthman yah bude yah shiga sukayi sallama da shi suka tafi gida.....


UMMUKULTHUM
By Adermerh_MD

48su kaltume anata shirye shirye fara waec ah skul karatu takeyi ba wasa ah gida kuma murja anata shirye shiryen komawa gida dan majid cewa yayi basea tayi arba'in ba hajiya kuma batace a'ah ba saboda matarshi cee amma zatayi kewansu sosai more especially ma kaltume saidai bbu wanda zatayi neh.....

Malam sadi yadawo cikin gombe shida matarshi baba furera mutumiyar arziki tasan yakamata anan yaketa sana'arshi murja da kaltume suna yawan zuwa musu ziyara sosea malam sadi yana jin dadin hakan sosea saboda baida kamarsu ah duniya suma suna nunawa baba furere so dan tadaukesu kaman yayanta abu dai yayi kyau za'ace


UMMUKULTHUM
By Adermerh_MD

49satinsu biyu da komawa gidan majid su kaltume suka gama exams dinsu nah gama makaranta auren uthman da farida kuma saura 2 wiks anata shirye shiryen biki mommynsu farida kam har yanzu bata sauko bah seama abunda yah karu dataga biki yh kusa nema kow mai ta tuna ohoo tazo tasame daddynsu zainab tana bashi hakuri tana kuka shima yasan dai bah banzaba amma bainuna mata komea bah yace shyknn akiyaye gaba ta tashi tace ngd tah fita shikuma azuciyanshi yace Allah yh kareni daga sharrinki dai sukuma yaranta sunji dadin data daina fushi dasu mommy itama tafara shirye shirye irin naa uwar amarya kaman bah itaba .......
Uthman kam kaman bah ango bah dan duk yayi wani iri daga ganinsa kasan yana cikin damuwa hajiya tayi tayi yh fada mata amman yace bbu komea haka tah gaji tah kyaleshi dan bataso ta takura masa har abba ma yagane uthman yana cikin damuwa amma yabarsa neh yaga gudun ruwansa kozai fada musu!!
Yau saura 1wik bikin uthman yana kwance akan gadonsa yayi zurfi cikin tunani saiji yayi ance uthman inata sallama bakajini bane yayi sauri kallon inda yake jin murya wazai gani sea yaga babban abokinsa wanda sukayi makaranta tare tun suna yara har suka girma sun shaku sosea dan wasu kamma sun dauka twins neh shida umarr din uthman yataso da sauri suka rungumi juna yace haba bruh shine kawai sea dai naganka kaman daga sama kow kafada mun zakadawo umar yayi dariya yace i jst want 2 suprise yhu neh ae suka kara rungume juna yace wlhy dazun na shigo nigeria wanka kawai nayi nace barinzo gunka mama tana ta cewa natsaya naci wani abu amman nace aah sea naganka yace aikuwa kah kyauta umar yace tashi kah kaini gun hajiyana nayi missing dinta sosea wlhy uthman bayason shiga cikin gidan amma haka yah daure suka shiga yana ita kuma ta taho da sauri dauke da plate tana kallon bayanta tana yiwa mai aikin hajiya mgn kawai sea sukaci karo da uthman tazuba masa abinci ah jiki aikin tah rude mah tarasa mai zatace masa tah rufe ido kawai tana jiran saukan mari sea kuma tajj yace wai nikam ummukulthm yaushe zaki daina rawan kaii neh mutum kullum bazea sa kansa waje daya baa tace wlhy yaya uthman bansan kah shigo bah am srry plz sea anan neh umar yace muje kah chanja kaya mana bada saninta baneh ae yayi tsaki yh juya umar kuma ya tsaya kallon halittar Allah itakuma kaltume dataga yah tsaya kallonta sea tace laaah malam ae yatafi yah barka umar kam baima san tana mgn bah dan shakala wajan kallon ta dataga abun nasa yayi yawa ta murguda masa baki tayi tafiyarta umar yace towh wannan kuma wacece bansanta bah yana tsaye agun saiga uthman nan yah dawoo suka shiga......UMMUKULTHUM
By Adermerh_MD

50 suna shiga falo suka samu murja da babynta gefe kuma kaltume neh keh kwance kan cinyar hajiya sai kuma hajiya maryam ah gefe kanwar hajiyansu majid hajiya tana ganin umar ta washe baki tace laaah ashe manyan baki neh ah gdn namu sannu da zuwa umar yaushe akah shigo yace wlhy dazun nan nashigo suka gaisa yah gaisheda murja da hajiya maryam uthman yah tashi yah karbo babyn murja wato nana yana mata wasa hajiya tace wa kaltume ke baki gaida mutane neh tace ae mungaisa hajiya tace aena knn tace dazu mana hajiya ae munhadu dazu ah waje umar yace ehh mun gaisa hajiya tace ohh kaima kazo auren abokin naka neh?? Umar yace ehh wlhy kuma yayi daidai da hutu nane maa hajiya tah kalli kaltume tace kawo musu abinci ummukulsum tace hajiya daga gdnsu fh yace miki yake ae bayajin yunwa hajiya kam sake baki tayi tanajin ikon Allah itakuma koh ajikinta sea chewing gum takeyi murja tace dan Ubanki idan daga gidan yake sea kuma yace miki bazea cii bah kow miye uthman yace idan maso kikeyi kikunyatani ah gaban abokina towh shima dan gd nehh kaltume kam shuru tayi abunta tana dariya ciki ciki murja neh ta tashi taje tah dauko musu tana mai jin haushin hali irin nah kaltumen nan umar kam yarinyan tagama burgeshi komai nata yana masa kyau........ kuji bako fh yaga kaltus

Adermerh_MD
Share:

UMMULKULTUM***40---44

img-20151113-173905.jpg

[8:10AM, 11/20/2015] Bana: UMMUKULTHUM
BY ADERMERH_MD

40murja kudaden data samu ah suna taraba kashi uku tadauki kashi daya ta budewa babanta babban provision store acikin kasuwan gombe kuma tasaya masa gida anan anyi auren talatu satin daya wuce ankaita chan kano malam sadi maa yasamu mata za'a aura auren kwanan nan da anyi auren zasu dawo shida matar.......

Hajiya sunyi shiri ita da murja zasuje wajan karban maganin yara tare da majid suka fita shi yayi office suma suka wuce wajan mai maganin kaltume ce akabari ah gd sea uthman shima yana harhada takaddunsa neh akan nxt wik zaifara fita aiki ah bank yashigo falo neh yana duba abu yaga kaltus sea fama da waya akeyi yayi sallama batama jishi bh yazo kanta yh karbi wayan yace bakya jin sallama neh tace toh ae bakayi bh balle ah amsa yace kekam dea nah fahimci bakida kunya ummu kulthm tace haba yaya uthman Allah ya baka hqry suna cikin haka neh sea sukaji sallama daga jin muryan sunsan maiyin sallaman kaltume neh tah amsa uthman kuma yah zauna ta shigo da murmushinta tana ganinsu tare tah bata fuska ta shigo tah zauna uthman yace sea yau kk ga daman zuwa ganin babyn tace ynxun maa ae bah ganin baby nazo yi bah gunka nazo kaltume taceyi dariya tace farida kike ma kow waye neh ae baby kamma batason ganinki kuma mai ganin babby ae sea mai tsada ta tashi zata barmusu gun sea uthman yace dawo ki zauna kaman kartadawo dan dai kar uthman yace tamasa raini neh ta dawo tazauna farida kan sake baki tayi tana kallon ikon Allah


UMMUKULTHUM
BY ADERMERH_MD

41 abun yayi mugun bata mata raii tana juya mgn nn da ummukulthm tayi mata neh taji uthman yace farida am all
Ears inajinki tace uthman wato kaine kasa wannan yar matsiyatan tamun rashin kunya kow tah juyo tah kalli kaltume taje wato kekuma kin shigo birni an waye koh yar matsiya ta kawea wlhh nafi karfin kici mutunci kow uwarki ma balle keh ae kuwa kafun tace wani abu ji kk tas tas uthman neh yah mareta mari har 3 duk abubuwan da take fada ah kunne hajiya da murja.....


UMMUKULTHUM
BY ADERMERH

42bah kaltume kadai bh har murja taji zafin abunda farida tah fada kaltume kam kuka takeyi sosea farida ta dafe inda uthman yh mareta tace nika mara uthman hajiya tace ashe dama bakida kunya farida haka kk zama lallea ma kam tace hajiya bakisan meye yh faru bh karki bani rashin gsky hajiya tace kozaki huce akaina neh marar kunya ae kekam dama halin uwarki kk dauko nacin zarafin dan adam da halin ubanki kk dauko ae da kin huta farida cikin gatsine da rashin kunya tace hajiya kidea zage mun uwa wlhy inbaka haka baa wlhy zan rama aikuwa nn uthman ya fara ball da ita har waje daga ita har food flask din nata

Tana isa gd ta fadi kan mommyn ta tana kuka tana fadan karya da gsky mommy tace kut run uba yau za'ayita kam tadauko ashar ta maka zainab kam tayi dariya harta gaji tace wlhy mommy sun min daidai ynzu haka rashin kunya tamusu mommy tafara durawa zainab ashar ae bh shiri tah koma dakinsu ta zauna tana maiyiwa mommy addu'an shiriya .......

Muhadu ah cigaban UMMUKULTHUM

BY ADERMERH_MD
www.abbagana.pun.bz
[8:12AM, 11/20/2015] Bana: UMMUKULTHUM
By Adermerh_MD

43hajiya kam da kyar tashawo kan ummukulthm tadaina kuka shikuma uthman duk kunyan murja yakeyi saboda gani yakeyi ah dalilinsa akayi hakan da Alh yadawo hajiya ta fada masa abunda yh faru baiji dadin hakanba sea dea kuma baiji mamakin hakan bh dan yasan halin uwarta shikam cewa yayi Allah yh shiryesu hajiya tace aamin.....

Farida kuma wuni tayi kuka har dare gashi ah ranar daddynsu yayi tafiya da daddare neh farida sea kuka take baccin maa yaki zuwa zainab tah tashi tace dallah malama kin dameni da kuka inbaza kiyi bacci bh kitashi kikoma falo tayi tsaki farida kam kukanta tacigaba dayi zazzabi mai zafi yh dauketa dataga bah sarki sea Allah takira sunan zainab tace meye kk kirana tace ki taimakeni zainab zan mutu kirjina zainab ae kuwa nan da nan ta taba jikinta taji zafi rao taje dakin mommy da gudu ta kira tah suka dauki farida sea asibiti......

UMMUKULTHUM
By Adermerh_MD

44suna isa akabata taimakon gaggawa da kyar akasamo kanta zainab kam data rude har daddynsu ta kira tace fareeda kam zata mutu tana asibiti daddy yace gobe yana hanya ISA
Washe gari da safe neh farida na bude idonta taga mutane akanta hadda su hajiyan uthman mommyn tane kadea bata gun tafara kuka tana cewa hajiya ku yafe mun dan Allah wlhy ba laifina bane sharri shaidan neh da huduban mommy kuyi hqry karku rabani da uthman zainab ma aikin tausayin farida ta fara kuka tazo kusa ta ita tace kiyi shuru my sister kinji kiyi shuru doctor na zuwa yayi mata alluran bacci yace wa daddy yanason ganinsa daddy yabishi office doctor ya shaidawa daddy fareeda nh dauke da ciwon zuciya daddy seada yayi hawaye dan bakin cikin matarsa da halinda take son saka su aciki doctor yh basu magunguna bayan 2 days aka sallameta ......
Share:

UMMULKULTUM***36----39

img-20151113-173905.jpg

[8:50PM, 11/19/2015] Bana: UMMUKULTHUM
BY ADERMERH_MD

36farida kam tayima kanka alkawarin sea tabi duk wata hanyan dazatabi tah wulakanta ummukulthm ji takeyi ah ranta har hajiyar uthman dinma haushinta takeji taje tasamu mommyn ta tace fada mata komea da abunda aka gada mata mommynta tace ki kwantar da hankalinki ISA zaki auri uthman dayake uwarta ta ma gogeggiya ce tayiyyi mata magannanu nah sanyaya zuciya tukun na farida taji sanyi aranta gani takeyi kaman ansa ranar aurensu yayarta da gefe tanata daddanna waya tace nidea shawaran tazan baki shine gwara ma kincire son uthman aranki dan baya miki irin son da kk masa idan ma anyi auren kezaki wahala barin fada miki mommy tace dan ubanki ubanwa yasa bakinki ah mgn nn mu kokuma ance zainab neh iskancin banza kawea wlhy zainab kikiyayen fh itako zainab tashi tayi tabarmusu dakin dan bakin cikin rayuwa irin nah mamanta da kanwarta mstw Allah shi kyauta (aamin)
Hartabar dakin mommy bata daina zaginta bh data gama zagin neh tace shgy mai halin ubanta wlhy yarinyan halinsu daya da daddynku farida tace nidea chan musu suji da wa'azinsu dea mommy tace wlhy kam anan sukagama yanke shawaran idan daddy yazo mommy zataje tasameshi da mgn nn farida kam aranan ta kwan cikin farin ciki..........

Washe gari da safe nehh har daddy yh gama shiri mommy tace laaa ina da mgn dea yace keh kullum sea mutum zai fita kice kinada mgn tow fadi ina jinki seata washe baki tace dama mgn nn yaran nn neh yace wasu yara knn tace uthman da fareeda manah tunda sunason juna sea kuyi mgn da alh abba ayi musu aurensu daddy yace tow yaushe neh farida tagama makaranta da zakiyi mgn nn aure mommy tace ba'a karatu da auren neh daddy??
Daddy yace tow naji sai nayi shawara da dan uwana tace tow ayi shawara mai kyau dea yayi tafiyarsa abunsa yana tunanin.....,


UMMUKULTHUM
BY ADERMERH_MD

37washe garin suna neh arnd 9am hajiya da murja da kaltume nah kallon kayan sunan da akakawo da kyaututuka saiga abba neh yah sauko daga dakinshi da wani kwali yazo yah zauna bayan yazauna neh saiga majid sunzo shida uthman nan bayan an gaisane abba ya dauko kwalin nn yace ummukulthm kema ga kyautarki yazo takarba yana washe baki tace abba ngd Allah yasaka da Alkairi tana budewa taaga waya ce kirar iphone 6 ta kara godiya ta kaiwa hajiya itama ta tayata murna sanann takaiwa murja ma tagani tah nunawa majid maa yatayata murna ta koma ta zauna sea uthman yace yato kin rainani nibazaki nuna mun bah kow hajiya tace ai tasan halinka neh ta gwale mutane shiyasa kaltume tace hajiya shiyasa ma ban nuna masa bah tace amma kayi hqry ta kaimasa yace aah bazan gani bah ae tunda kunce haka keda hajiyanki akayi dariya gaba daya Alh Abba ya kalli hajiya yace tow nikam nah fita tashi tayi masa rakiya uthman yh mike ya dauko baby akah daki yadawo falo da ita kaltume tace haba yaya uthman yanzun fh nakwantar da ita yace kow bakisani nah maida itane tayi shuru tana murguda baki

Bayan anyi sallan magrib neh Daddyn farida yazo gdn Alh Abba yaga baby yatasu murnar samun karuwa daga nan yah hau sama wajan dan uwansa yasameshi yana kallon BBC nan yah zauna sukayita hira har sukayi sallan ishaa bayn nan neh yake fadawa alh abba abunda yakawosa alh abba yace towh Alhmdullh ae tunda dea kace suna son junarsu kuma yan uwanjuna neh suu tunda kaine mahaifinta idan kabashi ae shyknn daddy yace tow Alhmdullh sea ka sanar dashi uthman din abunda muka yanke sea abar auren nan da 6 month kow yahh kagani alh abba yace masha Allah towh Allah yh nuna mana daddy yace aamin yh rabb......
TOW FHA AUREN UTHMAN DA FARIDA
Muhadu ah cigaban littafin donjin mea zai faru
By Adermerh_MD♡
[8:54PM, 11/19/2015] Bana: UMMUKULTHUM
By Adermerh_MD

38Alh abba yasamu hajiya yayi mata mgn nn tace tow Allah yh zaba mana mafi alkairi yace ameen......
Bayan an kwanbiyu neh daddy yake fadawa mommynsu farida ansa bikin 6 months tayi farin ciki sosea anan taje yasa farida take fada mata farida kam ji takeyi kaman ansaka tah ah aljanna sea dadi takeji tah dauki waya ta kira kawarta fadila take fada mata yanda sukayi ita tayi mata murna sosea tadawo dakinsu take fda wa addanta tace masa Allah yasa ayi ah sa'a fareeda ta kunna waka ah wayanta sea rawan dadi takeyi zainab kam dan bakin ciki tasa mgn tayi sea can take cemata maimakon kije kiyi safilfilu kiyi wa godia shine kk rawa abunki kow tace aah barni wlhy dama farida kam batason sallah sea tayi sati 3 bata kalli gabar bh bbu ruwanta itakam wanda yake mata mgn nn sallah ma batason hulda dashi......
[8:56PM, 11/19/2015] Bana: UMMUKULTHUM
BY ADERMERH_MD

39 washe gari da safe neh tun karfe 6:00am neh mommy tace wa farida tazo tah rakata anguwa bataso zuwaba seada taji mommy tace wajan malamin da zai mana addu'a neh akan aurenku da uthman aikuwa nan da nan ta shirya sune basu isa inda zasuje bah har wajan 8:43 awani jeji mommy tacewa farida tayi parkin bayan sun sauko neh farida tace mommy akwea mutum anan kuwa tace ahh kina wasa maa knn suka shiga jejin seada sukayi tafiya sosea suka hango wani bukka tana isa sukayi sallama sukaji shuru sea chan sukaji mgn farida kam fitsarine dabatayi bah amma ta tsorita kam mommy tace sannu boka yace meke tafe daku mommy tamasa bayani yace toh yabasu wani magani wea asamasa ah abinci dayan kuma tayi wanka dashi anan suka ajiye masa kudi sukayi gaaba farida kam kasa driving tayi dan tsoro sea dai mommy neh tayii.......

Aranan kam da zazzabi farida tah wuni sea washe gari da safe neh taji sauki taje tayiwa uthman girki mai raida lpy tayi wankan magani tukun tayi mommy sallama ta tafi gdnsu uthman......

Muhadu ah cigaban UMMUKULTHUM
Share:

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive