shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday, 28 November 2015

KAUNA CE SILA***31----40

kauna-ce-sila.jpg

[8:50PM, 11/26/2015] Bana: KAUNA CE SILA 32



MUHD-ABBA~GANA



ina hanya amma duk tunanin ya ahmad nake yi gaskiya ya ahmad yana da kyau kai anya akwai mai kyau shi kuwa a cikin mawaka anan namu gashi ya iya kwalliya dan Allah ji wata irin shiga da yayi ga wata rigar sanyi mai kyau akan kayan da ya saka da irin wadannan tunane tunane na karasa gida washe gari ya ahmad ya kira ni a waya bayan mun gaisa yace wai ni soyyya muke yine? nace a"a me ya faru yace yan nan gurin kowa sai cewa yake yi wai soyayya muke yi to ke kina sona? bude baki da zanyi sai nace masa ai kai ba saurayi na bane yaya nane yace haka ne nan muka yi sallama wata irin kauna nake yiwa ya ahmad wanda nake jin shi har cikin raina kuma ina ganin kamar gudan mu daya ko a ina na ganshi da gudu zan karasa na sameshi nayi ta masa surutu yana yawan zuwa gurinmu amma baya hawowa same sai dai ya tsaya kasa yace min cD yazo siya ya tafi wani lokacin ka sai yace min ruwa zan bashi ya sha ya tafi wani abin mamaki bana so naji ana fadin laifin ya ahmad bare kuma naji an zage shi duk yanda muke da kai naga kana bata shi to zaka ga bacin raina shi kuma kome ya ga nayi sai ya tambayi dalilin yi kamar yazo bai ganni ba ko takalmi ya gani a kafata to zai ce mai yasa kike son irin wannan takalmi bare kuma ya ga na dan rame hatta dan haske idan yaga nayi sai yace naga kinyi fari nakan ce masa ba komai wataran kuma idan yace yaga na rame sai nace masa aikai ne sai ya ce ni bani ba ne yayi dariya ya tafi wata rana fiddausi tace na raka ta wani biki a daula hotel an gayyaceta nace mata gaskiya sai naje na tambayo umma tunda kince da magariba ne tace idan kika fito sai muje nace mata bara na dawo


MUHD-ABBA~GANA


www.abbagana.pun.bz

KAUNA CE SILA 33




MUHD-ABBA~GANA





Lokaci da muka je gurin biki sai naga ashe mawaka ne da yawa dan akwai wata maryam a zaune ga wasu mawakan maza muna zaune ina daga idona sai naga shigowarsu ya ahmad kawai naji gabana ya fadi duk da naji na rikice yana zuwa kuwa sai naga ya zauna a kujerar da take kusa da ni ba dan gaisuwa ba abin da muka kara yi sai na juya muka cigaba da hira da fiddausi ina nuna mata wasu hotuna a waya ta sai naji yace bani wayarki na juya don naga me yake nuna min sai naga ashe hoton salisu ne akan waya ta ni na manta da shine ma akan wata ta naji ya kuma maimaita min tambaya da yayi min sai na hau kame kame nace ba saurayina bane shi ya bani wayar shi yasa kaga hotonsa sai yace hmmm ai nima ya taba cewa yana son budurwata nace wace yace oh yace daga yau ma itama ki dinga ce mata aunty tunda ai waccan maryam din ma aunty kice mata kuma ai duk sun girmeki nace to an gama munyi kamar sati daya bamu hadu da ya ahmad ba kuma bamuyi waya ba ranar ina idar da sallar magariba sai kawai naga missed calls dinshi ai kawai na fara neman layin shi tana fara ringing sai naji ya dauka yace ki kashe zamu kira ki kalmar dana ji ya fada ce ta karshe ta firgitani nan dai ina ta tunani sai da yayi kamar minti ashirin sai kiran shi ya sake shigowa dana dauka mamaki ne ya kamani muryar salisu naji a wayar bayan kuma layin ya ahmad ne yayi shuru na kasa magana sai naji yace mamaa gani da yayanki yace wai karna sake na yaudareki kafin nayi magana sai naji ya ahmad ya karba yana cewa na fada masa idan auranki zai yi to ya hanaki fitowa,


MUHD-ABBA~GANA



www.abbagana.pun.bz
[8:54PM, 11/26/2015] Bana: KAUNA CE SILA 34




MUHD-ABBA~GANA




idan kuma ba da da gaske yake ba to ya bar ki ki samu wani bawan Allah nace masa tam ni dai jikina duk ya mutu muna na rasa me yake min dadi na kuma rasa dalilin jin hakan wani canji dana fuskanta daga ya ahmad shine yanzu ya daina kira na a waya kamar da kuma ko da na kira shi ba ko yaushe yake dagawa ba idan na samu ya daga na fara masa korafi sai yace aiki ne ya masa yawa duk da nasan a yanzu aiki ya masa yawa dan kusan ya kara shahara kusan ko wanne film wakar shi zaka ji albumd na wakokin shi yana ta fitar da su daban daban amma a nawa tunanin wannan dalili bai isa ya hanashi kirana ba a matsayina na kawarshi da nake ji dashi ina tura masa sakon text a waya kusan ko wacce juma'a bai taba bani amsa ba dama kuma sakon baya wuce addu'a ana cikin haka wata rana yace na zo nayi masa aiki bayan naje sai ya tashi yasa wani yaro yayi recording din dan bama idan shi ne ya ce zaii yi recording din ba zan iya ba dana gama na fito sai na same shi zaune ban masa magana ba nazo zan wuce yace min zo nan sai na matsa kusa da shi ya kalli idona yace ina salisu? sai nace yana nan sai naji yace bara na kira shi ya zo nan muyi magana gani ga ki nace dan Allah ya ahmad ya kyaleshi wallahi duk mutane sai fada masa ake yi wai soyayya muke yi sai ya ce min to ai in na kira shi tun ma kina ciki gashi nan ma zuwa ina jin ya fadi haka na bar gurin ko shi bai san ta ina na bi na gudu ba ina hanya kiranshi ya shigo waya ta na dauka yace kina ina ki dawo nace wallahi naa kusa gida.





MUHD-ABBA~GANA



www.abbagana.pun.bz
[8:59PM, 11/26/2015] Bana: KAUNA CE SILA 35




MUHD-ABBA~GANA





sai kawai ya kashe nayi kamar minti talatin ina shiga gida sai kiran salisu shima ya shigo ina dagawa naji yace yanzu ke ya kamata abin da kika yi kenan nace masa me nayi yace meye na fadawa ahmad cewa ana ce min soyyya kuke yi ban bashi amsa ba kawai ji yayi na sak iwani kuka mai karfi yace mamaa niya kamata nayi kuka ba ke ba nace to amma ai kasan me mutane suke cewa yace shi kenan kiyi hakuri zanzo da daddare daya zo gidan mu haka yayi ta min maganar shi fa baya son wata mu'amala tsakanina da ahmad dn shi kawai gani yake soyyaya muke yi nace masa ni fa yaya na ne kai kuma saurayi nane abinda kawai na sani kenan a wannan lokacin na fahimci wai abu ashe duk mutane sun san tsakanina da ya ahmad ashe har yi dani ake ana cewa idan ana so aga nayi fada to a taba shi wasu kuma sunce in dai kai maganarshi a gabanta to kuwa kamar yaji an gama ire iren wadannan surutan na mutane sune suke dagawa salisu hankali dan shi kanshi yasan ina bawa ya ahmad muhimmanci fiye da komai yana ganin idan har soyayya zata shiga tsakaninmu to yasan zan rabu dashi ana cikin wannan yanayine wataran salisu yazo gidan mu muna zaune sai nace bara na shigo gida ina zuwa ina fitowa naga salisu ranshi ya bace sosai ba kamar yanda na barshi ba nace masa ya ka tashi sai kawai naga ya miko min wayata yace tafiya xanyi yau ma kunyi waya da ahmad kuma me kika fada min bayan kiran ki yanzu amma gashi naga kin kirashi yau shima naga missed call dinshi a wayarki sai nace wallahi salisu aiki na masa amshi sai sa ya kirani.



MUHD-ABBA~GANA


www.abbagana.pun.bz
[8:43PM, 11/27/2015] Bana: KAUNA CE SILA 36




MUHD-ABBA~GANA


nan dai salisu ya tafi ya barni da tunani a daran nayi ta kiran shi amma yaki dagawa daga karshe ma sai ya kashe wayar sa j kuma har safiya ban same ba haka naje makaranta ba wani kuzari a tattare dani husna ce ta shigo sai nake bata labarin abin da ya faru nace mata kinga husna ya ahmad ma yanzu kwata kwata bai da mu da ni ba ko waya baya min sosai tace bani number salisu naba ta shi bayan ya dauka naji tana bashi hakuri yace a wuce amma dole sai dai ta goge number ya ahmad daga wayata husta tace zatw goge yanzu nace gaskiya ba zan iya ba a zuciyata kuwa cewa nayi to ai kona goge ma ina da ita a kaina dan na haddace tare muka zo zoo road da ita wai dan ta bawa salisu hakuri yace mata ya hakura ba komai sannan ta tafi gida ni kuma na hau sauran benan mu wani abin haushi a wannan lokacin mutane sun sani a gaba sosai ko ina zan ce na ake yi cewa ina bala'in son ahmad cewa bana son laifinshi ba a taba shi kuma wai zan iya batawa da kowa a kanshi idan kuma a gabana sai kaji ana cewa ai ita mamaa ahmad ne yayanta sai nayi dariya nace na jini ma kuwa shi kuwa a bangarenshi yanzu ko ganinshi bana yi sosai kuma ya canja min sosai wannan ne yasa ko ganinshi nayi bana masa irin yanda na saba idan bamu hadu kusa da kusa ba bana bari ya ganni idan a nesa na ganshi sai nayi ta kallon shi har sai ya bar gurin yauma irin hakan ce ta faru yana kasan gurin mu suna magana da wani mai shirya film sai na labe a jikin kofar mu ina kallonsa ashe nura yana baya na yana gani na sai naji yace to ki sauka mana sai na juyo nace kai nura wallahi ba zan ma bari ya ganni ba.



MUHD-ABBA~GANA




www.abbagana.pun.bz
[9:11PM, 11/27/2015] Bana: KAUNA CE SILA 37




MUHD-ABBA~GANA



kawai sai na ji nura ya fara kiran sunanshi ni kuwa sai nayi dayan studio na kusa dan na shige ciki nayi kamar minti biyar sai kiran shi ya shigo wayata yace ina kika shiga fito gani a vocal ina zuwa sai ganinshi nayi a zaune a reception da wata mujalla a hannunshi na ce masa ina wuni sai naga ya kalleni kawai yace ance guduwa kika yi da kika ganni bakya son ganina? nace a'a yace to me nayi miki nace kai ne ka daina kulani sai yace to ai mamaa kin fi karfina kina da samari da yawa nace wallahi ni ban da samari yace salisu ba saurayinki ba ne har hotonku tare ya nuna min sai na ce rannan ne zamu je yin alwala ya ganni shine fa ya ce na tsaya a mana hoto yace shi kenan karki damu ya tafi ya barni a nan zaune yayi tafiyarshi muna zaune tare da su zainab ranar nan a reception sai ga ya ahmad kawai ganin shigowarshi nayi naji suna gaisawa da yan gurin sai na sunkuyar da kai kasa har zai shiga ciki sai ya dawo yace min keh sai na dago kai sai naji yace sai na yiwa salisu rashin mutunci ban ce komai ba sai naji mana jan mu yana dariya yana cewa mai yayi maka sai naji yana cewa wai yayi maka sai naji yana cewa wai cewa yake yi soyyaya nake yi da yarinyar nan ban san me manajan yace masa ba dan ciki suka shige saboda wata waka yazo dorawa mai gurinmu da aka yiwa matar da zai aura mawaka da yawa kowa baiti daya yake zuwa yana dorawa ina ganin fitowarshi na bi bayanshi nace masa ya ahmad sai ya juyo nace masa wadannan din da kake fadawa salisu yayi maka laifi sune masu fada masa cewa soyayya mukeyi.



MUHD-ABBA~GANA



www.abbagana.pun.bz


KAUNA CE SILA 38




MUHD-ABBA~GANA




nace wai dama abin da ya maka kenan sai yace wai dan nace masa kuna kama da shi ne ni kuma yace min wai muna kama dariya ce ta subuce min sai naga ya sha kunu yace ba kina sonshi ba kawai kuje kuci gaba da soyyarku nace ni ba sonshi nake yi ba kawai dai yace yana sona nace masa to yayi tafiyarsa ya barni ban tsaye ban iya komawa studio ba har sai da naga ya shiga motarsa ya tafi wani abin takaici tun daga wannan lokacin ya ahmad ya daina shiga al amurana waya ko na kira sau nawa baya dagawa babban abin takaici ko gaisheshi nayi baya amsa min kamar da don idan yana cikin mutane ma ya ganni sai ya dauke kai idan kuwa muka hada ido sai dai naga ya harareni dana ga abin da gaske yake kawai sai na fara canja hanya idan na ganshi kiran nashi ma sai na daina duk da bana ji dadin hakan da muke yi haka na hakura na tattarashi na ajiye shi yau alhamis ina zaune a vocal sai kawai na tsinkayi muryar ya ahmad yana sallama ban san me yazo yi bs na dai ji yana gaisawa da mutane dana dago kaina sai kawai muka hada ido a take naji wata muguwar faduwar gaba wadda ban taba jin irinta ba tun da mahaifana suka kawo ni duniya ga wani yanayi dana tsinci kaina a ciki wanda ban taba jin irinshi ba wani abu ne naji yana fisgata tun daga tsakiyar kaina har kasa kafata numfashinta ne naji yana neman daukewa sai kawai na fita ban san iya tsawon lokacin daya diba ba na dawo daukar jakata na samu ya tafi dana je gida akasa komai nayi nayain da nake ciki daban ne ban taba shiga kwatankwacin shi ba bayan na idar da sallar magariba naje na samu uman mu nace mata umma yau daga ganin ya ahmad gabana yake ta faduwa har yanzu na ma rasa me yake damuna.



MUHD-ABBA~GANA





www.abbagana.pun.bz
[9:12PM, 11/27/2015] Bana: KAUNA CE SILA 39





MUHD-ABBA~GANA



umma tace ba komai ki dinga addu'a insha Allah babu komai na tashi na koma dakina kiral ayin shi sai yaki dagawa gannin bai daga ba sai kawai na kyaleshi a yan kwanaki nan na shiga wani mawuyancin hali ni kaina ban san haka na damu da ya ahmad ba dan ko yaushe tunaninsa ne abin yi nada shi nake tashi da shi nake kwana a raina har gizo yake min gashi kwata kwata na daina ganinshi wayarshi ma yanxu ban fiye jin ta a bude ba a hakan ne kuma na fara jin rade radin cewa wai ya ahmad aure zai yi ranar da naji ban iya hakuri ba sai da na kira shi dana kira naci sa'a ya daga bayan na gaishshi yace min kwana biyu nace ai ni na rasa in da kake buya yace ina nan aiki ne kawai ya boye ni sai nace ya ahmad wai aure zaka yi sai yace E kema kawai ki nemi miji kiyi aure ko kin fi so kiyi ta waka nace masa a'a zan yi sai yace yawwa na gode duk abubuwan da nake ji a zuciyata game da ahmad ban daina jiba kamar ma karuwa yake yi wata rana na sauko zan tafi gida sai na hango ya ahmad a xaune a kan motarshi shi da wani abonkinshi marwan yayi min kyau sosai dama ya ahmad karshe ne gurin kwalliya wata riga ya saka fara da bakin wando da farin takalmi banje gurin ba na tafi hanyar titi ina zuwa zan tsallaka titi sai na waiwayo don na kalleshi ga mamakina shi ma ni yake kallo har na tafi dana fito washe gari sai muka hadu da marwan wanda na gansu tare jiya yace jiya shine kika yi kamar baki ganmu ba koh?



MUHD-ABBA~GANA






www.abbagana.pun.bz




KAUNA CE SILA 40






MUHD-ABBA~GANA



nace ba haka bane naga kuna magana ne yace min yayanki fa auran shi ya zo nace masa eh na sani wai sauran kwana nawa ne yau yace bazai kai kwana ashirin ba nace Allah ya kaimu da daddare na kira layin ya ahmad na ce masa wai bikin ka saura kwana nawa sai naji yace wallahi ban san saura kwana nawa ba nace masa baka sani ba? yace da gaske ban sani ba nace to shikenan bikin ya ahmad ya zo duk inda naje zancen bikin ake yi na san hakak baya rasa nasa ba da tashi da yake yi a yanzu sannan bikin su biyu za a hada tare da abokan shi wanda shi kuma kida yake yi ina ji ana ta zancen wasu ma ni suke tambaya wai dame dame za a yi nace ina jin dinner ne kawai ranar ina tsaye sai ga salisu yana waya ban san da wa yake magana ba sai kawai naji yace nima ga matata zaku gaisa ashe ya ahmad ne kuma a ranar aka daura aure gobe dinner za a yi ina dora wayar a kunnena naji yace ina gajiya nace lafiya ban sake cewa komai ba naji yace ku yaushe ne bikin naku ina ji yana fadin haka kawai na mikawa salisu wayar shi na bar wajan nasan ya ahmad ya san nice ban yi niyyar zuwa gurin bikin ba har cikin zuciyata duk kuwa yanda muke da shi ina gida bayan magariba sai husna ta kirani tace gamu a gidansu amaryar ahmad muna shirin zuwa gurin biki sai nace nifa bana jin zanzo




MUHD-ABBA~GANA



www.abbagana.pun.bz
Share:

2 comments:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive