shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Friday, 13 November 2015

divorce*** daries---71---90

divorce-diary.jpg

[11/2, 4:08 PM] Âbbá~Gãñä: 71Sai dai bayan kwana 2 ya kan kira ni ya bani hakuri har ga Allah ni na hakura abinka da rashin hankali irin nawa Wanda yai maka irin haka har kake tunanin kara zama dashi to gaskiya rayuwata na bani kamar yayi nadama, a haka na ci gaba da zaman gida sai da nayi sati daya lokacin ne ya kara aiko wani uncle dinshi
[11/2, 7:58 PM] Âbbá~Gãñä: 72Yazo yayi magana da mum aka bashi number dady but still mama tace sai bayan auren Fareeda sister na da nake gaya muku kuma duk Wanda ya aiko ce mishi yake shi baisan wani abu ya hada ni da shi ba shi baiyi fada da matar shi ba haka kawai ta tafiyan ta
[11/2, 8:00 PM] Âbbá~Gãñä: 73 ana bikin Fary saura 2 weeks dady yace ai lallai in shirya ina koma gidan mijina akayi akayi yace ina shi lallai sai na koma sun dame shi da kira kuma ya gaya musu zan koma bet week Sunday kuma maganar nan da nake muku tunda na bar gidan shi bai taba kira na a waya ba not to think of yazo gidanmu
[11/2, 8:03 PM] Âbbá~Gãñä: 74 har ana saura 3 days to in koma bawan Allahn nan shiru baizo ba haka bai kirani ba kawai sai na yanke shawarar bari ni na kira shi haka akayi kuwa na kira shi tayi ringing 3 ya dauka nace Sahib ina wuni ya aiki yace lpy kalau nace ance fa Sunday zan koma yace eh ai ya sani nace to Allah ya kaimu
[11/2, 8:06 PM] Âbbá~Gãñä: 75Yace ameen nace don Allah idan da abinda nai maka kayi hakuri ka yafe ni yace hmmm bari ina gaya miki sanam kin min abinda bazan taba mantawa da shi ba kin sani bakincikin da har in mutu bazan manta da shi ba kin sani kukan da koda na rasa iyaye na banyi shi ba
[11/2, 9:19 PM] Âbbá~Gãñä: 76 kin bata min suna a gari kin min cin mutuncin da ba'a taba min ba kin fallasa ni sanam wllh ki rike a ranki sai na rama
[11/2, 9:26 PM] Âbbá~Gãñä: 77 kawai suka fara sauka a eyes dina ban San yanda zanyi ba na gayawa mama tace kada in fada ma dady zai dauka komawar ne bana son yi Allah sarki uwata ita ta tayani kuka kwana ukkun nan da ya rage wllh kullum sai mama tayi hawaye akan komawa ta
[11/2, 9:31 PM] Âbbá~Gãñä: 78A haka ana saura 6 days bikin fary aka maida ni tunda na koma gidan nan na rasa kwanciyar hankali na bakin cikina ya dawo sabo rigimar safe daban rana daban dare daban duk nabi na rikice na hargitse
[11/2, 9:33 PM] Âbbá~Gãñä: 79mukayi bikin Fary muka gama aka zo kai amarya yace bazani ba.... jama'a ku duba min ikon Allah bikin yar uwata jini na uwa daya uba daya fa, yace bazani kai amarya ba hmmmm
[11/2, 9:39 PM] Âbbá~Gãñä: 80 Haka na hakura aka kai amarya bada ni ba aka daura aure bai je ba anyi biki da sati daya nace mishi sahib don Allah ina so inje in ga gidan Farynmu yace ko'ina bazaki ba nace to Allah ya sauwaka ya kama hanya yai ficewar sa nai kuka abina har na koshi ranar har ciwon kai ya kamani.



duk wani I LOVE YOU KARYANE WALLAHI INJI NI



muhd abba gana
09039016969
[11/3, 8:04 PM] Âbbá~Gãñä: 81Haka muka ci gaba da zama wasa wasa auren fary 2 months yanzu kuma cikin ikon Allah fary ta samu juna biyu bakuji yanda murna ta kama ni ba lokacin da naji labari yana dakin sa kuwa naje da murna na ce mishi sahib fary is pregnant hmmmm sai yace to sai me naji Allah ya taimaka
[11/3, 8:15 PM] Âbbá~Gãñä: 82Nace Ameen na fice daga dakin so disappointed muna haka auren fary ya cika 3 months har yanzu kuma ban San yanda gidanta yake ba jama'a ranar na yanke hukuncin sai dai muyi rigima amma sai ya barni naje na duba yar uwata
[11/3, 8:18 PM] Âbbá~Gãñä: 83Aikuwa na sameshi a palour na ce mishi sahib gaskiya ni yau gidan fary zanje ina so na nuba ta haba jama'a ya za'ayi ace yar uwata uwa daya uba daya amma auren ta tau wata 3 ban San hanyar gidanta ba gaskiya bazai yiwu ba da sake
[11/3, 8:21 PM] Âbbá~Gãñä: 84Ke sanam kar kimin hauka anan bari ma in gaya miki idan baki sani ba na tsani wannan fary din asali ma ko sunan ta naji rayuwa ta bace take na tsane bana son ta saboda haka ba inda zaki je nan dau mukayi ta rigima da yaga na tsaya akan baka ta na sai dai naje din ne fa ya hakura ya kaini,gogana komai sarautan ka a wajene a gida kaima bawa ne
[11/3, 8:28 PM] Âbbá~Gãñä: 85Wata rana ina zaune kawai sai naga sahib na kira na da Etisalat line dinsa lokacin ina cikin mutane wai ni mai miji mijina ya kira ni kawai sai na tashi na wuce cikin daki na ina shiga na dauka hello sahib kawai sai naji muryar mace "an gaji da zaman gida an dawo, wata guda kikayi gidan ku bai je biko ba shine kin gaji kin dawo kai wasu dai basu da zuciya wllh an dai ji haushi zanyi magana sai ta kashe wayar
[11/3, 8:44 PM] Âbbá~Gãñä: 86Ranar ta kai karshe na sai na kirata bata dauka ba na aika mata text kamar haka "amma dai kinji haushi wllh don ke abun kunya yayi wa yawa a rayuwa Alhmdllh naji ni miji na kasa rikewa to ke ko mijin ya miki wuyar samu sai yawon bariki kike kuma don baki da kunya har kina da bakin magana wai har kwando zai ce da rariya tana yoyo ance dai mai wanka bai dubi bayan sa ba keda bakin hali yasa aka saki uwar ki ni bazan bata lokacin akan wadda bata da albarka a rayuwar ta ba tunda uwar ki ta tsine miki ni ba abinda zan ce miki sai Allah ya shirye ki idan kina da rabo mara sa'a kawai wadda bata da wayo
[11/3, 8:57 PM] Âbbá~Gãñä 87Da ya dawo na same shi nace mishi sannu da kokari mara zuciya and he was like kina da hankali kuwa daga dawo wa na zaki mun irin wannan magana haka nace eh mana ai duniya banga Wanda ya kai ka rashin zuciya ba Don wllh duk namiji mai zuciya bazai yi abinda kayi ba wai don baka San kunya ba zaka dauki waya kaba wata katuwar banza ta kira matar ka ta sunnah ta zage ta an dai ji kunya idan an santa nai tsaki na fita ina Jin shi yana kira na nayi banza dashi na shige side dina na rufe na barshi yana borin kunya
[11/3, 9:10 PM] Âbbá~Gãñä: 88 da safiya ta waye ya same ni side dina koda yazo ina kwance akan gado na ko tashi banyi shiya tayar da ni ina sanye cikin night dress dina red iya cibi sai dan pant dina ina Lullabe a cikin blanket dina sanyi Ac na ratsa ni gashin kaina sai naji ana shafa mun kaina a hankali na Bude ido sai naga gogan naki zaune gefen gadona
[11/3, 9:14 PM] Âbbá~Gãñä: 89Sai kawai yayi kokarin ya kai bakin shi akan forehead dina nikuwa da naga haka sai na yunkura da karfi zan tashi sai ya rike hannuna nayi kokarin kwace wa na kasa
[11/3, 9:24 PM] Âbbá~Gãñä: 90 Nace Sahib yace naam nace sake min hannu na ya tsaya yana wani murmushin munafurci nace dakwai sauran mutuncin ka a ido na leave my hand na bata face na kwace hand dina da karfi na tashi tsaye akan gadon
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive