shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Sunday 28 February 2016

BANA KAUNARKA!!! 30

bana-kaunarkajpg.jpg BANA KAUNAR KA!!! 30 MUHD-ABBA~GANA--------------------------------------- sun rushe gidansu gaba daya an gyara shi an canza masa fasali yayi kyau ainun raba shi biyu sukai ya kasance kofa daya ce amma kowa barinsa daban bbu mai iya ganin wani koda kuwa za,a shekara daya gidajan sun tsaru iya tsaruwa in ba wanda ya sani ba sai yayi tsammanin gidan mutum daya ne,sannan da dan tazara tsakanin gidan wannan da wancan a wannan lokaci aka sa ranar bikinsu mahida da haidar,mamy da ya faruq. A school ina zaune ina shan lemo rani,direba nake jira can na hango bom boy yai fakin bai fito ba na mike na karasa na bude motar na shiga tare da sallama ya zuba min kwala-kwalan idanunsa bai ce min komai ba ya tada motar har muka bar makarantar har muka isa gidansu dake GRA tun daga net nake kallon gidan,gaskiya gidan ya tsaru a kayataccen falon muka zauna ya kawo lemo da keck na dan tsakura domin hankalina na gida kan carpet ya zauna yace min sauko na sauko muka zauna muna fuskantar juna,ya matso daf dani har muna jin sautin numfashin junanmu kamar mai shirin maidani ciki. wahida na dago muka zuba wa juna ido wani irin yarr naji haka nan gabana ya shiga faduwa jikina ya dau rawa amma sai na dake na basar na sunkuyar da kai look wahida ina son ki bani ten minutes,na dago ba tare da shakka ba amma sai me sam na kasa jure kallon kwayar idonsa da kyar na iya minti biyar na sunkuyar da kai wahida ya furta cikin wata kasalalliyar murya na"am wani taimako nake so ki min dan girman Allah wahida ina son fitowa maganar auranmu wahida don girman Allah ki taimaka min wata tafiya ce ta kamani ta tsawon shekara daya in mun samu nasara kan shekara ma zamu dawo ina so ki yadda a hada auranmu da na su haidar a daura inna dawo sai ayi biki a tare,wahida ki taimaka min na mike tsaye tare da kare masa kallo na yamutsa fuska wallahi ka bani mamaki ka bani kunya wai shahid kai wanne irin dakiki ne sau nawa zan fada maka i don't like you na fada yafi a kirga shahid amma zan maimaita maka so ko bana sonka BANA KAUNARKA,wato shi yasa kaje har makarantarmu ka dauko ni kin san abin da kika fada ya fada cikin karaji nine dakikin? i don't know idanunsa sun kada sun yi jajir ya janyo dirowa ya dauko wata kwalba ya daga me zan gani ni wahida barasa dole ne ki sa min mafita cikin biyu daya ko ki amince da bukatata ko kuma yanzunnan insha abin da ba kya so,ka sha man me ya dame ni ya kara rungumo ni idanunsa na fidda hawaye sai dai ko a jikina nace mallam sake ni anki a sake ki nace dama haka ka iya wa ya san abin da kake yi in ka tafi dama irin ku ne masu kama yayan mutane kuna.........saukar mari naji tas,tas, gaba daya na gigice cikin tsananin bacin rai yace tunda nake ban taba zina ba ina mayi ne wahida akanki zan fara ya fizgeni kamar kayan wanki yai dakinsa dani wata irin matsa yai min wadda na tabbata da ciki ne dani da bbu abin da zai hana dan cikin bullutsowa. Abbagana hausa novels @ facebook. www.abbagana.pun.bz
Share:

Thursday 25 February 2016

BANA KAUNARKA!!! 29

bana-kaunarkajpg.jpg BANA KAUNAR KA!!! 29 -------------------------------------------- cikin tsawa zaka san ko ni waye,amir yanzun nan zan maka bayanin ko ni waye,nine shahid bomboy jikin amir ya dauki karkarwa ya san bom boy kamar yunwar cikinsa bom boy yana da sauki yan da zafi muddin aka taba shi ba wasa tunda sun taba yin sa insa wadda basu jima da shiryawa ba gashi yanxu ya bullowa kansa ya salam tabbas ya san yana son wahida amma fa ba irin son nan ba me zafi domin karfin son sha'awa ce yarinyar komai nata burgeshi yace sannan bbu abin da yafi daukar hankalinsa irin kirjinta me dauke da albarkatu sannan mazaunanta masu birkita masa kwanya abin da yake jan hankalinsa kenan har yake tunanin ko sonta yake to yanzun ma so yake ya lallabata taso shi sannan cikin dabara ya samu ta biya masa bukatarsa in yaso sai ya samfe abinda yake so kenan.amir ya shiga bawa bomboy hakuri ya kwantar da kai amma a zuciyarsa ya dau alwashin sai ya lalata rayuwar wahida........kana jina amir ka fita daga sabgar janwata,amir na sonka fiye da yadda ka san kanka wallahi har in ji in gani ka san Allah ko magana kar ka kuma shiga tsakaninku in kunneh yaji jiki ya tsira,ya kashe wayar .bom boy yaiwa abba sallama abba yace haba shahid ka kwana mana ai duk gida ne shahid yai murmushi tare da duba agogon hannunsa 1:30pm ya ce Abba ina da wani aiki ne a gabana to shahid Allah ya taimaka,amin abba na gode.washegari da wayar boy na karya hello,nace cikin muryar bacci kin tashi lafiya? lafiya lau bomboy bana ce miki bana so ba ni kuma nace ina son bom boy yai dariya haba tawa kina so ki dinga cemin yayanmu su tasu suma suce min dariya ta kwace min domin ina tunanin wasa yake min nace ai sai mu hana su yace na yadda amma da shahid in munyi aure zaki dainace min,nai dariya cikin dariyar nace na yadda.ina kwance cinyar mom sai faman shagwaba nake mata mahida na kicin yaya faruq sai hararata yake yi ni kuma na kara shagwabewa mom tace auta kin manta goma daidak al'amin zai iso? da sauri na mike na fada dakin yaya tunanina gyara masa dakin ko ina kamshi ke tashi gaskiya ina son yayana al'amin. ina kwance a dakinmu naji yana my sister da gudu na fito na fada jikinsa yaya nayi missing dinka ainun yaya don Allah karka kara tafiya ka dade ba zan kara dadewa ba in ce sai kin gyara min dakina na girgiza kai yace kin soma nai dariya yace kin girma da yawa la,ni din don bakaga mahida bane.na hada breakfast na kai masa lokacin yana wanka don haka na ajiye masa na koma dakinmu ina me farin cikin ganin ya amin mai sona dawowar ya amin ba dan karamin dadi tai min ba domin yana dawowa ya soma yi min kiciniyar makaranta ba,ayi wani bata lokaci bana soma zuwa makaranta na tsaida hankalina akan karatu bbu wasa,wayata kanta cire sim card dinnan na ajiye saboda bom boy kam ya takura min. Abbagana hausa novels @ facebook. www.abbagana.pun.bz
Share:

Tuesday 23 February 2016

BANA KAUNARKA!!! 28

bana-kaunarkajpg.jpg BANA KAUNAR KA!!! 28 MUHD*ABBA*GANA 09039016969 -------------------------------------------- din motar dan na san da magariba ba kya gani saboda bacci naifar tare da kanne ido nace kamar ka sani domin har na soma jin bacci na bude motar na shiga domin na lura na haifar masa da kasala mamy ta leko gaskiya kun yi min kyau gashi kamarku daya Allah ya barku tare for ever amin yace tare da mika mata bandir din naira dari dari nace keh mamy kin taba ganin yayan da ya yakeso ya auri kanwarsa? bom boy yace za a fara akanmu mun soma tafiya ya kira sunana "wahida" na'am kar in kara jin bomboy a bakin ki na dago muka hada ido na rausayar da kwayar idona nace toh yaya muna zuwa gida na fito muka jera mom muka tarar a falo bom boy ya gaisheta sannan ya wuce dakin ya faruq mom tace auta maza tashi kiyi sallah wash mom na fa gaji ta kalle ni a kafa kuka taho na girgiza kai to maza tashi kiyi sallah na mike da hanzari. mun hadu muna cin dinner da mom ta tanadar mana waya tace ta cika falon da kara na dauka amir ne nai tsaki kai wannan amir da naci yake na kashe wayar na cilla kan kujera ta ganni kowani yake kallo ba kamar bom boy sai na mike ina gunaguni na bar falon,mom ce tai kira nazo auta na jawo na zana waya bata miki idona ya karo ruwa cikin shagwaba kamar zan kuka nace ba wannan amir din bane abokin yaya al'amin ya takura min ni kuma wallahi bana sonsa na shige dakinmu ina shigewa ya shahid ya shigo wahida ta waya bata miki rai,b wannan nataccen amir din bane ya takura min ke me yasa ba kya sonsa na dago na zuba masa ido tare da turo baki na kara shagwabewa kamar zanyi kuka nace na fada muku ni karatu zanyi ba kya sonsa kenan? na daga kai to shikenan dakko min wayar na mike na dauko na bashi a daidai lokacin wayar ta shiga ringing,abba ne yace wahida maza kizo,to abba nai saurin mika wa bom boy wayar na fita.abba gani yace wahida waye yayo miki waya na zauna na kwashe duk yadda akayi na fada masa to ke meyasa ba kya sonsa? nai narai-narai idona ya kawo ruwa nace abba karatu na fada masa ba yanzu zanyi aure ba,abba kinga abinda yake hada ni dake to meye abin kuka to abba bana so yana bugo mi waya to shi kenan kiyi hakuri zan yiwa ya amin din magana ya faruq yace gaskiya abba ku kuke shagwaba wahida shi kenan ita kowa bata so,abba hannu kawai ya daga masa ya mike yana jin haushina ya bar gun abba yai ta lallashina tare dayi min nasiha. bom boy ya latsa lombobin amir wayar ta shiga ringing amir cikin zumudi ya dauka hello,hello my sweety heart don Allah kin amince,Allah ina tsananin sonki wahida taimaka ki bani amsa tun kan gubar sonki ta halakani,wahida ina sonki...............bom boy ya cije lebe yana jin tsananin takaici ransa ya baci hankalinsa ya tashi ya mike kamar wanda aka cakawa allura yai saurin katse amin din stop it!! har ni zaka fadawa maganar banza,wanne kai? in ji amir. Abbagana hausa novels @ facebook. www.abbagana.pun.bz
Share:

BANA KAUNARKA!!! 27

bana-kaunarkajpg.jpg BANA KAUNAR KA!!! 27 MUHD-ABBA~GANA 09039016969 -------------------------------------------- nai sallama sama da goma da sauri na shiga yana zaune ya hada kai da gwiwa a salube na karasa na tsyngunna nasa hannu na dago fuskarsa wadda ta jike sharaf da hawaye idanun nan sun kada sunyi jajir ya shahid menene ba ka da lafiya ko anti ce?wayyo shahid ka bar yiwa anty kuka cikin kuka na furta kuka nake sosai na rike hannunsa gam yayi shiru wahida bbi abinda yake damuna da sauri muka zubawa juna ido har sai da muka gamsu dan kanmu na hango tsantsar kauna ta cikin kwayar idonsa ganin kallonsa na haifar min da kasala na sunkuyar da kai nace don Allah ka tashi kai wanka nan ma ba musu ya mike ya shiga toilet da hanzari na gyara masa dakin na feshe shi da airfresner sannan na fita. Shahid na fitowa sanyin ac da kamshin airfresner ya sanyaya masa zuciya hannu ya daga Allah ka bani wahida don hasken annabi da alkur'ani ya zauna gaban mirror yana kallon kansa tabbas ya rame rama ba yar kadan ba yai make up shadda yasa marun ya fesa turarensa me tsananin kamshi ya fito cikin kwalliya bakin takalmi yai amfani dashi yana fitowa wahida na mikewa inna ni zan tafi wahida ki kwana mana ayya inna ban ce zan kwana ba sai dai inna sake zuwa to ki gaida mom din.na shiga mota ina shirin tayar da motar ya bude ya shigo na kalle shi yai min kallo muje kawai na tada motar kai tsaye gidan baba rabiu ba nufa dake sabon titi ya kalle ni ina kuma zamu? na kalleshi nace yaya ina son bawa mamy sako ne bana so fa kina ce min yayan nan na kalleshi to me zan ce maka? kice min nawa ko kice min my darling uhum sai dai ince my brother ya harareni kasan sunan da nake tsananin jin dadinsa? ya girgiza kai ina son sa kai kuma baka so muce maka shine bom boy,daidai lokacin nai fakin da gudu mamy ta fito ta rungume ni ta kalli shahid dan uwa ku shigo daga ciki mana bayan mun gaisa da umminta muka wuce dakinta ta shiga hidima damu sai data cika sannan ta zauna shahid ina wuni kun wuni lafiya? ya muka ji da hakuri hakuri mun gode wa Allah Allah yai musu rahama "amin don albarkar annabi(S.A.W) n gaishe ta tace ina kika baro min mahida? tana gida.waya ta ta shiga kuka na dauka hello,naji ance daga can bangaran,salamu alaikum,aim wa alaikasalam,wahida "na'am wanene kai? wahida ba ki gane ni ba? amir ne ya hakuri? Alhamdullilahi to Allah ya jikan musulmi amin na gode,amir sai anjima na kashe tare da cilla wayar jaka don ganin yadda bom boy kole watsomin harara da wa kike magana oh yaya kenan na fuskanci tunda na soma magana hankalinka na kaina,to amir ne abokin yaya al'amin ya bugo yai min gaisuwa waya ba shi number ki ina tunanin ko gun ya amin ya amsa okey zamu haduda al'amin din taso mu tafi mamy ta ce oh bom boy ba dai kishi ba tun yanxu daku bari kuyi sallar magariba da sauri ya fice yace ba kya cewa mu kwana naiwa ummi sallama muka fita ya cemin bani key, Abbagana hausa novels @ facebook. www.abbagana.pun.bz
Share:

Saturday 20 February 2016

BANA KAUNARKA!!! 26

bana-kaunarkajpg.jpg BANA KAUNAR KA!!! 26 MUHD-ABBA~GANA gargadi:ban yarda wani ya cire koh ya kara wani abuba -------------------------------------------- ina tunanin daga masallaci suka fito shida shahid ne yai gun anti nai saurin cewa ya shahid kar ka tashe ta ta samu bacci cak ya tsaya ya zuba min kwala kwalan idanunsa masu tsananin kyau na lumshe idanuna ina jin wani sanyi na ratsa min duk ilahirin jikina toko shine so? no! ni nasan ko kadan bana som bom boy kome yasa oho ma muryar shahid din ita ta dawo dani hayyacina yace anty tayi sallah ne? a,a gani nai ta samu bacci shi yasa na kyale ta da sauri ya karasa ya kama hannunta jin sa yai kamar kankara yai saurin yaye bargon da wahida ta rufa mata tare da taba jikinta inalillahi wa inna ilaihi raji'un ya dago a firgice yana karkada hannu yana fadin abba anty bbu,anty bbu ya sulale tare da dafa kai da sauri abba ya karasa mikewa da gudu na karasa ina girgiza anty,anty ki tashi don Allah kar ki tafi ki bar mu anty kuka nake sosai a daidai lokacin likitoci suka shigo tun daga lokacin ban kara sanin meke faruwa ba sakamakon suman da nai.shahid bai taba shiga tashin hankali irin na wannan rana ba,don ma karfin addu'a da taimakon ubangiji ya samu nutsuwa. Bayan sati biyu wahida zaune ta hada uban tagumi wasu irin hawaye ke shatata akan kumatunta ya faruq ya shigo ya zauna wahida ya kira sunan cikin sanyin murya na dago na kalle shi sai dai sam na kaaa tsayar da hawayen,wahida ya kamata kiyi hakuri addu'a zakiyi wa anty,tashi kiyi wanka kinji Allah ya ji kanta "amin" na mike na nufi bedroom dinmu nai wanka na fito cikin atamfa gold star ba wata kwalliya nai ba nasa hijabina dakin mom na shiga nace mom zani gidansu bom boy mom ta kalle ni wahida kin ga kuwa yadda kika rame na rausayar da kai ta ci gaba,din Allah wahida ki kwantar da hankalinki ko kina so kema mu rasa ki? na girgiza kai tace to kar ki dade wai ma me zaki yi a gidansu bom boy din? mom kayana zan kwaso sannan ina son ganin bom boy domin na san..... shigowar ya faruq ce ta katse min maganar na mike kawai na fice, na zauna a motar ina shirin tayar da motar hassan me bawa filawa ruwa ya rugo da gudu yana daga min hannu, hassan dattijo ne domin a kalla zai yi shekera hamsin muna mutunci sosai domin akwai shi da ban dariya yana zuwa ya tsungunna,an gaishe ki sarauniyar kyau na tabbata duk nigeria bbu mai kyanki wahida ta mahida hajiya wahida ta alhaji al'amin family dinku na kaunarku muma muna kaunarku,domin kuna fita hakkinmu ya dan sassauta yana washe baki na harare shi ta kasan mutuwa akai min ba sorry ya hakuri? nace mun gode Allah to Allah ya jikan musulmi Allah yai musu rahama, amin nace sannan na dauko dubu biyar na bashi ya zube yana kwara godiya ya bani tausayi ainun a sallibe naja motar. nai sallama falon kakarmu da haidar suna zaune suka amsa sallamar na zauna ina gaishe su,kakarmu tace yanzu nake cewa zanje duba ki ashe kina tafe na sunkuyar da kai nace shahid na nan kuwa tace eh dakinsa na shiga nai sallama, Abbagana hausa novels @ facebook. www.abbagana.pun.bz
Share:

Friday 19 February 2016

BANA KAUNARKA!!! 25

bana-kaunarkajpg.jpg BANA KAUNAR KA!!! 25 MUHD-ABBA~GANA 09039016969 -------------------------------------------- ina shiga na kankame ta ina kuka hannu ta daga da kyar ta shafa kaina wahida ba dai abin sa sukai miki ko? a daran yaya shahid dani muka kai anty wani babban asibiti kudi basu yi wata-wata ba suka shiga da ita emergency likitoci sunyi nasarar cire mata bulet din ina zaune na hada kaina da gwiwa ya shigo taso mu tafi yace min na mike na bishi muna isa muka tarar su abba mom atu baba rabiu duk sun zo har anyiwa daddyn wanka kukan da nake yine yasa abba yayi min magana tashi ki koma daki ina kallo shahid na kwararawa mahaifinsa addu'a waya naiwa haidar cewa maza ya taho gida bbu lafiya kan kice meye wannan gidan ya cika da mutane tashin hankali, haidar ya iso ya tadda ana shirin fita da mahaifinsa daga dakinsa lokaci daya ya birkice da kyar aka shawo kansa yaiwa mahifin nasu addua,amma sumansa uku koda za,a dauke shi kukan kura yai ya rike makarar ya dinga duka masu rike da ita,shahid shi ya dauki haidar yasa shi a daki ya kulle sannan aka samu damar fita da mahaifin nasa a asibiti kuwa sunce basa bukatar dan jinya sai dai anti da kanta ta roki a bata wahida saboda haka wahida ce a gurinta.bayan sati daya ba laifin jikin antin yana sauki ranar shahid da haidar abba da baba rabiu anty ta soma yi musu magiya hadda kukanta su fada mata gaskiya ina mijinta yana raye ko kuma ya rasu kukanta ya daga hankalinmu ainun,haidar yace anty sai dai hakuri amma maganar gaskiya daddy ya rasu yaune kwanansa bakwai gaskiya ta girgiza domin bbu wanda ya ankara sai ganinta akai wanwar a kasa ta fadi tuni jini ya balle haidar ne ya kira likita,likitoci sukai hanzarin dauke ta wani likita ne ya dinga fada kun gani kun wargaza mana aiki shi yasa muka fada muku bamu.....kan ya karasar bom boy ne cikin fushi ya dakatar dashi ya dinga yiwa likitan bala'i da kyar abba ya ja shi suka tafi.tsakad dare ina zaune kan abin sallah tace wahida ban ruwa insha na mike na dauko robar swan na tsiyayo a cup na dago kanta na bata tasha sosai har tace ya ishe ta na maida ita ba kwantar tace sannu wahida nace yauwa wahida Allah yai miki albarka ubangiji Allah ya raba ki da sharrin makiyanki amin,wahida ki taimaka ki bawa dan uwanki ishassun hadin kai shahid yana tsananin sonki anty ba wai bana sonsa bane ina son karatu ne to wahida Allah ya taimaka ameen,ta koma ta kwata ina jin ta tana ta jero kalmar shahada koda inda saboda yace na saba jin irin wannan saboda koda yaushe sannan duk irin baccin da anty take yi muddin akayi kiran sallah ta kan ce in taimaka mata tayi alwala tai sallah yau ma ina zaune har akayi sallar asuba sai dai nayi mamakin yadda har aka idar anti na bacci komawa nai na kishingida bacci ne ya soma daukata sallamae abbana naji shi da ya shahid. Abbagana hausa novels @ facebook. www.abbagana.pun.bz
Share:

Wednesday 17 February 2016

BANA KAUNARKA!!! 24

bana-kaunarkajpg.jpg BANA KAUNAR KA!!! 24 MUHD-ABBA~GANA -------------------------------------------- bom boy sadaf! sadaf! ya shigo saboda haka bbu wanda ya ganshi kai tsaye dakin wahida ya shiga ganin dakin a bude ya razana shi yana danna kai ya soma jin ihun wahidar ogan yana rike da ita gaba daya ya gama fita a hayyacinsa bbu abin da yafi buri irin ya cimma burinsa,ta baya bom boy ya anyo ransa ya gama baci hankalinsa a tashe gaba daya ya birkice shi kuwa oga tuni ya mance da abin da ya kawo shi wuka bom boy ya soka masa a kirji ina kuka na mike da gudu na kankame shi ya daga aina muka gama ido ban taba ganin shahid cikin irin wannan yanayin ba cikin kakkausar murya yace bai taba kiba ko? cikin kuka nace eh maza ki sa kayanki ki kulle dakinki tuni na rike shi ina kuka to saka kayanki in kai ki dakina ki kulle nasa hijabina ya kaini dakinsa na kulle yace kar ki fito kin ji nace to dakin anty ya nufa gaba daya y tasar musu kasancewar yana da wani sirri wanda shi kadai ya sanyar wa kansa sani don haka cikin kankanin lokaci ya dama dasy ya shiga dakin kwance ya ganta cikin jini inna lillahi wa inna ilaihi rajiun dagowar da yayi ido hudu da wasu suna shirin guduwa yai amfani da piston ya harharbe su ta bude idonta da kyar take magana kaje dakin wahida da mahaifinka da sauri ya mike ya nufi dakin mahaifinsa a kulle ya ganshi cikin jini harbi biyu daya a kai daya a kirji kadan ya hana shahid zautuwa sai dai albarkacin kalmar da yake ta maimaitawa yasa nutsuwa tazo masa ga abinda yake cewa, innalillahi wa inna ilaihi rahiun Allahumma a jirni fi musibatin wa aklifli khairan minha Allahumma la sahla illah maja alhu sahla wa anta taj alul hazna iza shi ita sahla.koda naji shiru bbu alamar motsi sai na fito da gudu nai dakin anty na dinga tsallake su ina wucewa caraf wani ya damko min kafa tuni na shiga ihu wayyo shahid kaxo zai balla min kafa wayyo da hanzari ya fito ya duba dakinsa bai ganni ba a dakin anty ya ganni tsawaya doke min ke wacce irin yarinya ce waya ce ki fito ba yi magana ba na ci gaba da kukana ina nan ina kuka naga sojaji sunata shigowa bayan sun gama shigo wa daya daga cikinsu ya kalli shahid cikin harshen turan ci yace ma akai min ina ji yaya na masa bayani kafa yasa ya doki hannun da gudu nai dakin anty bbu wanda suka taba ko? shahid ya daga rinanim idanunsa aya ce sun harbi dady har guri biyu dad dina Allah ya amahi abinsa sannan sun harbi anty a kirji gaba daya suka sa salati amma musulman cikinsu daga nan yai musu jagora dakin mahaifinsa sun kwace shi sun shimfidar dashi a gadonsa tuni likita ya shiga aiki. Abbagana hausa novels @ facebook. www.abbagana.pun.bz
Share:

Thursday 11 February 2016

BANA KAUNARKA!!! 23

bana-kaunarkajpg.jpgbana-kaunarkajpg.jpg

BANA KAUNAR KA!!!

23

MUHD-ABBA~GANA


09039016969
--------------------------
Allah ya kiyaye ni bana son biriziyya to ai gashi nan ya kalli bati ai kuwa har Allah ya isa nai masa oho ke zata bi. bom boy ya shigo shi da small boy na mike na bar musu falon domin ni haushinsa nake ji sai bayan la'asar mahida ta tafi na zauna ina kallo dakin anty yai sallama yayi shiri na kalli agogo lokacin fitarsa yaya sai kuma gobe da safe na mike na fice ya kalli anty,anty zan tafi sai da safe anty ta janyo wani galan ta dauko glass cup ta cika masa shi da rubutu ya amsa yai bismillah ya shanye tace ka shirya kaje katsina malam baba yana son ganinka to anty yaushe zani kin san fa bani da lokaci ka daure dai kaje ko wuni kayi to anti kaci abinci ya shafa cikinsa rabonsa da abinci tun karin safe ya kalli anti yaga tana kallonsa yace yanzu nasa wahida ta kawo min okey miko min zam zam din can ya mike ya dauko ta juyo a cup tai masa tofi a ciki ta bashi ya sha tai masa nasiha irin tasu ta manya daga nan yai mata sallma har ya fita ya dawo anty ina small, small ya tafi katsin can zai kwana me yasa bai fada min ba kayi hakuri ya fada min in sanar maka mantawa nayi okey Allah ya dawo dashi lafiya amin dakin wahida ya shiga tana zaune tana zuba abinci ya zauna ta mike ta bar masa abincin yai murmushi tare da riko hannunta dan girman Allah ki zauna billahillazi rabona da abinci tun karin safe please help me ta koma tare da cigaba da zuba mana tare muka ci yana min hirar irin nasarar da suka samu a tafiyar da suka yi,muna gamawa ya min sallama ya tafi na mike nai alwala nai sallah sannan na kwanta.bakin dare misalin karfe biyu na shiga toilet na fito ne ina shirin kwanciya sai naji kamar ana dirowa dif!! dif!! dif!! tuni kafafuna suka soma karkarwa jikina ya dauki rawa karar bindiga ita ta dawo dani hayyacina tuni na shiga laluban wayata na shiga danne danne har n nemo ya shahid layinsa na celtel a kulle tumi na tafi glo cikin sa,a ya shiga,hello yaya kana ina? gida a rude nake sosai nutsu ki fada min me ya faru? yaya ka fito barayi sun shigo mana gida barayi wahida to gani nan zuwa har ya kashe y bigo,wahida ki kulle dakinki ki zare key din kar ki fito har sai na dawo cikin kuka na ce to kayo sauri yaya daina kuka yanzu zan dawo shiru ba yaya haba tuni na fita da gudu nai dakin ya shahid na dinga dukan kofar ina kiran sunansa na koma dakin small nan ma a kulle wayyo nai dakin anty anan na gansu dukkaninsu sun wani nannade kansu da fuskarsu nan da nan nayo kansu ina dukansu ina ihu wani daga ciki ya daka min tsawa ke ina zaki? ban sani ba shegu tsinannu,la"anannu ogansu ya haska ni da toch light sanye nake da rigar bacci iya gwiwa wata mahaukaciyar dariya ya saka yace cool down beb ya kalle su ku karasa bari mu daidaita da baby yes sir,cak ya dauke ni na shiga dukansa har da cizonsa ina zaginsa amma bai dire ni ko ina ba sai bedroom dina runi ya raba ni da rigar jikina da gani sai pant ya shiga murzata san ransa,inallilahi wa inna ilaihi rajiun Allahumma ajirni fi musibatin wa aklifi khairin minha,la haula wala kuwata illa billahi aliyul azim,wala haula wala kuwata illah billah aliyul azim,wala haula wala kuwwata illah billahi.....sai kawai ya....to me kake /kike tunani iyeh!! iyayen gulma toh baza kuji ba

Abbagana hausa novels @ facebook

www.abbagana.pun.bz bana-kaunarkajpg.jpg
Share:

Wednesday 10 February 2016

BANA KAUNARKA!!! 22

bana-kaunarkajpg.jpg

BANA KAUNAR KA!!!


22


MUHD-ABBA~GANA



09039016969


gargadi:ban yarda wani ya cire koh ya kara wani abuba
--------------------------------------------
Gaskiyaba zaki koma ba yaya naga dakin ka duk ya canza shima ai yayi missing dinki bebinmu maza huta ki gyara mana dakinmu dakin abban kuma mun sha hira da abba sai da abba ya fiti na shiga dakin yaya faruq na wanko masa toilet sannan na ciro zanin gadon na shimfida masa wani lallausan bargo na goggoge na share na kunna turaran wuta dakin yaya amin shima ba gyara fes na janyo dakin na kulle dakinmu na koma ba zan iya fasalta muku irin yadda dakin ya koma bana dai gyara shina hada kayan wanki na bayar saida na kammala girki dare na gyara kicin din sannan na koma dakin nai wanka har lokacin su yaya basu dawo ba nai wasu mom sallama na tafi.
faruq na dawowa dakinsa ya tura haba sanyin a.c da kamshin turaran wuta dan maiduguri ya buga shi kujera ya zaina tare da fadin thank you sister ya zare kayan jikinsa ya shigo toilet shima sai kamshi yake gaskita faruq yaji dadi sosai haka zalika al'amin ya gode wa wahida.
iba zuwa gida ya shahid zaune a falo nai salama ya amsa min ciki ciji dakin anty na wuce nai sallama tana zaune ta amsa da fara'arta zama nai kusa da ita tace sannu da zuwa nace anty ya gida lafiya lau ya kika baro su mahida suna nan lafiya lafiyansu klau dakina na shiga wayata ta shiga ringing ya faruq sunansa ya bayyana akan screen din wayar cikin sanyin murya na amsa "hello wai a tunanina laifi nai masa me yasa kika ki bari mu dawo mu kawo ki gida? umh gani nai yamma tayi,okey naga dakina yai fes na gode fa dariya kawao nai.
Wahegari na tashi da matsanaicin ciwon kai da kyar na iya fitowa dakin anty naje na gaishe ta sannan dakin daddy sannan dakin small kamar in shiga dakin shahid wata zuciyar tace kawai in share shi daki na koma na cire hijabina sanye nake da wata yar bingilar shimi shara-shara domin kawai na kirjina a bayyane yake kasancewar bbu mai shigo min daki kwanciya nai anty ta shigo min da break fast din da magani ina zaune ina shan tea sun hadu gurin breakfast bom boy yace anty ina yar takine bata jin dadi ya mike me ke damunta bai maji amsar da antin ta bashi ba domin sam hankalinsa baya jikinsa ina zaune ina shan tea yai sallama zama ya yi a gabana ya zuba min ido oho ni na manta ya shahid ina kwance jin shiru nace au good morning domin in ance masa ina kwana ya kan ce mene kuma ina kwana? ikon Allah ganin yadda ya shagalta da sauri na kalli kaina wa iyazubillahi gaba yai mumunan faduwa shi kenan ya gama kalloba inalillahi nai waurin janyo hijabina na rufe jikina nakalle shi cikin bacin rai nace wallahi ka kalli haram ban yafe maka.....yasa hannu ya doke min baki uban wa yace ki zauna a haka to wa ya ce ka shigo min dakina na fada cikin kuka ya mike ya fice nasa kafa nai boll da tea din na shiga birgima shi kenan ya gama kallon abin da zai kalla ni ya cuce ni ya cuci masoyina mahida ta fado dakin ke kuma me kike wa kuka na shiga bata labari na ciro hijabina kin ga fa rigar toke me yasa ba kya son sa bireziyya




Abbagana hausa novels @ facebook.




www.abbagana.pun.bz
Share:

BANA KAUNARKA!!! 21

bana-kaunarkajpg.jpg

BANA KAUNAR KA!!!

21


Muhd Abba Gana


gargadi:ban yarda wani ya cire koh ya kara wani abuba
--------------------------------------------

Yaya ai na share maka ya kalli dakin cike da takaici ko tsarar da tai bata kwashe va a kofar dakin ta barta sannan dakin buzu buzu faruq yace ayya kadan daga cikin aikin mahida,Al'amin ai tayi maka mai kyau ni dana sata gaba daya karkashi gado ta tura min sharar ka ganta nan bbu abin da ta iya sai kallo sai soyayya Al'amin ya hau salati da kin san baki iya ba kice min to kanwar kanwarki ta fiki iya abin duniya,mahida kuka ta saka ai kun san tuni ya ba kuka sani al'amin dan haushin bai karasa magana ba lallai ya shiga tattare sharar.
kwalliya nayi sosai na shirya cikkin wani ratsatten less,leshin ya amshe ni nayi kyau ainun na rataya jakata na sa karamin hijabi dakin dubai anty na tafi to wahida ki gaida mom amma fa kar ki kwana to anty a wacce mota zanje? ta mike ta dauko min mullin nace la! anty motar yaya shahid umh ni dai tsoro nake kin san motarsa da sunansa kar inje aka mani,antu tai ta dariya bbu me kama ki kallo daya za,ai miki a san ke kanwarsa ce,bbu me kamaki na juya na salube kai gaskiya notar akwai kyau, mota ce wadda ta amsa sunanta rantsattsiya kirar zamani gaban motar kawai zaki kalla kinsan waye me motar da manyan baki aka rubuta BOM BOY sai dana gama karewa motar kallo sannan na bude na shiga wayyo sanyi da kanshin me motar yaso rudata na shiga lumshe ido kwance nai cikin luntsumemiyar kujerar motar jina soma gyangyadi nai kirgil hoton me motar dake jiyawa gaban motar na zubawa ido yana murmushi yayi kyau ainun hannu nasa na shafi a fuskarsa tare da fadin i love you so much yayana,wannan shine rashin sani wanda yafi dare duhu,ashe duk abinnan da nakeyi bom boy na bayan motar yana kallona,ohi sam ban sani ba koda na hau titi nayi mamakin irin yadda mutane da dama suka dinga daga min hannu kasancewar glass din motar mai duhu ne bbu wanda ya ganni gaskiya kan naje gida na kara tabbatarwa shahid mutumin kirki ne mai jama'a.
ina fitowa mai gadi yace sannu da zuwa yauwa baba tsoho ya gida? lafiya lau ina shiga sister ta fito da gudu muka rungume juna dakin Abba muka karasa abba sannu,yauwa sister wahida abba ina kwana? lafiya lau wahida,ya kika baro yar uwar tawa tana nan lafita ta mace in gaishe ku muna amsawa da sauri na mike da gudu nai dakin yaya faruq hello yayana na fada jikinsa ya dago fuskata sister amma kin dawo kenan? la! anty wata in dawo anya anty ba zata bar man keba,umh ai nafi son can saboda me? can sunfi sona basa dukuna da sauri na fita hello ya amin hello ya amin dina na dawo na rungume yayana yace yaushe kika zo sister yanzu nazo amma kin zo kenan munyi kewarki,




Abbagana hausa novels @ facebook.



www.abbagana.pun.bz
Share:

Sunday 7 February 2016

BANA KAUNARKA!!! 20

bana-kaunarkajpg.jpg

BANA KAUNAR KA!!!

20



MUHD-ABBA~GANA


gargadi:ban yarda wani ya cire koh ya kara wani abuba
--------------------------------------------
Muna nan zaune bom boy yai sallama a,a kace muna da manyan baki hadda mahida a gidan? mahida tace Allah yata muna zuwa kaine dai ba a samu ka ga yanxu ma tun dazu muka zo ba don Allah yayi zamu gana ba har sai mu tafi ba ka nan,ni sister ma ce min tayi kwata kwata baka kasar tabbas jiya cikin dare muka iso ku bani ten minuti in yi wanka sai daya soma duba anty sannan ya shiga dakinsa nace yauwa ya amin ga bom boy muna so ju fada mana cikinku waye babba? mahida tai caraf la! baki sani ba ai tsiransu kwana biyu shi yasa ma aka hada sunansu akayi rana daya ke ni dai ban yadda ba duk......bom boy ne yai sallama idona har cikin nasa yai min kyau yana sanye da fakistan ruwan madara karasowa yayi kusa dani cikin rada yace gimbiya me zan samu rabona da abinci har na manta na mike na shiga kicin dama tuni nai masa tanadi na musamman gaba daya na hado musu dasu ya amin can lambu na koma i na zaune ya amin ya shigo ya zauna ya kalleni yace ince dai yanzu soyayar tayi karfi murmushi nai kawai domin nasan babu wata soyayya.bayan isha'i suka tafi mahida taso kwana nina hana ta domin inta kwana bbu mai taimakawa mom wajen shirya abinci duk illahirin yan aikin gidanmu sam mom bata bari suyi mata girki ita take yi duk da kullum sai an fita da abinci masallaci komin yawansa ni zan taya ta ko kuma niyi ni daya sam koka dan mahida bata son aiki aikinta kwanciya game,kallo,karatun littafi,Allah ya sani sam bana son halin mahida domin ya mace ko ba komai aure za ai mata san a rayuwTa bbu abin dana tsana irin kazanta muddin ina gida in kin ganni zaune da dalili shi yasa duk irin fadan da muke da ya faruq ko kadan baya so ya budi ido yaga bana gidan domin in ina nan dakunansu kullum ne saina gyara musu nice wanke musu toilet gyaran gado hatta yan aikinmu su kanyi missing dina.
ina zaune dakina small ya shigo wahida bom boy na kira na kalle shi nace yana in ne? yana dakinsa na mike nasa hijabina na fita nai sallama yana kwance ya kalle ni cikin lumshe ido wahida nai masa shiru donni tsoro ya bani ma tunani ko wani abin yasha domin idanunsa sunyi jajir WAHEEDAH ya kara furtawa na'am na ce cikin sauri wahida bani da lafiya me yake damunka kece wahida kece ya kamo hannuna,hannunsa zafi kamar garwashi ba tausaya masa ainun amma don kar in kyale ya samu damar sai na fisge hannuna na ce bana son iskan....kafin na karasa ya fizgo ni ya rungume ni waye dan iskan? gabana ya shiga faduwa, ma don kar in nuna naji tsoro ya samu wata sabuwar damar sai na dake nace kaine dan.......yasa hannu ya doke bakina ya murde min lips ina wayyoahna! kafa yasa yayo ball dani sai gani a kofar daki da gudu na fita nayi sa'a falon ba kowa daki na shiga na kulle nai kuka mai isata.
maheedah zaune tana game Al'amin ya siga dakin mahida ya kira sunanta ba tare data bar abin da take ba tace na"am kanna dawo ki shiga dakina ki gyara min kin ga yayi kura sosai to sai ka dawo nai taci gaba da harkar gabana sai kusan magariba ta tuna tai saurin shiga dakin ta burbura sharar minti biyar tana fitowa ya amin ya shigo kai tsaye yai dakinsa ai bai karasa shiga ba ya kwala mata kira mahida da sauri tazo me na saki?

Abbagana hausa novels @ facebook
www.abbagana.pun.bz
Share:

BANA KAUNARKA!!! 19

bana-kaunarkajpg.jpg

BANA KAUNAR KA!!!





19
MUHD-ABBA~GANA

09039016969





gargadi:ban yarda wani ya cire koh ya kara wani abuba
--------------------------------------------

fari sol tunda ina da wanda zai min inji sanyi da ace bani da shi sai inyi kuka da samunka a matsayin yayana ke wahida Allah in na fito sai na zane ki Allah sarki duka don Allah in zaka fito ka taho da tabarya ko bindiga,na kashe wayar ina dariya a can gida kuwa,a fusace faruq ya fito hannunsa rike da belt kai tsaya yai dakinsu wahida mahida kwance ta takarkare tana waya yana shiga ya soma laftarta wayyo me nai maka ina wahida me za kai mata billahillazi in baki nuna min ita ba sai na zane ki mahida ta dinga dariya tace, wallahi wahida bata nan domin tana gidan anty yanzy fa ta yo min waya ta kare min rashin kunya dakin mom ya shiga mom ina wahida? wahida kwananka biyu da tafiya itama ta tafi gidan sister khadija ya juya yana gunguni dakinsa ya koma ya dauko waya bugu daya ta dauka hello kin san Allah in nazo gidannan sai na lahira ya fiki jin dadi banzamara kunya,Allah ya faruq kasan fa masoyina soja ne ni nasan in kazo gidannan ka taba ni sai ya harbe ka in kuma ka musa to kazo ni kuma zan masa waya ince ga wani yazo zai taba lafiyata kasan yana sona zai iya komai a kaina oho dai dadin abin ba sonsa kike ba la! da ka sani yanxu muna tsananin son juna na kashe wayar ina dariya.faruq ya cika da mamaki dama wahida na son shahid in kuwa haka ne gaskiya bom boy yayi dacan big girl kuma beautiful gentel girl dakin Al'amin ya shiga yake fada masa Al'amin yace kana mamakine? haba dole in yi mamaki ko dan ganin irin tsantsar kiyayyar da wahida ke nunawa shahid wallahi ka bar mamaki domin ka san bom boy dan soyayga ne tabbas zai iya lankwasa wahida san ransa.
ina zaune ina karanta wani littafi da ya shahid ya siyo min mahida day amin da ya faruq wayyo dadi ihu na sak na kankame mahida cike da tsatsan farin ciki kicin na shiga na hado musu abin motsa baki sannan na zauna ya Al'amin ina wuni sister ya gida? lafiya lau na lalli ya faruq koda ba gaishe shi kallon arziki bai min ba,anty ta fito tace a'ah lalle yau ina da manyan baki wahida me kika bawa ya"yan nawa? nai murmushi su ya amin suka gaishe ta na kalli mahida mahida ince ko kin taho min da kayana? ai zuwa muka yi mu tafi dake lalle ma keni ba yanzu ba Allah ko sai yaushe? na mike na koma kusa da ya faruq nace ke ni bar ni mu gaisa da yayana,na dafa cinyoyinsa ina tsungune kan gwiyoyiwa nace yaya faruq don Allah kayi hakuri wai ma me nai maka? na kwantar da kaina kan cinyarsa please ya faruq im sorry baki fada kunya Allah in baki bani guri ba zan yo boll dake,stupid girl,mahida ta taso kai don Aah yaya kar kasa ta kuka,ina laifi data baka hakuri,to ban hakura ba wato ke me yar uwa to kamo ni taso kinji anty wahida dadin ta ma ba Abba bane nice ke ma ba zan wani bashi hakuri ba muka koma kusa da yaya Al'amin muka ci gaba da hirar mu.




MUHD-ABBA~GANA



Abbagana hausa novels @ facebook



www.abbagana.pun.bz
Share:

Friday 5 February 2016

BANA KAUNARKA!!! 18

bana-kaunarkajpg.jpg

BANA KAUNAR KA!!!
18

MUHD-ABBA~GANA

09039016969
--------------------------------------------
to autar bom boy ai kuwa bom boy na gaishe ki ince dai yanzu kuna son juna haba dai mahida kina wasa dani wato kin mantani kenan kin sanni in nace in so to fa ina so in kuma bana so bana so na fada miki yanzu bani da lokacin soyayya karatu ne a gabana.....to uwar biro da takarda ya ishe ni ke kuma uwar soyayya fadi ki kara wallahi sai Aliyu haidar, da ya yamma ina kwance ya amin yayo waya salamu alaikum ya Al'amin ka tashi lafiya? lafiya my sister yaushe zaki dawo? kai yaushe zaka zo in ganka? in kinga shahid ai kamar kin ganni tunda kin ce muna kama koya kika ce?a'ah kai daban shi daban wai yaya su small sun girme ku? ke kin yadda? na dan yadda kadan amma to shi kenan ki tambaye shi kwana nawa ya bamu to ya ka gaisarmin da mom me zai hana ki buga ki gaishe ta? wayar tawa ce bbu kudi a ciki okey ki jira zan turo miki,godiya mara iyaka.minti ashirin ba'a yi ba naji karar text message ina budewa kuwa na shigar da lambobin #3000 ya sako min naji dadi sosai hello "na"am auta ya kike? "normal mom" auta ya gida yasu small? "suna lafiya mom ina nan zan zo "to sai kin zo mu kai sallama.
SHAHID tsungune gaban anti,tace wai ina za a tura ku shahid?"anti addu'a kawai zakiyi min domin tafiyar tanada........kai k sanar da su baka da lafiya ba zaka ba shahid bana son rasa ka bana son aikin sojannan anti ni dai addu'ar nake muradi shi kenan ki sanar da Dad dinku dadditunkan lokacin na sanar dashi okey Allah ya taimaka, amin mom ta dauko wani littafin addu'o'i ta dauko ta mika masa ya amsa yasa aljihu sannan ya mika mata hannunsa ta sumbace shi,yaso ganin wahida sai dai bata nan domin ta tafi gidansu lokacin haka ya tafi amma ba don yaso ba yaso ganinta suyi sallama! bayan sati biyu muna zaune a falo "hello mom wahida kin wuni lafiya? lafiya lau mom kice mahida ta kawo min kayan ke me zai hana ki fada mata mom kin santa raina ni ina fada mata cewa zatayi ba zata kawo min ba leda ita waye ya raina wani? mom ita ta fara raini nike da ita wacece babba? mom ita ta girme ni da kadan amma ashe dai ta girme ki zan sa ta kawo miki insha Allah to mom na gode sai anjima.
yaya faruq hello yayana ina jinki yace ince dai lafiya oh yaya kaga abin da yake hadani da kai ba ko ka tambayi lafiyata kace ya nake bana son jin yadda kai ken mun kai dai wallahi baka da sakin fuska kai dai me ganin fara'arka daga mahida sai sahibarka anty mamy,to ya ranki?


MUH'D-ABBA~GANA


Abbagana hausa novels @ facebook

www.abbagana.pun.bz
Share:

BANA KAUNARKA!!! 17

bana-kaunarkajpg.jpg

bana-kaunarkajpg.jpg

BANA KAUNAR KA!!!
17

MUHD-ABBA~GANA



gargadi:ban yarda wani ya cire koh ya kara wani abuba
--------------------------------------------
wahida in ce dai ta san kana yi? bari kaji in da ake soyayyar gaskiya ya dauko waya hadda sa handfree hello my dear kina lafiya? lafiya amma ba lau ba what? me ke damunki? ciwon rashin ganinka ina sister ta saku? wani zancan sister ki tana nan lafiya to ka gaisar min da ita kafin nazo okey zata ji yanzu me kike yi? tunaninka da son ganinka okey zan zo anjima me kake so in tanadar maka? nafi so ki akan komai na gode Allah ya kara mana son juna amin my sweety i love you so much gaba daya suka sumbaci wayar small ya kalli shahid ka gani kuma kaji da kunnanka shahid yace tsaya kaji nima ai tana sona tsabar ajine amma bari kaji ya kira wahida cikin sassanyar muryarta tace salamu alaikum amin wa'alaikaikumus-salam kana lafiya?yai murmushi farin ciki ni kaina saida naji sautin murmushin me kike yine? ina kwance ko wani abu zan maka? a,a kawai dai ina son jin ya kike ne? to na gode my brother a,a ban yadda ba to my shahed tabbas yaji dadin yadda ta furta a tunaninsa tunda aka rada masa sunan bai taba jin wanda ya fadu sunan yai masa dadi ba sai wahida yai murmushi yace ban yadda ba to my bom ke! ke! ke! please i am sorry my lovely tank u very much tsalle ya dinga yi yana adungure small ya rike baki anya ba allurar shahid bace ta motsa? small yace anya brother ko dai allurar ce ta motsa dariya kawai yayi,da rana bayan an gama girki ina kwance dakin da aka ware min ina wasa da waya wato game wayar tai kara hello sister ya kike? yadda kike mon,abba sahibina suna nan lafiya? nace baki tambaye naki shahibin bane? ai yanzu muka gama gaisawa sannunku uwayen soyayya,kefe ke ni soyayya bata gabana karatu nasa a gaba to anry wahida daga karatu sai me-ke ki daina ce min anty to me zan ce miki? usaina wayyo kin cuce ni ki ce min autar mom da abba da ya al'amin kin san ko yanxu mom ta haihu kin tashi daga auta? me zai sa mom ta haihu ai daga kaina aka rufe fayil din'


MUH'D-ABBA~GANA

Abba Gana hausa novels @ facebook

www.abbagana.pun.bz

Ku ajiye comment pls
Share:

Thursday 4 February 2016

BANA KAUNARKA!!! 16

bana-kaunarkajpg.jpg

BANA KAUNAR KA!!!

16



MUHD-ABBA~GANA

09039016969

gargadi:ban yarda wani ya cire koh ya kara wani abuba
--------------------------------------------
ina gyara dakin anti antin tai sallama nace sannu da zuwa anty yauwa wahida sannu da aiki small ya shigo anti tace lafiya na ganka kamar mara lafiya? ya shafa cikinsa yunwa muke ji tun daxun muke jiranki bafa abin da muka ci sai take away ao sorry my son bari inyi sallah in shiga kicin bayan kowa yayi sallah anty na zaune dukkanin su sun hallara a falo sai na shiga jera abinci kowa na kallona sai dana zauna anti na soma zubawa sannan mu kuma na shimfida dadduma domin nafi son cin abinci a kasa gaba dayanmu na hada mana bomboy yai tsuru domin yasan wahida ta san baya son tuwo shine kuma tai tuwo amma kuma zai bata mamaki,Allah sarki bai gama tunani ba yaga ta janyo kula da filet ta soma hada masa nasa na musamman tuni su al'amin suka ce ba,a isa ba sai dai suci tare kasancewar da yawa sai na hada yadda zai isa ai kuwa suna ci suna santi gaba daya sai da suka share abincin nan suka koma kan tuwo nan suka dinga santin tuwan bom boy na gefe small yace Allah bom boy cikaji tuwan yafi dadi loma daya yayi ya kada kunne gaskiya yai dadi amma na koshi sosai,bayan sun gama an sha lemu ba kwashe kayan sannan na gyara gurin,ya amin yace ki zo mu tafi dare nayi anty tace ka barta tai min kwana biyu yace shi kenan,har gun mota na kara shi ya kalle ni yace yanzu sister sai yaushe kenan? sai randa anti tace in dawo zan dawo to duk randa zaki dawo ki yo min waya,Allah wahida nafi sonki kusa dani sam bana son ki min nisa nai murmushi yayana kenan,ni kaina nafi son zama cikin yan uwana to amma yaya zan yi? ya tada motar na daga masa hannu har ya fice ina tsaye tabbas ina bana son rabuwa da yaya dan dai ba yadda zanyi ne.
Da safe da wuri na shiga kicin na hada breakfast anty ta shigo oh wahida break fast din ma bazaki kwanta ki huta ba anti ina kwana lafiya lau wahida ya gajiyar jiya ba gajiya , daki na koma nai wanka sannan na fito cikin doguwar riga gaba daya suna falo na tsunguna na gaida dad dinsu ya shafa kaina yace ina mahida nace tana gida dad dinsu bomboy yana da kirji ga wasa da dariya mutum ne mai kirki sam bashi da wulakanci.bom boy ne zaune yasa hoton wahida gaba yana ta faman sambatu yace wahida me nai miki me yasa ba kya sona? me nake dashi wanda ba kya so ko sana'a tace ba kya so? billahillazi in ba kya so na ni kuma zan iya bari,me yasa ba kya sona wahida me nai miki ki tuna fa ni dan uwanki ne ya kamata ki sassauta min ki tausaya min ya daga hoton wahida kin yadda kina sona? za ki kasance me farantamin? zaki zamo uwar yayana daure ki ban amsa haba yar uwata abar alfaharina haidar ganin dan uwansa na shirin zautuwa akan mace yace haba my big brother ne yasa kake wahalar da kanka akan mace? kai rufe min baki ko dan kaga ka samu taka shine kake min bakin ciki akan tawa? haba bom boy in ban da zarewa sai kasa hoto gaba kai ta sambatu ni wallahi dana dauka kai da wahidar ne sai dana shigo naga ashe hoto ne kai small tashi bani guri don na gane so kake ka raba mu to kayi kadan domin kaunarta nake small ya kwashe da dariya sannu mai sahiba,


MUH'D-ABBA~GANA
www.abbagana.pun.bz

Abba ganahausa novels
@ facebook


Ku ajiye novel pls
Share:

Wednesday 3 February 2016

BANA KAUNARKA!!! 15

bana-kaunarkajpg.jpg

BANA KAUNAR KA!!!







15







MUHD-ABBA~GANA



ya amin yace mom zamu gudan anti to amma kar ku dade kun san abbanku ya kusa dawowa nace anty mahida zo muje mana ta kara makalkale mom tace wallahu naji dadin kwanciyar bacci zanyi nace mom ki ture ta kar ta karasa ki min isa gidan bom boy a falo tare da small suna kallon kwallo mu kai sallama suka amsa na zauna kusa da ismail yaya amin yace ina anty? anty ta tafi katsina gaisuwa amma yau zata dawo inji bom boy, ya amin ya kale ni nina so na manufarsa amma sai na share,bom boy ya taso ya dawo kusa dani yace anti wahida ba gaisuwa? na kalle shi ya rame sosai yayi wani irin kyau yace me kike so in kawo miki ne nai masa banza haba my dear daure mana ki min magana caraf ya kamo hannna ya murza Allah ba dan na tuna maganar ya amin ba da tuni na tofa masa yau,cikin kasa da murya kamar yadda yake min magana kasa-kasa nima nace "bana so kana tabani,no ki barni in samu nutsuwa....... Allah sai dai kar ka samu muddin sai ka........shut up kina so tara min tawage ne kike daga murya,ai gani nai irinku sai da daga murya........me kike nufi wallahi wahida ki shiga taitayinki muddin kika shigo hannu sai kin.....Allah abbana ko ince Allah Al'amin kanina ne Allah ya kyauta kaine ka girmi ya Al"amin? to ki tambaye shi mana na mike domin ya ishe ni ni lambun gidan na wuce nai kwanciya iska na kada gashin kaina duk saiya lullub min fuska.
jin motsi kusa dani sai na tattare gashin tsugunne yake gabana ya zuba min mayatattun idanunsa na hararw shi yai murmushi yace sahiba tunanin me kike? wace sahibar kaje ka nemi sahibarka ba dai wahida ba wahida me yasa kike garani kike gasa min gyada a hannu? saboda BANA KAUNARKA! inda wanda nake so,ko ka gane? keh! wallahi na fara gajiya da wannan wulakancin na ki ko don kinga ina sonki? to kayi zuciya mana ka sake wata zan baki mamaki ba zan sake wata ba amma zaki gane kuranki,aikin banza ai na dauka zaka yi zuciya ashe ba a da ita,ya finciko ni cikin zafin nama sai gani wanwar a jikinsa sai kawai na saki kuka ya hankade ni ya barni gun a zuciyata na ce Allah ya isa mugu kawai na mike na goge fuskata.
kicin na shiga na dan yi wa anti girki kasancewar na san dadin su bomboy yafi son tuwo sai nai tuwan shinkafa nayi sa,a tuwan yayi kin yadda nake so na nannade shi a leda sannan na daura miyar agushi wadda ta amsa sunanta domin taji nama ina gamawa sai na daurawa shahid nasa domin sam baya cin tuwo miya ina soya sannan na dafa shinkafa na yanka salat na ajiye gefe sai dana kammala nasa sannan na hada lemuka kala uku nasa a firij kasancewar na san shahid na son gashasshen nama sai na gasa sannan na yanka kanana-kanana daidai yadda zai iya hada da abincin koma wa nai na gyara falon domin gaba dayansu suna dakin small na kunna turaran wuta.





MUHD-ABBA~GANA

www.abbagana.pun.bz


Abbagana hausa novels
@ facebook
Share:

BANA KAUNARKA!!! 14

bana-kaunarkajpg.jpg

BANA KAUNAR KA!!!







14







MUHD-ABBA~GANA



zagewa nai na wanke toilet din nasa turare sannan na hada kayan wanki na bayar na cire zanin gadon na sa wani na share na goggoge ko ina nasa wa dakin turaran wuta ina sallah haidar yai sallama ita kuma tana kwalliya bayan na idar na gaishe shi na fice a zuciyata nace da haka zai zo ya samu dakin kamar bola? ina kwance a falo bom boy ya fito daga dakin yaya al'amin ya karaso ya tsugunna gabana wani kallo nai masa tare da nace lafiya dai ko? yace lafiyar ce ta kawo haka please ki taimaka min in taimaka maka da me? so? ya furta nace so menene kuma so? kina son sanin menene so? look at me na mike domin na san ba zan iya abin daya sani ba caraf ya kamo hannuna a fusace na juyo tare da tofa masa yau ina daga idona muuka hada ido daya al,amin gabana yai wani mumunan faduwa shi kenan ta faru ta kare an yiwa me zani daya sata wata irin harara ya wullo min ai da gudu nai dakin mom na fada jikinta mom ki yiwa bom boy magana nace bana sonsa bana kaunarsa! meye zai dinga takura min?,yakike so in yi masa wahida? so kike in tare shi ince kar ya kara kula ki? in kin yi tunani koba komai shahid ai dan uwankine da mahaifiyarsa da ubanki cikin su daya haba auta kiyi hakuri ki sassauta wannan bawan Allah ni wallahi nafi miki sha'awar shahid ko kina da wanda ya fishi,gaskiya mom ku hana shi zuwa gidannan in ba haka ba sai in bar masa gidan in koma katsina mom inaji ana cewa soja akwai zuciya shi kuwa wannan ba shi da zuciya mom tace ai so daban zuciya daban kuma wallahi na amince da son da shahid ke miki na mike na fita don bana son zancan daki na koma dakin bbu kowa da alama sun tafi yi musu rakiya na kwanta sai ka na mike na shiga toilet nai wanka gidansu wata yar class dinmu tun muna primary ina kallo yaya alamin ya shigo fuskarsa bbu walwala yace wahida duk irin rashin kunya da cin mutuncin da ake cewa kina wa bom boy ban taba yadda zaki aikata ba sai yau ashe baki da kunya a gabana kika tofa shahid yau na zumburo baki nace to yaya ai shi ne bashi da gaskiya dan me zai dinga rike min hannu ni kuma na dau alwashin muddin zai taba ni sai na tofa masa yau amma komai ya mike keki kaja tunda kin san yana sonki wahida ya kamata ki sassauta wa shahid ki dinga fada masa kalamai masu kwantar da hankali ko ba kya sonsa bai kamata ki dinga yi masa abin da kike masa ba yaunzu ki taso muje ki bashi hakuri tabdijan gaskiya ba san iya ba ni dai na fada miki kai don Allah yaya kana gani na ci kwalliyata gidansu da yar ajinmu zani yai tsaki ni dai nace ki jira ni in shirya ya fice nai zaune ina mamakin yaya al'amin naga alama so yake inji kunya yanzu ba kunya sai inje in bawa ya shahid hakuri hum'um ai ba zata zabu ba ina nan zaune ya shigo yayi kyau sosai ya rankwafo ta mudubi na kalle shi yaya kana kama fa da bomboy ainun wahida bom boy bai fini kyau ba no haske kawai ya fika amma kamarku har ta baci na dauko hijabina muka shiga dakin mom,





MUHD-ABBA~GANA





www.abbaganw.pun.bz
Share:

BANA KAUNARKA!! 13

bana-kaunarkajpg.jpg

BANA KAUNAR KA!!!







13







MUHD-ABBA~GANA


muna zuwa gida da gudu na fada jikin mom ina murna mom ta ture ni ni daga ni kai mom baki gane ni ba autar ki ce fa wahida me nai miki mom? kin fi kowa sani to yi hakuri mom na daina mahida ta fito tana hararata kai anti mahida me nai miki ta dungure ni ni ce ai zan ce miki anty ta kamo hannuna taso muje dakinmu na bita gaba daya dakin ta zagaye shi da manyan hotunan haidar da bom boy wani muduka sai wanda tasa aka hada mu nida bomboy ina sanye da wani material me tsananin kyau domin hoton ya dauku domin nayi kyau ainun mun dauki hotanne lokacin da mukai partin candy dinmu shima yayi kyau dama tare muka dauka amma lokacin bai nuna manufarsa a kaima ba yadda mu kai hoton in kin gani sai ki rantse muna son juna don gannin yadda na shisshige masa munyi kyau sosai ni kaina ina son hoton na kalle ta sai naga tana faman dariya na karaso yana da manyan idanu masu tsananin kyau da idanunsa ban tsoro domin in ya zare min ido sai nayi fitsari amma a yanxu suna birge ni inason kalar idanunsa masu zubin ruwan gol sam bana iya hada ido dashi domin wani shokin yake sakar min idanunsana hargitsa min lissafi sannan suna tsuma min zuciya toko shine so? kai ni na so ba son sa nake yi ba kauna ce ta yan uwantaka sannan yadda wannan dogon sajan dake kara fito da samartaka dogo ne shi domin bashi da kiba sai dai yana da faffafan kirji sannan yana da kirar karfafa jaruman maza fuskar nan kulum dauke da annuri kamala,kwarjini duk fa yadda naso fasalta muku bom boy ya wuce haka sai dai ince duk inda namiji ya kai da kyau iya diresin bom boy ya kai har ya wuce.
mahida kin san abin da yake hada ni dake kuwa? a,a kin gan ki wallahi za,ayi muguwar kazama saboda me kika ce haka? a farko kin ga dakin nan ina tunanin tunda na bar gidannan baki taba daukar tsinstiya da sunan zaki share dakin nan ba ko kin share? to ai bai yi dauda ba da kyau kinga kan kayan kallonnan kalli yadda sukai mugun kura mahida kalli zanin gado kalli tunin kayan dauda ke dai sai dai ki fidda goma ki tsoma biyar Allah kar ki ce na rana ki kece me son auro muddin kika ce kazanta zakiyi wallahi kinyi asara soyayyar kanta bata yiwuwa sai da tsafta ko ba komai da tsafta tafi inganci tsafta cikon addini ke kenan daga kallo sai karatun soyayya Allah ya kyauta nai shigewata (toilet) ina shiga na fito saboda wani zarni (toilet) keyi nace mahida kin banu toilet din ma ba kya wanke wa??






MUHD-ABBA~GANA




www.abbagana.pun.bz
Share:

BANA KAUNARKA!! 12

bana-kaunarkajpg.jpg

BANA KAUNAR KA!!!







12







MUHD-ABBA~GANA



ya janyo ni ya rungume tsam yana fidda wani irin numfashi nace ka manta na hana ka taba ni? juyo dani yayi ya zubo min mayatattun idanunsa duk na dabarbace da kyar na ture shi nace ashe dama ba sona kake ba sha'awata kake yace what? na hankade shi da gudu yasha gabana wallahi sone ba sha'awa ba ce kauna ce na ce cikin tsawa kai dallacan rufe min baki ya finciko ni tare da doke min baki ya kara yi min wawuyar runguma anyi sha'awar taki ba a kaunarki za'ayi sha'awarki stupid kawai,nace ashe ai ban san kai dan iska bane.....yau ai kin sani nan gaba zaki karasa ni kin gane, yawu na tofa masa nace mara zuciya kawai kamar jira yake ya lashe yawun da sauri na fice.tana fita ya fadi a gurin yana numfashi sama sama me yasa wahida bata sona me nai mata ko dai hakura zan yi da ita kai ba zan iya hakura da ita ba ba zan iya ba ya fada cikin karaji da gudu haidar ya shigo ya rike shi kayi hakuri bom boy ya fincike haidar fada min me nake dashi wanda ban cancanci a soni ba? ka cancanci aso ka bom boy kana da kyau kana da aji kaine yammata ke rubibi a kanka ne zai hana ka hakura da wahidar nan ka nemi wata ba zan iya ba small ina so wahida so bana wasa ba.....tobya zaka yi tunda ita bata sonka kana ganin irin rashin kunyar da take maka kai dana sonka da zuciya kana gani fa har yawu take tofa maka kawai ka share ta no ba zan iya ba small ina sonta zan jure duk wani salon kiyayyar da wahida zata nuna min.
wannan shine takaitaccen labarina amma ku biyo ni don jin ci gaban labarin.mamy ce ta dawo dani daga duniyar tunanin da na shiga tace wahida mun shiga uku me kika yiwa bom boy na tashi zaune wani abu yace miki nai masa a,a yanzu naga dan uwansa ya kamo shi ya fita dashi hannunsa kan kirjinsa ko meke damunsa na tabe baki Allah ya kyauta atu tai sallama tace lafiya na ganki cirko cirko umh wai bom boy ne ba lafiya subahanallahi ba muga ta zana ba meke damunsa mamy ta nuna itace wallahi atu wahida yake so ita kuma take gara shi ta kalleni cikin fada tace kin san Allah muddin jikana ya mutu akan sonki wallahi mun kulla kun san duk cikin jikokina nafi son shahid nace ai sai ki aure shi tunda kin fi sonsa ni dai bana sonsa amma fa a zuciyata a fili kuma nace inma ya mutu shi sayo ni kan ko a kaina da gudu ta wawuro tsintsiya ta bini.



Ranar litinin al,amin ya dawo bayan ya huta sai kiran mahida yace mahida ina wahida? wallahi ai tun ran daka tafi ta bar gidan....saboda me? dan ya furuq yai mata duka shine ta tafi abba yace inje in taho da ita amma tace in munga ta dawo gidannan to dan uwanta ya dawo al,amin ya mike dakin faruq ya shiga ya finciko shi wai kai wanne irin mugune azzalumi me wahida taimaka faruq yaja shaka yace yi hakuri big brother ba zan kuma ba so nake ka fada min abin da tai maka da har ka raba tada gida faruq ya fada masa duk yadda akayi tsaki yayi ya juya ya fita bai zame ko ina ba sai gidan atu ina sharar tsakar gida yai sallama nai ciki datsin tsiyar na rungume shi ya dago ni ya dunguran goshi me ya rabo ki da gida nai raurau yaya in baka nan ab tsaneni kullum cikin duk ni kuma na baro musu gidan yace min fa rashin kunya kike masa ni ba rashin kunya nai masa ba wai dan nace ba zan cewa mahida anti ba to shikenan ki shirya mu tafi ya wuce dakin atu.





MUHD-ABBA~GANA





www.abbagana.pun.bz
Share:

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).