KAUNA CE SILA***21---25
[1:18PM, 11/24/2015] Bana: KAUNA CE SILA 21
MUHD-ABBA~GANA
.
Ga kuma computer da speakers a gabanshi idan yake kall kuma a nan nake yin wakar shima kamar daki amma an raba shi da glass idan kika shige to kofa kika rufe za a dinga kallonki ta glass din nan a ciki dai akwai micro phone da kuma earpeace da shi zaki wakakarki ina nan ina ta dube dube sai naji ifan yana cewa wai shima dan kamfanin ne to yanzu zata fara ne? kafin ya bada amsa naji gabana ya fadi yace E mana tunda dama ita take jira ifan yace min shiga ciki na dan zunguri maryam sai tace haba kawai ki shiga kawai na mike na mika mata jakata da wayata na shiga ina shiga ifan yace ki saka abin a kunnenki zakiji abin da za a saka miki nace to duk da gabana yana faduwa amma sai na dake sai naji nura yace min kina jin kida a kunnenko nace masa E H yace to idan kika ji ta fara duk abinda ta fada shi zaki maimaita nace to yace zan nuna miki hannu nace masa to ai kuwa haka akayi sai gashi ko bata ban yi ba ina gamawa sai naga su nata tafawa har da maryam ina fitowa sai naji nura yace ai wallahi kamar ma murjace don gaskiya kin yi kokari nan naji wani farin ciki ya rufeni sai ya kunna kawai sai naji muryata tayi min dadi nacewa maryam kinji muryata tace ai tayi gaskiya murya ki da dadi muna cikin ji sai mama tayo waya gata a kasa sai ifan yace dama ai sai gobe za a cire mana tunda suna da aiki yau da yawa.
MUHD-ABBA~GANA
www.abbagana.pun.bz
[1:23PM, 11/24/2015] Bana: KAUNA CE SILA 22
MUHD-ABBA~GANA
muka sauko tare muka tafi gida muna ta bawa mama labari ni kuwa baki ya ki rufuwa don kamar mafarki nake jin abina ban shiga gidan su ba dan kawai sauri nake yi naje gida na kai labari ina zuwa kuwa n farw bawa umma labari nan tace ikon Allah lallai to Allah ya taimaka ya sanya alkairi a ciki washegari ni kadai naje a can na same su shi da oga yace naji wakarki tayi dadi ifan ya yi min bayanin komai keta gida ce bana bukatar sai nace zan gana da iyayenki saboda haka kin zama yar kamfaninmu kuma mawakiyarmu ina so ki nutsu ba ruwanki da kowa kuma ki sa a ranki aiki kika zo nace masa na gode da magariba na dawo gida dan dama banje gurin ba saboda go slow har da cd plate dina na waka ta na dawo ina zuwa na hau jona socket ina gwadawa umma shiru tayi ta kasa magana da taji muryata ta cemin yanzu mamaa kece wannan nace wallahi umma nice sai naga umma ta daga hannu sama tace Allah mun gode maka kuma na fuskanci itama tana cikin farin ciki matsananci yau tace ai kuwa babanki yana zuwa zan saka masa ke kuma sai kiyi masa bayani nace to na tashi don yin sallah ina zaune ina cin abinci kiran baba ya same ni na tashi a tsorace naje gaban baba na tsugunna yace min zauna sosai na zauna yace da gaske ke kikayi wannan wakar nace masa E nice yace min ke meyasa kike so kiyi waka nace masa tun ina makaranta nake so kuma baba ana fadakarwa ta hanyar waka ga mamakina sai naji yayi dariya yace shi kenan Allah ya shige mana gaba
MUHD-ABBA~GANA
www.abbagana.pun.bz
[8:00PM, 11/24/2015] Bana: KAUNA CE SILA 23
MUHD-ABBA~GANA
amma ina so ki sani zan bar kikiyi waka ne idan har baxa ki bar karatunki ba kuma ko daza ki karatu to ya zama bakya wasa nace insha Allah sai baba yace shikenan ki kula da kanki sosai bana so abinda zai ja mana abin magana sannan ki sani ina da wannan da nake mu amala dasu da yawa wadanda aikinsu ya shafi kamar irin wannan sannan kain san harka irin wannan da ake kira industry basu da sirri duk abin da suke ciki mutan gida suna sani a wani lokacin ana hada musu da sharri saboda haka kiji tsoron Allah kuma ki kama kanki tace masa in Allah ya yarda yace tashi kije nace na gode baba da safe muna karyawa umma tace min mamaa nace ma'an tace bani hankalinki na kalli inda take zauna tace min dan Allah kar ki bani kunya wallahi na yarda da ke fiye da zatonki na san mun yi miki tarbiyya daidai gwargwado amma a hakikanin gaskiya nutsuwarki daga Allah ne ina yi masa godiya ki kula da kanki kar ki sake hali ba ruwanki da samari iri na gurin dan nasan baza ki iya fada ba dama ba abin so bane kin san yanda muke jin labari mata suna fada akan samari nace mata insha Allahu umma ba zan yi saurayi ba har in bar waka (hmmm ashe zaki tsufa a gidan ubanki) tace to kiji tsoron Allah ki bawa duk wanda ya girmeki girma ki zauna da kowa lafiya nace zan kiyaye tace Allah yayi miki albarka ya tsareki ya sa ki fara a sa'a nace amin ina murmushi har wannan satin ya kare ban koma zoo road ba amma kullum sai na ji waka a kuma duk wanda ya zo gidanmu dan unguwa
ko dan uwa sai na saka masa yaji ranar litinin da misalin karfe tara na safe na shiga makaranta ina shiga na hadu da wani dan unguwar mu jamilu yace min kin gama komaine nace masa eh amma ban saan department din printing ba yace nan aka kaiki nace masa E yace zo muje ai kin fita daga gate din nan su anex suke lectures nace muje dan Allah ka nuna min ajin yace to tafiyar ba wata mai nisa bace tsakanin gate din biyu titi ne dai ya rabasu muna zuwa ya nuna min kofar aji yace nan ne nace masa na gode ya juya ni kuma na shiga aji ina dan dari dari dan ban san kowa ba ina karasawa wajen zama sai na zauna a layi na biyu a kan wata kujera ina zama naga wata tazo ta zauna a kusa dani da alamar tashi tayi ta dawo sai tace min sannu nayi mata murmushi nace yauwa tace kema nan aka kawo ki nace E tace sunanki fa nace mata mamaa tace ni sunana husba ismail muhammad nace mata anan zamu dinga daukan lectures ne sai tayi dariya tace baki taba zuwa ba koh? tace ai har an fara ga time table ma ta nuna min nan tayi min bayanin abin da ban gane ba muna cikin haka sai ga wata itama ta shigo amma da alamar sun san juna don naji tace maryam har kin dawo tace na dawo
MUHD-ABBA~GANA
www.abbagana.pun.bz
[8:02PM, 11/24/2015] Bana: KAUNA CE SILA 24
MUHD-ABBA~GANA
sai naji tana gabatar mata da ni cewa yau na fara zuwa aji ta miko min hannu tace welcome nace mats tank u ina jinsu suna ta hira sauran yan aji ma kowa yana ta hada hadarsa sai dai na lura duk yan ajinmu maza ne mu matan bamu fi biyar ba bayan mu na hango wata a bayanmu tana karatu a gabanmu kuma da daya wadda daga gani ba musulms bace kuma zata girme mu ina ganin wannan dalilin ne ma yasa banga alamar wasa a tattare da ita ba sha biyu da rabi muka tashi daga makaranta tare da husna muka fito wani abin mamaki kusan tsayinmu daya da ita haka yanayin jikinmu har kusan kamanni ni dai ban ce mata komai ba har ta hau mashin tayi gida ni kuma na hau nace a kaini zoo road a daidai kasan vocal na sauka na hau sama ina shiga nayi sallama ban dade da zama ba sai ga wata mawakiya mai suna hasiya yanda naji yan gurin suna mata magana nasan ba bakuwa bace na bude baki zan mata magana sai naga ta harareni duk da haka na gaisheta ta amsa da kyar ina ji an fara kiran sallah azahar na cewa ifan zan tafi gida tace tun yanxu nace daga makaranta nake kawai biyowa nayi yace min to ya rakani har ya tsallakar dani sai da yaga na hau mashin sannan ya juya dana koma gida ban bawa umma labari abin da a kai a zoo road ba amma nace mata na biya, washegari tun takwas saura na bar gida ban wuce makaranta ba har sai da takwas ta wuce da minti goma ina zuwa kuwa na tarar da malami a aji ana lecture yana koyar da chemistry na shiga na samu guri na zauna dan ko motsi baka ji a ajin ina zama na bude jakata na dauko dan memo na fara jotin abin da yake cewa sai na fahimci kusan duka abin da muka yi a farkone sai de kamar wannan a bude shi sosai.
MUHD-ABBA~GANA
www.abbagana.pun.bz
[9:41PM, 11/24/2015] Bana: KAUNA CE SILA 25
MUHD-ABBA~GANA
malamin da ya shigo na karshe ne har zai fita sai ya ce to tunda an baku time table kuma kowa ya san numbern shi da ajin shi gashi har an fara lectures sosai daga yau ko wanne dalibi takwas ta zama kana aji don idan mallami ya riga ka zuwa ba zaka shiga aji ba sannan attendance yana da matukar amfani kuma muyi karatu yan ajin suka amsa da cewa to muna fitowa bakin aji wayata ta fara kara ina dubawa naga ifan yace kina ina ne? nace ina makaranta amma mun tashi yace yaywa zo kiyi wa wani amshi nace masa to gani nan mun rabu yau mada husna a bakin gate kamar jiya dan ita maryam ba da ita muka fito ba wai tana jiran wata yar uwarta yanda husna ta fada min
dana shiga sai na tarar da mutumin yana ciki yana wakar gaskiya ban sanshi bada alama dai bako ne yazo yin waka dan wakar siyasa ce da ya fito sai na shiga aka saka min na fara bin yanda yayi da farko banyi daidai ba sai aka kara saka min a nan buyun sai nayi daidai dana gama na fito na zauna nan aka fara gyara masa dan a daidai ta masa da kida muna zaune sai wata ta shigo ita ma daga gani anan take sun gaigaisa ita ma dai naga ko kallo ban isheta ba mai wakar ne naji yana magana da ifan wai ashe tam baya yake wa zai bawa kudin aikin ni ko shi sai naji yace mamaa karbi kudin hannunshi dana fito zan tafi sai na cewa ifan ba ka karbi kudin ba sai yace ai nakine nace to ka raba mana yace a'a kar kiji komai dana je gida yau ma duk abin da ya faru sai dana kai labari tun daga wannan
rana dai kusan kullum sai naje studio don ina barin makaranta nake wucewa wata rana naxo kamar daya saura na rana ban dade da zama ba aka kira sallar azahar sai nace wa ifan ina zanyi salla sai yace na shiga daya shagon wanda daga vocal sai shi ina shiga naga wata tana zaune a kujera na gausheta ta amsa nace Dan Allah sallah zanyi tace zoki shiga nan ta bude bandaki na shiga nayi alwala sai naji tana cewa idan kin fito ga sallaya nan kiyi a nan ina fitowa naga har ta shimfida bayan na idar sai naga ta shigo tace min ashe ke ce sabuwar mawakiyar vocal koh? nace mata E tace ni sunana zainab barkanki da zuwa nace na gode tace min bara nayi salla sai muje mu ci abinci
nace mata to bayan ta idar ta re muka jera har gurin abinchi wani restaurant da yake kallon benen da muke wato shab'an bayan mun fito muka koma nan muka hau hira har da su kwatancen gidajen juna ashe ita ma waka take yi amma ba guri daya muke ba zan iya cewa duk matan dana fara haduwa da su ita kadai ce ta karbe ni hannu biyu a farkon ganintada ni xan iya cewa a wata daya zuwa biyu na gama gane industry dan na fuskanci ita ma kamar makaranta ce daan akwai bangare bangare kuma ko ina da mawaka maza da mata haka duk studio akwai makada ko makidi haka kawai yaran studio masu kuma aiki daban daban zainab tana daya daga cikin wa yanda suka nuna min gurare don a mafiya lokuta muna zaune idan aka kira ta aka ce to zo tayi amshi sai tace dan Allah naxo na rakata to kusan a haka nasan wasu guraren da studios din.
MUHD-ABBA~GANA
www.abbagana.pun.bz
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.