shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Friday, 6 November 2015

AL'AMARIN~ZUCI***51------55.

al-a-marin-zuci.jpg

[9:32PM, 10/21/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky giro
51Momy!....yaya faruk!......Mimi ba lafiya,kafin kace me faruk har ya haura sama,koda yatafi yaga halin da mimi take ciki sai cewa yayi"shi ke nan kin kaini kin baro,Mimi why!why Mimi!!....cikin ya zube ko faruk?Momy cikin ya zube Mimi ta min asara,innalillahi wa innailairaji'un,faruk hakr zakayi...yanzu a dauke a kaita dakin duba marassa lafiya ka dubata,momy ai wannan jinin da ya zuba kadai ya isa ace cikin ya zube,ba sai an wani duba ta ba,wanka kawai ya kamata tayi zan kawo magani, yanzu,momy ce ta taimaka mata tayi wanka,bayan ya dawo ne, yayi mata allura hadi da bata magani,ya kwantar da ita,sannan ya kama hanyar fita daga dakin.....Mimi ce ta dakatar da shi ta na mai riko hannusa.
Yaya pls........bana son jin komai daga kareki Mimi, ya fita abinsa,bai zame ko ina ba sai bangarennsu a dakinsa,da isar sa, kaya kawai ya cire ya fada toilet ya sake showertun daga saman kansa har kasa,ko zai ji sassauci,
Bayan ya fito yayi zaune saman gado,ya dafe kansa da hannayensa,yana fitar da hawaye masu zafi.
Ita ma mimi inbanda kuka, ba abinda take,tana tunanin yadda zata shawo kansa ya fahimci cewa Ita kaddara idan Allah ya rubto ba makawa sai anyita, dukda dai tasan da laifin ta aciki, amma ai ba da gangan bane,tana cikin haka ne su Momy suka shigo,saurin rufe idon ta tayi domin bata da abin cewa........ da dai kin bude idon da yafi,fada kan ba makawa,sai kinsha shi tunda ke ba kya aikin hankali,Momy inda take shiga ba nan take fita ba,ji take kamar ma ta dake ta,.....haba fadan ya isa haka,ki barta da zafin zubewar cikin mana, kinsan cewa Mimi yarinya ce,yakamata ki bita a sannu,umman faruk ai yarinta ba hauka bane.

Written by Bilkeesu giro
[9:32PM, 10/21/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky giro
52Amma ai kya duba mata, Mimi har nawace,she is 17 years old, har yauzun bata ko shiga 18 ba fa,haka na sami faruk a nakinsa,wai kuka yake yi wanda yakamata ace ya rungumi kaddara,har nayi mamaki ina hankalinsa yatafi, hmmm uman faruk abinda da ciwo,kinsan faruk idan yasa abu a ransa,sawa yake dawa.....to baga irinta ba,.......amma dai abbanta baya nan ko?baya nan sa'ar da taci kenan,domin nawa fadan ma mai sauki ne.
"Mimi kukan ya isa haka kinji,Allah ya kawo wani tsayayye mai albarka,ameen umma nagode,kina jin yunwa?a'a umma a qoshe nake koda abin ya faru, to kicire damuwa a ranki indai faruk ne zai sauko, daga kanta tayi alamar taji, tana mai share hawaye,nan suka bar dakin ita da Momy, ya rage daga Ita sai Zainab,wacce tunda abin ya faru ta kasa cewa komai, gani take kamar itace sila.......Zainab kidaina tunanin a dalilinki ne abin ya faru dama can haka Allah ya rubuto,sai da ta nisa kafin tace,"to Mimi Allah dai ya sauwaka, amma......No Zainab kar kice komai pls,kawai A barwa Allah komai.

Yau kwana uku kenan Mimi bata sa faruk a idonta ba,kowa gdn yazo dubata amma shi tun lokacin bai sake dawowa ba, hakan bai hanata kiransa a waya ba yafi a qirga,domin ta bashi hkr,sai dai baya dagawa,ganin haka ne ya sa ta koma tura masa text,amma duk daya,hakanne yasa ta yanke shawarar zata je ta sameshi a dakinsa ko zai hkra.

Sai da tayi wanka,ta shirya ne cikin wani tsadadden less, ash color yayi mata kyau sosai,dinkin riga da siket ya dan kamata ba sosai ba,sai zuba kamshi take.

Written by Bilkeesu
[9:32PM, 10/21/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky giro
53Koda ta fito ba kowa a falon,bata zarce ko ina ba sai bangaren su faruk,ta nufi dakinsa tana mai nocking,amma shiru kamar ba mutum a ciki,har zata sake nocking sai taji muryashi yana cewa, yes!ta shiga ne tare da sallamar ta,ya amsa sallamar ba yabo ba fallasa,yaya barka da wuni, barka dai,yaya dama nazo ne akan inkara baka hkr don Allah kayi hkr inshaAllah......."hakan bazata sake faruwa ba,faruk ne ya karasa maganar tare da cewa dama nasan haka zaki fada, amma ba kya aiki da hakan,ba haka bane yaya inaso ka fahimci cewa idan Allah ya rubuto abu ba makawa sai ya afku,sannan da bakin ka fada cewa "cikin nan yana da matsala,wata qil Allah ya hango wahalar da ke tartare da shi,shi yasa ya mun sauki,amma ka kasa gane hakan, kamata yayi mu roqi Allah da ya sauya muna da mafi akhairinsa,Mimi! Pls get out of my room,ba musu ta tashi ta fita,ganin yadda ya hasala.

Bayan kwana biyu da faruwar hakan,Mimi ce ke saukowa daga kan bene zuwa falo,ta samu Momy zaune tana waya da daddy,Mimi sai cewa take "Momy bani shi mu gaisa,ai ya ma katse wayar,
Ashe kinyi waya da daddyn ki,bayan faruwar zubewar cikinki? eh Momy,amma ga alama bai miki fada ba?haka ne Momy ai yaya faruk bai gaya ma kowa ga dalilin zubewar cikin ba,keda umma kawai kuka sani sai Zainab,gaskiya ya kyauta ana son haka a rayuwa,Allah ya biyaka faruk,Ameen momy.

Written by Bilkeesu giro
[9:33PM, 10/21/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky giro
54Ni kuwa Mimi banga kina shirin tafiya ba,gashi naji kamar faruk yace gobe zaku tafi,gobe Momy?eh mana bai gaya maki ba,sati daya fa yace zamuyi kuma ai bamu yi sati ba, kika sani ko canza shawara yayi,may be ya canza shawara, tayi maganar ne cikin rashin jin dadin zancen.
Saida ta bari Momy taje kicin, sannan ta tashi domin zuwa jin zancen tafiyarsu,tana isa bangarensu ta samu ya dawo kenan daga wani guri,sannu da zuwa yaya, kamar bazai amsa ba,sannan yace "yauwa sannu,dakin ya bude tare da cemata bissmilla,shiga tayi ta ta zauna shiko yana rage tufafin jikinsa,ya dawo daga shi sai singlet da short niker,
Inajin ki me kuma kika zo dashi yau,batun tafiya ne yaya naji ance gobe zamu tafi amma sai baka gaya min ba,haka ne amma ai ba dake zanyi tafiyar ba, meyasa yaya? Sbd baki da wani amfani agare ni,sosai ta kalleshi,sannan tace "bani da amfani fa kace yaya?yanda tayi maganar har saida ya kusa dry,anan take kuma ya sha toka,ai gsky na fada,na daya dai ko cikin kika kara samu zubaddashi zakiyi,sbd yarinta na damunki,sai naga,gara na tafi ni kadai,tunda akwai 'yan mata in inada buqata, abinci ko ba matsala ta bane,kin ga baki da wani amfani kenan...tabbas bani da amfani,sbd sha'awa ta kawai kake basona ba, ta fita batare da ta ji me zai ceba.

Dariya yake sosai yana cewa"my mimi,hatta ma sha'awa da so baki banbanta su ba.

Written by Bilkeesu giro
[9:34PM, 10/21/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINA Bilky giro
55Tana isa dakin ta,ta fada saman gadonta ruf da ciki tana fitar da kuka marar sauti.
Shiko faruk yana nan yana kallonta a laptop dinsa domin yasa camera a dakin,tana cikin kuka sai momy ta shigo,saurin share hawayen ta tayi domin batason Momy ta gane,zo muje kici abinci,sai da suka fita daga cikin dakin, ya rufe laptop,yana mai cewa "Mimi nima banso ace nayi tafiyar nan ba da ke ba,lalura ce kawai.

Washe garin ranar.
Faruk ne tare da umma,Abba,Hafiz, da alama tafiya zai yi suko suna masa fatan Allah ya kiyaye hanya.
Hafiz muje karakani a other pert nayi musu bankwana.
Bangaren su Mimi suka fara zuwa,ba kowa a falon,faruk ya haura sama zuwa dakin Mimi.
Bacci take abinta daga ita sai rigar bacci fara tas, bazata wuce iya cinya ba, gashin kanta duk ya baje har zuwa fuskar ta,sannu a hankali yake yaye mata gashin da yazo gun fuskar ta,tare da jaye pillown da ta rungume,ya maye gurbin pilon,Mimi taji abin kamar a mafarki,ta Kara rungume shi kamar za'a kwace mata shi,..... sallamar Momy yaji,tana mai cewa ai zata shiririta ka indai Mimi ce....Momy bacci take bana so tashi,sannu,sannu yayi maganar kamar mai shinfidar yaro, to jeka dai Hafiz na jiran ka,"yace lokaci na tafiya, sai da ya bata kiss sannan ya tashi,yana cewa "har yanzu bacci masu ciki bai sake ta ba fa Momy, da dane, da yanzu ta tashi, lallai kam,cewar momy.faruk ya fita tana masa Allah ya kiyaye hanya.
Yaran nan kamar basu ne aka samu 'Yar matsala abaya ba,amma yanzu cikin ikon Allah soyayyar su ta yanxu, harta fi ta da.

Written by Bilkeesu giro
Share:

1 comment:

  1. Abdullah ayeesha7 November 2015 at 23:44

    Wow! novel dina yana da bala'i dadi dan allah ka samo mana wani hausa love story thank you

    ReplyDelete

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive