shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Sunday, 1 November 2015

AL'AMARIN ZUCI 31------------------35

al-a-marin-zuci.jpg

[10:07PM, 10/5/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky giro
31ya nuna mata dakinta, shiko ya tafi nasa dakin,wanka tafarayi, ta kwanta domin ta samu ta sauke gajiyar tafiya, bacci barawo ya dauke ta.

Koda ta tashi,ta samu ya aje mata takeaway gashi dama tana jin yunwa sosai,ta zauna taci saida ta koshi, bata da abinyi kuma tana fashin sallah,tashi tayi tana yawata wa,a cikin gidan anan taga wurin wasan basket ball gashi ko a gida wasanda sukeyi kenan hakan yayi matukar yimata dadi, ai ko saida tayi ball sannan ta koma ciki,ganin marece tayi.


Wuraren karfe goma na dare tayi shirin bacci kenan,taji motsin shigowar sa,"wai yanzu naji dama, ni kadai a gida tun dazu sai kace maiya,kwantawarta keda wuya ya shigo dakin da sallamarsa ,ta amsa sallamar tare da gaishe shi, ya mika mata ledar hannusa tare da amsa gaisuwar,ba yabo ba fallasa.


Gasashiyar kaza ce da hollandiya milk a ciki,taci sai, dai ba sosai ba, domin taci ragowar na dazu,tasa saura a firij,tayi kwanciyar ta,sai safe.

Written by Bilkeesu giro
[8:45AM, 10/6/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky giro
32Ba ta farka ba sai wuraren karfe goma na safe, tayi wanka,ta shirya cikin wasu kana nan kaya,riga da siket, rigar iya cibi, sai siket dinma ma iya cinya tayi kyau sosai,saida ta gyara ko ina fes,sanna taje kici neman abinda zata ci, ba komai a kicin din,illa kayan tea,sauran kazar jiya ta dumama ta hada da tea ta ci.

Kwance take falo tana game da wayarta,da tagaji ne da game ta kunna tv, tana kallo.

Yau sati daya kenan amma ba abinda ya canza kullum abinci saye take ci,ga kadaici na damunta,tun zuwanta bata yi waya da kowa ba,sabida bai saya mata layin canba,shi ne ta yanke shawarar idan ya shigo xata masa magana.


Bashi ya shigo ba sai karfe tara da rabi,tana kan sallaya tana karatun Qur'ani taji shigowarsa,saida da takara minti talatin sannan,ta je dakinsa da sallamarta,sai da yabata izini sannan tashiga.


Zaune ta same shi bisa gado yana dan wani aiki da laptop,daga shi sai singlet da wando.
Yaya sannu da aiki,yauwa sannu yabata amsa ne batare da ya ko kalli inda take ba.

Writing by Bilkeesu giro
[1:49PM, 10/6/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky giro
33yaya dama cewa nayi me zai hana a siyo kayan abinci,akan wane dalili? ganin nayi zaifi sauki,gashi kuma nagaji da cin abincin sayarwa,ni da nake siya bance miki naga gaji ba sai ke,da ci ne kawai naki,dan kin raina ni ko?yaya meye raini anan kuma,ganin nayi siyen kayan abinci yafi sauki,saboda kinfini fini sanin abinda yakamata ko?mamaki ya bata sosai ganin a hasale yake magana,
Allah ya huci zuciyarka,ta furta hakanne tare da fita daga dakin a tsorace domin ganin take ko dukanta zai iya yi.

Ta koma dakinta cike da mamaki,tana cewa"rashin so bala'i ne, idan ba haka ba wannan maganar ce zata hasala shi,ina ma ace yanzu ne kake so na ba a lokacinda nake gidanmu ba,amma sai lokacin da zan yi rayuwa a gidanka zaka ji baka sona,yaya meyasa zuciyarka ta zo maka da wannan al'amari? Wanda ni bazan iya jureshiba,why?yaya. Kuka take sosai,tana rokon Allah ya sauya mata wannan al'amari,cikin sauki, tana cikin kuka ne bacci barawo ya saceta.

Ba ita ta farka ba sai asuba,tayi sallah taji baza ta iya komawa bacci ba saboda yunwar da take ji,kici ta nufa domin ta hada tea,ga mamakin ta sai taga kayan abinci makil ,wato dama jiya yaya ya siyo kayan abinci,shi ne yayi tamin fada,kamar ma ba zai siyo ba.

Nan take, tahada musu breakfast mai rai da lafiya, gida duk ya kamsashe,a dining table ta jera komai,sannan taje tayi wanka,ta shirya ne cikin super Holland riga da siket sun dan kamata kadan, tayi daurin dankwalinta, mai kyau ta jashi baya, gaban gashin ya kwanta sosai,ta sake sauran gashin a bayanta.

Ta fito das,das,da ita sai kamshi take,dakinsa ta kwankwasa sai gashi ya fito da shirin fita,saida yaji wani abu da ya ganta,tayi kyau sosai,cike da murmushi ta gaishe shi, ya amsa ba yabo ba fallasa.

Written by Bilkeesu giro
[8:13PM, 10/6/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky giro
34yayana breakfast na jiranka,batare da ta tsaya jin me zai ce ba,ta juya hade da jawo jelar gashinta zuwa gaba, wato ta maida shi saman kafadar ta,hakanne yabashi damar ganin show me your back,tafiya take kamar wacce ba qashi a jikinta,tana wani irin laudi,ga hips da Allah yabata duk da haka bata kiba ba rama,ya salam,Allah yayi halitta anan, tun randa nake da mimi ban taba ganin tayi kyau irin wannan ba,cewar faruk.

Abinci suke ci amma sai mamakinta yake kamar wacce bata da damuwa a tattare da ita.Da zai tafi har bakin mota tarakashi.

Haka sukaci gaba da rayuwa har tsawon wata ba wani sauyi,kwalliya nan tanayinta yadda ya kamata,abincin ta lafiya ko makiyinta yaci bazai ce baiyiba,tana masa biyayya dai dai iyawarta, gata da tsafta,uwa uba tana ibada ba dare ba rana.

To ni Mimi mena rageshi da shi,amma nakasa miado sona,ko dai zan hakura da kaine yaya....a'a Mimi gajen hakuri bana ki bane,ki tuna fa a kwai Allah,kici gaba da hakuri da kuma addu'a, cikin ikon Allah sai ki ga komai yadawo daidai.
Tana magana ne da zuciyar ta, haka ne fa,tayi maganar ne a fili.

Faruk ne zaune a falo yana kallo,kamshin turaren ta ne ya dawo da hankalinshi wurinta sanye take da doguwar riga ta kanti baka mai dogon hannu, anyi mata kwalliya da fararen duwatsu,ba dankwali a kanta,tayi matukar yin kyau.

Written by Bilkeesu
[11:26PM, 10/6/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCiNa Bilky giro
35Sai dai yanayin fuskarta ya nuna akwai damuwa a tare da Ita.
Zama tayi akusa dashi, yana saman kujera ita tana kasa,tafara da cewa.
"Yaya kaje a bainar jama'a ka tozartani baka dubi zumuncin da ke tsakanin mu ba,ballantana har kaji kunyar mahaifina, agabansa ka furta cewa baka sona,
hawaye ne shar ke fita a idonta amma hakan bai hana ta cigaba da maganar da takeyi ba,yaya idan har wani laifi naima meyasa baka kira ni a gefe ka gaya min ba har saida kaje a cin jama'a, kasa iyayenmu a cikin bacin rai da bakin ciki,nayi hakurin wannan, amma bazan iya jure wannan ba .....

Ya isa mimi!....ya isa haka!... wai me kikeson cewane da har sai kin bata min rai kafin ki fada?yaya tun lokacinda muka zo banta taba fita ba, bantaba waya da kowa a gida ba, ko da yaushe ina cikin kadai ci, yaya, ya kake so nayi da rayuwata ne...kuka take sosai shiko faruk duk gabadaya tausayinta ya lullube shi, jikinsa yayi sanyi sosai.

Mimi pls kiyi hakuri tun zuwammu da kwana biyu na saya miki layi, koda naje kai miki nasamu kina bacci,shi ne na saka, a cikin drawer,Allah na manta in gaya miki amma kiyi hakuri,kinji,
Yaya kana nufin Abba bai taba tambaya ta ba,Mimi ko nakira Abba baya daga wayana yayi fushi dani kuma inajin kunyar kiransu daddy,sai su Alhji da kaka kawai, amma sukan tambaye ki,sai dai, akanyi rashin sa'a bana gida.

Written by Bilkeesu giro
Share:

1 comment:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive