shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Thursday, 4 February 2016

BANA KAUNARKA!!! 16

bana-kaunarkajpg.jpg

BANA KAUNAR KA!!!

16MUHD-ABBA~GANA

09039016969

gargadi:ban yarda wani ya cire koh ya kara wani abuba
--------------------------------------------
ina gyara dakin anti antin tai sallama nace sannu da zuwa anty yauwa wahida sannu da aiki small ya shigo anti tace lafiya na ganka kamar mara lafiya? ya shafa cikinsa yunwa muke ji tun daxun muke jiranki bafa abin da muka ci sai take away ao sorry my son bari inyi sallah in shiga kicin bayan kowa yayi sallah anty na zaune dukkanin su sun hallara a falo sai na shiga jera abinci kowa na kallona sai dana zauna anti na soma zubawa sannan mu kuma na shimfida dadduma domin nafi son cin abinci a kasa gaba dayanmu na hada mana bomboy yai tsuru domin yasan wahida ta san baya son tuwo shine kuma tai tuwo amma kuma zai bata mamaki,Allah sarki bai gama tunani ba yaga ta janyo kula da filet ta soma hada masa nasa na musamman tuni su al'amin suka ce ba,a isa ba sai dai suci tare kasancewar da yawa sai na hada yadda zai isa ai kuwa suna ci suna santi gaba daya sai da suka share abincin nan suka koma kan tuwo nan suka dinga santin tuwan bom boy na gefe small yace Allah bom boy cikaji tuwan yafi dadi loma daya yayi ya kada kunne gaskiya yai dadi amma na koshi sosai,bayan sun gama an sha lemu ba kwashe kayan sannan na gyara gurin,ya amin yace ki zo mu tafi dare nayi anty tace ka barta tai min kwana biyu yace shi kenan,har gun mota na kara shi ya kalle ni yace yanzu sister sai yaushe kenan? sai randa anti tace in dawo zan dawo to duk randa zaki dawo ki yo min waya,Allah wahida nafi sonki kusa dani sam bana son ki min nisa nai murmushi yayana kenan,ni kaina nafi son zama cikin yan uwana to amma yaya zan yi? ya tada motar na daga masa hannu har ya fice ina tsaye tabbas ina bana son rabuwa da yaya dan dai ba yadda zanyi ne.
Da safe da wuri na shiga kicin na hada breakfast anty ta shigo oh wahida break fast din ma bazaki kwanta ki huta ba anti ina kwana lafiya lau wahida ya gajiyar jiya ba gajiya , daki na koma nai wanka sannan na fito cikin doguwar riga gaba daya suna falo na tsunguna na gaida dad dinsu ya shafa kaina yace ina mahida nace tana gida dad dinsu bomboy yana da kirji ga wasa da dariya mutum ne mai kirki sam bashi da wulakanci.bom boy ne zaune yasa hoton wahida gaba yana ta faman sambatu yace wahida me nai miki me yasa ba kya sona? me nake dashi wanda ba kya so ko sana'a tace ba kya so? billahillazi in ba kya so na ni kuma zan iya bari,me yasa ba kya sona wahida me nai miki ki tuna fa ni dan uwanki ne ya kamata ki sassauta min ki tausaya min ya daga hoton wahida kin yadda kina sona? za ki kasance me farantamin? zaki zamo uwar yayana daure ki ban amsa haba yar uwata abar alfaharina haidar ganin dan uwansa na shirin zautuwa akan mace yace haba my big brother ne yasa kake wahalar da kanka akan mace? kai rufe min baki ko dan kaga ka samu taka shine kake min bakin ciki akan tawa? haba bom boy in ban da zarewa sai kasa hoto gaba kai ta sambatu ni wallahi dana dauka kai da wahidar ne sai dana shigo naga ashe hoto ne kai small tashi bani guri don na gane so kake ka raba mu to kayi kadan domin kaunarta nake small ya kwashe da dariya sannu mai sahiba,


MUH'D-ABBA~GANA
www.abbagana.pun.bz

Abba ganahausa novels
@ facebook


Ku ajiye novel pls
Share:

1 comment:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).