shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Sunday 29 November 2015

KAUNA CE SILA***41---45

kauna-ce-sila.jpg

[8:55PM, 11/28/2015] Bana: KAUNA CE SILA 41





MUHD-ABBA~GANA






sai tace haba ke kuwa don Allah ki zo ko gaisawa ai ma yi nace mata to amma ba dan ina da shirin zuwa ba nasan ita kawar amaryace kusan yar uwa ne to ni kuma fa nan na ce dan ango zani shima ce min yake bai san ranar ba har ranar tazo na tashi zan yi alwalar salllar isha sai naji wayata na kara ina duba mai kira sai naga marwan abokin ya ahmad ina dagawa yace baza ki zo bane gamu an hadu za a tafi nace nifa ba zani ba yace amma da baki da kirki bikin yayan naki guda nace E ni ba zan iya zuwa ba yace don Allah ki zo akwai abin da yasa nake son kizo idan kina kaunar Allah da annabinsa ki fito yayi ta min magiya nace masa shikenan bara na taho



MUHD-ABBA~GANA



www.abbagana.pun.bz


KAUNA CE SILA 42




MUHD-ABBA~GANA




yace yawwa koke fa har na ji dadi gurin ya cika sosai lokacin dana isa gurin ango da amarya basu karaso ba amma naga kawaye na nan muka tsaya muna ta sururu muna dariya mu ce wanan muce wancan saboda yawan mutane ni bana iya hango kowa sai waka tana tashi sai kuma karar sifika muna nan din dai tsaye muka ji sanarwar ango da amarya zasu shigo kawai sai muka ji alamar bindiga kamar irin wadda akeyi wa sarki ai kuwa sai ga amar da ango hannun su rike da juna ango yayi kyau sosai ita ma haka ina ganin su naji wata muguwar faduwar gabaa kawai na fara innalillahi wa inna ilaihi rajiun har suka je suka zauna na daina ganinsu saboda mutane anan inda muke nan sauran kawaye na suka barni ni ba zan iya yawo a cikin gurin ba ina tsaye sai naji maganar marwan yace ana zuwa yin hoto da ango da amarya kizo muje



MUHD-ABBA~GANA




www.abbagana.pun.bz
[11:14AM, 11/29/2015] Bana: KAUNA CE SILA 43



MUHD-ABBA~GANA


Nace wallahi ba zani ba ai ba abin da nazo yi kenan ba sai naga yayi dariya yace haba ke kuwa menene na saurin yanke hukunci kuma tare da rantsuwa nace ba zan dai je ba ban dade ba na fito na tafi gida shima marwan waya na masa nace nifa na wuce gida yace to bama yaji na saboda hayaniya ina zuwa gida nayi shirin kwanciyar bacci ina tsaka da bacci naji wayata na kara na rasa me ya mantar dani ban kashe ba na duba nan naga marwan na dauka da alamun bacci nace hello marwan sai yace au bacci kike yi nace wallahi na fara bacci yace ikon Allah dama zaki iya bacci sai na bude ido sosai nace ban gane me kake fada ba yace a'a ji nayi ana ta hirar ki wai yau an san ba zaki iya bacci ba yayanki yayi aure nace lallai to waye ya fada yace yanzu ake fada anan zoo road nace to gashi ina yi kuma komawa ma zanyi sai da safe yace Allah ya tashe mu lafiya nace ameen na kashe wayata ba sai na nemi bacci na rasa ba kawai na tsaya ina tunanin maganganun da muka yi da shi nace wai me mutane suke nufi da ni ne? ba komai Allah yana nan na juya nayi kwanciyata tun daya Ahmad yayi aure sai na daina kiran shi amma ban daina tunaninshi ba dan abune wanda ba zan iya hana kaina ba haka na ci gaba da gudanar da rayuwata yadda na saba a ban garena da salisu yanzu ya dan kara sakin jiki dani koh dan yaga ya ahmad yayi aure ne oho yaci gaba da zuwa gidanmu amma yanzu ba kamar da ba.



MUHD-ABBA~GANA


www.abbagana.pun.bz


KAUNA CE SILA 44



MUHD-ABBA~GANA



ZA ayi kamar wata biyu da bikin ya ahmad wata rana kamar misalin karfe daya saura ina zaune sai kawai na hangoshi yana kokarin rufe motarsa yana waya ina zaune ya shigo yana shigowa na gaisheshi ni dai naga ya kalkeni sai da ya dade yana kallona sannan ya amsa ashe gurin mai gidan mu ya zo a yi masa kida ina nan naji har an fara masa kidan akwai wata hauwa itama a gurin mu take tare da ita muke zaune lokacin daya shigo nace mata tashi muje kasa muyi alwala ta riga ni fitowa daga inda muka yi salla ina zuwa sai na tarar da su dukan su a zaune har da ya ahmad sai ya kalleni yace ina zan samu gurjiya? sai na kalli waje nace suna wucewa bara na duba ai kuwa sai na fita neman gurjiya dana samo sai naga shi ya koma inda ake masa kida kafin ya fito sai hauwa tace min waya fa aka masa sai naji yana cewa gurjiya to ko matar sa ce tace tana so nace mata oho yana fitowa sai naji yace a juye gabansu to ni dai anan naga yana ci dan su mai gurin ma duk sunci kamar biyu da minti goma ya sake fitowa yace min baki bani wake da shima fa tace bara a kawo maka yace to ya koma inda ake masa kida nan na gugice ina neman food flask jikina har rawa yake naje na wanke na cewa zainab dan Allah tazo ta rakani ai kuwa sai sa naje har dangi naje na siyo masa na kawo masa ya ci ranar ya dan dade a gurin mu dan sai da uku ta wuce sannan ya tafi yana tafiya hauwa ta sakani a gaba wai nice uwargida amarya tana gida tunda yace na bashi abinci nace a'a ai ni ba saurayi na bane yaya nane kuma ai ba wani abu bane dan yace na bashi ko sai kawai tayi dariya.




MUHD-ABBA~GANA


www.abbagana.pun.bz


KAUNA CE SILA 45



MUHD-ABBA~GANA





Wata rana da safe na fito kamar sha daya da rabi dan a lokacin yajin aiki muke yi bamu ma da ranar komawa sai marwan ya kirani yace in gani a kasanku zanci waina kina sama ne nace eh bari na sauko bayan mun gaisa sai yace wannan yayan naki ne ya fito dani aiki nake so yayi min wallahi bara ma na kira shi sai ya fara neman layin shi daya dauka sai naji marwan nace masa ya jikinka Allah ya baka lafiya yanazu zaka fito? sai nace a'a gaskiya idan ba kudi zaka bashi ba ba zai fito ko bashi wahala ba sai naji narwam yana cewa kana jin kanwar kako ban san me yace masa ba har suka gama suna gamawa sai naji waya ta na kira ina dubawa naga sunan ya ahmad ina dagawa sai naji yace kuna zoo road ne sai na cemasa eh yace gani nan sai nace ya jiki yace da sauki sai na rasah me zance sai na kashe na cewa marwan bari na koma sama yace min to shikenan ina zama kawai na fara rubuta masa text kamar haka" SANNU ALLAH YA BAKA LAFIYA YASA KAFFARA CE YA KARA SAUKI
bai yi min reply ba amma dai nasan ya gani dama bai saba yi min reply ba saboda haka ban damu ba ranar nan mun sauka za muyi alwala sai kawai naji ina san kiran ya ahmad ina kira ya daga nace masa nifa bana ganinka sai yayi dariya ya ce ya gari ya kano? sai nace ya kano kuma? sai yace to ya vocal? nace vocal lafiya yace ya komai nace lafiya yace to yayi kyau by muhd abba gana





MUHD-ABBA~GANA




www.abbagana.pun.bz
Share:

2 comments:

  1. yayi kyau admin .muna taredakai dari bisa dari

    ReplyDelete
  2. muna jin dadi allah yakara basira

    ReplyDelete

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive