shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Sunday 1 November 2015

AL'AMARIN~ZUCI 26------------------30

al-a-marin-zuci.jpg

[3:36PM, 10/7/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky giro
26Abbah don Allah kayi hakuri nasan nayi kuskure,ko kallon inda faruk yake baiyiba ya tafi abinshi.

Faruk kodai wata ce kagani kanaso?ko daya umma ,abin sai kace tabin jinni, ko wani abu ya hadaka da wani ne ko sabani akan mimi ko yace yana sonta kaci mai mutunci,umma gsky babu,hmm faruk kenan mai hankali bazai ji wannan zance ya yadda dashi ba,dole akwai wani a bu kasa,umma...faruk, tashi kawai kabani guri.

Zainab kizo akwai magana,ok sai nazo kenan,ta aje wayar tare da share hayen da suka zubo mata.

Barka da wuni mommy yauwa Zainab yau kece a gidan namu?eh mommy, to ya mutan gida lafiya lau,jeki Mimi na daga ciki.

Mimi ya ake ciki ne? naga duk kin ya kuce...Zainab aure za'ayi min da Wanda baya so na,aure Mimi?kuma da wanda baya sonki?kwarai kuwa zainab,waye wannan, yaya faruk,dama kuna da wani dan uwa ne faruk bancin faruk dinki,shi dai da kika sani zainab,shine guda ba kari,kuma shi da kansa yace baya sona.....

What!!Mimi meyake nufi da haka....cin amana, mana har sai kin tambaya bayan ke da kanki kin taba nunamin halin da namiji naki yarda .....innalillahi wa innailaihi raju'un amma yaya faruk yaci amanar soyayya....ganin nake kamar wata ya samu,tunanin da nake kenan mimi.

Written by Bilkeesu giro
[3:36PM, 10/7/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky giro
27Wato Mimi kin nuna masa so, ba ko dan ajin nan na mata,matsalar kenan, zainab,ai ya fahimtar dani yanzu,amma nasan abinyi.

Koda Zainab ta fito suka yi kicibis da Hafiz zai shiga dakin mimi,tsaya wa yayi yana kallonta batare da ya bata hanya ta wuce ba.
Sai yaga tayi mai kyau sosai fiye da kullum....yaya Hafiz ina so zan wuce,oh sorry Zainab,sannan ya bata hanya ta wuce.

Yaune ranar daurin auren Mimi da faruk,anyi matukar yin taro kamar ba'a mutuwa,bayan an daura aure ne za'ayi walima,baxa su samu damar yin wasu buku kuwa ba,domin basu da isasshen lakaci, saboda zasuyi sammako zuwa London.

Zainab ce ke shirya Mimi sai tsokanar ta take,amarsu ta ango kinga yadda kikayi kyau kuwa na tabbata ko makiyin ki yaganki sai ya sake kallo ,meye amfanin haduwar, miji baya so...hmm ni bana son kina zancen nan fa...Allah, to na daina.

Kina birge ni mimi ta yadda kika cire damuwa a cikin ranki,kamar ba abinda ya faru.

Written by Bilkeesu giro
[3:36PM, 10/7/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky giro

28 Zainab na fahimci idan nasa damuwa a raina bani da wata riba face rashinta,na fiso in maida lamarina a wurin ubangiji, da yaddar Allah inhar da gaske yaya keyi na yadaina sona inshaAllh idan na dage da addu'a zai soni.

Zainab ko London muka je zanyi harkar gabana ne,zan nuna kamar dama can bamu shakuba, amma zan masa duk wata biyayya da mata take ma mijinta.

Mimi kenan meyasa zakiyi haka.... so kike in shishshige masa in yaso ya kara jin haushi na ne...hmm zainab muma daina maganar nan pls, saboda raina kara baci yake.

Bayan angama walima, Mimi da Zainab ne a daki, suna kallon fotunan da suka dauka a waya,Mimi wannan foton duk yafi kyau,bari a turama yaya faruk yagani tunda bai ganki ba....a'a Zainab karki tura...da sauri zainab ta tashi domin ta gudu.

Written by Bilkeesu giro
[3:36PM, 10/7/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky giro
29Ita ma Mimi biyo ta tayi aguje,Zainab na kai wa bakin kofa taci karo da mutum, gata rungume a jikinsa, sannu,sannu take tada kanta, saboda tana fargabar waye, koda ta dago idonta taga Hafiz,
da sauri ta janye jikin ta, cikin jin kunya, har bata son hada ido da shi shiko gogan wani farin ciki ya ziyar ceshi sai tunani yake ina ma ace mallakin sa ce......

yaya hafiz yi hakuri bada sani na bane...no zainab,ba komai ai ya wuce

Mimi, faruk yace "tunda safe ne tafiyar ku,daga kai tayi alamar taji,domin dariya ne sosai ta keji,saida yafita sannan, ta fara dariya sosai tana nunin zainab,shi ne dai dai dake...kinga banaso to ni inaso,kanki ake ji,kin tura foton? ai dama wasa nake miki....a'a ai tunda kin tura a kirjin yaya Hafiz zai je wa yaya faruk ko?Mimi!!...Zainab...yayi zan rama ne, cewar zainab.

Mimi ce agaban mommy da daddy su nayi mata nasifa akan tabi mijinta sau da kafa,nasifar ta ratsa ta, hakan ya sata kuka sosai,kenan dai zantafi in barku mommy zanta fi gurin wanda baya sona ni kadai ke sonsa mommy.....yi hakuri kinji mimi ya isa,tashi muje cikin gida ki musu bankwana.

Written by Bilkeesu giro
[3:36PM, 10/7/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky giro
30 A filin jirgi,Mimi sai kuka take mai cin rai ta rirrike abba,tana cewa,"Abba na fasa auren tunda shi baya sona.....kaka ki gaya ma su da gaske nake na hakura....Alhaji don Allah ka taimakamin kajenye auren nan nafiso na zauna daku, haka take binsu tana kuka amma bawanda yace mata kala saboda ta basu tausayi har basu san me zasu ce mata ba,baba Bashir kadai ne yayi karfi halin yaimata magana, yi hakuri Mimi nasan cewa, yayanki bazai cutar da ke ba, amatsayinki na kanwa a gare shi, ki yi hakuri kinji, daga kanta tayi alamar taji tana, mai share hawayenta.

Zainab ce ta rungume ta suna jin kamar kar su rabu, faruk ne yaxo, ya ja hannuta su ka shiga jirgi,suna masu yi musu bye bye.

A cikin jirgi ne faruk ke kallon Mimi yana magana a cikin zuciyar sa"yau wai Mimi ce ke kukan bazata bini ba, bayan ada kuka take zata bini,lailai nayi kuskure.

Bayan sun isa ne,Mimi sai kallon gidan take yayi matukar birgeta gashi da fadi,mutun zai sakata ya wala,haka ta fada a cikin zuciyarta.

Written by Bilkeesu giro
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive